Showing 1 words to 3000 words out of 34919 words

Chapter 1 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt

[05/07, 9:30 pm] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DAoXdILRZKjC042FBN7HEK?mode=r_c Kina neman inda zaki samu kaya masu sauqi da quality taho nan mamana kayanmu sunada kyau ga sauki farashin sarine muna aika kayan mu ko ina in sha Allah


*AURE A YAU!*



NA
*SADIYA ABDULRAZAK*


MARUBUCUYAR
Sandar dukan uwargida
Miji goma
Wani zaman
Zuciyar mace
Iya ruwa
Wani auren
Wutar ƙaiƙayi
Da walakin
Matar shige, dss

*First class writers association*


Page 1


Kowace mace kafin ta yi aure tana da buri da mafarkai masu kyau, a kan yadda take so rayuwar aurenta ta kasance, burin kowace mace ne ta samu kulawa, kyautatawa da kuma soyayyar mijinta, sai dai mafi yawan mata bayan an yi aure burinsu yana zama mataccen buri, hakan ke saka su kasance cikin rayuwar ƙunci da takaici, tamkar a cikin ramukan ƙaburburansu suke ba a wannan duniyar ba, yadda lamarin rayuwar aure ya zama a yau ya rushe jarumtar mata masu yawa, wasu sun tsani maza da ma auren bakiɗaya, amma kuma suna zaune a cikin gidan auren saboda dalilai masu yawa, walau masu rauni ko ingantattu.

Haka rayuwar Sabila ta kasance, kuma tana ɗaya daga cikin matan da ke da aƙidar mace ta zauna ta rayu a gidan aurenta duk runtsi, ya fi a ce ta fita ta bar yaranta a halin ƙila wa ƙala, ta koma gida ta kafa kujerar zawarci, wanda kare da doki kowa zai zo ya hau da sunan neman aurenta, ta sani don cim ma wannan ƙudurin nata tana buƙatar jajircewa, mantuwa, mayar da komai ba komai ba, uwa-uba kuma haƙuri. Sai dai a kullum halayen da mijinta yake buɗewa sababbi dal a kwalin tsiyarsa yawa gare su, suna ragargaza zuciyarta, suna sare mata gwiwowinta da ƙarfin zuciyarta, ta yadda take tunanin anya za ta iya kuwa? Shin za ta kai gaci ko sai dai gawarta ta kai? Amma ta saka a rainta za ta gwada ɗin, don haka take ta shaƙar baƙincikin safe da ban na dare da ban.

Gida ne ɗan ƙarami ginin fili kwata, a ciki akwai ɗakuna guda biyu, waɗanda suke a jere, sai ƙaramin kitchen da banɗaki, akwai filin tsakar gida mara yalwa, mai ɗauke da shirgin su randar ruwa, bokitan wanka da wanki, da kuma kwando mai ɗauke da kwanukan amfani, wanda ba su da matsuguni a kitchen ɗin, saboda ƙanƙantarsa, sai murhun girki na gawayi, shi ma a tsakar gidan yake rayuwarsa, hakan ya sa ya zama ɗan filin bai wuce a saka ƙaramar tabarma ba, daga zaure kuma akwai kwandon zuba shara, a nan take ajiye tsinyayarta da abun kwashe sharar.

Ɗaki na farko wanda yake a matsayin falo, ledar tsakar ɗaki ce shimfiɗe a ƙasa, da tsofaffin kujerunta waɗanda suka ga jiya suke ganin yau, da keken ɗinkinta, ɗan amanarta kenan mai rufa mata asiri, sai ɗayan ɗakin wanda gadonta yake ciki, mai ɗauke da laƙumammiyar katifarta samfurin lamimiya, kayan gadon dama can masu araha ne sosai, don haka yanzu da take da shekara bakwai da aure duk sun tsufa.

Baccinsa yake yi hankali kwance, ya yi kwanciyar rub da ciki, ta kalle shi da takaicin yadda yake ta sharar baccin kamar a tsakiyar dare, alhalin lokacin ƙarfe bakwai da rabi ne na safe, kuma ko sallar asubahi bai yi ba, sakamakon rashin kwanciya da wuri, don jiya sai ɗaya da rabi ya shigo gidan. A karo na uku ta sake yunƙurin tashinsa, amma bugun zuciyarta da fargabar abin da hakan zai haifar yana saka harshe da laɓɓanta nauyin da ba za ta iya buɗe bakinta ba, amma ganin lokaci yana ta tafiya ya sa ta daurewa ta buɗe baki cikin sanyin muryarta ta halitta ta ce"Abban Amal, Abban Amal".

Bai amsa ba, amma ya motsa ƙafarsa alamar yana jinta, kuma ta san tun da ya yi hakan ba zai amsa ɗin ba ne, don haka ta sake cewa"Abban Amal ina magana".

Sai kuwa ya zabura, sai ga shi a zaune yana muzurai ce"Kike cewa uban me!?"

Gabanta ya ba da rass, saboda har yanzu na kasa sabawa da masifarsa, amma hakan yana da nasaba da yadda take gudun fushinsa.

A sanyaye ta ce"Ka san babu abin da za mu karya da shi, kuma ba zan tura yaran nan makaranta da yunwa ba".

Ya yi tsaki ya ce"Kar ki tura su ɗin mana! Idan sun zauna a gidan a kaina za su zauna?"

Ya kwanta ya juya mata baya, zuciyarta ta fara kumbura, kamar yadda ta saba ji idan ya yi mata magana mara daɗi, ta yi kamar minti ɗaya tsaye a ɗakin, kamar za tasake cewa wani abun ne, ko kuma tana jiran wani abu, sannan ta ja ƙafa ta fita ta koma falon, ta samu Amal da Minal zaune a falo, ita Amal tana ɗaure da tsohon towel ɗin wanka, yayin da Minal ke gefe tana ta ɓata rai, ko ba ta tambayi dalilin ɓacin ranta ba ta san a kan Amal ta riga ta ɗaukar towel ne, tabbacin ita za a fara yi wa wankan. Ta zauna a sanyaye ta ce"Amal cire towel ɗin nan ki mayar da kayanki, wanka sai anjima".

Lokaci ɗaya yarinyar ta canza fuska, kamar za ta yi kuka ta ce"Ammi yau ma ba za mu je makarantar ba kenan?"

Yayin da Minal ta fara tsallen murna tana cewa"Yee yau ma ba sai mun je makaranta ba, dama Aunty ta ce yau sai ta ba mu homework mai yawa".

"Ammi don Allah mu je, Uncle ya ce idan karatu yana wuce ni ba zai yiwu na zama likita ba". Amal ta yi maganar cike da damuwa.

Sabila ta ce"Yi haƙuri Amal, in sha Allah gobe za ku je, kin ga mun tashi ko gawayi babu, da me zan dafa ruwa na yi muku wanka? Kuma ba na so ku tafi da yunwa, sannan yanzu lokaci ya tafi za ku yi latti".

Idon yarinyar ya kawo ruwa ta ce"To".

Yayin da ita kuwa Minal ta shiga sabgar gabanta. Shekarun Amal shida, amma tana da hankali da nutsuwa, ga gudun zuciya, zai yi wuya ta ɓata wa mahaifiyarta rai da gangan, idan kuwa ta nuna fushi a kan laifinta sai ta ba ta haƙuri, kuma jikinta ya yi sanyi, tana son karatu sosai ta tsani ta yi fashi, ita kuma Minal shekarunta huɗu, sam ba halinsu ɗaya da yayarta ba, ba ta jin magana, ba ta son karatu sam, ba za ta taɓa yi mata laifi ta ba ta haƙuri ba, idan ta yi laifi ta ce za ta dake ta Amal duk dai ta ruɗe ta ce mata ta bada haƙuri, amma haka za ta yi ƙirmisisi sai dai ta zaɓa ko ta dake ta ɗin ko ta haƙura, sannan tana burin ta ga Amal ta yi laifi an yi mata faɗa ko an dake ta, sai ta yi ta jin daɗi, saɓanin Amal ɗin da take damuwa idan ta daki Minal ɗin, halayen nan na Amal ya sa ta zama mafi soyuwa a rainta, har tana mafarkin nan gaba za ta ji ƙanta, za ku ma ta yi zumunci da son kyautatawa danginta.

Garam! Ta ji ƙarar ball da aka yi da buta daga tsakar gidan, wannan halin Sanusi ne, muddin ya zo zai yi amfani da buta bai tarar da ruwa a ciki ba, sai ya yi ball da ita.

Ile kuwa, ba ta gama jin faɗuwar gaban ba ta jiyo shi cikin hargagi"Sabila! Ke Sabila!".

Ta tashi ta fita da sauri tana amsawa, da murtuke fuska kamar bai taɓa murmushi ba ya ce"Wai ke daƙiƙiyar ina ce?Wannan wane irin wulaƙanci ne? kullum sai na ce a zuba mini ruwa a buta za a zuba?"

A sanyaye ta ce"Ka yi haƙuri" Ta duƙa ta ɗauki butar ta nufi randar ruwan.

A fusace ya ce"An ƙi a haƙura ɗin! Dalla ba ni". Ya warci butar bayan ta zuba ya shige banɗakin.

Ta janyo bokiti ta zuba masa ruwan wanka, domin next shi zai buƙata, ta koma ɗaki na zauna, bayan ya gama komai ya zo zai fita, ta fita ta same shi a tsakar gida, ya sha wani farin yadi, sai ka san shi talaka ne sannan za ka gane yadin mai sauƙin kuɗi ne, saboda yadda ya yi masa kyau ya ji guga sai sheƙi yake yi, ya yi kyau sosai, kamar kullum sai ƙamshin turare yake yi, Sunusi ba wani kyakkyawa ba ne, amma yana da farinjini da shiga rai, ga tsafta sosai, don gayunsa yana ɗaya daga cikin abin da ya fizge ni na yarda da soyayyarsa har ta kai mu ga aure.

"To me za mu ci?" Ta tambaye shi gabanta yana faɗuwa.

Ya yi mata mugun kallo ya ce"Ku cinye ni mana!".

Ya zo zai wuce ta bayan ya gama goge takalmin da ya saka, ya daidaita hular kansa, kamar za ta yi kuka ta ce"Wallahi ba Ni da ko naira biyar, kuma yunwa muke ji".

Ya ce"Ni ma haka na tashi, kuma yunwa ba ku fi ni ji ba, sai ku bari idan na fita na samu na dawo na kawo muku".

Daga haka ya fice daga gidan yana cewa"Don ba ki yi mini a dawo lafiya ba ba shi yake nufin ba zan dawo lafiyar ba, addu'ar iyaye da ta abokan arziƙi ma ta ishe ni, ko da safen nan da fatan alkhairin matan da suka fi ki na buɗe wayata".

Hawaye ya sakko mata, ta yi saurin ɗauke su tana ƙarfafa zuciyarta, ga cikinta da yake ta yi mata kiɗan general, don rabonta da abinci tun jiya da rana, har gara yaran sun ci guntun na rana da daddaren, ba ta son komawa ɗakin don kar yaran su gane rauninta, don haka ta kama wanke-wanke, wanda ɗauraya ce kawai tun da babu omo.

Tunani take yi a ranta, wai yau ita Sabila ce omo ma ya gagare ta a gidan aurenta? Hmm lallai ruwa ya daki babban zakara, idan ta tuna irin farinjinin da ta yi a lokacin 'yan'matancinta sai ta yi murmushin takaici kawai, a ranta ta tambayi kanta wannan rayuwar da take ciki yanzu ƙaddara ce ko ganganci?

Ta shiga ɗaki ta zauna, tana fakar idon yaran tana ɗauke ƙwalla a hankali, can sai Minal ta ce"Ammi yunwa nake ji".

Ta yi shiru kamar ba ta ji ta ba, ta sake cewa"Ammi yunwa". Wannan karon kamar za ta yi kuka.

Ta kai dubanta ga Amal wacce ta yi shiru, kuma ta san ita ɗin ma yunwar take ji, ta tashi ta shiga kitchen ta buɗe ɗan bokitin da take ajiye-ajiye, wai ko za ta samu guntun ƙanzo ko garin kwaki, duk da ta san babu, ba ta kuma samun ɗin ba, sai ta yi zaune a kitchen ɗin, hawaye yana cigaba da sakko mata, ta riga ta ƙulla abota da kuka, tun farkon aurenta da Sunusi.


Shi kuwa Sunusi yana fita bai zarce ko'ina ba sai teburin mai shayin da ya saba zuwa, ya zauna aka haɗa masa shayin da ya ji madara da biredi, yau kuɗin nasa ba zai kai ya ci ƙwai ba, don haka aka saka masa bota a ƙaton biredin, ya ci har ya ishe shi, ya kalli almajiran dake nesa da wajen, suna jiran wanda zai ƙoshi ya ba su sauran, kamar ya ba su, sai kuma ya tuna ya baro yaransa a gida ba su ci komai ba, sannan ya san sun daɗe ba su ci biredi da bota ba, sai ya ji gara ya kai musu guntun nan, har ya saka shi a leda sai kuma ya ga idanun mutanen rumfar na kan shi, ya ji kunya ta kama shi, a ce da class ɗinsa ya ci biredi ya tafi da guntun? Hakan ya sa ya yafito almajiri da hannu, ya zo ya miƙa masa, ya bar wajen yana hamdala saboda yadda ya ji cikinsa ya ɗauki ɗumi, gumi yana yanko masa.


GIDAN YUSUF

Ba iya mata ne masu fuskantar wannan ƙalubalen ba, ta wani fannin ana samun rashin dace daga wajen matan, sai ka ga miji har miji, gida har gida, amma ba a yi dacen mace ta gari ba, wata duk yadda miji ya kai ga kyautata mata da son a zauna lafiya sai ta botsare, sai dai miji ya yi ta haƙuri, wani kuma ya yanke hukuncin da zai iya janyo al'amura masu dama.

Cikin takun nutsuwa Yusuf ya ƙarasa ƙofar gidan nasa, ya saka mukulli ya buɗe ya shiga, a kan ball ya sauke ƙafarsa, wanda hakan ya haddasa masa yin sufa ya kusa faduwa, da sauri ya ce"Subhanallah!" Ya ciro wayarsa ya haska, ya ɗauke ball ɗin ya rufe gidan ya ƙarasa ciki.

Babban gida ne, akwai filin tsakar gida mai girma, wanda zai iya yin packing ɗin motoci biyu kuma a samu sauran fili, daga gefe akwai ɗaki falle ɗaya, da banɗaki a kusa da shi, sai ƙofar da za ta sada ka fa kitchen, duk da kuma akwai wata kofar daga cikin falo, akwai baranda babba, wacce aka ƙayata ta da zagaye ta da ƙarfe ta kasance kamar rela, kafin ka shiga babban falon mai ɗauke da manyan beadroom guda uku, kowanne akwai banɗaki a ciki, sannan akwai banɗaki a cikin falon, sai dining room, da kitchen wanda yake haɗe da store.

Yusuf ya shiga falon, ya tarar da shi shiru babu kowa, sai TV da take ta aikinta, ita da fanka, ga falon ya yi kaca-kaca da kayan wasan yara, can wandon Areef, nan rigar Yusra, ga kuma ɗankwalin mai gayya mai aiki, wato matarsa Zubaida, ya ƙarasa ya kashe TV, ya ƙarasa dining inda yake saka ran ganin abincinsa, nan ɗin ma ba a cewa komai sai hamdala, don teburin kaca-kaca yake, har ƙasansa, an yi wadaƙa da shinkafa, ga ƙasusuwan kaza ta ko'ina, da wanda aka taune da wanda ba a tauna ba, farantai da kaloli duka suna kan teburin a buɗe, duk da da sauran abinci, sai tashi kular wacce aka zuba masa abincinsa ce a rufe, ya ɗakko ta cak ya bar wajen, ɗakinsa ya nufa ya buɗe ya ajiye, sannan ya shiga wanka, ya fito ya zauna ya ci abincin da aka cika yaji a ciki, ga shi gishiri ya so ya yi yawa, ba ya son yaji duk da ba shi da ciwon olsa, haka kuma ko magi ya tsani ya ji ya yi yawa a abinci ballantana gishiri, har ya gaji da yi mata magiyar ta daina saka masa gishiri a abinci.

Bayan ya gama ya fita da kular ya mayar da ita dining ɗin, don ta bi sahun danginta, ya nufi ɗakin yara, ya tura ya shiga, ya tarar da su kowanne a gadonsa, ya yi wa kowa addu'ar bacci ya shafa musu, ya gyara musu kwanciyarsu, sannan ya bar ɗakin.

Ya tura ɗakin Hajiyar zuciyarsa na bugawa, saboda fargabar yadda za su kaya, tun jiya yake cikin yanayin buƙatuwa, ga shi ta kafa sabuwar dokar idan tana bacci ba a tashinta, shiyasa jiyan ya rabu da ita, yau kuma ya so dawowa da wuri aiki ya yi masa cikas, kuma ba ya jin zai iya haƙura ya danne buƙatarsa a wannan daren.

Yana shiga ɗakin ya haɗiyi yawun takaici, ganinta ta yi wata irin kwanciyar rub da ciki, a tsakiyar gadon take, amma daga yanayin kwanciyar za ka gane ba shirin bacci ta yi ba, ya dai ɗauke ta ne kawai, tun da abaya ce ma a jikinta ba rigar bacci ba. Ya ƙarasa kusa da ita, sai ya ga alamar wayarta tana aiki, yana dubawa ya ga a cikin tiktok take, wani hatsabibin ɗan tiktok yana ta rawa ta rashin ɗa'a, a ransa ya raya 'wa ma ya san tun yaushe ta yi baccin? Wa ya san sau nawa bidiyon ya maimaita kansa?' Ita dai da alama ta yi nisa da bacci, tun da lokacin sha biyu da rabi na dare ne.

Ya kashe wayar zai ajiye, sai ya ga cajinta 15% don haka ya jona mata ita a caji, ya kashe hasken ɗakin, ya rage sai iya na fitilar wayarsa, ya hau gadon, ya ja ta don gyara mata kwanciyar, ta farka a ɗan razane ta ce"Ha'a! Waye haka ne?"

Murya can ƙasa yana sake riƙe ta ya ce"Ni ne fa, kwanciya na gyara miki".

Ta ja dogon tsaki tana fizge jikinta ta matsa gefe, ya kashe fitilar wayar tasa ya ajiye a gefen fulo, ya sake matsawa kusa da ita, murya can ƙasa yake cewa"Zubaida ya ne?"

Murya a sama ta ce"Ka ga Malam babu wani ya ne da za ka ce mini, kawai ka tashi ka tafi, wannan ai cutarwa ce, sai ina tsaka da baccina ka zo ka tashe ni, kaina ciwo yake yi ma".

Ya riƙo ta yana cewa"Ki yi haƙuri, ban san aikin zai kai ni dare ba wallahi, taimake ni ki yafe min yau ɗaya dai".

Ya ƙarasa maganar da ƙoƙarin raba ta da rigar jikinta.

Ta fizge tana cewa"Haba Yusuf, na ce maka kaina ciwo yake yi fa, kai ba ka da tausayi ne?"

Ya ce"Shikenan Allah Ya sawaƙe".

Ya lalubi wayarsa ya kunna fitila, ya sauka daga gadon yana cewa"Kin sha magani?"

"Umm na sha" Ta faɗa tana juya masa baya.

"Allah Ya sawaƙe" Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin, ya ja mata ƙofa.

Ya koma ɗakinsa ya kwanta rai babu daɗi, ya san yau da ƙyar bacci zai ɗauke shi.



GIDAN HAMZA

Madaidaicin gida ne, mai ɗauke da a jere guda uku, kowanne ciki da falo ne, sai wani ɗakin falle ɗaya, wanda yake a farkon shigowa gidan, sannan banɗaki a tsakar gidan, sai kitchen mai girma shi ma a tsakar gidan, da filin tsakar gida babu laifi, wanda aka malala masa fasassun tayals.

Mata biyu ne zaune a tsakar gidan, kowacce tana aikin gabanta, Sahura da take tatar ruwan awara, ta kalli Saude ta ga tana ta ɗinkinta hankali kwance, ta kunna waƙar ɗan musa ta zafin nema wacce take fito da muhimmancin sana'a, tana bi tana ɗinkinta, Sahura ta saki tatar ba don ta gama ba, ta riƙe ƙugu da hannuwa biyu ta ajiye gauron numfashi, sai ka ce gajiya ce ta saka ta hakan, amma a zahiri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login