Showing 24001 words to 27000 words out of 34919 words
Chapter 9 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
amma ba na son jin maganganun nan haka don Allah, kuma zancen aure ai kin gama tsayar da miji, ni fa ba na son doguwar rana ne, shiyass na ce sai na gama shiryawa, bayan sallah da sati ɗaya in sha Allah kin zama tawa".
Ta ce"Allah Ya nuna mana, je ka samo min don Allah, ba na son harkar ƙaranta wallahi, yanzu sai ka sa ƙawayena su fara raina ni".
Ya ce"Ina zuwa in sha Allah komai dare zan kawo miki".
Ya tafi yana ta tunanin inda zai samu, ya yi nisa da gidan su Karime ya samu ƙofar wani gida ya zauna, tun da bai san ma inda zai fara zuwa neman kuɗin ba, wayarsa ya ciro ya kira wani abokinsa suka gaisa ya nemi aron dubu ashirin ya ce babu, ya ce dubu goma ya ce masa ko biyar ba za a samu ba, sai da ya kira abokansa uku duk ba a samu ba, hankalinsa fa ya tashi yana ta tunanin mafita, can dai ya tuna ai ya ga atamfofi ɗazu a falon Sabila, zuciya ta raya raya masa ya sata kawai ya je ya karyar da su ya siyar, komai ta fanjama fanjam, Indai ya fita kunyar Karime shikenan, amma zai fara jin cikinta idan tana da kuɗi ta ara masa, ifsn ta ƙi kuma ta gani a kayan mutane, da wannan shawarar ya nufi gida, ya same ta a falo tana ta ɗinkinta, yaran sun yi bacci, ya shiga da sallama, har da dan sakin fuska.
Ta ce"Sannu da zuwa, yau da wuri ka dawo kenan".
Ya ce"E to, ba dawowa na yi bacci ba".
Ya zauna a kujera yana cewa"Wallahi Maman Amal wata matsala ce ta taso mana".
Ta ajiye ɗinkin, ta juyo ta ce"Subhanallah me ya faru?"
Ya ce"Hmm! Wallahi wani abokina ne ya shiga matsala, matarsa ce kwance a asibiti tana naƙuda, kwana uku kenan muna ziryar asibiti, shiyasa kika ga duk raina a ɓace, ko tsawar da na yi miki jiya wallahi da biyu, damuwa ce ta min yawa, saboda na baro matar nan tana ta zunduma ihu abun tausayi".
Ya ce"Sabila ki tuna ciwon naƙuda, cikin awa uku kike gama naƙuda ki haihu, amma idan aka kalle ki ido zuru-zuru kamar an jijjiga ɓera a buta, to ina ga ita da ta yi kawana uku tana ɗanɗanar wannan azaba?"
Sabila ta ce"Allah sarki, gaskiya na tausaya mata, Allah Ya raba su lafiya".
Ya ce"Ina fa rabuwa lafiya? To yanzu dole sai dai a yi mata CS a ciro ɗan, kuma shi ATM ɗinsa ya samu matsala, dole sai ya je banki gobe, ita kuma an ce idan ta ƙara yin awa ɗaya ba a yi aikin ba za ta rasa ranta ma duka, kuma mun ce su yi aikin gobe da safe yana zuwa banki aka gyara zai cire kuɗi ya ba su, wallahi sun ce ba za ma su sake taɓa ta ba".
Sabila ta ce"Kai amma da tausayi abun".
Ya ce"Ai ba ki ga tausayi ba, kin ga da na leƙa ta windo? Sai juya kai take tana karanto kalmar shahada, shi yanzu abokin nawa ya ma cire rai da rayuwarta, sai kuka yake yi, mun je duk inda za mu je Sabila an rasa mai imanin da zai ranta mata kuɗi ya ba da a ceci rayuwar matar nan, yanzu ya saddakar ma kin gan shi a ƙofar gidan nan, jira yake a kira shi a ce masa ta mutu kawai".
Sabila ta ce"Kai amma dai likitocin nan ba su da tausayi, yanzu ya kenan?"
Ya ce"Kayya, ai su a kan aikinsu suke, yanzu ni ma na bi duk anokaina wallahi ban samu aron kuɗi ba, shi ne na ce to Sabila ko za ki taimaka ki ranta masa? Wallahi gobe yana zuwa banki aka gyara ATM din zai ciro kuɗinki cass ya ba ni na kawo miki".
Ta yi jim tana tunani, tabbas ta tausayawa matar nan sosai, tun da ta san zafin naƙuda, to amma tana tunanin ta ba da kuɗin mutane, a zo a samu matsala.
Sunusi ya ce"Sabila tunanin me kike yi ne? Habawa ke kuwa, taimakon mace ne fa 'yar'uwarki".
Ta ce"Gaskiya da kuɗi a hannuna dubu arba'in, amma wallahi na masu ɗinki ne, ka ga atamfofin can, suka ce nan da kwana shida suke so, kuma da gobe nake son siyo kayan ɗinki na fara yi musu".
Ya ce"To Alhamdulillah! Ashe ma kina da hanyar taimakawa na tsallake nake ta nema a waje, don Allah Sabila ki taimake ta ki ba da kuɗin nan, dubu hamsin ake buƙata, amma na san idan aka ba da dubu arba'in ɗin za su yarda gobe sai a cika musu goman".
Ta ce"Amma fa ka san na mutane ne, don Allah a bayar goben".
Ya ce"To me zai hana? Ba fa kuɗin ne babu ba, ATM ne ya samu matsala wallahi".
Har ta tashi za ta ɗakko masa, sai kuma ta ce"To amma tun da matsalar ATM ce ai zai iya transfer ko?"
Cikin ƙosawa ya ce"Kayya Sabila, to kuma abu da ba opay ba? Wannan sabon banki ne, sunansa risky bank, ke dai ɗakko min na je don Allah yana jira na".
Ta je ta ɗakko duka dubu arba'in ɗin ta ba shi, ya kirga ya zura a aljihu yana cewa "Ma sha Allah sun cika, Allah Ya haɗa mu a ladan".
Ya fita daga gidan cikin sauri, ita kuma ta koma ta zauna jiki a mace, tana fatan Allah dai ya sa goben ya dawo mata da su da wuri.
Shi kuwa Sunusi yana fita ya tsaya ya ware dubu ashirin, ya raba musu aljihu, ya nufi gidan su Karime, ya kai mata ashirin ɗin, ai kuwa ta kashe shi da fari da ido da kalamai, tana cewa"I love You miji na gari, da an yi auren ai yau da na goye ka da zani".
Ya washe ba ki ya ce"Kuma za ki iya?"
Ta ce"Ka jira dai a yi auren har wanka ni zan dinga yi maka".
Ta dinga kalamance shi, ba shiri ba niyya ya ƙara mata dubu goma ya ce ta yi lalle da kwalliyar biki, ya tafi majalisa nan ma ya sayi ƙwaya da kodin na dubu biyar, don ya yi wa kansa cajin da zai ketawa Sabila wulaƙanci ko da za ta yi zancen kuɗinta, ya tsira da dubu biyar a jikinsa.
GIDAN YUSUF
Da asuba ya ɗauki waya me sabon layi, ya saka lambar Zubaida a ciki, ya kuwa ganta a WhatsApp, hotonta ne ma a dp, ta ci uwar kwalliya ta ɗaga hannunta mai ɗauke da zoben gwal, kuma riga ce ta atamfa mai tsada a jikinta, ɗinkin ya kama ta sosai, saboda tana da ƙiba, tana da cikar ƙirji, kishinta ya kama shi, kuma ganin hotonta a dp da last seen dinta ya tabbatar masa da gaske blocking ɗinsa ta yi, shiyasa ya daina ganin status ɗinta, ya sauke numfashi ya yi mata sallama, ya rubuta Hajiya ya kike ya kasuwa? Ya ajiye wayar.
Sai da zai tafi office ya tafi da ita, an yi sa'a yau ta yi abun kau, ta tashi ta yi musu abun karyawa na arziƙi, kunun gyaɗa ta yi da ƙosai , yara sun ci sun tafi makaranta babu latti, can da aiki ya yi masa sauƙi ya ɗauki wayar ya kunna data, ya ga alamar ta hau online amma ba ta duba saƙon shi ba, ya sake ɗaga mata hannu ya rubuta mata "Hajiya ina so mu yi magana ne".
Babu jimawa ta duba ta amsa sallamar ta ce"Ok".
Ya ce"Ya kike ya hutu?"
Ta ce"Mun gode Allah".
Ya ce"Dama maganin maza nake so amma wanda mijinki ya tabbatar da ingancinsa".
Ta turo masa sticker dariya ta ce"Ai mu duka kayanmu ma su inganci ne Alhaji".
Ya ce"To ai gara dai wanda mijinki yake sha, tun da kin ga ke ce za ki ga aikin maganin mai kyau ne sosai ko ba sosai ba".
Ta ce"Ni mijina babu kalar wanda ba ya sha, don haka ka gwada duka kalolin".
Ya ce"Amma kina ganin kyaunsa kuwa da gaske?"
Ta ce"Ƙwarai kuwa, idan one round kake yi za ka fara yin five".
Ya ce"Kuma kina jurewa?"
Ta ce"Sosai kuwa, amma ita ma matar taka ya kamata a haɗa mata".
Ya ce"To Allah Ya sa dai za ta sha, saboda ba ta yarda da ni sosai, raguwa ce, wataran ma sai ta ƙarfi nake samu fa, ko kin san matsalar?"
Ta tura masa sticker kuka sannan ta ce"To gaskiya idan ka ga irin haka ɗayan biyu, ko dai tana da infection ne ko kuma tana da raunin sha'awa, akwai kalolin da za a haɗa mata idan kana so".
Ya ce"To a fara da nawan dai, nawa ne duka haɗin?"
Ta ce"Dubu hamsin ne, amma fa za ka gode mini sosai Alhaji".
Ya ce"To babu damuwa, ba ci account anjima zan saka kuɗin".
Ta tura masa tare da godiya.
Can anjima ya ga ta ɗora status alamar har ta yi saving din lambarsa, ya kuwa buɗe ya gani, feedback ɗin mutane ne kala-kala da suke ta yabon kayanta, a ƙarshe ya ga na wani namiji, ta rufe sunan ba a gani, amma a cikin firar cewa yake tun da yake bai taɓa amfani da maganin da ya ji daɗinsa irin wannan natan ba, don haka gobe zai aiko mata kyauta har gida, a ƙasan hoton ta rubuta "Ina godiya Alhazaina, yanzu fa maza nema suke su ƙwace product ɗina gabaɗaya, wani ma ɗazu ya ce shekara uku da aure matarsa ba ta samu ciki ba sai yanzu silar wannan maganin, don haka mata a dage a dinga siyasa maza ko su ba su siya ba.
Yusuf ya yi mata comment da cewar"Ni ma idan na gwada na ga kyaunsa na yi alƙawarin zan yi miki kyauta".
Ta ce"Ai kawai ka tanadi kyautar Alhaji, don kuwa ina tabbatar maka matarka ba za ta gane ka ba".
Ya ajiye wayar yana ta mamakin Zubaida. Yana tashi daga aiki ya tsaya wajen me P.O.S ya tura mata dubu hamsin, ya tura mata shaida, ya ba da address ɗin abokinsa, ta ce gobe za a aika masa yanzu ta tashi daga office. Ya yi godiya yana ayyana wato falonta ne office ɗinta. Ko a fuska bai nuna mata ba, washegari ta ce masa ga kaya a hanya, sai ya katse aiki ya je inda ya ce a kai, ya karɓa, ko buɗe kayan bai yi ba, da ya koma gida ma ajiyewa ya yi, kuma washegari kawai ya ga ta ɗora status ɗin wata waya mai tsada da cewar wannan Alhajin na jiya ya cika alƙawari, ana ta yi mata murna tana sake ɗorawa tana godiya, ya daure bai yi mata maganar wayar ba, kuma bai canza mata fuska ba, bayan sati ɗaya sai ta yi masa sallama, suka gaisa ta ce"Alhaji kyaun alƙawari dai a cika, na tabbata ka shanye daɗin magani kuma na ji shiru babu kyautar da ka ce za ka ba ni".
Ya ce"Matar tawa ce ba ta da lafiya, amma yanzu ta ji sauƙi yau zan fara amfani da maganin".
Ta ce"A'a ka bari sai ya ratsa ka tukunna, ka yi kwana uku kana sha".
Ya ce"To na gode Hajjaju".
Ta ce"A ji daɗi lafiya Alhaji".
Yusuf yana ta mamakin Zubaida, shi sam ya manta rabon da su zauna suna fira da ita, ashe har tana yi da customers maza ma ba mata ba.
Tun daga ranar ya fara shan maganin, kuma tun a ranar farko ya fara jin tasirin maganin a jikinsa, na sha da shi ne kala uku, idan ya tashi duka ukun yake zubawa ya dafa shayin ya sha, tana can tana bacci ba ta san yana dafa shayin ba ma. So ya yi dai ya yi sati yana sha sannan zai je mata, amma a rana ta huɗu da ya sha ya ji ba zai iya jurewa ba, lokacin sha biyu na dare, ya so a ce ba daga bacci zai tashe ba tun da ba ta son haka, amma haka dai ya yi ƙundunbala ya nufi ɗakin nata, ya tura ƙofar ya shiga, ya yi mamakin ganinta a zaune a tsakiyar gadon,sannan ta zabura da ganinsa, ta yi saurin kifa wayar ta fara 'yan kame-kame, alamu sun nuna ko dai waya take yi ko kuma chatting, kuma idan tana da gaskiya a kan me za ta gan shi ta ajiye?
Ya dai maze ya kau da wannan tunanin ya ƙirƙiro murmushi ya ce"Hajiya Zuby ba a yi bacci ba?"
Ta fara sosa kai ta ce"E, wani aiki na karasa da safe zan tura kaya Jos".
Ya ce"Ok, ki ce ma Allah Ya taimake ni, tun da ba ki riga kin yi bacci ba babu korafi ai ko?"
Ta canza fuska ta ce"Amma fa a gajiye nake wallahi, kuma fa na faɗa maka sai na san matsayina a wajenka a ina muka kwana?"
Ya kashe hasken ɗakin ya nufi gadon sannan ya ce"To tun da kika ji shiru ai kin san na haƙura na bar ki ne".
Ta ce"To ni dai a gajiye nake wallahi".
Ya ce"Sorry, taimaka dai".
Haka dai ta haƙura ba don ta so ba, ita dama can abun bai dame ta ba, kuma sannan yanzu Yusuf ɗin ya gama fice mata a rai, shiyasa ts tsani ma ya raɓe ta, neman hanyar da za ta kufcewa aurensa take yi, amma shi kamar ba ya ganewa.
Zubaida ba ta san kyaun maganinta ba sai a yau, yau ta tabbatar da duk mazan da take siyarwa magani feedback ɗin gaskiya suke ba ta, tun tana da ƙarfin ture Yusuf har ta gaza, ta yi liƙis kamar majinyaciya, duk roƙon da za ta yi ta yi, amma sai kiran sallar asuba ne ya cece ta daga hannun Yusuf, tana hawaye ta ce"Ban yafe maka ba".
Ya yi 'yar dariya ya ce"Wannan fa feedback ne na ba ki na maganin da kike siyarwa mazan mutane ne, idan taimakon matan kike yi yau kin gani, haka ma idan cutarsu kike yi, yau sai ki faɗa musu kyaun maganinki na gaskiya a status, ba na ƙaryar da kika saba yi ba, raguwa kawai". Ya fice daga ɗakin
Ta tsaya tsam tana juya maganganunsa, ta rasa me yake nufi, fa ta yi tsam ta maimaita kalamansa sai ta gane nufinsa, to amma a ina ya samu maganin da take siyarwa ya sha? Ta san dai akwai abokinsa da yake siya, tana kyautata zaton shi ne ya ba shi, nan take ta kudurce a ranta wannan abokin nasa ya ci taliyar ƙarshe kuwa.
08028966015
[12/07, 3:11 pm] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture
*AURE A YAU!*
NA
*SADIYA ABDULRAZAK*
*First class writers association*
Page 9
Sosai Yusuf ya yi mamaki da bayan kwana biyu Zubaida ta ɗago shi a WhatsApp take sake tambayar shi ina alƙawarinta, tsoro da takaici ne suka tarar masa, kenan ma roƙo take yi a wajen customers ɗinta maza? Abun ya ba shi mamaki, ya tura mata dubu ashirin ta account ɗin abokinsa, ta yi godiya ta ɗora a status, hatta abinci tun daga kan na safe har na dare kullum sai ta ɗora a status, ya lura duka rayuwarta a status take, kawai idan kana son saninta to ka juri bibiyar status ɗinta, kullum sai ta ɗora hotonta ko vedio, yana da kishi, idan a son ransa ne ko a dp ba ya son matarsa ta dinga saka hotonta, amma sai ga shi ƙaddara ta haɗa shi da mace irin wannan, tun sanda ta ɗora an ba ta kyautar wayar nan yake ta lura ds wayar hannunta, amma sai ya ga wacce ya sani ce dai, ba ta fara amfani da sabuwar ba, wannan maganin bai cigaba da amfani da shi ba, saboda dam ba shi da buƙatarsa, kuma ba su fasa wannan rayuwar ba ta hana shi hakkinsa, sai dai kawai idan ya ji ba zai iya jurewa buƙatarsa ba ya toshe kunnensa ya karɓa ta ƙarfi.
Yau da daddare da ya dawo ya ga falo fess, ba kamar kullum ba da yake samunsa kamar an yi ƙaramin yaƙi, har tashin ƙamshi gidan yake yi, ya zauna ya ci abinci wanda shi ma ya ji daɗinsa sosai, washegari da safe ya ji motsi a kitchen, yans sha'awar shan kunu don haka ya fita don ya faɗa mata idan da dama ta dama masa, ko kuma shi ya dama, dayake yanayin zafi ne, gajeren wando ne a jikinsa dai singlet, ya shigs kitchen ɗin, ga mamakinsa sai ya ga wata saɓanin Zubaida ce take ta hada-hadarta, yarinya ce da ba za ta wuce shekara goma sha bakwai ba, ta juyo da fara'arta ta ce"Barka da fitowa Alhaji, ina kwana".
Shi kuwa kunya ce ta kama shi, ya juya da sauri ba tare da ya amsa ba ya bar wajen, sam bai ji daɗin yadda ta gan shi da wannan shigar ba, ɗakin Zubaida ya shiga, tana ta sharar bacci, ya tashe ta, ta tashi da tsaki tana cewa"Lafiya?"
Rai a ɓace ya ce"Mun yi baƙuwa a gidan shi ne ba za ki faɗa mini ba?"
Ta ce"Baƙuwa kuma?" Wace ce ta zo?"
Ya ce"Wace ce na gani yanzu a kitchen?"
Ta yi tsaki ta ce"Na manta ban faɗa maka ba, wacce take yi mana aiki wani satin ne aurenta, shi ne na ɗauki sabuwa, kuma ita ba 'yar gari ba ce, to a nan za ta dinga kwana, na ba ta ɗakin baƙi ta zauna a ciki".
Ya ce"Ki ɗauki 'yar aiki ba tare da izinina ba kuma sannan ke za ki tsara a nan za ta zauna har ma ki ba ta ɗaki?"
Ta tashi zaune ta ce"Wai ni Yusuf me kake nema ne? Kai shikenan ba ka so a zauna lafiya? Na gaji da ƙananun mitar da kake yi dama ai, ka dinga faɗan kullum da daddare gida a hargitse, ka san wuni nake yi ina aiki, a