Showing 18001 words to 21000 words out of 29993 words

Chapter 7 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf

12 Jul 2025

1238

ban
san cewa nan hanyarku bace da ba zan biyo ba."
"Kada ki ji tsoro Aisha ba laifi kika yi min ba, ina
son kuma ki kwantar da hankalinki ki daukeni a
matsayin uwa kamar yadda wani daga cikin
kakaninki na can baya ya daukeni shekaru dari da
ashirin da suka wuce." Balbelar ta ce tana
mimmike dogon wuyanta.

"To, baiwar Allah yanzu me kike son yi dani
kuma?" Aisha ta ce jikinta na kyarma.
"Abin da nake so dake Aisha shi ne idan kin je
gida yau, ki shiga daki ke kadai sannan ki cire
layar da ke makale a wuyanki ki warwareta domin
akwai wani tsohon sako na kakanki na can baya
ya barwa wani daga cikin yayansa, amma basu
sami damar budawa ba domin sun dauka layar
maganin tsautsayi ce. Abin da basu sani ba shi
ne, layar ba maganin komai bace sakone aka
rubuta a ciki tun tsawon shekaru dari da ashirin
din da suka wuce sakon yana rufe har yau ba a
sami wanda ya karanta sakon ba. To amma yau
ina son ki warware layar ki karanta sakon da
yake ciki domin arzikinki yana cikin layar a
nannade."
Farar balbelar ta yi shiru tana duban Aisha wace
hannayenta biyu ke dafe da layar da ke makale a
wuyanta.
"Aisha na ga kamar kina shakkar abin da nake
cewa. Ina son yanzun nan ki warware layar a
gabana ki karanta koda sidira biyu ce domin ki
tabbatar da abin da nake fada miki."
Cikin rawar jiki sai Aisha ta ciro layar dake
wuyanta, ba wai dan ta yi imani da abin da
balbelar ta fada ba, sai don a tunaninta idan taki
bin umarnin aljanar mai siffar balbela za ta iya
halakata. Cikin abin da bai fi mintuna biyu ba,
Aisha ta warware layar da kyar tana gumi sannan
a hankali kamar mai yin tiyata sai ta fara
warware rubabbiyar takardar, ba a dade ba ta
warware layar baki daya sannan ne to ta dubi
wasikar cikin kaduwa da kuma mamaki.
Rubutun wasikar da AJAMI na Larabci aka yi shi
bada rubutun Hausa ba. Aisha ta dago kai gumi
sai zuba yake kamar ruwa. Aisha ta dubi balbelar
ta kakkafa fiffike cikin lalaci.
"Karanta farkon wasikar Aisha kafin ki je gida ko
kya dada gaskata ni." Aisha ta dawo da idanunta
kan rubabbiyar takardar dake kokarin rabewa gida
biyu, sannan ta kurawa kananan rubutun idanu.
Ta fara karantawa kamar haka:
Daga sarkin barayi ZANGERU

Zuwa ga dana AMADI. Kafin in sanar da kai
komai ina son ka sani cewa tun da nake a
rayuwata ban taba tsinana wani abin kirki a
rayuwata ba sai SATA!
"Ya isa haka nan." Balbelar ta katseta. Sannan
sai ta yi girgiza, har sau uku. Wani dan kankanin
dutse fari mulmulalle ya fado daga bakinta.
"Dauki wannan dutsen Aisha, na san nan ba da
dadewa ba za ki bukaci ganina. Idan bukatar
ganin nawa ta taso, sai ki murza dutsen har sau
uku a tafin hannunki za ki ganni na bayyana."
Aisha ta durkusa ta dauki farin dutsen jikinta na
rawa ta jefa shi cikin jaka, sannan sai ta dago kai
zata dubi balbelar.
Gaban Aisha ya fadi, domin bata ga komai ba, ko
sama ko kasa balbelar ta bace sai famfonan mai
tsiyayar da ruwa.
"Mafarki nake yi?" Aisha ta ce muryarta na rawa,
sannan sai ta leka cikin jakarta.
Har yanzu farin dutsen nan na nan.
***
Shafi'u ya kurkurda ta tsakanin tarin motocin
cikin sauri ya nufi inda motarsa take, ya bude
kofar motar kafafunsa a kasa ya zauna akan
kujerar gaba ta motar sannan ya dubi agogo cikin
damuwa.
"Me ya tsayar da Aisha ne?" ya tambayi kansa.
Ko shakka ba ya yi lokacin tashinta ya yi, kuma
ya tabbata ta nan Aisha zata zo wucewa.
Shafi'u ya lalubi aljihun wandonsa cikin damuwa
ya dauko naira darin karshe da ta rage masa ya
fara juyata a hannunsa, sannan sai ya shigar da
kafarsa daya cikin motar ya jingina kansa da
majinginin motar kana ya lumshe idanu yana
kulle-kullen zuci, kulle-kullen da yake fatan su za
su kai shi ga dora hannunsa a kan makudan
kudin da yake fatan ya taimaki Aisha dasu.
Wannan saurayi Shafi'u dogone kyakkyawan
gaske, wankan tarwada me kyawun fatar jiki,
yana da tarin gashin gira, haka nan kuma yana da
tarin gashin ka duguzunzum kamar kayar
bushiya. Wata sa'ar idan ta rayawa Shafi'u sai
ya runa gashin ya mayar dashi baki sidik. Wata

sa'ar kuwa sai ya mayar dashi fari fat kamar
gashin tunkiya, wannan shi yasa da yawa daga
cikin abokansa na gida da na jami'a suke kiransa
da suna Sisko. Duk wannan bata dami Shafi'u ba,
domin tun da aka haifeshi a duniya ya fara wayo
akidar samarin Amurka ta shiga zuciyarsa. Ya
sha cewa shi fa da akai shi Makkah ya yi sati
guda wai gara a kaishi Amerika ya yi sa'a guda.
Shafi'u Sisko ya sha bakin cikin jin cewa wai an
taba zuwa dashi Amurka, amma a lokacin yana
goye a bayan mahaifiyarsa, duka duka bai fi
shekara guda ba a duniya...........
KUDI DA MACIJI - 22
.
Aisha ta girgiza kai cikin gaggawa sannan ta dubi
kawayen ta dake can gefe guda tace
A'a na gode tare muke da wadancan
ba sai in dauke ku gaba daya ba.?
Aisha ta dada girgiza kai kayi hakuri wallahi mun
gode sannan saita dan juya tace Sai gobe ko
shafiu ya goge gumi ya dubeta zuciyarsa a karye
yace a sanyaye to shi kenan Aisha Allah ya
kiyaye daman so na ke kawai na ganki muyi
sallama shiyasa nake ta jiran fitowar ki tun dazu.
Koda ya fadi haka sai aisha taji tausayinsa ya
kamata akaro na farko a dan takin lokacin sai
zuciya tace da ita tsaya koda mintiuna biyar ne ki
saurare shi can kuma sai wata zuciyar tace da ita
ke rabu dashi sha sha sha yi tafiyarki kawai kada
ki saurare shi Iblis ne so yake ya hure
kunnuwanki me wannan dan karyar yagani ajikinki
da har zaice wai yana kaunarki wannan ita tasa
aisha juyawa bayanta tanufi inda kawayenta suke.
Koda su aisha suka juya suka nufi gurin shiga
motar sai aisha taji ajikinta cewar shafiu na nan
inda ta barshi tsaye haryanzu yana kallonta duk
da haka bata juyo ta kalle shi ba domin abin
dayafi damun zuciyarta alokacin shine
maganganun da Aljanar balbelar nan tayi mata da
kuma mulmulallan dutsen nan data bata A
tunanin Aisha gani takeyi kamar kowane lokaci
daga yanzu mulmullen dutsen rikewa zaiyi ya
zama wani Katon ALJANIN.

** ** ** **
Sa'ar da aisha ta isa gida saita wuce kai tsaye
zuwa cikin dakinta sannan taja kofa ta rufe lokaci
guda kuma tasa jakarta agaba ta kuma mata
idanu bata ko kiftawa zuciyar ta na wasi wasi
shin yanzu zan karasa karanta bayanin wasikar
nan ne ko kuwa na bari saida tsakar dare aisha
ta tambayi kanta duk kuwa da cewa tayi imani da
bazata taba iya karanta wasikar layar da tsakar
dare ba tunda dai ta shafi aljanu aisha ta godewa
Allah domin lokacin data dawo daga makarantar
uwar rikonta bata nan tafi unguwa dan haka babu
kowa agidan daga ita sai tattabaru da kaji da
kuma wata shegiyar akuya mai kukan tsiya
wannan shi ya baiwa Aishat damar shiga daki ta
kulle kanta aciki.
Tsahon lokaci tana nan zaune tayi tagumi wacce
akayiwa mutuwa daga karshe dai sai ta yanke
shawarar bari ta karasa karanta wasikar kada
taki karantawa tayiwa Aljanar laifi cikin lalaci
jikinta na rawa aisha ta lalubo takardar daga cikin
jakarta amma bata yarda dutsen nan da aljanar
ta bata yataba taba aisha ta warware wasikar
sannan taci gaba da karantawa kamar haka.
.
......Aduk iya tsayin zamanin danayi ina sata ban
tara komai ba da zan iya bar maka gado gashi
kuma mutuwa ta rutsani adaidai lokacin danake
dab da cimma nasarar sata ta karshe aduniya
wacce daga ita ne nake sa ran yin bankwana da
sata Amadi inason idan ka gama karanta wasikar
nan ka bari sai bayan shekara biyu ka nufi
katuwar fadamar nan ta DANMASU dake daf da
gandun sarki kabi bangaren arewa zaka ga wata
doguwar bishiyar giginya a daf da fadamar idan
ka duba kadan daga arewa da bishiyar zakaga
wani dan kwari mai kama da lalatacciyar
kushewa
ina umartakar daka tono cikin ramin zaka sami
duk irin dukiyar da kake bukata a zaman ka na
duniya ina kuma gargadin ka da cewa da zarar ka
dauki dukiyar kayi hanzari ka dauke mahaifiyarka
TAGOGORI kubar garin domin zamanku na da

hadari matuka.
Nine mahaifinka ZANGERU.
.
Aisha tayi ajiyar zuciya sa'ar data kai karshen
wasikar sannan saita sake dawowa da baya ta
fara karantawa tun daga farko sannu ahankali har
saida ta karanta wasikar sau goma sha uku
amma bata fahimci komai aciki ba aisha ta share
zazzafan gumin dataji ya fara sartu akan
goshinta.
.
Ina umartar ka daka tona cikin ramin zaka samu
duk irin dukiyar da kake bukata a zamanka na
duniya.
.
Kalaman wasikar suka fado azuciyar Aisha shin
wacce irin dukiya ce acikin ramin a binne kuma a
ina ramin yake?
Shin haryanzu dukiyar tana cikin Ramin.
Wannan dama wasu sune irin tambayoyin da
suka fara kai kawo acikin zuciyar Aisha haka nan
kuma tasan duk duniya babu mai bata amsar
tambayarta sai Aljanar Balbelar nan mai dogon
wuya idan har akwai abinda aisha take tsoro
shine tayi kiran balbelar tunanin mulmullen
dutsen nan dake cikin jakarta ya fado mata.
.
Inason ki warware layar ki karanta sakon dake
ciki domin arzikinki yana ciki.
.
Kalaman balbelar suka fara kai kawo acikin
kwakwalwar Aisha shin da gaske arzikin nawa ne
aciki ko dai Aljanar ce ke son wasa dani Aisha ta
tambayi kanta acikin zuciyar ta ai kuwa balbelar
tace daya daga cikin kakanninta ne ya rubuta
sakon.
Aisha taci gaba da cewa cikin zuciyarta
.
Tunda nake ban taba tsinana wani abin kirki
arayuwata ba sai SATA.
.
Aisha taji gabanta ya fadi sa'ar data tuno daya
bangaren kalaman wasikar shin dukiyar da aka

binne din ta sata ce? Ta sake tambayar kanta.
Aisha na nan zaune cikin rudani zuciyarta kunshe
da tambayoyi sama da tasbaha guda duk babu
amsoshinsu har zuwa sa'ar dataji an kwankwasa
kofar dakinta da karfi Ance.
Ke dan ubanki me kikeyi ke kadai acikin daki
kamar Boka.
Marakiyarta ce keta banbanmin fadan wajen cikin
sauri aisha ta dauke takardar wasikar ta cusa
cikin jakarta sannan ta nufi kofar dakin ta bude a
tsorace ta dubi......
KUDI DA MACIJI - 23
.
.
GORON SALLAH GA YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI
MASU BIBIYAR WANNAN LABARI NA
KUDI DA MACIJI
GORON SALLAR ZAI ZO AKALLA GUDA 4 KO 5 A
WANNAN RANAR
.
Marikiyarta ce ke ta banbamin fada a waje cikin
sauri aisha ta dauke takardar wasikar ta cusa
acikin jakarta sannan ta nufi kofar dakin ta bude
a tsorace ta dubi masifaffiyar uwar rikon nata.
.
Mama.....sannu da zuwa har kin dawo?
Eh na dawo me kikeyi ke kadai acikin dakin?
Zauna kenan daga makaranta shine na... Rufamin
baki shegiya uwar gulma malalaciyar banza
malalaciyar wofi shine wato tun da safe nace
kizo ki wanke tsummokaran ki da kayan kikace
saikin dawo daga makaranta shine kuma kika
dawo kika shige daki abinki ko? To fitowa zakiyi
yanzun nan sai kin wanke kayan gaba dayansu in
ma bazaki wanke naki ba sai kin wanke nawa.
Ba'a fi mintuna biyar ba da faruwar hakan sai
aisha ta fito zuwa tsakar gidan tafara wankin
tsummokaran kayanta hawaye yana kwarara akan
kumatunta sa'ar data dubi kayanta taga duk sun
rube sun kokkode gashi kuma kala hudu ma
kawai suka rage haka nan kuma babu ranar
samun wasu tunanin mahaifanta ya fado mata
azuciya duk da cewar sa'ar da suka mutu batafi

yar shekara bakwai aduniya ba amma haryanzu
tana iya tuno zaman farin ciki tayi dasu a kuma
mummunan hadarin daya kawo karshen
rayuwarsu ya kuma kawo karshen duk wani farin
ciki nata aduniya.
.
Shekara goma sha bakwai da suka wuce baya
yarinya aisha tana gaban mahaifan cikin jin dadi
da gata mara misaltuwa.
.
Mahaifanta Ahmed da saudatu bawasu masu
hannu da shuni bane to amma suna da rufin asiri
na zaman duniya mahaifin aisha malamin
makaranta ne wanda bai dauki duniya da zafi ba
haka nan bawan Allah ne nagari ma'abacon
tasbihi ga ubangiji akusan kowane lokaci sa'ar
dayake raye abokansa na kuruciya sunfi kiransa
da A.A domin sunansa daya da mahaifinsa wanda
shima sunansa Ahmad ayadda abokansa ke fadi
ance wai kakansa ma sunansa Ahmadu acewar
su wai sunan ya zamewa iyalin gidansu kamar
gado kusan kowa sai ya sanyawa sunan dansa
irin sunan mahaifinsa koda kuwa daga bangaren
mace dan yafito.
Irin wannan al'ada ita tasa mahaifin Aisha
addu'ar allah yabashi da namiji domin ya sanya
masa sunan mahaifinsa kamar yadda shima akayi
masa Allah mai yadda yaso sai yabashi diya
mace wacce aka sanya mata sunan AISHA.
Wata safiyar talata da safe mahaifin aisha tare da
ita sukayi shirin tafiya wani guri domin sadar da
zumunci lokacin da suka fito zasu tafine to
mahaifin aisha ya lalubi aljihunsa ya dauko wata
laya ya mikawa Aisha ungo wannan layar rataya
ta a wuyanki maganin tsautsayi ce in dai kina
tare da wannan layar in Allah ya yarda babu
abinda zai taba samunki na daga tsautsayi
aisha ta karbi layar tana dariya ta rataya a wuya
alokacin tana karama dan haka saita dinga murna
don daman sa'ar da take ganin layar a wuyan
mahaifinta tasha kokarin ta rabashi da iya yana
Ki.
Baba wannan layar a kasuwa ka sayo min?

Mahaifin aisha ya fashe da dariya yadubi
mahaifiyarta saudatu kinajinmu da Aisha? Wai a
kasuwa na sayo mata wannan layar
saudatu ta dube shi da murmushi tace
Ina ruwan yar baba
mahaifin aisha ya dubeta da murmushi sannan ya
dafa kanta yace
wannan layar gado ce aisha nima mahaifiyata ce
ta bani ita tun ina karami kamarki ki riketa da
kyau kada ki jefar da ita kinji Aisha? Idan
wataran kin sami 'ya kema saiki bata.
Hakanan dayace da Aisha saiyasa lokacin da
suka shigo mota suka fara tafiya sai sukaga
maimakon aisha ta rataya layar a wuyanta saita
makalata a wuyan YAR TSANARTA mahaifan
aisha suka fashe da dariya
sha sha sha ba yar roba nake nufi ba mahaifinta
yace da ita cikin murmushi wannan shine ya
zamo murmushi na karshe da zaiyi agareta domin
awannan tafiyar ne kafin su kai garin da zasu
suka yi hadari babu wanda ya shura acikin motar
sai AISHA
An sami aisha agefen motar zaune da layarta a
wuya da yar tsanarta ahannu tana kuka Aisha
bata gaji wani abin kuzo ku gani agurin
mahaifanta ba inka dauke tsohon gidan mai
kamar makabarta da suke ciki sai tarin litattafai
da layar dake wuyan aisha gamida kudin
mahaifinta naira dubu uku da dari biyar aisha
bata gaji komai ba agurin mahaifan nata sai
hakuri da hankalinsu.
.
Bayan anyi sadakar bakwai sai HAJIYA KANDE
wacce kanwace agurin mahaifin aisha ta
bangaren uba haka nan kuma mace daya jal data
rage acikin yan uwansu na kurkusa ta dauki
Aisha.
Wannan mata Kande masifaffiya ce haka nan aka
haifeta da masifa kuma tanajin dadin masifa dan
ance wai sa'ar da tana budurwa a kullum sai
anyi fada sau goma da ita arana lokacin data
dauki aisha ta daukane akan dole ba don taso ba
sai dan tana gudun maganganun jama'a domin

ita kadaice mafi kusanci da aisha acikin danginsu
da suka rage a doron kasa don haka tun ranar da
aisha ta shiga hannunta tafara gallaza mata
kullum saita jibgeta kamar ganga wata sa'ar ma
har kan ruwan cikin aisha take hayewa tayita
duka gata da nauyin tsiya kamar Alhaki ance sau
biyu tana sumar da Aisha kafin ta zama budurwa.
Aisha tana yar shekara goma sha biyar Kande ta
sayar da tsohon gidan data gada.
Bazan iya wannan jaraba ba kullum sai na saya
miki abinci gaki da cin tsiya kamar gara to ga
gidanki nan na sayar kudin nake saya miki abinci
da sutura da kuma....
KUDI DA MACIJI - 24
.
Bazan iya wannan jaraba ba kullum saina saya
miki abinci gaki da cin tsiya kamar gara toh ga
gidan ki nan na sayar kudin nake saya miki abinci
da sutura da kuma daukar nauyin karatunki in ma
kin cinye kudin ki ne.
Kande ce ke ta wannan masifar sa'ar data sayar
da gidan sannu ahankali Kande ta cinye kudin
Aisha kakaf.
.
Don haka ayanzu da aisha take durkushe tana
wanki tana kuka tana tuna rayuwar da sukayi da
mahaifanta bata da komai aduniya sai wannan
layar dake wuyanta da kuma tsummokaran kayan
ta kala biyar da Dankwali biyu duk ya kode yan
tauye ya zama dan zarere kamar rawanin Maroki.
Aisha ta mike tsaye daga kan kayan wankin ta
goge hawayen dake sartu akan fuskarta koda
aisha ta koma kan wankin saitaji ga mamakinta
shafiu ya fado mata arai abin yabata mamaki me
yiwuwa ko don ta fahimci ayanzu bata da wani
mutum dake kaunar ta adoron kasa idan ba shi
ba babu mamaki kuma kodon zuciyarta tana
neman wanda zata fadawa sirrin dake cikinta
sirrin da duk duniya babu wanda yasani daga
Allah masanin komai sai Aisha saikuma Balbelar
data bata labarin sirrin.
** ** ** **
Washegari da safe misalin karfe bakwai aisha

tafito sanye da kodadden kayanta masu kamar
algarara dauke da jakarta a kafada zata tafi
makaranta.
Lokacin data fito daga dakinta zuwa tsakar gida
saita sami Kande zaune tana wanke wanke tana
ganin aisha saita mike tsaye a fusace sannan
idanunta suka kai ga wuyan Aisha
Dan Ubanki ina kika kai layar gadon taki?
Aisha ta sunkuyar da kai tace a sanyaye jiya ta
fadi a makaranta.... Kafin aisha ta rufe baki ta
kifeta da mari Tas Tas har sau biyu aisha ta rufe
fuska hawaye ya fara sartu azuciyarta kuma tana
cewa Wallahi ko kasheni zakiyi bazan baki labarin
layar ba.
Shegiya tsinanniya wato saboda kin gama raina
ni saida kika jefar da layar nan ko? Adaidai
lokacin da wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login