Showing 12001 words to 15000 words out of 29993 words

Chapter 5 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf

12 Jul 2025

1240

hannunsa sa'ar da wani kwaro ya fara
safa da marwa akan dogon wuyansa.
"Ni abin da nake gani shi ne me zai hana
idan mun kwace akwatin, mu koma da ita
cikin katon kwarin nan dake kusa da

fadamar Danmasu wacce ke makwabtaka da
gandun sarki sai mu haka rami mu binneta a
gurin gindin wata bishiyar giginya."
Yana gama fadin haka sai Zangeru ya fashe
da dariya ya ce.
"Ba ka da hankali mai masaba, in ba hauka
ba me zai sa mu saci kayan sarki mu rasa
inda zamu boye shi sai a kusa da gandunsa?"
Mai masaba ya dubi Zangeru shekeke ya ce.
"Abin da yasa nace mu binne akwatin anan
shi ne, idan bincike ya tsananta babu wani
mutum daga cikin baradan sarki da zai taba
tsammanin za a boye akwatin a gurin. Na
san da zarar mun kwace akwatin, duk
hankula zasu koma ne kan garuruwan dake
makwabtaka damu, wannan shi ne
dabarata."
Zangeru ya dubi Makwaro. Makwaro ya dubi
Zangeru sannan sai suka gyadawa juna kai.
Mai masaba ya dubi mutanen biyu ya yi
murmushi.
"Ina fatan kun fahimceni." Mutanen biyu
suka gyada kai, sannan ne to Zangeru ya ce.
"Ka tambayi sarkin dogarai hanyar da za su
bi?" Mai masaba ya gyada kai.
"Ta jikin duwatsun zungura za su bi, daga
nan sai su yi yanke ta mararrabar kudu
domin wai hanyar zata fi musu sauri."
Zangeru ya gyada kai sannan sai ya dubi
makwaro ya ce.
"Makwaro sarkin maharba wacce irin shiga
kake ganin za mu yi musu?" Makwaro ya
mirgina uban kansa ya ce.
"Abi da zamu yi sai mu zagaye su, ku sai ku
tare su ta gaba ni kuma na boye a bayan
duwatsun.
Daga sun bullo sai ku fara yi musu ruwan
kibiya, idan sun fara mayar da martini, sai na
fito ta bayansu na fara habo su daya bayan
daya har sai na kare su!" Zangeru ya dubi
katon kan Makwaro ya ce "Yaya kuma zamu
yi da yan kyawawan yaran nan yayan sarki?"
Mai masaba ya buda baki zai yi magana

kenan sai makwaro ya yi farat ya ce.
"Ba na ce daku zan yi maganinsu ba?"
Zangeru ya ji zuciyarsa ta harba, idan har
akwai abin da ya ki jini shi ne kisan
kyawawa. Yawun bakinsa ya kafe sa'ar da ya
tuna da irin tsabagen kyawun yar sarki
Gimbiya Hussaina.
"Me za ka yi musu?" Makwaro ya dubi
Zangeru da fuskar katako ya ce.
"Kashe su zan yi dan babu ruwana da
kyawunsu!"
***
Yau kwana biyu kenan daidai, tun bayan
haduwar Amadi da Gimbiya Hussaina Haka
nan ita ce ranar da ta yi daidai da alkawarin
sake haduwarsu a bakin fadamar kamar
yadda Hussaina ta bukata.
Kudi da Maciji... (14)
Lokacin da Hussaina ta isa bakin fadamar sai
ta yi mamaki sannan ta tsunduma cikin
damuwa domin ta dauka za ta zo ta tarar da
Amadi a gurin zaune yana jiranta. Maimakon
hakan sai ta iske tsuntsaye burjuk a bakin
fadamar suna ta kai kawo abinsu suna
wakoki cikin muryoyi iri daban-daban da
masu dadi da masu ban haushi kai ka ce
bikin yar sarkin tsuntsaye ake yi.
Gimbiya Hussaina ta yi tsaye bakin korama
tana yan waige-waige, amma babu ko
motsin Amadi. Cikin damuwa da tsananin
fargaba me yiyuwa ma ba zata sake ganinsa
ba sai Hussaina ta nufi dutsen nan da ta
same shi wancan lokacin zaune akai ta zauna
sannan ta zubawa tsuntsayen dake bakin
koramar idanu bata ko kiftawa. Gashi dai a
zahiri idan ka dubeta kamar tsuntsayen take
kallo amma a badini ba su take kallo ba,
babu abin da zuciyarta ke zayyana mata sai
kyakkyawar surar dan saurayi Amadi.
Gimbiya Hussaina ta tuno da daren jiya, ta
tuna da cewa ko da daidai da barcin sa'a
guda bai zo idanunta ba. Tun sa'ar da suka
rabu da kyakkyawan saurayin ta koma gida

sai ta kasa zaune ta kasa tsaye.
"Me ke damunki ne?" Hassan din ta ya
tambayeta sa'ar da suke zaune tare da shi
bayan almuru. Gimbiya Hussaina ta dubi dan
uwanta Hassan sai ta rasa me zata ce dashi,
domin ita dai ta san har suka rabu da saurayi
babu wata bayyananniyar magana a game
da soyayya da ta shiga tsakaninta da shi, to
amma kuma zuciyarta ta rigaya ta san ta
kamu da ciwon son wannan kyakkyawan
saurayi. A da can wani lokaci idan Hussaina
tana karanta labaran soyayya a cikin
litattafan larabawa ta kan ga wautar mata
da suke nacewa akan son da namiji, domin a
ganinta wauta ce kawai, yaushe ne ma za a
ce kamar ita yar sarki ta kamu da ciwon son
wani mutum talaka wanda shi bai ma damu
da ita ba. Amma a yanzu da yake Hussaina ta
tsinci kanta a cikin irin wannan yanayi sai ta
fahimci ashe dai matan nan da ta sha
karanta labaransu a cikin littattafan
larabawa basu da laifi, ashe daman haka so
yake kamar sartse!
Kwanaki biyun da Hussaina ke jira su zo sune
mafiya tsayi da ta taba gani a rayuwarta,
domin a washe garin ranar da suka hadu da
Amadi sau daya tak ta sami damar cin abinci.
Koda ta sa abincin ma a bakinta sai taji babu
dadi kamar tana cin danko, haka nan duk
sa'ar da ta tuna da Amadi sai ta ji zuciyarta
na harbawa. Gimbiya Hussaina ta ci gaba da
Allah-Allah gari ya sake wayewa ko ta sake
dora idanunta akan Amadi. Rana ta fara
haske amma Hussaina gani take yi kamar ma
yamma ba za ta yi ba a ranar ballantana,
kuma har gari ya waye ta sake ganin Amadi.
Da aka jima Hussaina ta fahimci kamar ranar
ba ta yi mata sauri, sai kawai ta koma daki
ta kwanta da zummar wai ba zata farka ba
sai magariba.
Lokacin da ta farka sai ta ji a lokacin ne ma
ake kiran sallar Azahar.
Abubuwan suka taru suka dagule mata.

Zuciyarta ta fara bata shawarar mai zai hana
idan ba za ta iya daurewa ba ta dauki
kuyanginta su raka ta har gidan su Amadi
mana. Ai kuma abin kunya ne ace yar sarki
tabi talaka har gida. Wata zuciyar tace da ita.
Dan haka a yanzu da Hussaina ke zaune akan
dutsen tana jiran isowar Amadi cikin rashin
tabbaci, sai ta yanke hukuncin cewa in har
aka jima bai zo ba, ko shakka babu gida zata
bishi.
Gimbiya Hussaina ta dan zame kadan daga
kan dutsen da take zaune sannan ta zura
kyawawan kafafunta cikin fadamar ta fara
wasa da ruwa.
A daidai wannan lokacin ne ta ji motsi a
bayanta.
"Ki yi hakuri ranki ya dade Allah ya huci
zuciyarki na ajiyeki zaman jira." wata
sassanyar murya ta ce daga bayanta.
Hussaina ta ji wani irin dadi ya mamayi
zuciyarta, cikin farin ciki ta juyo gare shi da
tattausan murmushi akan jajayen lebbanta.
"Sannu da zuwa Ammadi...ina fatan dai
lafiya?" Amadi ya dubeta da murmushi ya
gyada kai.
"Lafiya lau ranki ya dade wallahi mahaifina
ne ya tsayar dani." Hussaina ta lumshe idanu
cikin farin ciki.
"Ni da na dauka ma ba za ka zo ba." Amadi
ya girgiza kai cikin gaggawa.
"Haba ranki ya dade, ni na isa ki yi kirana na
ki zuwa...saboda tunanin alkawarin nan naki
ko cikakken barci bana yi."
"Saboda me?" Hussaina ta tambayeshi.
Amadi ya sunkuyar da kai kusan na tsawon
lokaci bai amsa ba, sannan daga karshe sai
ya dago kai ya ce.
"Saboda da na rufe idanuna sai na yi ta
ganin surarki ranki ya dade....ga shi kuma
tunanin kirkinki da karimcinki ya kasa barin
zuciyata." Hussaina ta ji dadi ya sake
mamayar zuciyarta a karo na biyu. Ta dago
kanta ta dubeshi ido-da-ido ta ce.

"Amadi wannan shi ne kawai abin da ya
hanaka barci ko kuwa akwai wani abin
daban."
Amadi ya dubeta cikin rashin fahimta ya ce.
"Ban fahimce ki ba ranki ya dade." Hussaina
ta sunkuyar da kai a wannan karon kana sai
ta ce cikin wata rarraunar murya.
"Ni kuwa tunaninka... Da kaunarka ce suka
hanani barci."
"Zuciyar Amadi ta harba tsakawa
hakarkarinsa kamar zata huda ta fito. Bai
taba tsammanin za ta fito fili ta bayyana
kaunar tata a gareshi ba.
"Ranki ya..." Amadi ya yi shiru bai karasa ba
sa'ar da ya ga Hussaina ta daga masa hannu.
Kudi da Maciji...
Part (15)
"Hussaina sunana, ina fatan ranki ya dade din
nan zata fita daga bakinka." Ta yi masa
murmushi sannan sai ta matso kusa da shi ta ce.
"fada min da bakinka Amadi kana sona."
Amadi ya ji zuciyarsa ta yankwane a guri guda ko
shakka ba ya yi ya san yana kaunarta, domin
shima abinda ya hana shi barci kenan a darare
biyun da suka wuce, to amma shi yasan wannan
soyayya dake kokarin faruwa a tsakaninsu tamkar
soyayyar mafarkice domin ina shi ina yar sarki!
"Ranki ya....Hussaina...tun sa'ar da na fara dora
idanuna a kanki na ji ina kaunarki to amma ni na
rigaya na sani bazan taba samunki ba domin
babu hadin dan talaka da dan sarki."
"Kada kace haka Amadi, domin kai baka san
gaibu ba...in Allah ya so kaine mijina Amadi."
Amadi ya sunkuyar da kai. A zuciyarsa ya ce. Kai
lamarin duniya na da ban mamaki ka ji kai
yarinya saboda shaukin soyayya tana sambatun
almara.
"Daman abin da ya sa na ce da kai ina son mu
sake haduwa anan domin mu yi sallma ne, ka san
jibi zamu bar garin nan ni da dan uwana
Hassan."
Amadi ya dubeta cikin mamaki.
"Wane gari zaku koma?"

"Wajen babban aminin mahaifin mu za a mayar
da mu sarki Lurwanu, na san me yiyuwa kasan
garin tun da kai mafaraucine." Amadi ya gyada
kai.
"Kwarai kuwa na san garin, domin wazirin sarkin
Lurwanu yasha fansar fatun damisa a gurina."
Gimbiya Hussaina ta yi ajiyar zuciya da jin cewa
ya san garin.
"Idan kana ganin ba takurawa Zan so ka bini
garin, amma ka bari har sai mun sauka a garin
da kwana biyu, idan ka je zan tare ka a bayan
gari. Ko ya ya ka gani?" Amadi ya gyada kai a
tsorace ya ce.
"Duk abin da kika ce haka za a yi....Hussaina!"
Hussaina ta dube shi cikin tsananin farin ciki ta
ce.
"Na gade Amadina, duk duniya bani da na biyunka
cikin ruhina." Amadi ya yi ajiyar zuciya gami da
duban tsuntsayen dake jajjere a bakin koramar.
"Yanzu yaushe za ku tafi."
"Jibi war haka muna shirin tafiya garin kamar
yadda muka yi alkawari."
Gimbiya Hussaina ta cire wani kyakkyawan zoben
azurfa dake dan yatsunta ta mikawa Amadi.
"Ga wannan ka ke tunawa dani kafin mu sake
haduwa, ni kuwa zan tafi da kanarin da ka bani
cikin keji, ya isheni debe kewa tunda dai kyautar
ka ce."
Matasan biyu suka kurawa juna idanu suna
murmushi, domin basu sun rabuwa.
Da sun lura da kyau, za su hangi wata farar
babelar daga can cikin tsuntsayen bakin fadamar
tana kallonsu cikin tsananin mamaki da kaduwa!
***
"Lah ka ga dogayen duwatsun nan da baba ya
sha bamu labari." Hussaina ta ce da dan uwanta
Hassan cikin doki, lokaci guda kuma ta mika
hannunta daga kan dokin ta taba dutsen da
kyakkyawan yatsanta. Hassan ya dubi dutsen a
yatsine sannan ya dubi yar uwarsa Hussaina ya
ce.
"Kin ga ni kuwa babu abin da na tsana a
rayuwata irin dogayen duwatsu."

"Me yasa?" Hussaina ta tambaye shi gami da
murmushi, domin ta riga ta san tafi dan uwan
tagwaitakar jarumta.
"Kawai dai ni son ganin dogayen duwatsu ne ba
nayi, wata sa'ar sai in ga kamar mutuwa ce ke
kokarin zuwa ta zare ni musamman ma a irin
wannan lokaci na duhu." Hussaina ta bushe da
dariya.
"Kai dai wallahi matsoraci ne, in ba haka ba ka
taba ganin an gujewa mutuwa? Ai duk inda
kwananka ya kare ko a akan duwatsu, ko a cikin
fadar babanmu sarki, ko a cikin duhu ko a hasken
ran sai mutuwa ta riskeka domin idan ta zo babu
tsimi babu dabara." Hassan ya dubi yar uwarsa
da murmushi a cikin duhun daren.
"Wannan gaskiya ne, ya yar uwata Hussaina."
Sarkin dogarai dake daf daf da su ya yi murmushi
a cikin duhun daren sa'ar da ya ji hirar da ke
gudana tsakaninsu. Sannan kamar yadda ya saba
fadi kullum cikin zuciyarsa, yanzun ma sai ya ce
ina ma ace yayansa ne. Sarkin dogaren ya juya
baya ya dubi yan rakiyar tasu mutum shida ko
wannensu cikin shigar yaki, dauke da kibbau
masu dafi, suna tafe sun sa kakkarfan dokin da
aka dorawa akwatin dukiyar a tsakiya, wata sa'ar
ko motsin ganye suka ji sai sun juya da shirin kai
sara. Kamar macizai.
Duk da wannan shiri da barazana da suke yi basu
taba tsammanin wani abu makamancin fashi zai
faru a kansu ba, domin sun yi imani da cewa duk
wani barawo dake hanyar ya san da irin
jarumtarsa ta baraden sarki, a tunaninsa babu
mai iya tunkararsa da wata barazana.
"Mutanen duniya basu da tabbas, suna iya ba ku
mamaki." Sarkin dogarai Hambara ya ce da su
sa'ar da za su baro gida. Wannna shi ya sa
baraden yan rakiya daukar takubba sabanin kwari
da bakan da suka dauka tun farko.
A can gefe guda a bayan duwatsun cikin duhu
Makwaro ne zaune ya dana kibiyarsa ta farko
wacce da ita ce yake fatan mika sarkin dogarai
lahira, tare da sauran jama'arsa. A can kuma
karshen duwatsun sarkin barayi Zangeru ne shi

da abokinsa sarkin makera da barayi Mai
masaba, sun yi kwanto suna jiran karasuwar
tawagar ayarin. Tun farkon shigowar almuru suke
nan makale, har sun fara kosawa, saboda tsabar
rikon kibiya a dane har hannun Zangeru ya fara
gumi.
Suna nan makale, lokaci guda kuma suna
makyarkyatar sanyin asuba da ya fara hurowa,
wata sa'ar jikinsu har buguwa yake da na juna
kamar zakarun da ruwa ya jika......
Kudi da Maciji... (16)
A daidai wannan lokacin ne to suka jiyo
motsin ayarin tawagar sun doso inda suke
boye.
Mutanen biyu sarakan barayi suka dubi juna,
lokaci guda kuma suka hangi inda Makwaro
yake make.
Daga inda suke zaune suna iya hango
rungumemen kan Makwaro wanda ke zaune
ya yi dani, baya ko motsi kamar gunki.
"Allah ya sa dai kada lalataccen can ya harbi
yaran nan biyu... "Zangeru ya ce, ba tare da
ya dubi Mai masaba ba. Domin tuni har sun
fara jiyo hayaniyar mutanen suna hira.
"Ai kuwa in ba wata sa'a ba da nisan kwana
sai ya kashe su, ka ga dai sana'armu daya da
shi amma wallahi ni kaina tsoron rashin
imaninsa nake yi."
Zangeru ya ji wani zazzafan gumi ya fara yi
masa sartu a doron baya. Har ga Allah ba shi
son abin da zai sa a kashe kyawawan yayan
sarkinnan domin shi dukiyar ce kawai
agabansa ba kisan kai ba.
"To sai fa gare mu ga sunan sun matso." Mai
masaba ya ce da Zangeru sannan cikin zafin
nama na ban mamaki sai ya gyara danin
kibiyar dake jikin bakansa, sannan ya cilla
harbi cikin ayarin ta tsakanin duwatsun. Ba a
dade ba suka ji an kwalla kara mai tsanani,
sannan sai sautin fadowar wani mai sauti
irin na buhun sumunti.
"Na sami daya kafiri!" Mai masaba ya ce cikin
karaji Zangeru jiki na rawa ya shafi gefen

tsafaffen bantensa inda ya kulle dutsen nan
da balbela ta bashi, ya tabbata yana nan,
sannan sai shima ya cilla harbi cikin ayarin.
Nan da nan hayaniya ta barke da hargowa,
da ife-ife cikin razana da kaduwa. Daga cikin
duhun Zangeru ya hangi Makwaro ya fara
cilla harbi cikinsu, har sau uku, duk harbin da
yayi sai ya jefa mutum daya kasa.
Ba a dade ba sai wajen ya yi tsit. Baka jin
komai sai gurnani da motsin dawakai. Mai
masaba ya dubi Zangeru jikinsa na rawa
yana haki ya ce.
"Mun ci nasara....lalat accen duk ya
kwantar da su." Zangeru bai ko dubeshi ba,
jikinsa sai kyarma yake yi. Abin da ke damun
zuciyarsa shi ne." kyawawan yaran yayan
sarki, ko shakka ba ya yi makwaro duk ya
harbesu. Ya kuwa tabbatar kibiyar Makwaro
tsafaffiya ce ba ta sukar mutum ya rayu. Ga
mamakin Zangeru sai ya ji akaro na farko ya
tsani kansa ya kuma tsani Makwaro, don
me....saboda me a wane dalili zai kashe
wannan kyakkyawar budurwa ita da dan
uwanta bayan shi kuma nasa dan Amadi
yana can gida lafiya kalau babu ko kwarzane
a jikinsa.
"Wayyo Allah na shiga uku na lalace wayyo
Hassan!" Ihun Hussaina ya ratsa cikin dajin,
amsa kuwwar ta watsu cikin duwatsu.
Sarakan barayin biyu suka dubi juna, sannan
lokaci guda suka dubi inda Makwaro yake.
Kotsam sai suka ga ya mike tsaye, ya zaro
kibiya daga cikin kwari ya danata sannan sai
ya yi awon cikin duhun inda suka ji ihun tun
farko. Zangeru ya ji zuciyarsa ta harba domin
ya san abin da Makwaro ke nufin yi. Cikin
zafin nama na mamaki sai Zangeru ya dana
tasa kibiyar ya saita wuyan Makwaro ya
harba. Kamar wasa sai kibiyar ta sami inda
aka yi nufinta. Makwaro ya kwalla ihu
sannan sai ya fadi a gurin. Mai masaba ya
dubi Zangeru cikin kaduwa ya ce.
"Haba Zangeru! Kanka daya kuwa? Me yasa

zaka harbeshi?" Zangeru ya harari Mai
masaba a cikin duhun ya ce a fusace.
"Me yasa zai kasheta, bayan kuma da sauran
kwananta a duniya, ko ya dauka shi kadai
yake da tsafin harbi, yau ko kunama ne shi
na kawo karshen karyar banza!" Mai masaba
cikin kaduwa ya mike tsaye a fusace.
"Ba zata yiyu ba Zangeru., dole ne itama ta
mutu, idan kai ba zaka iya taba ta ba, bari ni
in tafi na karasata."
Yana gama fadin haka sai ya fara gangarawa
kasan dutsen ya nufi inda suka jiyo ihun
budurwar.
A daidai wannan kokacin ne to Zangeru ya ji
kamar wani abu na sukansa a kugu. Cikin
sauri ya kai hannu gurin sai ya ji ya taba
tsinken kibiya. Jikinsa na rawa ya zare daga
kugunsa ya dagata sama a cikin duhun
daren. Ko shakka ba ya yi daya daga cikin
kibiyoyin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login