Showing 6001 words to 9000 words out of 29993 words
Chapter 3 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf
ita duk gani take yi
kamar balbelar za ta yi tsalle ta cakar mata
idamu koma ta makureta. Idan har akwai abin da
Ta gogari take tsoro bai wuce aljani ba. Sai gashi
yau da kanta ta dauko aljanar a hannunta za ta
kaita har gida.
Zangeru kuwa wanda ke gaba yana jan kafa da
kyar ji yake yi kamar an sa masa sasari a kafa. A
iya tsayin zamanin da ya yi yana harkar sana'ar
bera ya yi gamo da hadarurruka iri daban-daban,
amma har zuwa wannan lokaci bai taba gamo da
aljanu ba, domin shi a tunaninsa ma in banda ya
ji ana ta fada, kuma wani malaminsa wanda ke
biya masa karatun kur'ani tun yana karami ya
taba yi masa bayanin wata aya da take magana
akan aljanu, da sai Zangeru ya ce babu aljanu ma
sam-sam a duniya tun da dai bai taba gamo da
su ba. To sai gashi kuma yau da kansa ya
daukowa kansa jaraba.
Sannu a hankali har su Zangeru suka karaso cikin
gari. Sa'ar da suka shigo ta cikin babban
dandalin garin sai mutane suka yi ta binsu da
kallo cikin mamaki, domin abin mamaki ne ace
mutum ya rasa abin da zai zo dashi gida daga
gona sai balbela!
A daidai lokacin da suka karaso kofar gidan
sarkin aska ne, sai matarsa wacce ta kasance
kawace ga Ta gogari ta leko ta ce.
"Oh! Ta gogari yau kuma da balbela kuka zo
mana daga gonar, hala wannan balbelar yar
misirace?" Ta gogari ta dubi mijinta Zangeru
sannan ta dubi matar sarkin aska da murmushin
yake ta ce.
"Me yasa kika ce haka, ko gani kika yi kyawunta
ya yi yawa" Matar sarkin aska ta girgiza kai ta
ce.
"A'a, gani dai na yi duk balbelun dake cikin garin
nan basu isheku ba har sai kun zo da wata daga
daji."
A karo na farko sai Zangeru ya dubi matan biyu
dake jayayya ya ce.
"Ku fa idan kuka fara jayayya kun yi ta yi kenan,
da Allah Ta gogari taho mu karasa gida kada
almuru ya riske mu a kofar gidan wanzamai."
Matar sarkin aska na jin haka sai ta fashe da
dariya ta ce.
"A'a ha, Zangeru in dai yar sarautar nan tamu ce
kakewa bakin ciki bari kaima na baka sabuwar
sarauta, daga yau na nadaka sarkin balbelu"!
Suka fashe da dariya, sannan su Zangeru suka
wuce.
Lokacin da su Zangeru suka karasa gida almuru
ya rigaya yi, haka nan har yanzu cikinsu dure
yake da ruwa domin basu san yadda za su yi da
balbelar ba. A haka cikin tsananin fargaba suka
shigo katuwar farfajiyar gidan, ma'abociyar
shuke-shuken bishiyar zogale da kabewa. Daga
bangaren kudu kuwa na gidan baka hango komai
sai tarin ciyayi ko ina marasa amfani, haka nan
daga bangaren gabas wata tsohuwar rumfa ce
shekararriya wacce wasu awaki guda biyu ke
karkashinta a daure. Su kansu awakin asalinsu
Zangeru ne ya sato su a wani kauye dake
makwabtaka da su. In ka dauke rumfar dabbobin
fankadediyar farfajiyar gidan bata mallaki komai
ba sai wasu bukkoki guda uku, da kuma wani
tsohon rumbu, wanda rabonsa da ya dauki sama
da damin gero biyar tun Zangeru yana dan
saurayi.
Wadannan bukkoki guda uku da tsohon rumbun
gami da awakin nan guda biyu na sata su kadai
ne arzikin da zangeru ya mallaka a duk tsawon
shekarun da ya yi yana sata. Sau da yawa Ta
gogari ta sha nuna masa cewa shi fa zalunci ba
abin yi bane, kuma bai sa mutum ya yi arziki,
kuma koda ya yi arzikinma ba zai taba jin dadin
arzikin ba, to amma sai Zangeru ya dubeta ya
fashe da dariya ya ce.
Kudi da Maciji... (7)
"Ta gogari kenan! Ai idan kika ji ana cewa wai ba
a arziki da kayan sata to daman satar ba ta kai
sata ba." Wannan shi ya sa sa'ar da Zangeru ya
sato awakin nan guda biyu sai ya ce da Ta
gogari.
"Ga wadannan awakin ki ci gaba da kiwata min
su da sannu zan samo musu yan uwa, domin
lokaci ya yi da ya kamata na nuna miki cewa ana
arziki da kayan sata, kuma akalla dai a yanzu ko
da mutuwa nayi na san na barwa dan dana
AMADI gadon awaki guda biyu."
Wannan Amadi da Zangeru yake magana akai shi
ne babban dansa kwaya daya jal a duniya.
Sabanin iyayensa, Amadi kyakkyawa ne dogo fari
mai dan siririn fashin goshi, zai kai kimanin
shekaru goma sha tara a duniya, tun daga kansa
mahaifiyarsa Ta gogari bata sake yin ko batan
wata ba sai a wannan karon da ta sami ciki
akalla wata takwas.
Sabanin mahaifinsa Amadi ba shi da wani aiki da
ya wuce farauta wata sa'ar idan ya fita farauta
sai ya yi wata guda bai dawo ba.
Dan haka sa'ar da mahaifan Amadi Zangeru da
Ta gogari suka karaso farfajiyar gidan dauke da
balbelar sababin sai suka yi mamakin ganin
kayan farautar Amadi, gami da wasu zomaye
guda shida yankakku da beguwa biyu da damo
biyar duk zube a tsakar gidan.
Zangeru ya dubi kayan farautar, sannan sai ya
jefar da fartanyarsa ya zauna jagwab a gaban
kayan farautar. Ta gogari ta yi sauri ta zauna
kusa dashi sannan bakinta na rawa sai ta mika
masa balbelar ta ce.
"Ungo balbelar ka." Zangeru ya dubi Ta gogari a
tsorace, jikinsa na rawa kamar mazari, ya mika
hannu ya karbi balbelar yana mai addu'ar Allah
ya kawo dansa Amadi ko sa sami mafita, domin
ya san duk inda Amadi yake bai yi nisa ba tun da
dai ga kayansa nan ya dawo.
Kudi da Maciji... (8)
"Ki saki jikinki dani baiwar Allah ni mai
kaunarku ce sannu a hankali za ku saba dani
kamar yadda kuka saba da dan kyakkyawan
yaran nan naku Amadi mafarauci."
Ma'auratan biyu suka dubi juna cikin
tsananin mamaki da kaduwa. Zangeru ya
dubi balbelar cikin kaduwa ya ce.
"A...ina kika san Amadi?" Balbelar ta karkada
fukafukanta biyu ta ce.
"Mun sha haduwa dashi a cikin daji inda yake
farauta, tun yana karami nake ganinsa, shi
ne dai bai sanni ba." Balbelar ta dan yi shiru
sannan sai ta dubi namun dajin dake zube a
tsakar gidan ta ce.
"Ko jiya ma a gabana ya kashe wadannan
zomayen guda biyu." Balbelar na gama fadin
haka sai ta yi tsalle sama ta sake direwa,
sannan sai ta yi girgiza da karfi. Nan da nan
wata bakar guguwa ta turnuke gurin. Ta
gogari ta tashi a tsorace ta nufi inda
maigidanta Zangeru yake ta fada akan
cinyarsa ta kankame shi cikin razana.
"Kada ku tsorata, ba wani abu zan yi muku
ba Ai ni da ku alkawari ne babu cuta ko cin
amana."
Wata siririyar murya ce ke fadin hakan. Ba a
dade ba sai guguwar ta tsaya cak.
Ma'auratan biyu suka yi ajiyar zuciya, kana
suka dubi inda balbelar take. Har yanzu tana
nan tsaye, sai dai kuma wannan karon
Balbelar dauke take da wani dan
madaidaicin dutsen kankara fari sol a
bakinta. Balbelar ta yi tsalle ta sauka a
kafadar Zangeru, sannan ta saki farin dutsen
ya fado tsakanin cinyoyinsa. Ta gogari ta
dada kankame Zangeru a tsorace, ji take yi
kamar zata sume.
Balbelar ta dubi farin dutsen ta ce da
Zangeru.
"Dauki farin dutsen nan ka adana shi, duk
sa'ar da kake bukatar wani taimako daga
gareni, jefa dutsen kawai zaka yi a bakinka,
ko kuma ka murza shi tsakanin tafin
hannayenka zan bayyana." Balbelar ta yi
tsalle ta baro kan kafadar Zangeru ta sake
direwa a kasa sannan ta ce.
"Ni zan tafi sai kun bukaci ganina kuma!"
tana fadin haka sai ta tashi firrr! Ta tafi
abinta.
Zangeru da Ta gogari suka bi balbelar da
kallo cikin kaduwa, har sai da ta bace a
sararin samaniya sannan suka yi ajiyar
zuciya baki daya.
Ta gogari ta yi sauri ta bar jikin mijinta ta
zauna a kusa dashi, sannan ta dube shi
jikinta na rawa ta ce.
"Ga irinta nan ai, lalacinka da shisshiginka ya
janyo mana bakar jaraba har gida!" Zangeru
ya dauki dan farin dutsen da balbelar ta
bashi ya juya shi a hannunsa sannan ya dubi
Ta gogari cikin murmushi ya ce.
"Idan kika kara zaginta, sai na murza dutsen
nan na ta dawo miki yanzu-yanzun nan!" Ta
gogari ta ja da baya a tsorace.
"Ka rufa min asiri don Allah Zangeru. Wai me
ke damunka ne? Kai yanzu har ma fatan ka
sake ganinta kake yi? Ni Wallahi da zaka biya
ta tawa ma da sai ka jefa datsen nan cikin
rijiya, ka ga mun rabu da ita kenan har
abada."
Zangeru ya saki wani busasshen murmushi
kana ya dada duban dutsen dake hannunsa
ya ce.
"Kin cika yanke hukunci da wurwuri Ta
gogari, kika sani ko wata rana zamu bukaci
taimakon nata?"
A daidai lokacin da duk wannan ke faruwa
ne to Amadi ya shigo gidan dauke da kwari
da baka.
Mahaifan nasa suka yi shiru lokaci guda
sannan suka zuba masa idanu.
"Lafiya na ga duk kun yi jugum-jugum?"
Zangeru ya yi sauri ya saki murmushin yake
ya ce.
"Lafiya lau Amadi, Dawowarmu kenan daga
gona. Ina fatan ka dawo lafiya?" Amadi ya
ajiye kwari da bakarsa a gefe guda sannan
ya dubi mahaifiyarsa ya ce.
"Lafiya lau, amma ina jin gobe ma zan koma,
daman zuwa na yi na kawo muku wannan."
Ya nuna zomaye da sauran naman farautar
dake zube a tsakar gidan.
"An gode Amadi Allah ya saka ma. Bari ma in
tashi na gyarasu." Ta gogari ke fadin haka
lokaci guda kuma ta mike tsaye ta nufi inda
yankakkun zomayen suke. Ta gogari na
durkusawa akan zomayen kenan sai suka ji
kamar daga sama wata gargajejiyar murya
ta ce.
"Gafaranku dai masu gidan nan!" Ta gogari
ta juyo cikin sauri ta dubi kofar gidan. Nan
da nan ta ji yawun bakinta ya kafe, bugun
zuciyarta ya dadu.
Ko daman kafin ma ta juyo ta san duk
duniya babu mai wannan gwarjejiyar murya
mai kamar goge sai mutum daya, mutumin
da ya kasance babban amini ga maigidanta
amma har yau bata taba farin ciki da
ganinsa ba, domin Ta gogari ta rigaya ta san
mutumin tauraruwa mai wutsiya ne ganinsa
ba alheri ba. Mutumin dogo baki mai katon
kai da tarin gashin baki da bujujun gemu
gami da faffadan kirji kamar kofar gari ya
matso kusa da su ya dubi Zangeru da
faffadan murmushi yace.
"Tun a hanya nake ta addu'ar Allah sa na
sameka." Ya dan yi shiru "Tashi mu fita daga
kofar gida, wani labarine ke cina, shi ne na
zo maka da shi tun da dumi-duminsa."
Zangeru ya mike cikin sakin fuskarsa a
washe ya ce.
"Sarkin makeran duniya, MAI MASABA, ni
daman na san ai ungulu bata jewar banza.
Da me ka zo mana?" Mai masaba ya dubi
Amadi da Ta gogari sannan sai ya kiftawa
Zangeru idanu ya ce.
"Zo mu fita daga waje." Zangeru ya bishi
cikin sauri suka zagaya bayan danga. Ta
gogari ta dubi Amadi cikin kunan rai, shi ko
Amadi ya dubeta cikin mamaki ya ce da ita
cikin rada.
"Wai daman har yanzu BABA bai daina
muguwar sana'ar nan ba?"
Kudi Da Miciji
Part 9
Tagori ta ji kamar hawaye zai zubo mata dan
haka sai ta dauke kai gefe guda ta ce.
"Me hali ai baya barin halinsa Amadi."
***
Ina jin fa ga dukkan alamu Zangeru, tsuntsu daga
sama gasasshe na kokarin fadowa a cikin akushin
mu." Mai masaba ya ce da Zangeru sa'ar da
suka zauna akan ciyawar da ta mamaye jikin
dangar gidan suka mike kafafunsu kamar masu
daukar darasu. Daga inda jibga-jibgan mutanen
guda biyu suke, suna iya hango wata katuwar
duhuwa ma'abociyar yawan bishiyoyi da ciyayi,
haka nan a daf da duhuwar wasu jakai ne guda
biyu da shanu guda uku suna kiwo abinsu suna
harbin iska babu abin da ya damesu a duniya.
Zangeru ya muskuta ya lalubi katon goro ya bara
shi gida biyu ya jefa rabi abakinsa sannan ya
mikawa mai Masaba rabin sannan ya dada da
cewa.
"Bani labari na sha abokina, me ka gano mana?"
Mai masaba ya jefa bangwalelen goron mai
kamar kataura gaba daya cikin bakinsa ya fara
taunawa rumus-rumus kamar jaki na cin danyar
ciyawa.
Dazu-dazun nan na dawo daga gidan sarki, an
umarceni da na kera wata katuwar akwatin
karfe."
Mai masaba ya yi shiru yana duban fuskar
Zangeru.
Zangeru ya daga hannu cikin kosawa ya ce.
"To ci gaba mana ina sauraronka, an kira ka
gidan sarki an ce ka kero katuwar akwati uhm-
hum."
Mai masaba ya zura hannunsa baya ya karyo
wani dan siririn kara daga jikin dangar ya fara
sosa doron wuyansa da karan. Duk abin da yake
yi Zangeru na kallonsa ya lura akwai alamun
damuwa karara a fuskar mai Masaba.
"Abin ne yana da matukar hadari, domin idan
muka yi kuskure ko da kankanine zamu iya
hasarar rayuwarmu, idan kuwa muka yi nasara,
mun gama shiga sahun attajirai kenan, domin ba
su ba har tattaba kunnenmu sun rabu da talauci,
me yiyuwa ma dole ne mu bar garin."
Zangeru ya shura kafafusa biyu cikin rairayi
sa'annan ya dubi mai masaba cikin kaguwa da
damuwa.
"Ni har yanzu na kasa fahimtar inda soki
burutsun nan naka ya sa gaba, ya kamata ka
warware min zare da abawa." Mai masaba ya yi
ajiyar zuciya ya ce.
"Wato wannan katuwar akwatin karfe da nake
baka labarin ansa ni na kera, sarki Sabitu ne ke
son kwashe duk wasu ma'adinai masu daraja da
ya mallaka zai aike dasu zuwa gurin babban
amininsa Sarki Lurwanu." Zangeru ya saki wani
kwakkwaran huci, rairayin dake gabansa ya yi
sama fu!! Kamar yar karamar guguwa.
"Ma'adanan da kake magana a kai suturu ne ko
makamai ko kuwa me?" mai Masaba ya saki
wata kekasasshiyar dariya.
"Wata sa'ar Zangeru na kan dade ban ga
shashasha kamar ka ba, in banda abinka akan
wasu suturu ko makamai karafan banza zan
dauko kafa na biyo ka har gida dan kawai jin
dadin hira? To bari ka ji ina son ka bude
kunnuwanka da kyau, wannan akwatin da nake
baka labari cikata za a yi da gwala-gwalai, zinare
da lu'u-lu'u!" Zangeru ya zabura cikin kaduwa
nmfashinsa ya dauke.
"Ba ka da hankalimai Masaba, Lu'u-lu'u fa ka ce
cikin akwati!" Mai Masaba ya yiwa Zangeru
murmushin yake ya ce "kada ka yi shakkar duk
abin da na fada maka."
"To kai duk a gurin wa ka sami wannan labarin,
kada ka samu wahalar banza, na san dai nufinka
shi ne mu tare wanda sarkin zai aika muyi fashin
akwatin ko ba haka kake nufi ba?" Mai Masaba
ya fashe da dariya ya ce.
"Dadina da kai saurin fahimtar zance da inda
zancen ya nufa." Mai Masaba ya dan yi shiru
sannan sai ya dubi Zangeru ya ci gaba.
"Ka san sarkin dogarai tsohon abokina ne, a
gurinsa duk na sami labarin, dan shi ne shugaban
ma wadanda za a aika da kayan a cewarsa su
shida za su raka akwatin kayan."
"Shu Shida!" Zangeru ya tambaya. Mai masaba
ya gyada kai.
"Ka ga kenan in har muna son mu ji dadin yi
musu kofar rago muna bukatar karin mutum daya
kenan, kaga kowane daya daga cikinmu sai ya yi
maganin mutum biyu daga cikin fadawan kenan."
Mai Masaba ya gyada kai cikin gamsuwa.
"Kwarai kuwa muna bukatar karin mutum daya,
amma ina jin ai MAKWARO naka yana gari ko?"
Zangeru ya dan yi kasake yana tunani can sai ya
gyada kai ya ce.
"Kwarai kuwa muna iya tafiya da Makwaro,
kasan kuwa gwanine wajen iya harbi dan banza
da katon kai kamar murhu." Mutanen biyu suka
fashe da dariya sannan suka mike tsaye lokaci
guda Zangeru ya dubi Mai Masaba.
"Yaushe ne ranar da za su yi tafiya?" Mai
masaba ya shafi keya.
"Wannan shi ne ban sani ba, yanzundai kwana
uku aka bani na gama kirar akwatin, na san kuma
sarkin dogarai ne zai zo daukar akwatin, zan yi
kokarin na bugi cikinsa na ji ranar da za su fita
da kuma ta hanyar da za su bi. Domin yanzun
zuwa dai na yi na tsurkunta maka dan ka zama
cikin shiri."
"Kada ka ji komai" Zangeru ya ce, cikin gaggawa.
"Ni daman kullum a shirye nake, wanda ke neman
kuka ballantana aka jefe shi da kashin awaki ni
daman fa wallahi Mai masaba, na gaji da
kanana-kanan sace-sacen nan, kullum fatana shi
ne na yi katuwar satar da zan zama attajiri kaga
daga nan sai na tuba na bar sata." Mai masaba
ya fashe da dariya ya ce.
"Lallai abokina ko yaushe tunanina iri daya ne da
naka."
Mutanen biyu suka fara tafiya a hankali suka bi
yar siririyar hanyar da zata kai su har can cikin
gari....
Kudi da Maciji... (10)
Koda suka fara tafiya sai Zangeru ya dubi
mai masaba ya ce.
"Idan mun yi nasara ya ya zamu yi da
wannan tarin dukiya? Mai Masaba ya dan yi
shiru yana girgiza kai sannan sai ya ce.
"Lallai ka zo da babbar tambaya, amma
yanzu dai bari mu fara samun dukiyar tukun,
samunta ya fi yadda za ayi da ita wuya, idan
muka yi nasara ba sai mu bar garin ba me
kuma zai kara zaunar da mu a wannan garin,
gara mu tafi can nesa inda za mu sha gararin
gabanmu cikin nutsuwa ai KUDI DA MACIJI
MAGANINSU KASHEWA Zangeru."
Sa'ar da mutanen biyu suka zo rabuwa, sai
suka yi musabiha da juna, kai ka dauka wasu
shehunan malamai ne. A lokacin ne to
Zangeru ya dubi Mai Masaba ya ce.
"Yanzu sai yaushe kenan zaka zo mu yi shirin
karshe?"
"Da zarar na kai akwatin, na kuma bugi cikin
sarkin dogarai zan dawo. Kai dai sai ka yi
kokarin ka sanar da MAKWARO ya zama cikin
shiri." Mai masaba ya na gama fadin haka sai
ya juya cikin sauri ya bar Zangeru tsaye.
Zangeru na na tsaye yana kallon bayan
amininsa Mai Masaba, har sai da ya bace a
cikin duhun almurun. Zangeru ya juya ya
nufi gida zuciyarsa na ta sake-sake. Koda ya
fara tafiya, sai ya