Showing 6001 words to 9000 words out of 49670 words

Chapter 3 - HAMDAH Book 2 Complete Free By Rasheedat Director .pdf

min wani irin murÉ—a yayin da kai na yake
mugun sara min.
Na yi tafiya mai É—an nisa sai na zauna kan dakalin kofar wani gida,tare da tafe kai na dake
matsa nancin tsaramin, da hannuna É—aya É—aya hannun kuma na dafe cikina, tausayin kai na ya
kamani sai kawai na fashe da kuka mara sauti.
cikin muryar kuka nake faÉ—in
"Wayyo Allah cikina kai na wayyo Allah na, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un²".
wani sabon kuka ne yakuma zuwa min Allah sarki Inna banki a yanzu Allah ya É—auki raina
kamar yan da yaÉ—auki nata ba yafiye min wan nan rayuwar.


nayima ina kuka mai matukar kona zuciya kukun da naÉ—au lokaci mai tsawo batare da nasan
lokacin yakure har haka ba,guri yayi shiru bakajin motsin komai sai haushin karnuka da kukan
wasu tsuntsaye, na rakuɓe jikin garo na cusa fuskata sakankanin cinyoyi na,an ce bacci
ɓarawo ne to ni dai na tabbata duk iya satan sa bazai iya sace ni a wannan irin lokacin ba,ta ya
zai sami narasar saceni bayan ina tangare a dandamalin guri wan da a iya Æ´an shekaru na ban
taɓa mafarkin kasan tuwa a irin hakaba,ban taɓa rayuwa cikin bakin duhu irin haka ba,ina
zaune a haka gari yawaye..
nayi al'wala a panpon da ke jikin gidan da nakwana a kofar gidan nayi sallah.
Koda gari yayi haske jama'a suka fara zirga-zirga a kan hanyar duk wan da yazo wucewa sai ya
kalleni ganin na zame wa mutane abun kallo dai na mike naja akwati na,
a sannu narika kusawa cikin unguwar haka na rika zaga cikin unguwar idan na gaji sai na sami
guri na zauna in na huta sai na mike nacigaba da tafiyar da ban san in da zani ba.
ranar wuni zubur nayi ina haka yunwa kishin ruwa zafin rana sune abokan rayuwata...

Yau kwana na uku a kan layi nake kwana idan nayi ta yawo har dare ya riskeni sai na sami
kofar wani gida na rakuɓe gefe a haka zan kwana a zaune,batun yunwa kuwa tarigada ta shiga
jikina har ya zamana bana jinta sai dai cikina sai yayi ta murÉ—eni abun cikina yayi ta
motsawa,idan naji kishin kuwa sai na bazama yawon niman kofar gida mai panpo na tara da
hannuna nashi,
ina sha kuwa sai nayi hawaye sabo da murÉ—an da cikina zai yi ta min...
Zaune nake akofar wani gidan da nake tunanin a nan yau zan kwana dan yamma tayi sosai ana
daf da kiran magriba,
kishin ruwa ne ya dameni tun É—azu sai dai nayi yawo a layin da nashigo yau ban sami wani gida

mai panpo a kofar gidan ba,sai dai na fuskanci wannan unguwar na marasa karfi ne dan
gine-ginen su ma kaÉ—ai kagani zakasan unguwar talakawa ne.
a hankali na mike na janyo akwakina nacigaba da tafiya ko zan sami ruwa dan ina jin kishin
sosai,
ina sharar wata kwana can na hango rijiya mutane na tsaye a kansa anata jan ruwa a cikin sa,
da sauri na nufi gurin dan ruwan da nafi muradi kenan,ina isa gurin na tsaya gefe da wata Æ´ar
dattijuwar mata nace
"Dan Allah a sammin ruwa".
matar ta juyo kana tace
"Sha zakiyi ne?".
kai na gyaÉ—a mata tace "Ai ho". wani É—an kara min roba ta janyo ruwan ta zuba ciki tace
"ÆŠauka kisha".
To nace da sauri na É—auka nasoma sha nasha sosai sai da naji cikina ya cika sannan na aje
robar tare da yi mata godiya,ta É—au ruwan ta tatafi a hankali naji cikina na É—an murÉ—a min sai dai
ba kamar na duk lokacin da na sha ruwan panpo ba,a hankali nasoma tafiya naÉ—an yi nisa da
rijiyar kaÉ—an sai na zauna kan wani bulo dake gefen ciyawa jin cikin bai dai na yimin murÉ—a ba. kai na na cusa sakankanin cinyoyi na inajin yan da cikin ke ci gaba da murÉ—a ni,
da sauri na É—ago kai na jin abu na tafi a kafata,wani irin waro ido nayi cikin firgici da razana
ganin maciji a saman kafata,cikin zafin nama na mike tsaye tare da kwalla kara na yarfe kafar
da karfi macijin ya faÉ—i can gefe yashige cikin ciyayin dake gurin,
da iya karfina nake ihun ina yarfe kafar....


"Wane ne waye a nan?".
naji murya daga can ana tan baya,cigaba da tan bayar a kayi ana motsawa in da nake,niko sai
ihun nake ina tsalle da yarfe ƙafan,
jin an dafa kafaÉ—a na ana faÉ—in
"Subhanallahi Æ´ar nan menene?".
da sauri narike hannun matar da naji tana tan baya na da karfi cikin sananin tsoro nace
"Maciji maciji maciji".
nafaÉ—a da karfi ina cigaba da yarfe kafar,
a kiÉ—ime matar tace
"Ya cije ki ko au da ma kece? me yazaunar dake a nan tun da kinsha ruwan basai kiyi azamar
tafiya gida ba, kyazo gidan macizai kizau na ba'azo in da suke Bama ana tare-tare dasu acikin
gida bare kinzo nan cikin su,maza zo muje a samiki magani tun kan dafin ya haura miki,wani irin
zuwa unguwa ne har guri ya rufa baza'a koma gida ba". tafaÉ—a tana janyo hannuna,sai lokacin na gane matar itace wacce na roketa ruwa ta bani nasha
É—azun nan.
ta janyo hannuna ina É—angala kafar, tana cigaba da faÉ—in
"Dage kiyi sauri muje tun kafin dafin ya haura miki,waÉ—an nan abu ai sai a hankali har gida suke
shiga mana dan ma yanzu da sauki muna saka musu magani shine suke É—an yin nesa da
gidajen mu".
dai-dai lokacin muka isa kofar wani gida muka shige ciki, murya ta buÉ—e tashiga kwaÉ—a sallama

tare da faÉ—in
"Zainabu zainabu matar gidan nan tana nan kuwa".
wata mata tafito daga cikin É—aki tana amsa sallamar tace
"Ina nan, a'a Mama mai awara kece tafe".
Matar da muke tare da ita tace
"Eh,malam Musa na nan kuwa ko har yatafi masallaci?".
Zainabu tace
"Yana nan yanzu yake shirin fita yazaga ne, yauwa gashi ma yafito".
tafaÉ—a tana kallon hanyar bayi,
mutumin da a ka kira da malam Musa ya dube mu yana faÉ—in
"Sannu Mama mai awara ku ne da yammacin nan".
tace
"Eh wlh malam Musa maciji ne ya cije ta dan Allah a sa mata magani kafin ya haura mata".
ya dube ni da har lokacin ina masar kwalla
yace
"To subhanallah garin yaya?".
Mama mai awara tace "Can gefen fadama tabi kasan kuwa kamar gidan su ne".
"Kwarai kuwa Allah yasa ba mugayen bane".
yafaÉ—a yana shige wa cikin É—aki mama mai awara tace
"Amin dai". ni dai ina nan itana masar kwalla ban iya cewa komai ba, matar malam Musa wato
Zainabu tashiga tafito da taburma ta shin fiÉ—a tace muzauna,ba jimawa kuwa malam Musa yafi
É—auke da wata Æ´ar karamar jaka ya zauna gefen taburman kana yadube Ni yace na miko kafar
da yaga ina ta girgiza shi,na mika masa yazuge zip É—in jakar yaciro kayakin magungunar sa ya
zaro wani farin gyale ya gyara zaman sa da kyau ya ɗaura ƙyallen saman kafata kana yaɗauko
wani magani acikin kwalba yaɗan ɗiga kan ƙyallen dake kan kafar tawa.
yazubawa ƙyallen ido
sai kuma ya É—ago ya dube ni yace
"An ya nan ne kuwa".
kai na gyaÉ—a da sauri cikin matsar kwalla nace
"Allah nan É—in yahau".
nafaÉ—a ina daÉ—a girgiza kafar dan ji nake kamar har lokacin yana kan kafata,
Maganin yadaÉ—a É—igawa kan gyallen kana ya dubi mama mai awara
yace
"Babu wani alamun dafin maciji a tare da ita gashi nan dai kina gani".
sai ya mai da dubansa gare ni yace
"Amma yaya kikaji da ya sare kin?".
nace "Ganin sa nayi a kan kafata kawai ban san yan da akayi yahau ba".
kai malam Musa ya jinjina kana yayi murmushi da faÉ—in
"Allah ya tai make ki wata kila wucewa zaiyi ke kuma kika tsaya masa takan hanya yabi takafar
ki yawuce batare da yasan kina ma gurin ba da taimakon Allah".
mama mai awara ta sauke numfashi da karfi tace
"To Allah ya taimaka ina gama macijiya ce dan su matan basu fiye yin saraba sai sunji matsi".
Zainabu dake gefe tace "Haka ne kam Allah dai ya daÉ—a karewa".

suka amsa da amin nidai ido naketa cirewa cike da tsoro.
mama mai awara ta mike tana yiwa malam Musa godiya tayi wa zainabu sallama tayi waje nabi
bayan ta.


Muna fita ta dube ni tace
"Allah ya kare mugayen basu cije kiba,ai wannan mai maganin har wasu garuruwa suna kawo
masa jin yan sarar maciji dan shi gada yayi tun iyaye da kakani,idan maciji ya cije ka to da
wannan kyallen yake gane kalar macijin da ya sare ka,sai ya baka magani,idan yasaka kyallen
dai-dai in da maciji yazuba dafin sa to kyallen zai canza kala yakoma kalar jikin macijin,kinga ai
yan da yaÉ—au ra kyallen a fari a farin sa ya É—aga,babu rabon wahala Allah ya kare,
Maza kiyi gida yanzun nan muje na nuna miki hanya mai sauki da zaki fita bakin hanya,jirani a
nan na É—auko miki jakar ki".
kai kawai na gyaÉ—a mata yayin da naji wasu zafafan hawaye sun zubo min,yanayin yan da
matar take magana yasa ni tuno da Inna ta,
"Allah sarki Inna na tabbata in da kina numfashi bazan taɓa hofanta ba".
Kwalla na kuma share wa lokacin da matar tadawo gaba na tana mika min a kwatina,
tace
"Maza ki tafi gida dare yayi ke bakya tsoron kije gida iyayen ki su miki faÉ—a, Allah ma ya takai ta
ai da sai dai a kai ki gida da raunin maciji,
yi sauri muje na nuna miki kinga har na makara markaÉ—en awara nafito É—auka wa shine na jiyo
kururuwar ki da yanzu na dafashi har na tsane".

Duk abun da take faÉ—a sama-sama nake jinta wani irin kuna da raÉ—aÉ—i zuciya ta ke min sai
sharar kwalla nake.
muna fita gaban rijiyar nan da hannu ta nuna min hanya tace
"Ki mike nan hanyar ta ɓulle har titi Allah bamu alheri".
kai na gyaÉ—a kana a hankali nasoma tafiya,ita kuma tabi ta wani hanyar.
A hankali nake tafiyar idanuna a kasa sai gani nake kamar zan É—aura kafar kan wani
macijin,duk da kuwa guri yafara yin duhu lokacin........!★





Mommyn twins ce




*Masha Allah yau Allah yayi ikon sa na dawo Nagode da addu'o'in ku sosai*🥰

Ina ganin shige war matar cikin wani gida sai na rakuɓe kofar gidan da na iso yanzu,
hawayen tsoro ne suka shiga zuba min a ido shike nan Ni nasan rayuwa ta ta kare yau maciji
shi zai yi saniyyar barina duni,tun da kuwa garin su nazo,
wani sassanyar kuka na sake mara sauti nasadakar ma kawai macijin yacije ni na mutu ko zan
huta da wannan rayuwar kunci da bakin cikin.
Ji nayi an gasko min toci da sauri na É—ago kai na tare da kare fuskata da hannuna sabo da
hasken tocin dake haska min ido.
da sauri takaraso in da nake rike da roba mai É—auke da kullun waken awara a ciki,salati ta doka
tana faÉ—in
"Yau naga ikon Allah Æ´ar nan ashe baki tafi gida ba,kuma zama anan kikayi,hanyar koma wa
gida ne ta ɓace miki kokuwa wani laifin kikayi kike tsoron komawa,in ba haka ba mai zaisa kiki
komawa gida,ki zauna kina ta rabuɓe-rakuɓe a nan,
yaran zamani ga iya laifi ga tsoron hukunci,tun da kana tsoron hukunci ai sai ka riƙa gujewa ai
kata lai fi,to baki tsoron ki karawa kanki wani laifin ni sam banason yaro irin haka to menene am
fanin fitowa a gidan da har zaki ki koma wa gidan ki rakuɓe a nan kinata koke-koke, to in bugun
naki za ayi bagara ki koma a bige ki ya wuce miki ba, ka zauna ka karawa kanka laifi,É—auki jakar
maza kizo nan".
tafaÉ—a tana dubana.


Tana gaba ina biye da ita muka shige cikin wani É—an ma dai-dai cin gida mai É—auke da É—aki ciki
biyu sai kitchen da Kuma banÉ—aki a gefe,
da kaga kidan kasan na talakawa ne sosai sai dai a tsaftace yake babu kazanta ko datti a cikin
É—an ma dai-dai cin tsakar gidan.
tanuna min É—aya daga cikin É—akunan tace nashiga,
a kasa kan taburman dake malale cikin É—akin na zauna,
babu jimawa tashigo É—auke da kwano ta direshi gaba na tana faÉ—in
"Ci yanzu muje na rakaki bakin titi kihau abun hawa ki koma gida,
in ban da rashin hankali niyyar guduwa kikayi gaba É—aya a gidan da kika É—au jaka?,
Akul karki kuma wan nan ba ta'adar É—an kirki bane ci maza muje".
wasu zafafan hawaye na share kana da sauri har hannuna na rawa na buÉ—e kwanon,
tuwon jan dawa ne miyar bushashiyar kuɓaiwa,sai tashi da kamshin daddawa yake,
da sauri na sa hannu na soma ci.
ta fita ta kuma dawowa da kofin ruwa ta aje min,kana ta fita taje tasoma tatar kullun da ta É—auko
markaÉ—en sa.
cin tuwan nake tamkar na sami nama,yau kwana uku da wuni É—aya kenan rabun da nasa wani
abu mai gishiri a bakina.
naci tuwon sosai dan har nakusa cinye wa kana na kara da ruwa,
bayana na jingina da jikin garu tare da yiwa Ubangiji godiya,
a hankali narka jin murÉ—ar da cikina keyi min yana É—an raguwa, yayin da abun cikina da tun jiya

da cikin ya murÉ—a ni sai shima naji ya motsa sai ya sauka kasan marana ya dunkule guri guda
bai kuma motsawa ba sai yanzu naji yana É—an motsawa da harbawa a hankali...
can an jima matar taÉ—a go labule tace
"Zo kiyi sallah kafin awara ta ta dafu sai muje na rakaki".
"Tom". nace na mike nafito rike da lanta da ke cikin É—akin kasan cewar guri yayi duhu sosai,cikin
É—ar-É—ar nashiga bayin nayi sarki nafito kana nayi al'wala na koma É—akin na gabatar da sallar
isha,
bayan na idar ina zaune kan sallaya tashigo,ganin da al'wala tare da ita sai na mike nabata
sallayar na koma gefe.

Bayan ta idar ta mike ta dube Ni tana faÉ—in
"Taso muje ga dare nata yi ki tabbatar kin koma gida kuma kada kisa ke yin haka
kinaso kishiga fushin iyaye ne fushin su musufa ce yana jefa mutum cikin halaka".
wasu hawaye ne naji sun kuma zubomin
"innalillahi wa'inna'ilaihirra'un".
nashiga nanatawa a raina,shin nima haka zan tabbata da fushin iyaye,shin meyasa iyaye na
zasuyi fushi da ni kan abun da ban ai kata ba,me yasa zasu yanke min hukunci kan abun da
bana da masaniya a kansa??.
maganar ta naji a sama
"Yau kitashi muje kin tsaya kuka ne,ai har gida zansa mai abun hawan yakai ki, tukunna ma
inane gidan ku a wani unguwa kike? dan gobe zanje na tabbatar da kin koma ko baki koma
ba,kada ki sake ki kuma laifi kice zaki gudu ni bani son yaro irin haka a ina iyayen ki suke?".
kuka na fashe dashi cikin muryar shashsheka nace
"Ni bani da iyaye bani da komai haka zanyi tabin layi har rayuwa ta ta kare na mutu."
"Zancen banza kai, to tashi ki fita min a gida kije kikare rayuwar naki acan,an ya ma ba yawon
duniya kika fito ba?to ita duniya ta ishi kowa riga da wando tun da shi kika zaɓa je kibishi,tashi
maza ki fita min a gida ban mayi tunanin ko wacece keba na É—auko ki na kawo ki har cikin
makwanci na,tashi-tashi maza tashi nace". tafaÉ—a tana nuna min kofa da babbuga hannun ta,
da kyar na mike tsaye ina cigaba da kuka zuciyata nayi min wani irin mugun zafi,
Na rayawa rai na
tabbas idan nafi bakin titi kan kwalbatin da na zauna ranar da nashigo garin nan zan koma, har
idan wani yazo yace na bishi zai bani makwanci da abin ci zan bishi,
to menene am fanin rayuwa ta yanzu ratuwa ta bata da wani am fani yanzu.
idanuna na rumtse da karfi jin bugun zuciya ta ya tsanan ta,a duk san da zuciya ta tafara bijiro
min da irin waÉ—an nan tunanin sai magana ta da Inna na karshe yashiga yimin yawo cikin
ƙwaƙwalwa,
"kada rayuwa tajuya miki baya ki mance da uban gijin ki".
ƙwaƙwalwa ta tarika amsa kuwwa da wannan kalmar, sai nashiga nanata kalmar innalillahi
wa'inna'ilaihirraji'un.


a hankali na kai hannu zan buÉ—e labulen É—akin na fita tace

"da kata,baki da iyaye ajikin bishiya kika fito?".
juyowa nayi ido taf da kwalla nace
"A da ina dasu ayanzu kuma sun yanke alakar da kansu,yanzu ni bani da kowa na karɓi hakan
ne abisa umurnin su".
ina kaiwa nan najuya ina kokarin fita tace
"Zo nan kin taɓa jin yan da iyaye sukace sun yanke alakar su da ɗan da suka haifa?,
in ba wani shirin kike son kullawa ba Æ´ar kankanuwa da ke kin iya tsara zance".
wani murmushi nayi wan da yafi kukan da nake ciwo kana na dawo na zauna in da na
tashi,dubana tayi da kyau kana tace
"Wacece ke kuma suwaye iyayen naki? da kike shirya musu karyar sun yanke alakar É—a da
mahaifa a sakanin ku,sabo da kin kullawa ranki zaki shiga bariki, Allah shi kyau ta wannan
rayuwar ba mai É—aure wa bane zai fi miki kyau ki koma gare su ki nimi gafarar su, kirufawa
kanki asiri suyi miki aure kije É—akin auren ki asirin ki a rufe, in ban da zamani ma ai mu a da kamar ki ta isa aure, yanzu ne kawai wai sai yarin ya tagama
rika a gida kafin ayi mata aure,
da É—a da dukiya ba'a yi musu mugun ta idan na barki kika fita nasan bagidan zaki koma ba dan
haka bazan barki ki fita a gidan nan ba, ni da kai na zan dam kaki hannun iyayen ki,
yanzu dai dare yayi ki kwana gobe idan Allah yakai mu da safe zan kai ki gida da kaina"...

ni dai ban iya cewa komai ba sai sharar kwalla nake,har ta fita a É—akin can takuma dawowa tace
nataso na zo,na mike da akwatina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login