Showing 9001 words to 12000 words out of 29993 words
Chapter 4 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf
tuna da farin dutsen dake
daure a gefen bantensa. Balbelar ta fado
masa a rai. Ga mamakin Zangeru sai ya ji
hannunsa ya kai ga dutsen. Zangeru ya
mulmula dutsen da yan yatsunsa sannan sai
ya yiwa kansa murmushi.
"Anya kuwa lokacin da zan bukaci taimakon
balbelar bai zo ba?" zangeru ya tambayi
kansa, sa'ar da ya sake mulmula dutsen.
***
Washegari da la'asar sakaliya Gimbiya
Hussaina yar sarki Sabitu ta yi hawa ita da
wasu amintattun kuyangin sarki Sabitu
shida, suka nufi wani makeken gandun
sarkin wanda ke dab da katuwar koramar
nan ta Dan masu. Wannan shi ne karo na
farko da Hussaina ta fita irin wannan kilisa
ta shakatawa tun bayan da mahaifinta sarki
Sabitu ya kwanta rashin lafiya.
"Kada ku takurawa kanku akan rashin
lafiyata, ku tafi ganduna ku shakata ko kwa
sami saukin damuwa." Sarki Sabitu ne ke
cewa yayan nasa biyu a safiyar ranar domin
ya fuskanci tun bayan da ya kwanta rashin
lafiya bai kara ganin su cikin walwala ba.
Wannan shi yasa Hussaina hawa ita da
kuyanginta, duk kuwa da cewa Hassan na
can tare da mahaifinsa bai yarda ya bisu ba.
Lokacin da Gimbiya Hussaina da kuyanginta
suka karaso cikin ni'imtaccen gandun, sai
suka tarar tuni har bayin sarki sun kafa
musu wata katuwar rumfa ta alfarma an
shimfide cikinta da tausasan kilisai da
matasan kai da fitilu masu hasken gaske
domin ga ala'ada sukan kai har dare wata
sa'ar basu koma gida ba. Wasu kuyangi guda
biyu masu dan siririn wuya kamar na
barewa suka akamawa Gimbiya Hussaina ta
sauko daga kan dokinta. Tana sauka sai duk
farfajiyar ta game da kamshin dake tashi
daga jikinta. Cikin takama fuskarta na annuri
ta nufi cikin rumfar ta cire katuwar
alkyabbar dake jikinta sannan sai ta dubi
kuyangin ta ce.
"Bari in gangara cikin fadamar can na yi
wanka, ku shirya mana kayan sha na dangin
zaki, kafin na dawo." Kuyangin suka amsa
cikin girmamawa.
Gimbiya Hussaina ta nufi katuwar fadamar
ma'abociyar sansanyar iska, da tarin
tsuntsaye. Tun daga nesa Hussaina ta ji sanyi
ya fara bugun fuskarta, ga mamakinta sai ta
ji duk da muguwar rashin lafiyar mahaifin
nata, ranta ya yi fari tas, musamman da ta
jiyo tsuntsaye sai rera wakoki suke yi cikin
muryoyi iri daban-daban.
Wannan katuwar fadamar ni'ima da
Hussaina ta nufa, tana da girman gaske,
kuma wani dan karamin bangare nata ya
shigo ta cikin gandun sarki sabitu sau da
yawa ma da ruwan koramar ne fadawa suke
ban ruwan shuke-shuken kayan zakin dake
gandun na sarki. Dan haka a yanzu da
Hussaina ta yiwa koramar tsinke, sai ta
dinga bin gefen koramar da ya fara tun daga
cikin gandun sarkin har zuwa waje.
Sannu a hankali Hussaina na tafiya a gefen
fadamar, kyawawan kafafunta na fantsamar
da ruwa a cikin ciyayin dake gefen koramar,
har dai ta kawo dai dai wata yar duhuwar
dogayen ciyayi wanda daga sune Hussaina
zata riski inda take so ta yi wankan, domin
duk sa'ar da ta zo gandun anan take wanka
ba dan komai ba kuwa sai don dalilai guda
uku. Na farko dai ruwan dake dab da
wannnan dogayen ciyayi tsabtataccene, na
biyu kuwa ruwan ba shi da zurfi a wannan
bangaren, babban dalilinta na uku kuwa shi
ne gurin yana da matukar sirri, domin
dogayen ciyayin sun zagaye bakin ruwan
sunyi masa dan karamin kuri, wanda in tana
wanka a gurin babu wani mahaluki dake
wucewa ta kusa da koramar da ya isa ya
hangota, sai dai in ya kusanci gurin sosai.
Wannan kuwa bai cika damun Hussaina ba,
domin har kullum idan ta zo wanka ta kan
ajiye kayanta ne a gabar koramar kusa da
inda zata iya daukarsu cikin sauri, ya Allah
koda za ta jiyo motsin zuwan wani.
Lokacin da Hussaina ta kawo dab da wannan
ciyayi ne to ta ji wani kwakkwaran motsi a
cikin ciyayin, Hussaina ta tsaya turus, ta ji
kirjinta ya harba to amma bata tsorata sosai
ba domin ta riga ta san babu wani abu mai
hadari tattare da koramar to amma da yake
tun da take zuwa koramar bata taba jin
motsin komai ba sai ya sata faduwar gaba.
Kudi da Maciji... (11)
Hussaina ta ayyana a ranta cewa motsin ya fi
kama da na wani abu mai girma.
"Me yiyuwa wani dan karamin naman daji ne."
Hussaina tace cikin zuciyarta
tsawon lokaci Hussaina na tsaye cak a boye a
bayan ciyayin ita bata yi gaba ba, ita ko bata yi
baya ba shiru-shiru ba a sake motsin ba, jin haka
sai Hussaina ta saki wani tattausan murmushi.
"Hussaina yar budurwa kin cika tsoro, kamar ba
yar sarki ba." Ta ce da kanta. Sannan cikin
takama da tabbacin babu kowa a gurin ta turar
da dogayen ciyayin ta nufi bakin koramar. Tana
shiga tsakanin ciyayin ne to ta hango shi zaune
akan wani dutse da ta saba zama ta tsame
ruwan dake jikinta a duk lokacin da ta zo wanka
bakin koramar. Hussaina ta yi turus tsakanin
ciyayin zuciyarta na harbawa tsakanin
hakarkarinta domin a zuciyarta ta dauka aljanine.
Saurayin dake zaune akan dutse dogone fari
kyakkyawan gaske na gani a fadawa sarki,
saurayin yana dauke da wani dan siririn fashin
goshi. Haka nan dauke yake da wani kyakkyawan
kanari ahanunsa.
Matasan biyu suka kurawa juna idanu na dan
lokaci. Hussaina ta ji zuciyarta ta dulmiya, cikin
sauri ta sunkuyar da kanta a tsorace bata iya ci
gaba da kallonsa ba.
"Kai amma fa wannan saurayin ko aljanine da
kyawu yake zita!" Hussaina ta ce cikin ranta. Ga
mamakinta sai ta ji nan da nan tsoron dake
zuciyarta ya gushe, sannan shaukin ta sake ganin
kyakkyawar fuskar ya maye gurbin wajen. A
hankali sai Hussaina ta sake dago kai domin ta
sake kallon fuskarsa. Tana dago kai sai saurayin
ya yi mata murmushi. Sannan ga mamakin
Hussaina sai ta ji saurayin ya ce cikin wata
tattausar murya.
"Ki yi hakuri ranki ya dade, ga dukkan alamu na
tsorata ki ko?" Hussaina ta dada kallon
kyakkyawan saurayin, batare da ta shirya ba sai
ta ji murmushi ya subuce mata, lokaci guda kuma
ta girgiza kai ta ce masa.
"Uhm-Uhm...ai ba wani tsorata sosai na yi
ba...kawai dai ban taba tsammanin ganinka a nan
bane."
Dogon saurayin ya mike tsaye akan dutsen, kana
ya gyarawa kanarin dake hannunsa riko ya ce.
"Ni ma tsautsayine ya kawoni ranki ya dade,
wannan tsuntsun dake hannuna shi na biyo, da
kyar na kama shi."
Gimbiya Hussaina ta yi shiru tana sauraron
saurayin. Akwai wani amo da muryarsa ke yi
wanda yake burgeta.
"Idan kin yi min izini ranki ya dade ni zan tafi
daman abin da ya kawoni kenan kuma na
kamashi."
Ya dada nuna mata kanarin. Hussaina ta yi sauri
ta girgiza kai.
"Kada ka damu, ni baka yi min laifin komai ba."
Ta dan yi shiru tana dubansa.
"Na gode ranki ya dade, Allah ya karawa sarki
lafiya." Hussaina ta dube shi cikin mamaki ta ce.
"Anan garin kake ne?" Saurayin ya gyada kai.
"Ni talakanki ne ranki ya dade, gidanmu na nan
daga karshen gari mahaifina...manomi ne." Ya ce
da ita bakinsa na rawa.
"Amma kuma ban taba ganinka ba?" Hussaina ta
tambaye shi cikin mamaki.
"Ai ban cika zama agida ba, wani lokacin ma sai
na yi wata guda ko fiye da haka bana gari....ni
mafaraucine kusan duk rayuwata a cikin daji
take."
Jin haka sai ya burge Gimbiya Hussaina, dan
haka cikin sauri sai ta dago kanta ta yi masa
kallon girmamawa ta ce.
"Lallai ka isa jarumi...ni kuwa babu abin da na fi
so a duniya kamar jarumi." Ta dan yi shiru
sannan sai ta matsa dab da dutsen da yake tsaye
ta dubeshi da tattausan murmushi.
Dan saurayin yayi sauri ya sunkuyar da kansa
kasa sa'ar da ta matso dab dashi, haka nan
kwarjininta duk ya daddaure masa jijiyoyin jiki, to
amma duk da haka ya yi matukar jin dadin yabon
da ta yi masa na jarumi.
"Yaya ka yi shiru, ai gara ka sauko daga kan
dutsen ko, ko kuwa kafi son ka yi ta tsayuwa
akai?"
Jikinsa na rawa saurayin ya sauko daga kan
dutsen ya tsaya a gaban gimbiya Hussaina
kanarin rumgume a kirjinsa. Wata sassanyar iska
ta huro daga cikin fadamar ta fara fifita matasan
biyu saurayin ya ji wani ni'imtaccen kamshi ya
bugi hancinsa. Matasan biyu suka kurawa juna
idanu na tsawon lokaci, suna kallon bambancin
ajin dake tsakaninsu na yar sarki da dan talaka,
haka nan zuciyoyinsu na masu fargabar rikicin da
suke kokarin jefa kansu.
Hussaina ce ta fara ajiyar zuciya ta dube shi ta
ce.
"Amma kanarin nan naka na da kyau, ban taba
ganin irinsa ba." Saurayin ya yi mata murmushin
yake.
"Ko kina sonsa ne?" Hussaina ta gyada kai da
murmushi.
"Na dade ina son na yi kiwonsa a gida, da za ka
bani shi da na fansheshi da zinariya." Cikin sauri
sai saurayin ya mika mata tsuntsun.
"Gashi ranki ya dade na baki shi kyauta....tsaka
nina da ke babu ciniki." Gimbiya Hussaina ta
karbi kanarin cikin mamaki.
"Wai shin da gaske kake yi?"
"Tsakanina dake babu tsokana ko wasa ranki ya
dade." Saurayin ya bata amsa.
"Na gode madalla da wannan kyauta da ka yi min
ba zan taba mantawa da kai ba."
"Farin cikinki, farin cikina ne ranki ya dade."
Hussaina ta ji dadin abin da ya ce cikin zuciyarta.
"Ka ce kai mafaraucine ko?" Saurayin ya gyada
kai.
"Yanzu yaushe za ka koma?" Saurayin ya
sunkuyar da kai ya ce.
"Ni da asan samuna ne ma yau zan koma daji da
daddare."
Kudi da Maciji...
Part (12)
Ga mamakin saurayin sai ya ga yar sarkin ta
sunkuyar da kai cikin damuwa tana jujjuya
kyakkyawan kanarin dake hannuta. A zuciyar
saurayin ya ce.
"Kanarin ma har yafi dacewa da ita fiye dani, dubi
yadda ta rikeshi sai suka yi kyau a tare tamkar
taurari biyu karama da babba."
"Dole ne sai ka koma yau din?" Gimbiya Hussaina
ta tambaye shi. Saurayin ya girgiza kai ya ce.
"Ba dole bane ranki ya dade, amma in da zai
sami yadda nake so dai nafi son na yi tafiyata
yau domin zaman gida shi ke mayar da mutum
rago."
"Ni kuwa da asan samuna ne zan so mu sake
haduwa anan bayan kwana biyu." Saurayin ya ji
gabansa ya fadi ris! Tutuni ya rigaya ya sani
cewa rayuwarsa na cikin hadari, domin yana
tattare da masaniyar cewa kyakkyawar budurwar
dake tsaye gabansa yar sarki ce.
"Ko kuwa baka son ka kara ganina ne?"
Hussaina ta ce dashi cikin rarraunar murya sa'ar
da ta ga ya kasa magana. Cikin sauri sai
saurayin ya girgiza kai ya ce.
"Duk duniya babu wanda ya isa ya ce baya
kaunar ya sake ganinki ranki ya dade." Hussaina
ta ji wani dadi ya lullube mata zuciya, dan haka
sai ta dada matsowa kusa da shi ta ce. Cikin
murmushi.
"Zan fi jin dadi a zuciyata idan ka kirani da
sunana Hussaina maimakon ranki ya dade." Ta
dan yi shiru tana kallonsa da dara-daran idanunta
farare masu jirkita hankalin mazajen duniya.
"Gashi kuma har zamu rabu ban san sunan
wanda ya yi min kyauta ba." Saurayin ya dago da
kai a kunya ce bakinsa na rawa ya dubi
kyakkyawar fuskar yar sarkin ya ce.
"Sunana AMADI DAN ZANGERU!"
***
ZANGERU ya dubi MAKWARO a cikin hasken farin
watan, kana ya yi kaki ya tofar a cikin tarin
ciyayin dake dab dasu cikin damuwa.
Na rasa abin da ya hana mai Masaba zuwa
Zangeru ya ce da makwaro lokaci guda kuma ya
sake duban yar siririyar hanyar da ta bi ta bayan
gidansa har zuwa cikingari.
"Me yiyuwa ko sarkin dogaran ne ya hana shi
tahowa ka fa san shi da shegen surutu."
Makwaro ya ce.
Mutanen biyu dake zaune cikin duhun daren suna
jiran mai Masaba tun kafin shigowar almuru suke
gurin, domin kowannensu tattare da masaniyar
cewa yau ce ranar da Mai Masaba zai zo musu
da karin bayanin karshe a game da gaggarumar
satar da suke shirin yi.
Wannan mutum dake zaune kusa da Zangeru
sunansa Makwaro. Dan gajerene mai fadi a
dunkule yana da katon kai kamar murhu, hakanan
idanunsa yan mici-micine kamar idanun maciji,
bakinsa tsakakkene kamar gidan tsutsa. Yana da
faffadan hanci tababbe wanda ya mamaye kusan
rabin fuskarsa hakanan ya sa duk kusan yan
matan garin suka tsane shi. Tun makwaro yana
saurayi bai taba yin budurwa ba, kuma har
yanzun nan da yake dan kusan dan shekara
arba'in da daya bashi da aure, sai tarin muguwar
bakar zuciya wacce ta sa kusan kullum makwaro
a cikin kunci yake da bacin rai, akwai sa'ar ma
da shi kansa yake jin haushin kansa da kansa.
Tun sa'ar da uwar Makwaro ta haifeshi ta bar
duniya, mahaifinsa shi ne sarkin maharban garin,
har ya mutu bai taba kuskuren harbin duk naman
dajin daya sa a gaba ba sai sau daya jal! Shima
wannan hannunsa ne ke ciwo. Duk wani salon iya
harbi kwari da baka na mahaifinsa, sai da
Makwaro ya hardace shi har ma yafi mahaifinsa
ko dan yatsa ka daga masa zai iya harba da
kibiya babu kuskure, wasu ko suka ce wai ko
kurciya ce ta zo wucewa ta sama idan yada
gama yana iya harbin tsinin bakinta ba tare da ya
kuskure ba, An ce kuma wai wani shakiyin kauye
ya taba cewa da makwaro in har shi ya isa mai
iya harbi, to ya bari sai kakansa ya hau saman
bishiya saran ita ce, Makwaron ya sa kibiya ya
harbi saman hancin tsohon amma kada jini ya
zuba sosai. Haka kuwa aka yi Makwaro ya harbi
tsinin hancin, to sai dai kuma abin yazo da ajali
domin tsohon ko kwana bai yi ba ya ce ga
garinku nan.
Wannan da kuma wasu dalilan na kwarewar
Makwaro a fagen iya harbi su suka sa Zangeru
da Mai masaba suka zabe shi a matsayin cikonsu
na uku a shirin wannan gagarumar sata da suke
shirin yi. Zangeru ya riga ya dade da sanin cewa
Makwaro ma kwararren barawo ne, to sai dai
kuma shima kamar su har yau satar bata tsinana
masa komai ba dan haka sa'ar da Zangeru ya
tunkare shi da batun satar sai Makwaro ya kada
baki ya ce.
"Daman kullum fatana kenan, na yi gagarumar
satar da duk labarinta zai watsu a duniya."
wannan shi ne halin Makwaro, har kullum ya fi
son neman suna fiye da abin duniya.
Mutanen biyu suka ci gaba da zama cikin duhun
daren, fuskarsu sai naso take da gumi kamar
waina, kowannensu na sakar zuci.
"Ko jirana zaka yi anan na bi bayansa".
Zangeru ya ce da Makwaro. Makwaro ya mirgina
uban kansa mai kamar masaba ya ce.
"Ka ji kamar motsin tafiya ma nake ji ka ji ko..."
mutanen biyu suka yi fakare suna saurare kamar
zakaru. Tabbas sautin tafiya ne. Ba a dade ba
kuwa sai suka hango zabgegiyar surar Mai
Masaba a cikin dan hasken farin watan, yana tafe
cikin sauri, inda su Zangeru suke zaune kusa da
wata tsohuwar rumfa ce da ta gaji da tsayuwa ta
fadi.
Shekara da shekaru an rasa mai dogara mata ta
tashi.......
Kudi da Maciji... (13)
Lokacin da mai Masaba ya zo wucewa ta
kusa dasu bai gansu ba, domin shi duk a
tunaninsa a gida su Zangeru zasu yi jiransa.
Yana zuwa dab da gurin sai ya ji muryar
Zangeru ta ce.
"Ga mu anan, tun dazu kai muke jira." Mai
Masaba ya yi turus! Sannan ya juya gami da
kashe idanu a cikin dan hasken farin watan,
sannan ne to ya hangi mutanen biyu kamar
aljannu rakuye a bayan tsohuwar rumfar.
Mai masaba ya matsa kusa dasu kana ya saki
wani tattausan murmushi, sa'ar da ya hangi
katon kan Makwaro.
"Ashe kune anan". Mai masaba ya ce, sannan
ya zauna a kusa dasu.
"Ya ya ake ciki, bamu labari mu sha tun kafin
almuru muke nan make muna jiranka ni da
har na fara shawarar binka ma."
Mai masaba ya wangame baki kamar kada ya
yi wata doguwar hamma sannnan ya dube
su ya ce.
"Samun labarin babu wuya. Domin tun
la'asar mutumin namu sarkin dogarai yazo
shi da wasu fadawa daukar akwatin. Ka
sanshi da son banza, da man tun kafin ya zo
na sa matata Habi ta dama masa fura ta
zuba masa zuma a ciki. Ai yana fara shan
furar nan sai ya fara zuba kamar ruwan
sama, ni ko damar bugun cikin nasa ma ban
yi ba har sai da ya amayar min da komai."
Mai masaba ya dan yi shiru yana susar kugu.
Dan tsawon lokaci sannan sai ya ci gaba da
cewa.
"A cewar sarkin dogarai su shida ne za su
raka akwatin, kuma jibi da daddare bayan
isha za su tashi, to sai dai kuma akwai wani
abu da ke tattare da tafiyar wanda mu ba
mu yi tsammaninsa ba." mutanen biyu suka
dubi mai masaba sa'ar da ya yi shiru.
"Kamar me kenan kake nufi?" Zangeru ya
tambayeshi. Mai masaba ya yi atishawa ya
ce.
"Akwai yara guda biyu matasa yayan sarki
da su za a yi tafiyar." Mai masaba ya dubi
Zangeru sa'ar da ya fadi batun. A karo na
farko sai Makwaro ya girgiza katon kansa ya
ce.
"Menene abin damuwa dan zasu tafi da
wasu matasa? Ba sai na yi maganinsu ba. Ni
abin da kawai ma yafi damuna shi ne idan
mun kwace akwatin a ina zamu boyeta kafin
kura ta lafa, kun san fa da zarar mun yi
nasara duk hankulan sarakunan yankin nan
zasu tashi musamman ma aminan sarki
Sabitu, bincike na farautar mu zai tsananta
don haka dole ne mu san inda zamu boye
akwatin kafin kura ta lafa." jin haka sai
Zangeru ya dubi mai masaba ya ce.
"Makwaro fa yazo da babbar magana me
kake gani za a yi?" Mai masaba ya dube su ya
ce.
"Ai wannan mai sauki ne, ni daman tuntuni
na gama tunanin wannan matsalar har ma
na gama maganinta a zuciyata."
"Menene to maganin matsalar!" Suka
tambaya baki daya cikin doki. Mai masaba ya
kaiwa kakkauran wuyansa duka da tafkeken
tafin