Showing 21001 words to 24000 words out of 34919 words

Chapter 8 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt

gama. Da safe ta zari kuɗi ta siyo gawayi, gasara, suga, sannan ta tsaya a wajen mai ƙosai ta sayi fanke, ta dama koko suka sha, ta ajiye masa nasa a jug, fanken ne dai ba ta ajiye masa ba, saboda kaɗan ta siya, kokon ma wanda ta ajiye masa ya yi biyun wanda ta sha, ba ƙoshi ta yi ba, kawai dai don kar ya ce don ba shi da shi ita ce ta siya ta ajiye masa kaɗan, tun da ai shi ma ya ciyar da su, yanzun don ba shi da shi ne.

Ya tashi ya gama abin da zai yi, yana ta ɓata rai kamar wanda aka yi masa laifi, ta janyo kokon ta miƙa masa, ya buɗe ya yi tsaki ya ce"Da me kuka sha kokon?"

Ta ce"Fanke ne, ɗan kaɗan ne shiyasa ban ajiye maka ba".

Ya ce"Saboda dai an ga ban ba da kuɗi ba, kuɗinki naki ne, kuɗina ne na banza na bitalmanu kowa ma ya ci, ban da talauci ma ke har kya yi mini wulaƙancin da kike yi mini?"

Da mamaki ta ce"Baban Amal, me nake yi maka?"

Ya ce"Dalla rufe mini baki, ban sani ba, kin iya kwantar da kai kamar mage ta so cuta, hmm komai lokaci ne, gaba kaɗan za ki sha mamaki".

Ya ɗauka yana sha yana ɓata rai, ita kuwa ta tashi ta bar masa ɗakin, a tsakar gida ta zauna, da ya gama ya fito ta ce"To me za a yi da rana?"

Ya yi kamar bai ji ta ba.

Ta ce"Zan auno fulawa na yi ɗanwake ka siyo mai da barkono".

Ya ce"Allah Ya sa na gani". Ya fice.

Ta sauke ajiyar zuciya, ta san ba zai siyo ba tun da ya ce haka, idan ba haka ba ai da sai ya ba ta kuɗin ta siyo, haka ta rabu da shi yau ma ta zara ta yi cefanen komai, kamar za ta yi kuka saboda kuɗinta sun fara yin ƙasa, tana da buƙatu sosai, wanda kuɗin da take samu a ɗinkin sun isa su yi mata su, inda a ce mijinta yana yi mata komai da yake nauyinsa ne, wannan matsalar ita take dakushe mata da yawa, sai ka ga mace tana sana'a tana samun kuɗi daidai gwargwado amma ka ganta kullum jiya-iyau, ba ta iya yi wa kanta komai, wasu har su dinga zargi ko ƙananun maganganun me take yi da kuɗin? To namiji ba ya ciyar da kai ya bar maka gida ne za ka iya tarawa? Dole kana samu za ka kashe, ba za ka taɓa cin ribar wahalar nemanka ba, ballantana wani naka ya amfana.

Ta yi zaton zai dawo da mai, amma sai ta ga ya shigo hannu na dukan cinya, shi fa ko 'yar tsarabar yara ba ya yi, ba zai taɓa siya musu ko da biskit ba, sannan kamar ba yaransa ba, babu wata shaƙuwa a tsakaninsu.

Tana falo tana ɗinki ya dawo, abincinsa yana ɗakin gadon, yana zuwa kuwa kular ya fara buɗewa, ya ce"Hmm! Dama tana da kuɗin ai, kawai baƙin hali ne ya sa ba za ta ci ba, sai ta noƙe tana jiran nawa na banza, da kika ji uwar bari ba ga shi nan kina fito da kuɗin ba?"

Da yake yunwa yake ji, ko wanka bai yi ba ya zauna ya fara ci, ya yi rabi Sabila ta biyo shi ɗakin, ta ce"Sannu da zuwa, na ƙarasa aiki ne ba na so na saki".

Ya ce"Yawwa".

Ta ce"Na zata za ka taho da man".

Ya yi shiru.

Ta ce"Da ka taho da shi, ka ga na rage fulawa gobe sai a soya wainar fulawa, a siyo gasara a dama koko ko?"

Ya ce"To idan ba ni da shi sata zan yi? Ni yau yadda na fita haka na dawo, ko sisi ban yi ba".

Ta ce"Shikenan".

Washegari ma dai sai itan ce ta yi cefane tun safe har dare, ai kuwa cikin sati ɗaya kuɗin hannunta suka ƙare, da zai fita ta marairaice ta ce"Baban Amal, wallahi yau kuɗina ba za su isa komai ba, sun ƙare, don Allah ko taliya ce ka samo mana".

Ya ce"To Allah Ya sa na samu".

Haka ta gaji da jiransa, sai garin kwaki ta siyo da sauran canjinta, suka sha, suka rage wanda za su jiƙa da daddare, can da la'asar sai ga shi ya aiko yaro, ta karɓi ledar da murnarta tana buɗewa ta ga kayan miya ne zalla, har da green beans da su caras da kabeji, ko a nufinsa me za ta dafa oho?

Dayake tana da dakakken ƙuli-ƙuli sai ta yanka kabejin ta yi kwaɗo, suka ci da daddare suka sha garin kwakin, shi ma ta zuba masa nasa a kwano ta ajiye. Ya dawo ya yi wanka ya zauna ya janyo kula, yana buɗewa ya yi saranda saboda ganin kabeji, a fusace ya ƙwala mata kira "Sabila! Ke Sabila!".

Sai da gabanta ya faɗi, ta taho da sauri tana cewa"Baban Amal lafiya?"

Ya yi ball da kular ta bugi ƙafarta, fuska kamar bai taɓa murmushi ba ya ce"Uban meye wannan?"

Ta ce"To ai na ga shi ka kawo".

Sai kuwa ya tashi a fusace ya yi kanta, ya ɗaga hannu kamar zai mare ta, amma bai sauke ba, tsoro ya kama ta, ta kare kanta da hannuwanta tana jiran saukar duka, cikin hargagi ya ce"Ke don kaza-kazanki ni kike faɗawa ai shi na kawo? Ni kike faɗawa baƙar magana? Zan gwaggwara ki a nan wajen wallahi".

Ta matsa da baya ta ce"Ni fa ba haka nake nufi ba, to ai babu abincin ne".

Ya ce"Kuma saboda daƙiƙanci shi ne za ki yanka min kabeji ki saka a kula na yi zaton abinci ne? Akuya kika mayar da ni?"

Ta girgiza alamar a'a, hawaye ya sakko mata, ya yi ƙwafa ya ce"Za ki gane kurenki, wallahi na kusa fara saka miki hannu, don na lura rainin da kika yi mini kullum ƙara gaba yake, jakar banza jakar wofi".

Ya fice daga gidan yana ta zage-zage shi kaɗai.

Ita kuma ta zauna a bakin gadon ta fara kuka, har yanzu gabanta bai daina faɗuwa ba, saboda ta tsorata da yanayinsa na yau ɗin, ta ci kuka ta gode Allah, an fara kiran sallar isha'i Amal ta shigo ɗakin gadon ta miƙa mata wayarta, ta duba ta ga Maman Nawal ce, ta ɗauka tana kokarin danne damuwarta, ta ce"Maman Nawal".

Ta ce"Na'am Maman Amal mun dawo tun da yamma fa, ba na jin daɗin jikina ne, ki ɗan shigo don Allah idan da dama".

Ta ce"To ga ni nan".

Ta tashi ta wanke fuskarta, ta rufe gidan ta saka yaran a gaba suka shiga gidan nata, ta same ta kwance a kujera, kana kallon idonta ka san ta yi kuka, kuma yanayinta ya yi kama da marasa lafiyan, Sabila ta ƙarasa tana cewa"Subhanallah kuma da jinya kika dawo? Me ya same ki".

Ta tashi zaune a hankali, ta yi murmushin yaƙe tana janyo yaran ta ce"Ba ku yi bacci ba? Nawal ta yi bacci dayake ta kwaso gajiyar mota".

Sabila ta zauna tana cewa"Sannu da hanya, ya jikin?"

Ta share hawaye ta ce"Da sauƙi".

Ta ce"Zazzaɓi kike yi ne?"

Ta girgiza mata kai alamar a'a.

Ta ce"To mene ne?"

Ta ce"Gobe idan na shigo zan faɗa miki".

Suka yi shiru na 'yan sakanni kafin ta tashi ta je kitchen ta ɗakko mata roba babba mai murfi, ta ce"Ga wannan, a hanya ya siya mana, kuma ba ci zan yi ba, shi kuma ya tafi ma ba kwana zai yi a gidan ba, ku je ku ci".

Sabila ta karɓa ta ce"Mun gode, amma me za ki ci? Idan jikin ne ki faɗi abin da kike so sai na shiga na dafa miki, ina da kayan miya ma a gida".

Ta ce"A'a cikina ne babu daɗi, zan shayi kawai".

Ta ce"To bari mu koma sai da safe, Allah Ya sawaƙe".

Ta ce"Amin".

Ta rako su tsakar gida tana cewa"Minal gobe zan kawo muku tsarabarku kun ji?"

Suka ce"To".

Sabila tana ƙoƙarin buɗe gidan, suka ga Sunusi ya dawo hannunsa ɗauke da leda, sosai ya sake haɗe fuska ya ce"Daga gidan uban wa kike?"

Ta fara inda-inda cikin tsoron ta ce"Maman Nawal ce ba ta da lafiya na je na duba ta". Hannunta dai rawa yake ta ma kasa buɗe kofar, saboda ita sam ba ta son hayaniya da faɗa, yanzu sai ta gigice ta fara kuka.

Ya ce"Tun da ita uwarki ce shiyasa kika samu lasisin fita ba sai kin tambaya ba ko?"

Ta girgiza kai ta ce"Ba haka ba ne wallahi, da na ga wai kusa ne, kuma ka san muna da kyakkyawar alaƙa".

A tsawace ya ce"Dalla rufe min baki!".

Ta tura ƙofar suka shiga, idonsa a kan robar, yana son ganin mene ne a ciki, don haka shi ma falon ya shiga ya zauna, ya sa Amal ta ɗakko masa plate ya juye indomi fa ƙwai da ya siyo ya fara ci, Sabila ta buɗe robar, ta ga gurasa ce da nama mai yawa, ta tashi ta ɗakko faranti ta zuba masa ta je ta ajiye a gabansa, ta matsa kusa da yaran tana cewa"Ku saka hannu mu ci".

Ya ce"Kenan roƙo kika je yi ko? Kin je kin faɗa mata yau kabeji ne a gidan ko? Tun da ƙanwar babarki ce".

Ta ce"Wallahi ba haka ba ne, kirana ta yi ta faɗa mini ba ta da lafiya, kuma cewa ta yi ta ƙoshi shiyasa ta ba mu".

Ya ja dogon tsaki, kafin ya ce"Wallahi Sabila ki kiyaye ni, ki yi mugun kiyayata, ki shiga hankalinki fa!".

Ya gama cin indomin, ya janyo gurasar ma ya gama da ita, ya sha ruwa ya bar gidan.

Washegari yaran ba su je makaranta ba, saboda babu abinci, ba ta son tura su makaranta da yunwa, kuma haka ya tsallake ya bar gidan, wajen ƙarfe goma Maman Nawal ta shigo, ta ci karo da yaran a tsakar gida, ta ce"To, me ya hana ku zuwa makaranta?"

Sabila ta ce"Hutawa suke yi".

Maman Nawal ta ce"Hutu kuma? Ko dai kuɗin makaranta ne ba a biya ba?"

Minal ta ce"Abinci ne ba mu ci ba".

Maman Nawal ta kalli Sabila, ba ta ce komai ba ta juya za ta fita, Sabila ta ce"Don Allah ki rabu da mu Maman Nawal, ai ba nauyinki ba ne, wanda yake da alhakin ciyar da mu ma bai damu da ganinmu da yunwa ba sai ke?"

Ta ce"Ni ma ina da alhaki ai, ko ke ba maƙociyata ba ce tun da na san halin da kike ciki kuma ina da ikon taimakawa ai kuwa ina da hakki a kai".

Ta koma gida, ta haɗo musu shayi, da babban biredi har da bota, ta kawo, suka karya, jikinta duk a sanyaye.

Sabila ta ce"Jikin ne? Wai mene ne yake damunki?"

Ta ce"Jinyar nan tawa fa ta zuciya ce ba gangar jiki ba".

Sabila ta ce"Don Allah mene ne damuwarki?"

Ta sauke numfashi ta ce"Tafiyar nan fa da na yi ba biki na je ba, yaji na yi, saboda ya ƙi sakina, amma sai ga shi yana zuwa biko ko tattaunawa iyayena ba su ba da damar yi ba, suka ce na bi shi mu tafi, Maman Amal na gaji". Ta fara kuka.

Sabila ta ce"Don Allah mene ne matsalar mijinki?"

Ta ce"Ai na faɗa miki sirrina ne wannan, amma tabbas idan na gaji zan yanke hukuncin da ba zai yi wa kowa daɗi ba, shikenan iyaye idan suka aurar da kai kamar sun ba da kai kyauta ta har abada? Kawai ka zauna a gidan aure kar aure ya mutu har abada? Wallahi iyayena na tabbata inda za a basu zaɓi ko aurena ya mutu ko na mutu, sai dai su zaɓi rayuwar aurena ba tawa ba, kamar ba su suka haife ni ba?"

Sabila ta ce"To tun da dai ba za ki iya faɗa mini wannan sirrin naki ba, ni haƙuri kawai zan yi ta ba ki, Allah Ya ƙara miki haƙuri da juriya, Allah Ya sanyaya zuciyarki, kuma dama ita mutuwar aure ba ta da amfani, an ce duka maza fa haka suke, idan mun fita ba mu san inda za mu je ba, shiyasa gara ma ka yi haƙurin kawai, zawarawan da suka gaza haƙuri suka kashe auren suna nan suna nadama, wata sai ta shekara goma tana zawarci, to wa gari ya waya?"

Maman Nawal ta ce"Ni gara na dawwama ina zawarcin".

Sabila ta yi murmushin takaici ta ce"Faɗa kike yi Amina, ke dai ki cigaba da addu'ar neman mafita kawai, kuma ki ƙara haƙuri".

Suka dinga tattaunawa, wajen sha biyu ta tafi gida, ta ɗibo mata kayan abinci ta ba ta tana cewa"Don Allah idan ba ku da abin da za ku ci ki dinga faɗa mini, ko dai baƙincikin samun ladan kike yi mini?"

Sabila ta ce"Ba haka ba ne, in sha Allah zan dinga faɗa miki".

Ta tafi ta bar ta da tunanin inda za ta samu kuɗin gawayin da za ta ɗora girkin


08038966015
[11/07, 4:11 pm] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture


*AURE A YAU!*



NA
*SADIYA ABDULRAZAK*


*First class writers association*


Page 8


Ta ɗauki waya ta kira shi cikin fargaba, yana ɗagawa ya ce"Ya aka yi?"

Ta ce"Dama maman Nawal ce ta kawo mana kayan abinci har da mai da magi, kuma babu kuɗin gawayi a hannuna".

Ya ce"To sai me? Yanzu me kika kira ni kike so na yi? Ina tsaka da kasuwa katsewa zan yi na kawo miki kuɗin kenan ko?"

Ta ce"A'a".

Sai ya yi tsaki ya kashe wayar.

Tana ta tunanin mafita, wajen ƙarfe ɗaya sai ga wata ta zo karɓar ɗinki, ta ba ta cikon kuɗin ɗinkinta dubu ɗaya da ɗari biyar, ai kuwa nan take ta fita ta siyo gawayin na ɗari biyar ta ɗora girkin, tana ɗorawa sai ga almajirin maman Nawal da kula ta aiko mata abinci, suka ci, ta gama girkinta a tsanake, shinkafa da miya ta yi, ta zuba a kula don kaɗan ma ta dafa tun da sun ƙoshi, wajen la'asar ya kira ta a waya, ta ɗauka ya ce"Har yanzu ba a samu gawayin ba?"

Ta ce"An samu, wata ta kawo min cikon kuɗin ɗinki na sayi na ɗari biyar, har na gama girkin".

Ya ce"Me kika dafa?"

Ta ce"Shinkafa da miya ce, idan da salak ka taho da shi sai a yanka da daddaren, na je siya babu a unguwar".

Bai bi ta kan zancen salak ɗin ba ya ce"Me da me ta ba ki na kayan abincin? Akwai doya?"

Ta ce"A'a sai dankalin turawa".

Ya ce"To ɗan dafa min ki watsa shi a saman shinkafar".

Ta ce"To".

Sai bayan magriba ta dafa saboda ɗinki take ta yi, wata maƙociyarsu ce ta kawo mata ɗinkin 'yan gidansu na biki, har kala bakwai, kuma ta ba ta duka kuɗin ɗinkin dubu arba'in, saboda tana so a gama nan da kwana shida, ga shi ba ta gama na hannunta ba, gobe dai take son zuwa ta siyo kayan ɗinkin ta fara yi, shiyasa ta duƙufa a kansu take ta yi.

Da Sunusi ya dawo ya ci abinci ya ƙoshi, ya sha ruwa ya yi wanka ya tafi zance hankali kwance, sai dai yana zuwa Karime ta zo masa da wani batu, wai bikin ƙawarta za a yi aminiyarta, kuma gobe za a je siyo anko, ta ce musu ita ma za ta je don haka ya ba ta abin da yake hannunsa, Sunusi ya sosa kai cikin ƙosawa da bani-baninta ya ce"To nawa ne kuɗin?"

Ta taɓe baki ta ce"Ka san shi sha'anin biki, ba ka ƙayyade abin da za ka kashe, don haka ka ba da iya ƙarfinka kawai, tun da ni ko dubu ɗari a bikin nan ba isa ta za ta yi ba".

Ya jinjina kai ya ce"To amma ko a ƙiyasi nawa ne zai iya isarki?"

Ta ce"Kawai ka ba da abin da za ka iya dai".

Ya ce"To Allah Ya kai mu goben sai mu ga yadda za a yi".

Ta ce"Amma fa gobe da safen za mu je kasuwar, ka ga yau ya dace na kwana da kuɗina a hannu ai".

Ya ce"To kuma Karime ba sai ina da shi ba? Kin san dai sha'anin kuɗi yadda yake, ni wallahi babu ko sisi a jikina, amma zuwa gobe idan aka shiga kasuwa in sha Allah za a bubbuga a haɗa miki".

Nan take Karime ta haɗe gira.

Yana yi mata kallon soyayya yake cewa"Haba dai masoyiya, ai ba zai gagara ba in sha Allah, amma dai irin wannan ki dinga faɗa da wuri, ki saki ranki don Allah".

Ta ce"A'a dakata Sunusi, tsakanina da Allah ba zan ɓoye maka ba, ni ba zan iya wannan soyayyar ba, mazan yanzu kuna yi a waje idan aka shiga gida ku noƙe ina ga tun a wajen ba kwa yi?"

Yana ɗan murmushi ya ce"Ai kuwa ba a ce ba na yi ba, sai dai ko abu da talaka".

Ta taɓe baki ta ce"To ka san dai ni yanzu kai kaɗai nake kulawa ko? To idan ba ka yi mini ba waye zai yi min kenan? Ni ina mamakin mazan da za ku noƙe ba za ku yi wa wacce za ku aura hidima ba, amma kuma sai shegen kishi kuna so mace kar ta kula kowa sai ku, to wallahi ni ba zai yiwu ba, Indai da gaske aurena kake son yi Sunusi dole kai za ka dinga yi min abin da bazawari yake yi wa bazawara, idan ba za ka iya ka ƙara mai".

Ya ce"A haba dai Karime ya da haka? Gaskiya ba na son irin wannan wasan".

Ta ce"Ba zancen wasa a nan, a to magana ce ta gaskiya fa, biki za a yi na san abokan ango suna nan, gara ma na san inda ka ajiye ni don ba za ka yi mini sagegeduwa ba, idan wani ya ƙyalla ido ya gan ni ya ce aure ni amincewa zan yi".

Sunusi fa ransa ya fara ɓaci, kishi ya kama shi, ya ce"Kin ga Indai kuɗi ne zan samo miki a daren nan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login