Showing 15001 words to 18000 words out of 29993 words
Chapter 6 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf
baraden sarki suka sami damar
harbowa ce ta huda bantensa ta kuma dan
soke shi kadan a kugu. Babu mamaki tashin
hankaline ya hana shi jin sukar kibiyar tun
farko. Zangeru ya yi kamar ya jefar da
kibiyar da ya zare daga kugunsa, can kuma
sai ya fasa, lokaci guda kuma ya ji wani
zazzafan gumi ya fara wanke masa fuska. Ya
sha jin labarin cewa duk kibiyoyin dake
kwarin baraden sarki a shurbune suke da
masifaffen dafi wanda duk wanda ya soka
ba zai rayu ba.
Daga inda zangeru yake tsaye yana iya
hangen faffadan bayan Mai Masaba wanda
ke gangarawa a hankali ta tsakanin
duwatsu.
"Kyakkyawar budurwar yarinya ce karama,
bai kamata ta mutu tun yanzu ba, ni kuwa
tawa ta kare, kamata ya yi mu wuce lahira ni
da babban abokina." Zangeru na gama fadin
haka sai ya shafi kugunsa inda kibiyar ta
same shi. Bai yi mamakin jin gurin tuni har
ya fara kumbura ba. Ya ji wani zafi ya soki
kugun kamar ana hura masa wuta. Yanzu
kam ya tabbata dafi ne a jikin kibiyar.
Zangeru ya jinjina kibiyar a hannunsa,
sannan sai ya dana ta, ya daga kwarin sama
ya saita faffadan bayan babban abokinsa Mai
masaba, sannan sannu a hankali ba tare da
wata nadama ba domin ya san ceton rai
yake yi sai ya saki kibiyar CUL!
By nazir adam salih
Kudi da Maciji... (17)
***
Lokacin da Zangeru ya dawo bakin katuwar
koramar ta Danmasu, tuni har gari ya gama
wayewa. Yayi sa'a bai hadu da kowa ba sai wata
tsohuwa mai sammakon tsiya dake bayan gari a
musissika dake daf da koramar tana shikar gero.
"Sannu da zuwa bawan Allah." Tsohuwar ta ce da
Zangeru sa'ar da ta ganshi tafe bisa katon dokin
dauke da akwatin karfen yana tafe yana layi
kamar zai fado daga kan dokin, sakamakon dafin
kibiyar da ke daukarsa. Zangeru bai ko dubi
tsohuwar ba, ya wuce kai tsaye zuwa can cikin
koramar jikinsa na ta rawar dari sakamakon
mummunan zazzabin dake addabarsa, lokaci
guda kuma zuciyarsa na ta tunanin halin da
Hussaina take ciki.
Lokacin da Zangeru ya tabbatar ya harbe babban
abokin satarsa Mai masaba, ya gangaro daga kan
dutsen yana layi, ya shigo har inda tawagar
baraden sarkin suke duk a kwankwance, kuma a
marmace. Bayan da ya tabbatar babu mai wani
sauran numfashi, sai ya fara laluben inda
Hussaina take, ya dade yana lalube kafin ya gano
ta karkashin wani lankwasasshen dutse mai siffar
bil'adama tana kwance a sume. Zangeru ya
jujjuyata na dan lokaci ya tabbata suma ta yi ba
mutuwa ta yi ba sannan sai ya dafa ta ya yi abin
da rabonsa da yi tun yana karami, addu'a.
"Allah kareki kyakkyawa, Allah sa fatake su
tsinceki." Yana gama fadin haka sai ya nufi inda
nan, dokin akwatin dukiyar yake, ya yunkura ya
haye bisa dokin, ya juyo ya kalli gawarwakin
kallon karshe sannan sai ya karkata linzamin
dokin ya bi ta kan gawar babban abokinsa
marigayi Mai masaba ya koma da baya.
Dan haka a yanzu da Zangeru ya zo bakin
korama sai ya hangi wata doguwar bishiyar
giginya dake gangare. Ba a nan ya so ya tsaya
ba, to amma da yake jikinsa ya gama yin rauni
sai ya sauka a gurin. Bai yi mamakin jin
kafafunsa sun kasa daukar nauyinsa ba. A haka
sai ya fadi a gurin zaman yan bori, bai damu ba
domin tuni ya shirya abin da zai yi cikin
zuciyarsa. Jikinsa na rawa ya lalubi inda ya kulle
farin DUTSEN NAN a cikin bantensa, ya kunto
dutsen, sannan sai ya sa dutsem tsakanin tafin
hannunsa biyu ya murza.
"Gani Zangeru, me kake so masoyina." Farar
balbelar ta ce sa'ar da ta bayyana a gabansa.
Zangeru ya dubi balbelar yana haki bakinsa na
rawa ya ce.
Dan lokacin da ya rage min a duniya kadan ne,
shi yasa na neme ki domin ki yi min taimakon
karshe kuma mu yi sallama kafin na mutu."
"Me kake so?" Zangeru ya dubeta ya ce kai
tsaye.
"So nake ki sa yan uwanki aljanu su tona rami..
PAGE DIN NAN YA YI (damage) zamu tsallake...
Shima jiya Allah ya yi masa rasuwa. Ina son ki
layar nan da kyau ko da Allah bai kaddara aurena
da ke ba, ina son idan kin haifi da ko ya ke ma ki
basu layar domin na fada miki maganin tsautsayi
ce sosai, don da ita mahaifina ya yi ta amfani har
iya rayuwarsa." Hussaina ta dubi Amadi a razane
da jin abin da ya ce lokaci guda kuma ta dubi
layar da yake mika mata ta ce.
"Me ya sa kake irin wadannan maganganun? Wa
ya ce ma ba za ka aureni ba?" Amadi ya dubeta
cikin damuwa ya ce.
"Ke kin san abin ne da wuya Hussaina..." Ta kate
shi.
"Amadi, shi yasa na ce ka mayar dani gida domin
idan mun je zan ce da mahaifina kaine ka ceci
rayuwata a hannun barayin....na san tabbas idan
ya ji haka na nuna ina kaunarka babu abin da zai
hana ya aura min kai."
Tabbas maganar da ta fada ta yiwa Amadi
ma'ana, to amma duk da haka sai ya dada mika
mata layar ya ce.
"To gashi dai ki rike layar a gurinki, idan Allah ya
sa kin aureni din idan mun sami da ba sai mu sa
masa ba."
"Me yasa to kai ba zaka rike layar a gurinka ba?"
"Saboda maganin tsautsayi ce na fi son na ganta
a gurinki. Bari na sa miki ita." Kafin ta rufe baki
Amadi ya rataya mata layar a wuya, sannan sai
ya dubeta ya ce.
"Zo mu tafi." Hussaina ta juya hawaye na zuba
akan fuskarta ta yiwa gawar dan uwanta ganin
karshe sannan sai ta juya gami da dafa layar
dake makale a wuyanta ta bishi a baya.
Koda suka fara tafiya sai suka ji haniniyar doki a
bayansu. Hussaina ce ta fara juyawa cikin
mamaki. Dokin ya yi haniniya sa'ar da ya fito
daga cikin duwatsun sannan sai ya nufo inda
suke.
"Lah! Allah sarki ashe kaima Allah bai kari
kwananka ba." Amadi ya juyo ya dubeta ya ce.
"Wanene?" Hussaina ta nuna masa shi da hannu
ta ce.
"Dokina ne da nazo a kansa." Amadi ya ji wani
dadi ya lullubeshi a karo na faro, domin babu abin
da ya tsana irin ya ga Hussaina ta taka a kasa
har zuwa garinsu mai nisan tsiya daga gurin.
"Na gode Allah da ya kawo miki abin hawa."
"Kai fa ba zaka hau ba." Amadi ya girgiza kai ya
ce.
"Kada ki damu dani. Ke dai dafe layar nan dake
wuyanki kada ki jefar da ita idan kin zo hawa
dokin...me yiyuwa ki na cika mita akan layar nan
ni kuma abin da ya sa nake ta magana a kanta
saboda na san maganin tsautsayi ce."
KARSHEN BOOK1
Kudi da Maciji... (18)
>>>> Book (2) <<<<
Ga doki har doki, amma kofaton na sakaina. yar
budurwar tace cikin zuciyarta a sanyaye sa'ar
data dubi kanta a jikin dogon mudubin dake
fuskantarta. Ba wani abune yasa ta fadi hakan ba
sai hadin bautar ban haushin data gani a jikin
madubin. Gashi dai kyakkyawace doguwa mai
tsukakkiyar mara fatar jikinta a mulmule tana
sheki kamar kwalba a rana, hakanan dan iskan
can da a kullum sai ya gallabeta a makaranta
yasha cewa da ita.
"Kai!! Bebe wallahi ina son (Skin) din nan taki,
gata dai ita ba fara ba, ba baka ba kuma ba
jaba... (See you eyes) kyawawa juyayyu masu
firgita lakcarori yayin daukan darasi, ga kuma
fatan bakin ki (Looks very soft) tattausa shi yasa
kullum nake kaunarki ke wallahi da ni malamin
jami'a ne da har ki gama bake ba faduwa".
To amma duk da irin wannan kyawun nata sa'ar
da ta dubi madubin sai taji ranta ya gama baci,
badan komai ba kuwa sai dan yaroki-yarokin
tsummokaran dake jikinta bana fita kunya a
farfajiyar makaranta bane. Gata dai a tamfar ba
wata mai tsada bace kamar buhun busasshen
zogale, ta kokkode ta jeme kamar labulen
laburari, hakanan dan siririn kallabin dake dafe
akan kyakkyawan goshinta shima duk ya ji jiki
yayi shara-shara kamar buhun algarara, ga kuma
uwa uba abin dake dada bata mata rai a kullum
wato bangwaleliyar LAYAR dake makale kullum a
siririn wuyanta. Wannan laya tana matukar bata
mata rai, ta tsani layar nan kamar yadda ta tsani
dan iskan saurayincan na makarantarsu mai
takurawa rayuwarta a kullum.
Yar budurwa ta sake kallom kanta a jikin madubi
cikin takaici sannan sai ta shafi tsohuwar layar
dake wuyanta wacce a cewear masifaffiyar
marikiyarta wai layar ta dade a duniya kuma
waita gado ce, tun daga can wajen kakanninta na
farko ake ta gadonta har zuwa kanta. To koma
dai ta mecece ita kam wannan budurwa ta tsani
wannan laya, gashi dai ita ba wata suturar kirkice
da ita ba, kullum taje makaranta a rarrabe take,
bata iya shiga cikin kawayenta, badan komai ba
sai dan ganin su kullum tsaf suke cikin sutura
mai tsafta, amma ita kullum cikin tsumma, ga
kuma wata layar masifa an makalamata a
wuya.... To yanzu in ba son a muzantani ma
wane yaro ne a wannan zamani za'ce wai dole
sai yasa laya. Hawaye ya fara surtu a kyawawan
kumatunta yarinyara sa'ar data fara kokarin tura
layar cikin rigarta.
"kukan me kuma kike yi A'ISHA?" wata fikakkiyar
murya tace da ita daga baya. Aysha ta juya
firgigit tadubi mai rikonta jikinta na rawa.
"Ma......ma ba komai"
"Ba komai kamar yaya? Amma kuma ba komai
din kike kuka, ke dai wallahi Aysha kin shiga uku
da gulma, shegiya masifaffiya uwar jaye-jayen
magana wato yanzu tsakanina da ke ma abin har
ya kai ga sharri ko? Yanzu idan wasu dangin
namu suka shigo gidannan ai sai suce cutar
maraya nake to Allah ya gani dai tsinanniya
tunda iyayenki suka mace na daukeki ina faman
wahala dake ashe bakar jaraba na dauka to kyaci
kanki ba dai ki cinye niba zaki tashi ki tafi
makarantar ko kuwa sai na karaso naci ubanki a
nan in yaso kiyi kukan da dalili?".
Aysha ta mike a tsorace sannan ta dauki jakarta
dake kan kujera cikin sauri ta fice daga dakin
tanagoge idanu.
"saura kuma ki dawo na ga kin jefar da wannan
laya wallahi na lahira sai ya fiki jin dadi yar iska"
matar tace da ita tana bambami.
Aysha bata amsa ba sai ta fice tana kuka.
Karfe tara da kwata ta isa jami'ar, tuni tasan an
fara daukar darasi, kuma tana tattare da
masaniyar cewa muddin dalibi ya kara mintuna
goma sha biyar to bashi ba shiga dakin darasin
musamman ma idan Dafta Bashir ne ke koyarwa.
Tunanin hakan da kuma gudun kada taje shiga
dakin karatun Dafta bashir ya muzantata a gaban
dalibai, shi yasa Aysha ta karkata tabi ta cikin
inda ake fakin da motocin daliban, domin nan ne
kawai zata bi ta iya zuwa dakin kwanan dalibai
mata dake jami'ar. Ko banza dai, Aysha tace cikin
zuciyarta. Idan na je dakin kwanan daliban na
dan wanke fuskata na gyara kwalliyata, kafin
Dafta bashir ya fice daga ajin in yaso na halarci
darasi na gaba.
A haka Aysha ta kutsa ta tsakanin tarin motocin
burjuk kamar fari dake farfajiyar makarantar,
wanda mafi yawa daga cikin motocin duk na
dalibai ne. A dai-dai lokacin da take kokarin
wucewa ta kusa da wata marsandi ne to taji an
rike jakar dake rataye a kafadarta ta baya. Aysha
ta juya a fusace.
"Sannu da zuwa Aysha kema a makare yau kika
zo?"
Aysha ta dubi mai magana cikin takaici tace a
fusace.
"Dan Allah me yasa ne kullum kake son takurawa
rayuwata!!"
"Ki gafarce ni Aysha wallahi so nake kawai mu
gaisa, dan nasan idan muka shiga dakin karatu ba
saurararata zakiyi ba".
"Kuma dan kana so mu gaisa sai ka rikemin
jaka? Kai baka jin kunyar mutanen dake kallon
ka, duba fa can, da nan ko'ina duk dalibai ne
amma sai ka....."
"Aysha, kar ki zama kamar wata yar sakandare
mana (Remember) fa yanzu a jami'a muke ba
ruwan kowa dan haka idan ina soma (I can kiss
you, I don't care)".
Kudi da Maciji... (19)
"Allah ya yi min tsari da kai!" Aisha ta ce a
tsorace sannan ta fara ja da baya za ta wuce
shi.
"Aisha! Saurayin ya kira sunanta a tausace.
Ta sake juyowa a hankali kyakkyawar
fuskarta a murtuke ta ce dashi cikin
shisshika.
"Dan Allah dan Annabi ni ka kyaleni na huta,
ka takurawa rayuwata, tun da na zo
makarantar nan kake ta damuna da
maganganu marasa ma'ana na rashin kunya,
to ni na gaji, ka je ka nemi daidai da kai ni ba
yar kowa bace dubeni fa?"
Ta daga hannu ta nuna masa tsummakaran
kayan dake jikinta. Menene abin sha'awa a
jikina, tsummokaran ko me?"
Saurayin ya zura mata idanu na tsawon
lokaci yana kallon bangwaleliyar layar dake
wuyanta, baya ko kiftawa tamkar malamin
kimiyya mai nazarin kwayoyin halittun cikin
ruwa.
"Aisha, direshi kawai suka fiki ba kyau ba,
amma nitun da nake ban taba ganin wacce
nake kauna kamar ki ba, amma ke kin
tsaneni, kullum ina lura da ke da na yi miki
magana sai in ga kin hada rai kamar kin ga
mutuwarki, sai kuma ki yi ta wulakantani."
Gaban Aisha ya fadi sa'ar da ta ji ance ta yi
wulakanci.
"A'a...ka yi hakuri ni ban iya wulakanci ba...ni
irin maganganunka ne bana so."
"To daga yau ban kara yi miki su, amma
kauna ban iya dainawa Aisha kin shiga
rayuwata har abada!"
Aisha ta sunkuyar da kai tan wasa da yan
yatsunta, sannan sai ta dago kai matasan
biyu suka dubi juna na dan lokaci. Saurayin
ya sake kurawa layar dake makale a
wuyanta idanu zuciyarsa cike da mamakin
dalilin da ya sa wannan kyakkywar budurwa
yar jami'a guda take yawo kullum da laya a
wuya. Tun shekarar karatunsa ta farko a
jami'ar yake ganinta da bangwaleliyar layar,
da yawa daga cikin abokansa sun sha cewa
dashi.
"Kai bebe din nan karshe ce duk fakalti din
nan babu mai kyanta, amma rashin diresin
da katuwar layar nan da ke wuyanta shi ya
bata lamarin bayaninta."
Aisha ta yi sauri ta rufe layar da tafin
hannunta sa'ar da ta lura da irin kallon da
saurayin ke yi mata. Sannan sai ta juya tana
cewa da shi.
"Sai an jima ko?" Saurayin ya yi murmushi
cikin jin dadi domin tun da yake bata taba
cewa da shi sai an jima ba.
"Aisha...a dawo lifiya. Idan an tashi kuma,
zan so ki bani labarin wannan layar da ke
wuyanki."
Fuskar Aisha ta sauya launi sa'ar da ta ji abin
da ya ce.
"Babu ruwanka da layata." Aisha ta ce da shi,
ba tare da ta tsaya ba. Tana gama fadin haka
sai ta dada sauri ta nufi dakin kwanan
dalibai wanda dole ne sai ta bi ta tsakanin
wani dan karamin daji-daji kafin ta kai
dakunan.
Lokacin da Aisha ta biyo ta yar siririyar
hanyar kusan ita kadai take tafiya domin
duk kusan dalibai suna dakunan karatu suna
daukar darasinsu na ranar.
A daidai lokacin da ta kawo kusa da wasu
dogayen bishiyoyin turarene to ta ji an yi
kiran sunanta a baya.
"Aisha!"
Cikin sauri Aisha ta juyo a tsorace domin
muryar ba ta yi kama da ta mace ba, haka
nan kuma ko shakka babu muryar bata yi
kama da ta namiji ba. Sautin muryar ya fi
kama da sautin muryar da aka yi amonta ta
cikin bututun roba.
Aisha ta dafa kirji sa'ar da ta juyo tana
waige-waige cikin fargaba domin bata ga
kowa a bayanta ba sai wani famfo dake
zubar da ruwa shi kadai a cikin tarin ciyayin
dake karkashin bishiyoyin turaren gami da
wata kyakkyawar balbela fara mai dogon
wuya da tsinin baki, tana karkada fuffukenta
cikin nishadi.
Aisha ta yi sauri ta gyara jakar dake kokarin
subucewa daga kan kafadarta domin duk
ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari,
sannan lokaci guda kuma ta fara waige-
waige a rude.
"Shin ko ba sunana naji an yi kira bane?"
Aisha tace cikin zuciyarta. Daga inda take
tsaye tana iya hangen dalibai mata a can
nesa da ita a kofar (hostel) din, hakanan
kuma tana iya jiyo hayaniyar dalibai sama-
sama acan cikin makarantar inda dakunan
darussa suke.
"Lallai kam me yiyuwa kunnena ne yake fada
min karya." Aisha ta sake cewa zuciyarta.
Dan haka sai ta sake juyawa gami da yiwa
kanta murmushi.
"Aisha yar yarinya ke dai kin cika tsoron
tsiya wallahi." Ta ce da kanta.
Tana juyawa gaba ta fara tafiya sai ta ji an
sake cewa a bayanta.
"Aisha dake fa nake." Aisha ta yi mutuwar
tsaye domin ko shakka bata yi ta san
sunanta ne aka kirawo a wannan karon.
"Wa...nene!" Aisha ta juyo tana fadi a razane
domin har yanzu ba ta ga mai kiran ba sai
farar balbelar nan dake kan famfon nan mai
tsiyayar da ruwa tana dubanta.
"Ni ce Aisha, kada kuma ki ji tsoro na ni mai
kaunarki ce." Farar balbelar ce ke magana da
Aisha ko shakka babu.
Aisha ta yi tsalle gefe guda a razane ta dubi
balbelar idanunta kamar za su fado a kasa
saboda tsabar kadawa. Balbela da magana,
na shiga uku!! Aisha ta ce cikin zuciyarta.
Hannayen Aisha suka dauki rawa kar! Kar!!
Kar!! Jakar dake kafadarta ta kwace ta fadi
akan tarin ciyayin. Nan da nan iska ta fara
fatali da yan takardu da kuma litattafan
Aisha a cikin ciyayin.
Dauki jakarki Aishata ba cutarki zan yi ba,
tsakanina da duk danginku sai dai kauna.
Kudi da Maciji...
Part (20)
Na san tuni kin fara tunanin ko ni aljana ce, to
tabbas haka ne ni aljanace kuma na dade ina tare
da danginku yau kusan shekaru dari da ashirin
kenan, don haka ki saki jikinki Aisha so nake na
baki wani dan bayani a game da layar dake
wuyanki domin na ga kina cikin wahala da
tsananin rayuwa."
Aisha ta dubi farar balbelar ta ce.
"Baiwar Allah, dan Allah ki yi hakuri ki barni na
koma da baya zuwa cikin makaranta wallahi