Showing 3001 words to 6000 words out of 29993 words
Chapter 2 - KUDI DA MACIJI COMPLET by Nazir Adam Salih.pdf
sa jikinsa ke rawa. Zancen da ya ji na zinariya da
lu'u-lu'u su suka fi tayar masa da hankali fiye da
komai.
Domin duk da yake ya tabbata sarkinsu Sabitu
mutum ne mai tarin dukiya, amma bai taba
tsammanin yana da zinare da lu'u-lu'u da zasu
cika katuwar akwatin bakin karfe ba. Sarkin
dogarai ya ji bayan rigarsa ya fara jikewa da
gumi, haka nan zuciyarsa na ta raya masa cewa
ya kamata idan sun fita waje ya tambayi sarkin
dogarai cikin hikima me yiyuwa ya tsurkunta
masa dalilin da yasa sarki ake son ayi masu
akwatin.
"Ina son ka yi mata hannaye wadanda idan na zo
dora akwatin a bayan doki ba za a sha wuya
ba..."
Kalaman sarki Sabitu ne ke kai kawo cikin
kwakwalwar sarkin makera mai masaba. To
wannan na nufin kenan dukiya ce sarkin ke nufin
aikawa da ita wani guri. Wannan tunani shi ya
dada sa jikin mai masaba ya dauki rawa kamar
mazari.
"Nan da kwana uku nake son ka gama kirar
akwatin, zan tura sarkin dogarai ya dauka."
Muryar sarki Sabitu ta sake dukan kunnen sarkin
makera. Nan da na ya zabura ya dawo cikin
hankalinsa, a zuciyarsa yana cewa. Irin wannan
kuskure shi ke janyowa mutum yanka a gurin
sarakai.
"Ranka ya dade an gama, in sha Allahu nan da
kwana ukun zan gama."
Sarkin makera ya sake faduwa ya yi gaisuwa
sannan ya fice daga dakin jikinsa na rawa.
Ficewarsa ke da wuya sai sarki sabitu ya dubi
sarkin dogarai ya ce.
"Ina son ka zabo min amintattu daga cikin
mutanenka jarumai kamar mutum shida, ina son
zan aike ku da wasu kaya zuwa gurin babban
aminina, sarki Lurwanu." Sarkin dogarai ya
rankwafar da kai cikin biyayya, da girmamawa
sannan kuma da tausayawa. Ba tun yau ba ya
rigaya ya fahimci muguwar adawar dake tsakanin
sarkinsa sabitu da wazirinsa Dandunawa. Haka
nan ya riga ya san da yawa daga cikin fadawan
dake gidan sarautar duk Dandunawa suke goyawa
baya. Dan haka a yanzu da sarki ya ce da shi ya
samo amintattu daga cikin mutanensa bai yi
mamaki ba domin ya rigaya ya san cewa tun
sa'ar da tsohon sarkin ya fadi rashin lafiya goyon
bayansa ya raunana a gidan sarauta.
"Allah ya dade da ran sarki an gama." Sarkin
dogarai ya ce.
Wani zazzafan hawaye ya yi sartu akan kumatun
sarki Sabitu, sa'ar da ya dubi sarkin dogarai.
"Na gode da biyayya da kake yi min, na san kai
kadai ne ka rage mai kaunata daga cikin
mutanena, shi yasa nake son tattara dukiyata da
duk wani abu da na mallaka na daga gwala-
gwalai zinare, tagulla, da lu'u-lu'u, zan zuba su
cikin akwatin nan da na sa sarkin makera ya kera
min, za ku kai min ita gurin sarki Lurwanu, zan
hadaku da yayana Hassan da Hussaina ku tafi da
su can gurinsa, domin ni nasan tawa ta kare...ba
zan dada wasu kwanaki masu tsayi ba a
duniya..." Zuciyarsa ta karye ya fara shisshikar
kuka.
Sarkin dogarai ya yi sauri ya sunkuyar da kai
idanunsa cike da kwalla, tun da yake bai taba
ganin sarkinsa na zubar da hawaye ba ko da
kuwa barkono ne ya shigar masa idanu.
"Allah ya dada lafiya, kana iya dogara dani, in
Allah ya so zan isar ma da duk sakonninka a
gurin amininka sarki Lurwanu." Fuskar sarki
Sabitu ta dan saki, wani dan kankanin farin ciki
ya haskaka fuskar.
"Na gode, daman na san kai kadai ne zan iya
dogara da shi..."
Sarki Sabitu ya yi shiru a daidai lokaci da suka ji
wata zazzakar murya ta yi sallama a kofar dakin.
Ba a dade ba wasu kyawawan yara yan kimanin
shekaru goma sha hudu-hudu suka shigo cikin
dakin. Sarkin dogarai ya dubi Hassan da
Hussaina, cikin tsananin tausayi sai ya ji
idanunsa sun ciko da kwalla. Mahaifiyar yaran ce
ta fado masa a zuciya, yau kusan shekarunta
goma sha hudu kenan da mutuwa, tana haifar yan
biyun ta mutu. A zamanin da take raye ta taba
bashi kyautar rigar saki. Sarkin dogarai ya sake
kallon yaran sai ya ji wani dadai ya lullube
zuciyarsa, a ransa ya fara fatan ina ma ace
yayansa ne domin tun da yake bai taba haihuwa
ba. Haka nan bai taba gajiya da kallon kyawawan
yaran ba, musamman ma Hussaina tauraruwa
mai kyawun duniya, kamar yadda wani mawakin
sarki ya taba ce mata.
Yaran biyu suka shigo dakin, suka yi gaisuwa ga
mahaifinsu sannan suka zauna akan kilishin da
ya mamaye dakiin.
Kudi da Maciji... (5)
Sarki Sabitu ya yunkura daga kwance ya tashi
zaune da kyar, ya dubi yaran biyu ya ce.
"Ga su nan sarkin dogarai na baka su amana a
hannunka ka isar da su gurin aminina su da
dukiyarsu, kada ka bari wani abu ya samesu, duk
abin da ya samesu a hannunka!" Sarkin dogarai
ya ce.
"Allah ya dada ma lafiya, babu wanda ya isa ya
taba su in dai ina raye, har sai na isar da su."
Sarki Sabitu ya saki jikinsa gami da ajiyar zuciya
sannan sai ya koma ya kwanta. A daidai lokacin
ne to yarsa Hussaina ta dubeshi ta ce.
"Baba ina za a kai mu?" Sarki Sabitu ya dauke
kai gefe guda domin ba zai iya hada idanu da ita
ba, dan kada ta ga halin da yake ciki zuciyarta ta
sosu.
"Gurin aminina sarki Lurwanu za a kai ku."
Hussaina ta dubeshi cikin mamaki ta ce."
"Baba a can zamu zauna ko za a dawo damu?"
Sarki Sabitu ya yi shiru na tsawon lokaci sannan
sai ya ce.
"Me yiyuwa ku dawo...me zai hana watan wata
rana kuna iya dawowa ai nan garinku ne."
Hawaye ya subuce masa.
***
Lokacin da sarkin makera mai masaba ya karasa
gida, sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka nan
daga ya zauna ya dan sarara sai ya ji kalmar.
Zinare, lu'u-lu'u, tagulla na yawo cikin
kwakwalwarsa. "Me ke damuna ne?" ya tambayi
kansa da kansa.
Kusan sa'o'i biyu kenan da suka wuce yana
faman sintiri daga kofar gida zuwa cikin gida.
Tun sa'ar da ya dawo daga gidan sarkin, matarsa
Habi ta dama masa fura kana ta shimfida masa
tabarmar karauni kamar yadda ta saba yi ga
al'ada, sannan ta fice zuwa makwabtansu dan
yin ta'aziyyar mutuwa. Sarkin makera ya ci gaba
da kai gwauro yana kai mari, sannu a hankali har
sai da ya yi sawu goma sha biyar daga gidan
zuwa tsakar gida sa'ar da ya dawo tsakar gidan
ne to ya samu ya zauna akan tabarmar karaunin
dake shimfide a tsakar gidan kusa da wani murhu
mai dauke da wasu guma-guman duwatsu kan
kura har guda uku.
Mai masaba ya dubi katon kokon wanda ke
dauke da damammiyar fura, sannan ya dauke kai
gefe guda, ya kurawa wani katon rumvu dake
tsakar gidan idanu baya ko kiftawa.
Shekaru ashirin da suka wuce, sarkin makera
bashi da wata sana'a da aka san shi da ita sai
kira. To amma a boye a bayan kasa, ba shi da
wata sana'a da ta wuce SATA.
Mai Masaba garsakeken kato ne, baki mai tarin
gashin baki kamar ciyawa, hankanan yana da
tarin gemu duguzumzum babu kyawun gani, sau
da yawa idan ya dauki yan kananan yara da
niyyar zai yi musu wasa sai su fashe da kuka
idan suka dubi gemun, dan ya fi kama da abin
tsoro fiye da gemu.
To amma duk da haka sa'ar da yana saurayi
matarsa Habi tana mutuwar kaunarsa, a cewarta
wai gemunsa shi ya fi burgeta fiye da komai a
jikinsa.
Me yiyuwa matar tana da gaskiya, domin tun
daga saman sa har zuwa sahunsa babu wani
abin burgewa, domin komai a jikinsa babbane.
Babban kai, faffadan kirji mai kamar kofar gari,
manya-manyan tafukan hannu, wadanda ake jita-
jitar cewa wai ko doki ya mara da su sai ya
mutu.
Sarkin makera mai Masaba ya fara ne da turun
barayi, domin tun yana saurayi yake karbar kayan
sata ya sayar da su. Sannu a hankali har ya fara
gawurta. Ran nan sai wani mutum mai shigen irin
kirarsa ya same shi ya ce da shi.
"Ka ga mai masaba, ka daina batawa kan ka
lokaci a banza. Domin wannan sana'ar kirar da
ka sa a gaba ba wani attajiri zaka zama da ita
ba, haka nan zaka yi ta zama kullum kana
babbaka kirjinka a gaban wuta kamar fatar
ganda, kuma ka ga turun barayin ma da ka ke yi
ba wata riba mai yawa ke gare shi ba. Ni ina
ganin ka shigo cikin mu kawai sai mu fara koya
maka sana'armu ta dare..." tun daga wannan
lokacin mai Masaba ya shiga cikinsu.
Wannan kusan shekaru ashirin kenan da wani
abu, kuma har yanzun nan da yake zaune yana ta
sakar zuci kamar gizo-gizo bashi da wata
sana'ar da ta wuce SATA.
Dan haka a yanzu da mai Masaba ya zauna ya
sa kokon furar a gaba, sai ya fara tuanin ko
shakka babu ba zai iya samun saukin tunanin
zuci ba har sai ya kaiwa babban abokinsa labarin
katuwar akwatin da sarki ya sa a kera domin
aikewa da lu'u-lu'u da zinare a cikinta. Har
kullum babu abin dake damun mai Masaba sai
ganin yau kusan shekarunsa ashirin da doriya
yana sace-sace da fashe-fashe kamar bera amma
har yanzu bai wuce a kira shi da matsiyaci ba.
Tun da dai har yanzu jakinsa daya jal a duniya,
bayan kuma ga makwabtansa nan attajirai
ma'abota tarin dawakai dabbobi, da tumakai
gami da tsuntsayen gida burjik, kullum miyarsu
da mai da nama, amma shi kullum sai dai ya sha
fura da tsantsaman nono! Wannan ba zata yiyu
ba, ya dada jaddawa kansa. A daidai lokacin ne
to ya tuna da kokon furar dake gabansa. Cikin
lalaci mai masaba ya dauki ludayi ya kwarfo furar
nan ya kai bakinsa ya dan kurba. Ga mamakinsa
sai ya ji furar har wani daci-daci ta ke yi. Cikin
sauri ya fesar da abin daya guntsa, sannan ya
mike tsaye a fusace.
"Gafara dai." Matarsa Habi ta shigo gidan da
gafara dai, sannan sai ta yi turus tana kallon
mijinta, lokaci guda kuma ta kalli kokon furar
dake gabansa.
"Kada dai ka ce koma furar baka sha ba?" Habi
ta tambayeshi. Gami da rike tsantsa.

Kudi da Maciji... (6)
"Na fara sha sai na ji daci kamar kin watsa
shuwaka a ciki." Habi ta harareshi ta ce.
"Daci fa ka ce, ko kuwa dai bakinka ne yake
dacin?" Sarkin makera mai masaba ya juya ya
nufi kofa ba tare da ya sake dubanta ba.
"Ina kuma za ka?" Habi ta tambayeshi.
"Gidan babban aminina zani." Habi ta ji gabanta
ya fadi ras! Domin ta rigaya ta san duk duniya
mijin nata ba shi da wani amini da ya wuce
tsohon barawon nan. Shekaru ashirin da suka
wuce kullum a cikin fargabar rana zata bacewa
mijinta take, to amma cikin sa'a ga shi dai har
yanzu ko kai ba a taba fasa masa ba. Amma duk
da haka Habi ta san ko ba dade ko ba jima
watarana ba zata ga daidai ba. Dan haka a yanzu
da ya ce za shi gurin amininsa sai ta ji fargabar
da ta dade tana yi ta sake mamayar zuciyarta,
dan ta san aminan biyu basu taba kulla abin
arziki ba a tsakaninsu.
"Amininka wa kenan kake nufi?" Habi ta tambaya
duk kuwa da cewa ta san wanda yake nufin.
Sarkin makera ya dubeta cikin murmushi ya ce.
"Kin fi kowa ai saninsa, ke kin san duk duniya
bani da abokin da ya wuce ZANGERU!" yana fadin
haka sai ya fice daga gidan cikin sauri. Matarsa
Habi ta bishi da kallo cikin kaduwa. A daidai
lokacin ne jakin sarkin makera ya fara wani
mummunan kuka. "Uhu! U, wu! U!" Habi ta dubi
jakin a fusace ta ce.
"Allah ya yi min tsari da kai la'ananne. Ta sha ji
ana cewa duk sa'in da ka ji jaki yana kuka wai
shaidani ya gani! Habi ta yi mamaki in jakin
shaidanin ya gani yana bin mijinta a baya.
***
Zangeru na gaba dauke da fartanya matarsa ta
gogari na bin sa a baya dauke da balbela zugum-
zugum babu mai cewa kala kowa cikinsa ya duri
ruwa kamar masu zuwa gidan makoki.
Ta gogari da kyar take tafiya, haka nan balbelar
dake dauke a hannunta ta sa ji take yi kamar
dauke take da maciji, domin