Showing 18001 words to 21000 words out of 34919 words
Chapter 7 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
san ko aurenka na farko wanda ka ƙare a gudun hijira saboda sojoji suna nemanka ban damu ba, ka zo ka auro mai ciki nan ma muka zauna lafiya, ka auro mai aljanun tsafta, to ita wannan 'yar gwal ce da zan damu?"
Ya ɓata rai sosai ya ce"To ya ishe ki haka kuma, me ya kawo tashin-tashina? Ba na son ƙananun maganganu, aure ne dai sai na yi, sai dai ku mutu".
Sahura ta ce"A'a babu batun mutuwa, ko ciwon kai ba zan yi ba, abu da ba a kanmu za ta zauna ba? Abu ɗaya zai sa ka ga ikon Allah daga gare mu, idan ka ce za ka rage mana cefane saboda ka yi aure, ko ka fara nuna mana bambancin to fa nan ne kuma sai inda ƙarfina ya ƙare".
Ya kalle ta sheƙeƙe ya ce"To me za ki yi? Ai komai yanayi ne yake janyowa, kun san idan nauyi ya ƙaru dole wasu abubuwan za su canza, tun da Hausawa sun ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai".
Sahura ta ce"Ai wannan maganar duk ƙarya ce, sai dai idan ba a zabga masa man yadda zai ji ba, ko ba haka ba Saude?"
Ta ce"Ƙwarai kuwa haka ne, har yawa ma mai zai iya yi a dambu, indai an saka wanda zai isa ɗin".
Ya ce"To ba sai da kuɗin da za a zuba ya isa ɗin ba?"
Saude ta ce"Dole ne a dafa dambun? Ai ba a ce idan ba a ci ba za a mutu, don haka idan babu kuɗin mai sai a haƙura a ci shinkafa".
Sahura ta ce"Wannan shi ne maslaha, domin kuwa adalci ya zama dole, mata kiwo ne a wajen miji, haka miji kiwo ne a wajen matarsa, mu ƙaunarka muke yi, saboda haka dole ne mu tabbatar da ka yi adalci a gidanka, don kar ka tashi da shanyayyen ɓarin jiki".
Saude ta ce"Wannan gaskiya ne".
Sahura ta ce"Kuma dai ba za ka so na cigaba da binka kasuwa karɓar kuɗin cefane ba, tun da ai babu daɗi".
Hamza ya ɓata rai ya ce"Duk ku ƙaraci rashin mutuncinku, wai ma a ce ni da gidana an raina ni, ina faɗa ana faɗa? Hmm dama an ce haɗin kan matanka ba alkhairinka ba ne, gara wanda kullum za ka raba su dambe, amma kun haɗa kai ko kishin junanku ba kwa yi, saboda kun ga ba ni da kuɗi ba ku ɗauke ni a bakin komai ba, babu damuwa, zan auro wacce za ta san mutuncina ta dinga kula da ni tana ba ni girmana a matsayin miji".
Sai kuma ya yi murmushi ya ce"Hmm Hamza angon Mardis, Allah kai damo ga harawa".
Sannan ya ce"To kun san dai lefe zan duƙufa yanzu na ƙarasa haɗawa, don haka sai an yi haƙuri da yanayin gidan, komai ya samu ku karɓa kawai ku gode Allah!".
Sahura ta ce"Babu fa wannan maganar, tun da auren nan ba wai dole ya zame maka ba, ka bi haɗa lefenka a hankali mana".
Ya ce"Idan kuma dole na ɗauka fa?"
Ta ce"To a yi dai mu gani".
Ya ce"Ku je na sallame ku, dama don kar ku ji a gari ne ku ce ban kyauta muku ba".
Suka tashi suka fita, ɗakin Saude suka shiga suna ta tattaunawa.
To fa tun daga lokacin sai Hamza ya fara maƙe hannu, a hankali yake rage cefane, a da yana siyo crate ɗin ƙwai ya raba musu, zai siyo kayan shayi madara da milo, biredi har da bota, amma yanzu gabaɗaya ya daina, sai ma ya koma ajiye musu fulawa da taliya, kullum da safe su ne abun sarrafawa, sai dai a yi ta wainar fulawa, don ko fanke aka soya ya yi ta faɗa kenan yana cewa za a ƙarar masa da man gyaɗa, ƙarshe ma sai ya daina siyo man gyaɗa sai man ja, gero kuwa rabin buhu ya siyo, ana ta yin koko, babu batun shan shayi, haka kayan miya ma wanda yake siyowa a sati sau uku yanzu sau ɗaya yake siyowa, sai dai a yi ta cin mai da yaji, ita dai Saude ta zuba masa ido kawai, duk abin da ya kawo ba ta cewa komai, Sahura dai tana yawan yi masa ƙorafi, duk ranar da ta yi haka za su yi ta bala'i, don ma Saude tana tausarta, daga baya dai suka yi shawara, suke haƙura su yi cefanensu miya har da nama, shi kuwa su zuba masa mai da yajinsa, kuma yana kallo ba ya cewa komai, tun da ya san ba shi ya kawo ba. Amma a bayan idonsu idan ya je zance babu abin da ba ya faɗawa Mardiyya, ya ce shi zai yi cefanen komai amma sai a zuba masa mai da yaji, kawai saboda suna son ƙure haƙurinsa, don sun ga zai yi aure.
Idan suna irin maganar Mardiyya ita mamaki take yi, gani take lallai matan Hamza ba su da hankali, yanzu a zamanin nan ka samu miji mai haƙuri irin wannan amma ku haɗa kai ku dinga wulaƙanta shi? Murya a sanyaye take cewa"Wallahi My Love tausayi kake ba ni, har na matsu a yi auren nan, don na share maka hawaye, na nuna maka yanzu ka yi aure".
Hamza ya marairaice kamar abun tausayi ya ce"Hmm kin gani dai, kin ji yanayin rayuwar gidana, kin ji silar ƙarin aurena, sun haɗa kai suna ta gwara ni, babu ɗaya da zan jingina na ji daɗi, don Allah Baby idan kin shiga gidan nan duk daɗin bakin da za su yi miki kar ki yarda da su, domin ni da kunnena na ji suna tattauna a kan duk yadda za a yi ba za su bar ki ki zauna a gidan nan ba, to wallahi duk wani janki a jiki da za su yi na yaudara ne, ni ne na kawo ki gidan nan, ni kaɗai kika sani".
Ta ce"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah sai na share maka hawayenka kuma ai na san kaidin kishiya, ba ga ta nan tana gwara yayata ba? Wallahi sai dai su su fita su bar gidan ba dai ni ba, ban da baƙin hali ku ba ku ja miji a jiki ba kuma ku hana shi zama da wata? Kishin banza da wofi".
Ya ce"Kin ji dai yadda abun yake baby, ni wallahi wannan hana ni jar miyar ma yanzu duk ya fi damuna, yanzu na na san idan ba je gida ita zan tarar fara tass da man ja, ni ban ma taɓa ji an ci macaroni da yaji ba sai a wajensu".
Ta ce"To ko dai miyar zan dinga yi maka kana ajiyewa a ɗakinka? Ko kuma ka dinga cin abincin a nan gidanmu".
Hamza ya yi murmushi yana sosa kai ya ce"Raba ni da abun kunya, ina suruki a sama mini kwano a gidanku? Da za ki dinga yi mini miyar dai da na ji daɗi".
Ta ce"Me zai hana? Indai miya ce gobe ma zan yi maka in sha Allah!".
Ya ce"Ma sha Allah! Allah Ya yi miki albarka baby, na fara ji a jikina yanzu zan yi aure, da duk auren jekanayika na yi, Allah Ya mallaka mini ke ki cigaba da kula da ni".
Tana sunne kai ta ce"Amin".
Sannan ta ɗora da faɗin"Miyar kaji za a yi maka ko ta jan nama? Ko kuma kifi kake so?"
Ya ce"Duk wacce ta samu, amma dai kyanta ta jan naman, kin ga 'yan tsokoki ne kawai zan taune abuna, ba ma sai sun ga ƙashi ba".
Ta ce"Hakane, to kayan miyan za ka bayar ko kuɗin?"
Ya ji wani dam! Don shi a zatonta da kuɗinta za ta yi, ko ta ɗibi kayan miya a gidansu, ashe dai ya gudu ne bai tsira ba, bai bawa na gida ba, zai bawa ta waje ta yi masa, ya ce"Duk yadda kika ce, wanne ya fi?"
Ta ce"Ka ba da kuɗin kawai, dama gobe za a aike ni kasuwa, sai na yi naka cefanen".
Ya ce"To, amma yanzu babu cash a jikina, zan yi miki transfer".
Ta ba shi account number, ya tura mata dubu goma yana jin kamar ya fasa kuka. Washegari kuwa yana dawowa daga kasuwa gidansu ya zarce ya karɓa, ya yi mamakin ganin miyar dubu goma a cikin ƙaramar kula, amma babu halin ƙorafi haka ya karɓa yana godiya, a hanya ya tsaya a shago ya karɓi baƙar leda ya saka a ciki, don kar matansa su gani.
Ranar Saude ce da girki, kuma sanda ya dawo ya shiga ɗakin idonta a kan ledar, a tunaninta ma ko tsire ne ta siyo zai ci, ta bi bayansa ta kai masa abinci, farar taliya ce da man ja da yaji, ya buɗe ya yi tsaki kamar kullum, ta nemi waje ta zauna tana kallon ledar, ya ce"Me kike jira ne?"
Ta ce"Babu komai, fira zan taya ka".
Ya ce"Tafi harkarki kawai ba na buƙata".
Ta ce"To kuma sai ka ce dai a kanka na zauna? Soyayyar ce ta motsa yau, son kallonka nake".
Ya yi wata shegiyar dariya ya ce"Yaudarar ce ta motsa dai za ki ce, kuma na san wannan ledar da kika ƙyalla ido kika ga na shigo da ita kike yi wa, to gajerun wanduna be na siyo ba wata uwar ba".
Saude ta ce"Uhm!".
Sai dai ba ta da alamar tashi, ya ce"Kamar ya Uhm!? Ba za ki fita ba ne?"
Ta tashi tana cewa"Ai shikenan".
Ta fita, sai dai fa ba nisa ta yi ba, maƙalewa ta yi jikin ƙofar ta motsa labulen kaɗan tana leƙensa da ido ɗaya. Tana fita ya janyo kular ya buɗe, "Ma sha Allah!" Ya furta ganin mai lumƙum a saman miyar, ya kwashe yajin kan taliyar ya saka cokali ya zuba miyar, ya saka nama guda uku ya juya ya fara ci, Saude tana kallonsa ya ɗauki waya ya yi kira, bayan sun gaisa ya ce"Baby amma dai kin tashi kaina da miyar nan taki, wallahi ga ni sai zuba santi nake yi, ke ba dan kar na yi ƙarya ba da na ce tun da nake ban taɓa cin miyar da ta kai rabin wannan a daɗi ba, baby ke haske ce a rayuwata, idan kika shigo gidan nan na san har ƙiba zan ƙara".
Saude ta jinjina kai, domin ta fahimta, daga gidan buduruwarsa aka yi masa miya, takaici ya kama ta, ta saki labulen ta tafi ɗakinta, ko Sahura ba ta faɗawa ba, dare ya yi sun kwanta bacci, can ta farka tsakar dare, ta sakko daga gadon, ta haska ɗakin, a can bayan akwatinsa ta hango kular miyar, ta ɗauke ta cak ta fice daga ɗakin, ɗakinta ta shiga ta bararraje ta tsoma hannu a miyar ta fara tsamo naman tana ci, sai da ta cinye tass duk yawansa, sannan ta wanke hannu ta ɗakko gishiri ta zabga a miyar, ta rufe kular ta koma ɗakin nasa ta ajiye ta a inda ta ganta, ta koma gado ta kwanta ta cigaba da baccinta.
Dayake yanayin zafi ne, ga shi an sakawa miya hannu, kuma tana rufe a kula, kafin safiya ta fara bugawa, shi kuwa Hamza da safe ya fita ya siyo sunƙumemen biredinsa ya shige ɗaki, ya ɗakko miya zai dangwala ya ci, kawai yana buɗe miya ya ji wani gumm bashi ya daki hancinsa, shi ba abun ya fita da ita ya ce su ɗumama masa ba, haka dai ya daure ya fara dangwalarta da biredin, yana kaiwa bakinsa ya ji uban gishiri da tsami, gabansa ya faɗi ya shiga mamaki, shi dai ya ga jiya sam bai ji alamar ma akwai gishiri a miyar ba, amma yau ga shi nan kamar zai tsinka masa harshe, ransa ya ɓaci sosai, da ya ga ƙiri-ƙiri zai yi asarar dubu gomansa, sai ya yi nufin ya tsince naman ko ɗauraye su ne ya yi ya ci ye, ya laluba ya ji babu alamar nama ko yanka ɗaya, mamaki ya kama shi, don kuwa jiya ya ga nama da yawa kuma guda uku kawai ya ci, iya tunaninsa ya rasa me ya faru, kansa ya kulle, haka dai ya rufe miyar nan ya yi wanka ya sha koko da biredi, ya tafi kasuwa rai babu daɗi.
08028966015
[10/07, 2:11 pm] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture
*AURE A YAU*
NA
*SADIYA ABDULRAZAK*
*First class writers association*
Page 7
Kafin dare miya ta gama kumbura a kula saboda zafi, dama ya san ba za ta ciwu ba, don haka da daddaren da aka kawo masa abinci bai bi ta kan miya ba, Sahura ce da girki, kuma abin da ya ba shi mamaki da ya shigo ya ga yaranta suna cin doya da miya, amma yanzu ya buɗe kula ya ga shinkafa da mai da yaji ko wake babu, ya ɓata rai yana kallon abincin ya ce"Ba doya na gani yanzu a tsakar gida ba?"
Ta ce"Ita ce, yau ita muka yi sha'awa ni da yara".
Ya ce"To zubo min ni ma".
Ta ce"Sauranta kenan ba sakawa yaran, dama tun rana na yi, kuma kai da kai ce".
Ya haɗe rai sosai ya ce"Kenan ni yanzu a gidan nan ranar Juma'a ne kawai zan dinga ganin jar miya? Ko albarkar jollof ba zan samu ba, kullum sai dai fara da mai, so kuke basir ya yi mini illa na daina amsa sunan namiji ko? Saboda ana min baƙinciki zan yi aure, to ta Allah ba taku ba wallahi".
Sahura ta ce"Yau na ga ikon Allah! Abin da ka kawo ai shi za ka ci, mutum zai tsakuwa ne ya saka ran girbe tsaba? A'a kai ma dai da gangan za ka gaji da cin yaji" Ta ƙarasa maganar da 'yar dariya.
Ya ƙwalawa Saude kira, ta shigo ɗakin tana cewa"Sannu da zuwa".
Ya ce"Yawwa, ɗauki shinkafar nan ki saka min miya ko ki zubo mini abin da kika dafa".
Ta ce"Gurasa da miya na yi kuma mun cinye tass".
Ya jinjina kai ya ce"Duk ku yi son ranki na ɗan lokaci ne". Haka ya ci shinkafar don yunwa ba don daɗi ko son ransa ba. Yau bai je zance ba, tsakar dare ya tashi ya wanke miyar nan ya zubar, ya saka omo ya wanke mata kularta ya ajiye, a ransa yana Allah Ya isa dubu gomansa, washegari ya mayar mata da kular, da ta tambaye shi ko gobe za a ƙara yi masa? Sai ya ce ta bar shi ai ya yiwa matan nasa gargaɗi sun ba shi haƙuri sun ce za su gyara halinsu.
GIDAN SUNUSI
Kwanaki suna ja, haka kayan abincinsu suna ƙarewa, ta ga saurin ƙarewarsu sosai, musamman taliya da macaroni, tun da su yake siyarwa ba ya taɓa shinkafa, yanzu saura shinkafar ita ma kaɗan, babu mai babu magi, gara kayan miya duk sati yana kawo mai yawa, taimakon da Allah Ya yi mata shi ne kasuwar ɗinkin nata ta farfaɗo, ta samu ɗinkunan ankon bukunkuna da ake ta yi, azumi ya gabato masu shirin yin aure kafin azumi suna ta yi, da kuɗin ɗinkin take samun na cefane da sauran abubuwan, kuma kullum Maman Nawal tana kawo mata abinci na rana da na dare, tana dafawa ne kawai saboda Sunusi, don idan ta su ne za su ci su ƙoshi da abincin da maman Nawal take kawo musu, azumi ya rage sati biyu Maman Nawal ta yi tafiya, garinsu ta tafi biki, za ta yi sati ɗaya, ga shi a ranar shinkafarsu Sabila ta ƙare tass, da daddare take ce masa"Baban Amal wannan shinkafar nan fa daga wannan da kake ci yanzu ta ƙare tass, dama ina ta faɗa maka ta kusa ƙarewa, akwai dai rabin taliya za ta ishe mu mu karya da safe".
Ya ce"To Allah Ya hore".
Ta ce"Amin".
Washegari suka karya da taliyar, da da zai fita ta ce"To yanzu ya za a yi? Me za mu ci da rana?"
Ya ce"Ke ni fa ba ni da shi, ko sisi ban tashi da shi ba".
Ta ce"To ya kenan za a yi?"
Ya ce"Oho!"
Ya yi ficewarsa, ranta ya ɓaci, amma ta danne, tana ta jiran ko zai dawo ya kawo ko kuma zai yi aike ta ji shiru, ganin yara sun kusa tasowa daga makaranta sai ta siyo taliya leda ɗaya ta dafa fara, saboda babu kayan miyan ma, ta kira shi a waya ta ce"Na sayi taliya na dafa, ko za ka siyo mana mai, tun da akwai barkono sai a ci".
Ya ce"To Allah Ya sa a samu". Ya katse wayar.
Har yaran suka dawo shiru bai kawo ba, don haka ta siyo, dama tana da kuɗin kawai dai tana son ya siya ɗin ne, saboda tattala kuɗinta take yi don su samu kayan sallah, tun da ba yi musu yake ba. Can wajen la'asar ya kira ta a waya, ya ce"Har yanzu ba a samu man ba?"
Ta ce"An samu, na siya".
Ya ce"Ok" Ya kashe wayar.
Ba wani ƙoshi ta yi da daddaren ba, tun da leda ɗaya ce tun rana, amma haka ta ajiye masa tashi, har da siyan salak ta yanka, da ya dawo ya ci ya ƙoshi, ya yi wanka ya tafi zance, ya juyewa Karime kudin aljihunsa. Da ya dawo wajen sha ɗaya take ce masa"Yanzu da safe da me za mu karya? Babu komai a gidan fa".
Ya yi tsaki ya ce"Don Allah Sabila kar ki saka mini ciwon kai, ku kwaɗa ni ku cinye mana, ku mata babu abin da kuka sani sai a baku, kin mayar da ni ɗan wahala, kamar wani bawa ba ni da aiki sai bautar ku, komai na samu a kanku yake ƙarewa ke da yaran nan, to na gaji ba zan kashe kaina na, idan ina da shi a ci, idan babu kowa ya sha ruwa,ni ma ban ci ba ai".
Ta yi shiru har ya