Showing 1 words to 3000 words out of 29993 words

Chapter 1 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf

12 Jul 2025

1234


KUDI DA MACIJI (((1)))
Na :::::Nazir Adam Salihi:::::
A bakin wata katuwar fadama, da misalin karfe
hudu da rabin wata ranar juma'a ta karshen karni
na goma sha
takwas, wasu jinsin tsuntsaye suka yi sahu-sahu
a bakin fadamar suna ta shakatawa abinsu domin
kuwa
babu abin da ya dame su dan ba sa fargabar a
fada musu da yaki, ko kuma a kawo musu hari
kamar yadda
sauran jama'ar gari ke ta kwanan zulumin
kasancewar wadannan abubuwa guda biyu a
kansu.
Da yawa daga cikin tsuntsayen dake bakin
fadamar neman abincinsu suke yi, yayin da
wasunsu kuma ke ta
wanka abinsu, wasu ko sai shawagi suke yi a
gefen fadamar suna kaiwa yan kananan kifaye
hari ko Allah zai
sa su dace su sami abinci.
A can gefen fadamar daga yamma, wani manomi
ya jefar da fartanyarsa gefe guda ya mike tsaye
ya share
gumi, kana ya juya ya dubi matarsa wacce ke ta
famar aiki babu ko sassautawa kai ka ce ita ce
mijin.
"Ta Gogari." Mutumin ya kira sunanta cikin
damuwa. Matar ta dago kai ta dubeshi a yatsine
ta ce.
"To uban malalata yanzu fa sai ka ce har ka gaji
ko? Na dauka tun da duku-dukun na zo gonar
nan ban ce na
gaji ba sai kai da ka zo tsakar rana." Manomin ya
dubi matar cikin murmushi.
"Haba ta Gogari, ke kin san ai na yi kokari ma da
na kawo har ya yanzu ina noma, ni fa na rigaya
na fada
miki ba zan iya noma ba, gara ki kyaleni akan
sana'ata."
Ta Gogari ta dubi mijinta a fusace domin ta san
abin da yake nufi.

"Oh! Amma dai Zangeru wallahi ka ji kunya yanzu
ace mutum ya fifita sata akan sana'armu ta gado
noma?"
Zangeru ya dubi ta gogari ya fashe da dariya.
Sautin dariyarsa ya watsu a duk fadin fadamar
harda dama
daga cikin tsuntsayen dake gurin suka tashi
sama a tsorace.
"Haba ta gogari, kin manta da cewa abin da na
gada kenan tun kaka da kakanni?" Ta gogari ta
jefar da
fartaryar dake hannunta ta mike tsaye sosai ta
dubeshi.
"Kai kasan da tunfarko na san kai barawo ne na
rantse da Allah ba zan fara ma aurenka ba."
Zangeru ya sakato datti daga kogon kunnensa
cikin murmushi ya ce.
"Kin ga kuwa ni a ganina wallahi duk cikin
sa'anninki babu wacce ta yi dace da miji kamar
ke domin ke kadai
ce kika yi dacen auren jarumi." Ta gogari ta turo
baki gaba kamar suda.
"Wanene jarumin?" Zangeru ya bugi kirjinsa da
karfi ya bada wani sauti fus! Tsuntsaye suka
sake watsewa a
firgice ya dubi matarsa ta gogari ya ce.
"Ni ne jarumi, domin sana'ata bata rago ba ce."
"Ni kuwa a ganina babu rago kamar malalacin da
ya zabi sata fiye da noma, dubi fa ciki ne da ni
wata biyu
amma tun hudowar rana nake aiki har yanzu ban
gajiya ba."
Zangeru ya kurawa matarsa ta gogari idanu na
tsawon lokaci, sannan sai ya danki fartanyarsa ya
rataya a
kafada ya ce.
"Shi yasa nake son ki rabu da wahala amma har
kullum ina ta kokarin nuna miki Annabi kina
runtse idanu.
Dubi cikinki ya fara girma, amma kullum kina kara
cusa kanki cikin wahala." Ya dan yi shiru yana
kallonta.
Ganin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai ya ci

gaba.
"To ni yanzu ta gogari in banda abinki ma, dan
abin nan da zamu samu a wannan yar gonar
nawa yake? Shi
nan kanki ne a cikin dare guda ina iya tara miki
abin da za mu yi shekara guda muna ci amma
duk kin bi kin
dami kanki."
Ta gogari ta sunkuyar da kai tana murmushe
kasar dake mammane a jikin busassun yan
yatsunta wadanda
tsabar wahala da noma duk ya busar dasu kamar
itace. Akwai alamun gajiyawa a fuskarta, kuma
da yake
Zangeru ya kura mata idanu ya fahimci hakan.
Wannan shi ya kara masa kwarin gwiwar cewa.
"Dauki fartanyarki mu tafi gida, kin ga rana ta
tasamma faduwa." Ta gogari ta dago kai ta
dubeshi ranta a
bace, ta bude baki kamar zata yi magana sai dai
ta fasa ta dauki fartanyarta ta saba a kafada.
Zangeru ya
dubeta da murmushi ya ce.
"Kwantar da hankalinki ta gogari nan da badi zan
zama babban attajirin da ba a taba yin kamarsa
ba duk
garinmu." Ta gogari bata ce dashi kala ba sai
kawai ta bishi a baya suka nufi bakin fadamar
nan wadda ga
al'ada a duk lokacin da suka zo noma anan suke
dauraye jikinsu su sha ruwa kafin su koma gida.
Sa'ar da suka kai bakin koramar sai suka
tsuguna suka fara dauraye jikinsu. Sassanyar
iskar yammacin da ke
hurowa daga cikin fadamar ba karamin jefa
Zangeru cikin nisnadi ta ke yi ba. Sau da yawa ya
gwammace ya
wuni ya kwana gindin fadamar yana shan iska da
lofe a hannunsa fiye da ace noma daidai da
kunya biyu. A
daidai lokacin ne to ta gogari ta dubeshi ta ce.
"Na ji dazu kana yin wani mafalki wai kwanan
nan zaka zama babban attajiri ko? Ta yaya to za

ka zama
attajirin? Da lalaci to ko da me?" Ta yi shiru tana
kallon mijinta Zangeru wanda ke zaune ya tura
kafafunsa
biyu cikin fadamar idanunsa lumshe yana
sauraren kukan tsuntsaye. Zangeru ya bude
idanunsa ya dubeta.
"Kina shakkar zamana attajirin ne?" ta gogari ta
yi dariya a karo na farko.
"Attajiri fa ka ce, ni ko na ga mutumin da bashi
son ko kankani ba shi son ya sha wahala a
rayuwarsa ta yaya
zai zama attajiri" Zangeru ya girgiza kai ya ce.
"Ta gogari kenan. Wato wani lokaci ki kan bani
mamaki da kike daukata a malalaci, kada fa ki
manta cewa
sana'ata ta fi karfin rago."
Kudi da Maciji... (2)
Ya dan yi shiru yana girgiza kafafunsa
akan ruwa akwai alamar murmushi a
bakinsa, duk kuwa da cewa bai fito fili ba
to amma Ta gogari ta lura da hakan. Sau
da yawa idan taga Zangeru yana irin
wannan boyayyen murmushi bata
magana domin duk sa'ar da zai fita wata
gawurtacciyar sata irin murmushin ya ke
yi.
"Sannu a hankali zan tabbatar miki da
zamana attajiri." Ta gogari ta sunkuyar da
kai ta ce "To Allah sawwaka."
Daga nan basu sake cewa da juna komai
ba sai ma'auratan biyu suka ci gaba da
wanke jikinsu. Tsahon lokaci suna cikin
wannan hali. Zangeru na cikin tsananin
nishadi, domin wani sa'ilin shi kadai sai ya
daki tsakiyar ruwa da kafarsa ya fashe da
dariya. Ta gogari bata tanka masa ba.
Daga inda Zangeru yake zaune yana iya
hango jerin sahu-sahun jinsin tsuntsayen
dake ta kai kawo suna shawagi a saman
fadamar kamar jirage. A cikinsu ne to
Zangeru ya lira da cewa akwai wata
balbela ita kadai tana tsaye a bakin

fadamar. Abin ya bashi mamaki domin
duk cikin jinsin tsuntsayen ita kadaice
bata da yar uwa. Balbelar ta taso a hankali
cikin lalaci ta sauka a daf da inda su
Zangeru suke zaune. Zangeru ya dubi
balbelar cikin murmushi sannan ya dubi
matarsa ya ce.
"Ta gogari dubi wata balbela mai kyau ta
ziyarce mu." Ta gogari ta dubi balbelar
shekeke, ta ce.
"Na ganta." Ta dauke kai gefe guda.
"Ya ya naga kin bata rai?" Ta gogari ta
hade fuska ta ce.
"Haka dai ka iya, gashi nan yanzu ka
rabomu da aikinmu ka kawo mu bakin
fadama muna zaman banza, ka ga ni in ba
yanzu za ka tafi ba ni ka barni in tafi gida
ko kuma na koma gona na karasa sauran
aikin dake gabana."
Zangeru ya dubi Ta gogari cikin murmushi
kana ya dubi balbelar ya ce.
"Baki san irin yadda nake kaunar
tsuntsaye bane musamman ma balbela
shi yasa kike fadar haka. Dubi fa balbelar
nan fara mai dogon wuya da jan baki
kyakkyawa, kai ina ma ace, ina iya zama
tsuntsu da na zama balbela." Ta gogari ta
fashe da dariya ta ce.
"Oh! Zangeru al'amarinka sai kai." Zangeru
ya dubi matarsa cikin nishadi ya ce.
"Allah kuwa Ta gogari da gaske na ke yi,
domin ba ki ji yadda nake kaunar balbelar
nan ba. Bari mu gani." yana fadin haka sai
ya mika hannunsa zai kama balbelar. Ga
mamakinsa sai kawai ya ga balbelar ta
taso da kanta a hankali ya sauko akan
cinyarsa. Nan da nan ya dubi Ta gogari
cikin farin ciki.
"Kin ga abin da nake fada miki ko, ita ma
balbelar ashe tana kaunata?" Ya dauki
balbelar a hannunsa cikin tarairaya ya
dubi Ta gogari.
"Ungo rike min da ita zan tafi gida." Ta

gogari ta mike tsaye ta dubeshi ta ce.
"Ka ga idan ba ka da aikin yi ni ina da shi a
gida." Sai kawai ta juya zata fara tafiya. A
daidai lokacin ne to suka ji kamar daga
sama ance.
"Haba baiwar Allah, tunda ya ce dake ki
rike masa ni yana kaunata ba sai ki
daukeni din ba." Ta gogari ta tsaya cak
kamar an soke ta da kibiya, ta juyo a
razane, ko shakka ba ta yi ba Zangeru ne
ke yi mata magana ba. Zangeru ya ji
sautin muryar, shi kansa sai da abin ya sa
shi mutuwar tsohuwa. Zaune a bakin
fadamar numfashinsa ya dauke ya dubi
balbelar cikin tsananin kaduwa ko shakka
ba ya yi balbelar ce ke magana.
Ta gogari ta dubi Zangeru a tsorace ta ce
bakinta na rawa.
"Wa...nene ke yi min magana...na ji
muryar kamar ba kai ba?" Zangeru ya dubi
balbelar dake kan cinyarsa cikin kaduwa
sannan ya dubi Ta gogari.
"Ni ce nake yi miki magana baiwar Allah,
gani na yi ya dage akan cewa yana
kaunata ke kuma sai kokarin raba mu kike
yi."
Ta gogari ta ja da baya cikin kaduwa ta ce.
"Ki yi min rai baiwar Allah ke kike
ganinmu ba mu muke ganinki ba...wallahi
ban san..." Ta gogari ta kasa karasawa
saboda tsabar firgita.
"Kada ki ji tsorona domin ba zan taba
cutar ki ba tun da mijinki ya ambata yana
kaunata. Abinda nake so dake shi ne ki
daukeni kamar yadda ya umarceki ku tafi
dani gida domin daga yau har iya
rayuwarku zaku kasance tare dani ba zaku
taba rabuwa dani ba tun dai kuna
kaunata." Zangeru ya yi ta yan mata ya
tashi tsaye sai balbelar ta yi tsaye ta hau
kan kafadarsa ta ce.
"Zo ki daukeni Ta gogari."
Ta gogari ta ji kamar an doke kafafunta

da gora, nan da nan ta ji juna biyun dake
jikinta ya fara motsi kamar zata yi bari,
tun kafin lokacin haihuwarsa ya karaso.
***
A daidai lokacin da duk wannan ke faruwa
ne aka yiwa wani tsohon malamin gwanin
iya bugun kasa iso a gidan sarki Sabitu.
Wannan malami tsoho ne kwarai da
gaske, kuma babu wanda ya san
takamaiman shekarunsa a duniya domin
duk garin babu ko da wanda ya kusan sa'a
da shi. To amma duk da haka jita-jita na
cewa tsohon zai yi kusan shekaru dari
biyu zuwa dari biyu da hamsin a duniya.
Kai akwai ma wani makaryacin baduku a
garin da ya yi ta yada jita-jita cewar wai
tsohon ya kai shekaru dari biyar har da
tamanin. Wasu ko suna tunanin ma
tsohon malamin ba mutum bane aljanne.
To koma dai menene wannan tsohon
malami mai suna Malam Dawaye shi ne
babban malamin sarki Sabitu, kuma shi
kansa sarki Sabitun ya gaji wannan
malami ne a gurin mahaifinsa sarki mai
kwarangwama.
IDAN NAGA ANA SO INSHA ALLAH GOBE ZAN
CIGABA.
INNA FUSKANCI BA'ASO ZAN KYALE.
YAUWA.
Kudi da Maciji... (3)
Malam Dawaye dogone fari siriri sosai, ya
tankware kamar baka, tun daga kansa har
zuwa gemunsa babu alamar bakin gashi, sai
fari tas! Kamar an shafa masa garin alli, to
amma wani abin mamaki girar idonsa guda
daya bangaren hagu baka ce sidik har tana
kyalli, ko da yake wasu shakiyai sun ce wai
bakin shuni yake shafa mata. Lokacin da
wannan malami ya karaso gidan sarki la'asar
sakaliya ce. Sarkin dogarai Hambara shi ne
ya yi masa iso ya kuma wuce kai tsaye da shi
har zuwa inda sarki Sabitu yake kwance,
wanda yau kusan wata guda kenan yana

fama da matsananciyar rashin lafiya.
Malam Dawaye ya durkusa gaban shimfidar
sarki ya yi gaisuwa, sarkin dogarai ya amsa
masa. Sannan sai sarkin dogaran ya mike
tsaye zai fice daga dakin domin ya basu guri
su gana. Sai sarki Sabitu ya dago kai daga
kwance ya dubi sarkin dogarai sannan ya ce
cikin shakakkiyar murya.
"Idan an yi sallar magariba ina son ka zo min
da sarkin makera."
"An gama, Allah ya dada ma lafiya da imani."
Sarkin dogarai ya amsa sannan ya fice daga
dakin cikin sauri. A zuciyarsa yana cewa anya
kuwa sarkin nan ba mutuwa zai yi ba, domin
ya fahimci kusan kullum a yan kwanakin nan
sai sarki Sabitu ya gana da akalla aminansa
guda uku zuwa hudu kuma duk a cikin sirri.
Ficewar sarkin dogarai ke da wuya sai
malam Dawaye ya sake fadawa gaban sarki
ya dada gaisuwa sannan ya ce.
"Allah karama lafiya da nasara gani." Sarki
Sabitu ya dubi malam Dawaye daga kwance
na tsahon lokaci. Akwai alamun karaya da
sallamawa da duniya karara akan fuskarsa.
Malam Dawaye ya fuskanci hakan, dan haka
sai ya sunkuyar da kansa kasa, ba zai iya
hada idanu da sarkin ba domin sai ya zubar
da hawaye. Tsahon lokaci suna cikin wannan
hali daga karshe dai sai sarki Sabitu ya ce.
"Malam Dawaye, abin da ya sa na kirawo ka
shi ne na fahimci rashin lafiyar nan tawa ba
ta tashi bace, kuma ba tun yau ba ka rigaya
ka san irin muguwar kiyayyar da wazirina
Danduna ke yi min, kasan kuma cewa babu
makawa da zarar na mutu shi ne zai zama
sarkinku." Ya dan yi shiru yana mayar da
numfashi.
"Dawaye, a kullum na tuna da irin kiyayyar
dake tsakanina da waziri Dandunawa sai na
shiga cikin tsananin damuwa domin ban san
irin halin da yan kananan yayana Hassan da
Hussaina za su shiga ba. Wannan shi ne
dalilin da yasa na kiraka domin ka buga min

kasa ka gano min irin yadda zasu kasance a
hannun azzalumi waziri Dandunawa bayan
mutuwa" Sarki Sabitu ya yi shiru, yayin da
shi kuma Malam Dawaye ya shafi dogon
gemunsa fari tas mai kamar gashin tunkiya,
sannan ya janyo allon bugun kasar da ya zo
da shi zuwa gabansa, ya baza shi da
hannunsa sannan ya dubi sarki Sabitu ya ce.
"Allah ya baka nasara da lafiya an gama, bari
mu gani ai wuyar aiki ba a fara ba." Fuskar
sarki Sabitu ta washe kadan domin ya san
tsohon malamin bai taba bugun kasa an
sami wani kwakkwaran sabani ba. Domin a
tarihi, a kuma iya tsahon lokacin da sarki
Sabitu ya yi yana mulki, wannan tsohon
malami ya buga masa kasa sau goma sha
uku, inda duk ya tabbatar musu da samun
nasarar yaki, amma sau daya tak a ka sami
sabani inda suka yi kare jini biri jini, su da
kudawa. Wannan shi ne yasa duk wani abu
da ya shafi kasar tun daga hangen al'amuran
da suka shafi yanayin gari zuwa albarkatun
noma tsohon malamin ne ke bugawa ya
sanar da sarki.
Malam Dawaye ya dubi allon dubar dake
dauke da lallausan yashi, sannan ya fara
zana alkaluman lissafi na duba yana
gogewa, lokaci-lokaci sai ya daga kansa ya
girgiza, sannan daga karshe sai ya dago kai
ya dubi sarki ya ce.
"Allah baka lafiya da nasara, dabarar da kake
kokarin yi ita ce kawai mafita kana son
aikawa wani babban amininka dukiya mai
yawa domin ya boyewa yayanka ko?" Sarki
Sabitu ya gyada kai ya ce a tausashe.
"Tabbas, wannan shi ne nufina." Malam
Dawaye ya ci gaba da cewa.
"Tabbas wannan dabara ce mai girma,
domin a bayanka waziri Dandunawa tabbas
shi zai zama sarki, kuma abin bakin ciki zai
zamo daga cikin manyan azzaluman sarakan
da ba a taba yinsu a kasar nan ba. Ina son
kuma ka sani cewa da zarar ka mutu sarauta

zata bar hannun yan gidanku, za kuma a
cusgunawa yan gidanku, da yayanku guda
biyu Hassan da Hussaina wanda daga karshe
zai zamanto duk sun fice daga gidan
sarautar nan baki daya. Allah ya karama
nasara wannan shi ne abin da na gani."
Malam Dawaye ya yi shiru, lokaci guda kuma
ya sunkuyar da kai domin ya fahimci cewa
hawaye ne ke zuba kamar ruwa daga idanun
sarki Sabitu.
Shi kenan malam Dawaye, Allah ya hada
fuskokinmu a Darussalam." Sarki Sabitu ya
ce da shi. Malam Dawaye ya mike tsaye ga
mamakinsa sai ya ji hawaye ya kubuto daga
cikin idanunsa ya fara kwaranya akan
fuskarsa har zuwa cikin farin gemunsa.
Malam Dawaye ya sake duban sarki Sabitu
dake kwance, wanda tuni har ya rufe
idanunsa, ya kalleshi kallon da tuni jikinsa ya
bashi cewa me yiyuwa shi ne na karshe.
Sannan ya juya ya fice daga dakin.
Ficewar malam Dawaye ke da wuya sai ga
sarkin dogarai tare da sarkin makera sun
shigo, sarkin makera ya fadi gaban sarki
Sabitu ya yi gaisuwa.
Kudi da Maciji... (4)
Sarki Sabitu ya dubi sarkin makera mai masa ba
ya ce.
"Ina son nan da kwana uku ka keromin katuwar
akwati ta bakin karfe, wacce zata iya daukar
zinariya, lu-u lu-u da tagulla masu yawan gaske.
Ina kuma son ka yi mata hannaye masu karfin
gaske, wadanda idan an zo dora akwatin a bayan
doki ba za a sha wuya ba." Sarki Sabitu ya
saurara kadan yana mayar da numfashi, tuni har
idanunsa ya fara zubar da ruwa, gashi kuma
bakinsa sai rawa yake. Bayan ya dan huta sai ya
ci gaba.
"Ina son kuma ka yiwa akwatin manya-manyan
kwaduna guda shida, wadanda idan ba an yi
amfani da yayan makullayen kwadunan ba, duk
karfin mutum ka da ya iya budeta. Ina fatan zaka
iya?" Sarkin makera mai Masaba ya gyada kai

jikinsa na rawa.
"Allah ya dada ma nasara zan iya." Tun da ya ke
rayuwarsa bai taba shiga dakin shakatawar sarki
ba sai yau. To amma fa ba wai wannan bace ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login