Showing 27001 words to 30000 words out of 34919 words
Chapter 10 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
gajiye nake kaiwa dare, don haka ba ni da lokacin sake gyara gidan, ita kuma Salima iyayenta ka ga dokar da suka kafa, ƙarfe biyar take komawa gida, to dama ina ta son canzata na samo wacce za ta dinga kwana sai ga ma zancen aurenta, shi yasa na jinkita don kar a ce na kore ta ta ka ga babu daɗi, yanzu kuma ita wannan ɗin me za ta tsare maka?"
Ya ce"Ko ba ta tsare mini komai ba ai dai ina da hakkin da za ki sanar mini kafin ki kawo ta gidan ko?"
Ta ce"To yanzu ba ka ji ba?"
Ya ce"Na ji, amma ban amince da tsarinki ba, ba ni da wajen ajiye 'yar aiki, ta dinga zuwa tana tafiya kamar waccen".
Ta ce"Tabɗijan! To a kan me? Ni fa ban ce ka biya ta ba, ni zan biya ta da kuɗina abincinka ma idan ka ce kar ta ci babu damuwa, dama duk rabin cefanen gidan nan yanzu ni ce nake yi, don haka ciyar da yarinya ɗaya ba zai gagare ni ba".
Ya ce"To wa ya saka ki cefanen? Kuma ai status veiws ɗinki kike yi wa ba ni ba, na yi iya ƙarfina idan za ki ƙara ban hana ki ba".
Ta ɗan yi jim, tana tunanin ba ta yi blocking ɗinsa ba? Ta ina yake ganin status dinta?
Ta kau da tunanin ta ce"Yanzu kenan me kake nufi? Ka zaɓi falo ya dinga zama haka babu gyara?"
Ya ce"Me ya hana ki gyara? Kuma dama ina son faɗa miki ki samu wani ɗaki guda ɗaya a gidan nan ya zama na kasuwarki ba falo ba, sotari ina son zaman falo amma ya gagare ni saboda baƙinki, to pls wannan ɗakin na tsakar gida ya ishe ki, ki yi sabgarki a ciki, 'yar aiki kuma ba sai ta dinga kwana ba, idan ba ta da wajen zama a garin nan a haƙura a samu wata, idan babu wata ki hakura ki gyara gidanki".
Ta ce"Idan ba haka ba kuma fa?"
Ya ce"Na san matakin da zan ɗauka".
Ya fice daga daƙin, ta bi bayansa da harara, tana jin tsanarsa tana karuwa a zuciyarta.
Yana fita ta fita, gidan iyayenta ta je, tana kuka take sanar da su abin da ya faru, suka ba ta haƙuri, kuma sun ji haushin shi sosai, saboda ta faɗa musu kawai ba ya son cigabanta ne, so yake nan gaba ma ya hana ta sana'ar gabaɗaya, Mamanta tana kumfar baki ta ce"Ai kuwa bai isa ba, yanzu duk kadarorin da kika siya inda ba kya sana'a zai iya siya miki ne? Kuma sannan nawa yake ɗauka ya ba ki kyauta a wata? Sau nawa yake yi miki ɗinki a wata? Alhaji so yake fa ya kashe ta da ranta a gida". Ta karasa tana kallon baban Zubaida
Alhaji ya ce"Bari dai ya zo mu ji ta bakinsa".
Babu jimawa kuwa Yusuf ya shigo gidan, ya gaishe su a ladabce, babanta ya ce"Yusuf me yake faruwa ne? Zubaida ta kawo ƙararka".
Yana sunkuyar da kai ya ce"To ban san dai me ta ce muku ba Daddy, amma iya sanina abun bai kai na kawo ƙara ba, magana ce wacce za mu tattauna mu biyu mu fahimci juna".
Zubaida ta ce"Kana yi mini tsawa kana yi mini gadara shi ne za ka ce za mu fahimci juna? Daddy wallahi indai zai hana ni sana'ata gara ma kawai ya sake ni, ni dama na gaji da auren fa".
Alhaji ya ce"Yusuf mene ne matsalarka da kasuwancinta? Ka faɗi yadda kake so, amma babu batun ta daina, idan kuma so kake ta daina to ba za ka bar wajen nan ba sai ka rubuta mata takardarta".
Ya ce"Duk abun bai kai haka ba, dama kawai tana yawan yi mini abubuwan raini ne..."
Ya katse shi da faɗin"Ba wannan na tambaye ka ba, wannan tsakaninku ne, za ta saɓa maka kai ma za ka saɓa mata, mene ne matsalarka da kasuwancinta?"
Ya ce"Dama na ce mata ne ta koma ɗakin da yake tsakar gida da baƙinta, saboda sotari ina son zaman falo babu dama, sannan sanda suke gama zaman mai aiki ta tafi ita kuma ba za ta gyara ba, kullum kaca-kaca nake zuwa na same shi".
Babarta ta saka baki ta ce"To ta gaji ya za a yi ta gyara? Zubaida fa tana ƙoƙari sosai, tun tasowarta ba ta aikin komai a gidan nan, silar aurenka ta fara yi, yanzu kuma abubuwa sun fara yi mata yawa, saboda haka dole ne ta samu mai aikin da za ta dinga kwana".
Alhaji ya ce"Yusuf".
Ya ce"Na'am Daddy".
Ya ce"Ka ɗan yi haƙuri na sati ɗaya ta cigaba da zama a falon, kafin satin zan sa a sama mata shago a gyara, sai ya zama office ɗinta, ka ga ba za na ka dinga ganin mata a gidanka ba ko? Maganar mai aiki kuma dole ne ta dinga kwana, tun da ta ce a gajiye take kaiwa daren, to ka ga babu halin ta iya yin gyaran gida, kuma sannan za ta fara fita office, ka ga ya dace a samu wacce za ta zauna a gidan tana kula da yaranku".
Yusuf ya kasa cewa komai.
Alhaji ya ƙara da faɗin"Za ka iya tafiya, an warware matsalar nan".
Ya ce"To na gode Daddy, Momy sai anjima".
Ta ce"Ok".
Ya kalli Zubaida ya ga ta ɓata rai tana bin shi da wani kallo.
Yusuf bai sake tada zancen ba, haka ya zuba mata ido, amma shi kansa yana jin daɗin abincin mai aikin, a tare ma suke fita aiki a Zubaida, ya sauke ta a shagonta, wanda ba ya rabuwa da mutane, mata da maza a abokan kasuwancinta, masu taya ta packaging fa masu delivery. Wannan buɗe shagon ya sa status dinta sai abin da ya yi gaba, maza har shagon suke zuwa siyayya, shi dai ya bar wa Allah komai, yana ta addu'ar Allah Ya yi masa zaɓin alkhairi tsakanin zamansa da ita da rabuwarsu.
GIDAN SUNUSI
Washegari da safe ga mamakin Sabila sai ta ga Sunusi ya tashi da wani ɓacin rai, kamar ba shi ne jiya da daddare yake ta kalamance ta ba, da taliya suka karya, tana ta fargabar yi masa zancen kudin saboda yadda ya haɗe rai, da zai fita ya ce"Ai dai akwai komai ko?"
Ta ce"E".
Ki ciro dubu ɗaya ya miƙa mata ya ce"To ga wannan ki sayi omo, ni ma kayana sun yi datti, ko kala uku ne ki ɗan matse mini".
A da yana siyan omo, amma ɗan karami yake siyowa guda ɗaya,bai taɓa bata kuɗin omo har dubu ɗaya ba, don haka ta yi mamaki, ta ce"Na nawa zan siyo?"
Ya ce"Duk na yadda kika ga dama, kawai ba ki dubu ɗayan na yi".
Ta ce"Na gode sosai".
Ya zo fita ta ce"Yawwa na ce wannan kuɗin na jiya don Allah a dawo min da shi da wuri, saboda so nake na siyo kayan ɗinkin na fara a yau".
Ya sake haɗe rai ya ce"To yaushe garin ya waye? Kin ga Malama kar ki takura min don kin arawa abokina kuɗi".
Ta yi shiru ba ta ce komai ba har ya fice daga gidan. Ta zauna shiru abun ya dame ta, sun saba irin haka da shi, idan ta ara masa kuɗi ƙarshe da faɗa ake ƙarewa kuma ba zai taɓa biyanta ba, amma sanda ya zo karɓa zai kwantar da murya har sai ta ba shi, wannan ɗin ma don ta ga abokinsa ne ya karɓa ba shi ba, kuma mai naƙuda za a ceta, har wajen Azhar shiru bai kira ta da zance ga kuɗinta ba, ta gama yi musu wankin ta zauna ba ta komai, don haka ta kira shi, ya ɗauka ta ce"Sannu da aiki".
Ya ce"Yawwa, ya aka yi?"
Ta ce"Dama wannan kuɗin, na ga..."
Ya katse ta da faɗin"Kin ga me? Dalla kar ki raina min hankali dalla, don kin arawa mutane kuɗi za ki dame ni?"
Ta ce"Ba haka ba ne, amma ai na faɗa maka kayan ɗinki zan siyo".
Ga mamakinta sai ta ji ya yi tsaki ya kashe wayar.
Ranta ya ɓaci, ta rasa me yake yi mata daɗi, tuni nadamar ara musu kuɗin ta kama ta, ta ɗakko kayan ta fara yankawa jiki a mace.
Da daddare da ya dawo yana ta haɗe rai, ita a ganinta ai ita ya kamata ta yi fushi ba shi ba, amma yana nema ya haɗa mata zafi biyu, bayan ya gama cin abincin ta daure duk da gabanta yana ta faɗuwa ta ce"Baban Amal".
Sai kuwa ya zabura ya ce"Wai ya ne, dama na ga sai kallona kike yi, meye?"
Ta haɗiyi wani yawu kafin ta ce"Wannan kuɗin ka ce ba zai wuce safiya ba, ka ga yau na so na fara ɗinkin ma, amma..."
A fusace ya ce"Ke dalla can Malama kin dame ni haka, ke dai da mayya ce idan kika kama mutum wallahi sai buzunsa, cewa na yi ba zan bayar ba? Mutane nawa ne suke bi na bashi amma ba su takura mini ba sai ke? To wallahi idan kika ƙure ni ba zan bayar ba".
Ya tashi yana cewa"Aikin banza aikin wofi kawai". Ya fice daga gidan, bai dawo ba ma sai ɗaya na dare.
Sabila kuwa yana fita ta fara hawaye, ta yi mai isarta, ga shi wannan ɗinkin na gaggawa ne, inda kuɗinta ne ma da sai ta rabu da shi, to amma ba ta da kuɗij siyan kayan ɗinkin da za ta yi musu amfani da shi, shiyasa hankalinta ya tashi.
Washegari ma ba ta daddara ba ya gama komai zai fita, tana ta kokowa da zuciyarta da take ce mata ta rabu da shi, bakinta ya yi mata nauyi sosai, fargaba ce fal ranta, saboda ta san halinsa, amma dai ta daure ta ce"Baban Amal don Allah ka samo mini ko rabin kudin ne, na siyo kayan na fara aikin mutane".
Wata irin juyowa da ya yi sai da gabanta ya ba da rass, a hasale ya ce"Ke don kaza-kazanki ba zan bayar ba, na cinye! Na ƙarfi ne ki ƙwata!".
Ya tsaya a kanta yana zazzare ido kamar zai kai mata duka, ta fara kuka ta yi jarumtar cewa"Ai hakkina ne dole na tambaya, kuma ba zai yiwu ka cinye ba, na faɗa maka kuɗin mutane ne".
Ya ce"To ai shi ne na ce ki ƙwata, na ce na ƙarfi ne".
Ta ce"Ba zan ƙwata ba, amma dai dole ka ba ni".
Babu zato ta ji tass! Ya ɗauke ta da mari, ya ɗora da faɗin"Ke har kin isa kina faɗa ina faɗa? A kan banzar dubu arba'in? To na ce ba zan bayar ba, wallahi idan kika sake yi mini zancen kuɗin nan sai na tattaka ki, ba zan bayar ba".
Cikin kuka ta ce"A kan kuɗina ka mare ni?"
Ya sake matsawa dab da ita kamar zai hau kanta ya ce"An mare ki ɗin, ko za ki rama ne?"
Ta ce"Ba zan rama ba, amma ba zan yafe ba, kuma na gaji!".
Ya sake ɗaga hannu zai ƙara mata, sai kuma ya fasa, ya koma ɗaki, ita ma ɗakin ta shiga ta saka hijjabi za ta fita, ya ce"Gidan uban wa za ki je?"
Ta yi banza da shi.
Ta kai zaure ya ce"To idan kin fita kar ki dawo gidana".
Ta juyo ta ce"Me kake nufi?"
Ya ce"E ki je, ki tafi gidanku kawai".
Ta ji maganar ta dake ta, ga duka ga tsinka jaka? Shi fa ya yi mata laifi, kuma yake cewa ta tafi gida? Yunƙurin fitar da ta yi niyyarta ta shiga gidan maman Nawal, saboda zuciyarta ta yi mata zafi sosai, ta bar gidan ko za ta samu sassauci, sannan ta nemi aron kuɗin da za ta fara yiwa mutane ɗinkinsu, amma da ya ce ta tafi gida sai ta ga gara ta tafin, duk da ba ta sha'awar yin yaji, ta ce"Na tafi gida fa ka ce?"
Ya ce"E haka na ce, ki tafi ai ba wata uwar kike tsinana mini ba".
Ta dawo ta zuba ruwa ta shiga wanka, ta saka kaya masu kyau, ta dauki jaka ta tafi, saboda ba ta da niyyar kwana, za ta je ne kawai a yi musu sulhu ta dawo, yana gidan har ta fita, sannan shi ma ya fita ya rufe gidan.
Tafiya ta fara yi a sanyaye, tana ta tunanin me za ta je gida ta ce? Tana iya ƙoƙarinta wajen ɓoye irin halin da take ciki ga iyayenta, saboda ba ta so su sani su dinga ganin baƙin mijinta, tun da ta riƙe fadan da aka yi mata tun na aure, na cewar ta yi haƙuri, ta yi hakuri, mutane babu adadi sun faɗa mata kalmar nan, kuma sau babu adadi, shi yasa ta haddace ta, sannan ta riƙe cewar ta gani ta ƙi gani, ta ji ta ƙi ji, ta rufe sirrin aurenta, idan sun yi faɗa kar ta kwaso ta kai wa iyayenta ƙara, su kashe su binne, sai abun ya yi tsanani ne za ta faɗaws nashi iyayen, idan duk an yi haka ba a samu maslaha ba sai ta faɗawa iyayenta, shiyasa take ta haƙuri taba danne cutarwar da yake yi mata, yau ɗin ma har ta ɗauki hanyar gidansu, sai kuma ta canza ta nufi gidan iyayensa.
Da ɗan nisa amma haka take tafe a ƙafa, duk da tana da kuɗin hawa babur a jakarta, ko kallon masu baburan da suke tambayarta ko za ta hau ba ta yi, saboda zuciyarta ta yi nauyi, a hankali take ta furta Allahumma la sahla, illa maja'altahu sahla, har ta ji ƙuncin zuciyarta da abinda ya tare mata maƙoshi yana gushewa, da sallama ta shiga gidan cikin rawar murya, Umma tana tsakar gida tana suyar ƙosan siyarwa, da tsirarun masu siya a tsakar gidan, ta ƙarasa kusa da ita ta gaishe ta, ta ce"Lafiya lau Sabila, ke ce da safe haka?"
Gyaɗa mata kai kawai ta yi, tana kallonta dama ta fahimci ba zuwan ƙalau ba ne, ta ce"Ki shiga dakin, ina zuwa".
Umma ba ita ba ce mahaifiyar Sunusi, matar baban shi ce, shi babarsa ta rasu tun yana karami, wajen haihuwar ƙanwar shi wacce tana nan yanzu haka Nurse ce tana aikinta, ita ma Umma tana da 'ya'ya manya, amma dai Sunusi ne babba a gidan, saboda sai bayan babar su ta rasu ya auro Umma, kuma duk gidan Sunusi ne ya fita zakka, shi ne mai shaye-shaye, shi ne mara kirki, kodayake shaye-shayen ma duk zai iya zama silar canza halayyar tasa, idan ka ga ƙannensa duk a nutse kowa sana'arsa kawai ya saka a gaba.
Ta kai kusan awa ɗaya a ɗakin sannan Umma ta gama komai ta shigo ɗakin, zuwa lokacin Sabila har ta ɗan samu sauƙin zugin zuciyarta, ta miƙa mata kofin koko da kwano mai murfi wanda ta san ƙosai ne a ciki, ta zauna tana cewa"Wash Allah, Sabila na bar ki ke kaɗai, ki karya".
Ta ce"Sannu Umma, ai na karya ma a gida".
Ta ce"To kuna nan ƙalau dai ko?"
Sai ta fara hawaye ta girgiza mata kai alamar a'a.
Ta ce"Subhanallah me ya faru? Ke da Sunusin ne?"
Ta ce"E Umma, cewa ya yi na tafi gidanmu" Sai ta fara kuka, saboda ita fa wannan kalmar tafi gidan naku ta yi mata ciwo fiye da hana ta kuɗin da ya yi.
Umma ta ce"Kayya! Sunusi ba shi da kirki fa, wallahi duk da ba kya kawo ƙara na san haƙuri kawai kike yi, saboda kowa ya san halin shi, zama da shi sai mai haƙuri, auren ma an yi ne ana fargabar zai dore ko akasin haka, to dayake kina da haƙuri na san daurewa kawai kike yi, yanzu mene ne ya faru?"
Ta kwashe komai ta faɗa mata, ta ɗora da faɗin"Yanzu saura kwana biyar su karɓi ɗinkin, kuma ba ni da hanyar samun wani kuɗin".
Ta ce"Kayya, amma bai kyauta miki ba, na san halinsa tsaf a kan kuɗi, wallahi zai aikata fiye da wannan ma, Allah Ya shirya, ki yi haƙuri, kin ga yanzu ma baban shi yana nan, amma bai kamata a kai masa ƙarar nan ba, saboda yanayin jikinsa, ga shi da saka abu a ransa yanzu sai hawan jininsa ya tashi, amma bari na kira 'yan'uwanshi a waya, su san yadda za su yi da ke".
Sabila ta tashi tana cewa"Bari na gaishe da Baban" ta fita ta shiga ɗakin nasa, ita kuma Umma ta kira babban ɗanta ta faɗa masa, sannan ta kira Hajara ƙanwar Sunusin ita ma ta faɗa mata.
A gidan Sabila ta wuni, da dai ta ga lokacin tashin yara ya yi sai ta kira wata maƙociyarsu wacce ita ma yaranta s makarantar suke, ta roƙe ta ta ce don Allah idan an kawo yaranta daga makaranta ta saka mai babur ɗin ya dakko yaranta su zauna a gidan Maman Nawal.
Da yamma Hajara ta zo gidan, da kuɗi cash dubu arba'in ta ba wa Sabila tana ta ba ta haƙuri, saboda ita ma tana jin tausayin matar da ta iya zama da ɗan'uwan nata, saboda ta san halinsa ta san baudewarsa, ƙaninsa Adam ne ya ba da dubu ashirin ita ta cika ashirin ɗin, shi ne ta ciro mata kuɗin tun a hanya, ko da ta tambaye ta ko da wata matsalar bayan wannan, ba ta iya faɗa mata komai ba, ta ce ƙalau suke zaune, haka ba ta furta marin da ya yi mata ba, ba ta san dai lokacin da suka yi waya da Sunusin ba, amma ta ga ya zo bayan magriba, Umma tana ta yi masa faɗa ko a jikinsa, kuma ta yi mamakin yadda bai nuna fushi ba, sai ma cewa Hajara da yake yi me zai samu, suka yi masa nasiha tare da ba ni hakuri, yaba ta cewa"Ya wuce, ba zai sake faruwa ba".
Sannan ya kalli Sabila babu yabo babu fallasa ya ce"Ke tashi mu tafi ko?"
Ta tashi tana yi musu godiya, tana kallo Hajara da ta rako su ta faki ido ta saka masa kuɗi a aljihunsa, Sabila ta raya a ranta wani abun sai ɗan'uwanka na jini.
A hanya babu wanda ya ce da wani komai har suka ƙarasa gida, ta shiga gidan Maman Nawal shi kuma ya wuce gida, bayan sun gaisa take ce mata"Wai ina kika tafi babu sallama?"
Ta ce"Fitar gaggawa ce wallahi, gobe zan ba ki labari".
Yaran suka taso, ta haɗo su da kular abinci.
Da suka shiga gidan ta tarar yana wanka, ita kam ta ci tuwo ma, su