Showing 12001 words to 15000 words out of 34919 words
Chapter 5 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
yi ba wallahi, tun da kun riga kun saka sai dai ku siya, don wallahi idan ma ba ku ajiye kuɗi na ɗauka ba to zan zara s kudin cefanenku".
Sahura ta ce"Wai me kake nufi ne Hamza? Ko dai magagin baccin ka fara yi?"
Ya ce"A'a dag gidan mahaukata na tsinko, ki fito mini da leshena kawai, yau dubunku ta cika".
Tun da ya faɗi haka ta san ya kama Saude ne, ta ce"Ni dai na riga na kai ɗinki, kuma tun da sallah saura wata uku ai kawai sai a bar shi a na sallah, sai ka yi mini ciko".
Ya ce"Sahura kin san Allah a kan les ɗin nan sai na karya miki jarin awara?"
Ta yi wata dariya ta ce"Da gaske?"
Ya ce"Idan shi kin kai shi ɗinki na ji, ki fito mini da kayan baccin".
Ta fito da su tana cewa"Amma dai Hamza a zawarawan ma mara aji za ka auro ko? A ce har da gwanjo a lefen?"
Ya ce"Idan ma gumama ne babu ruwanki!".
Ya fizgi kayan da ta miƙa masa, ya ce"Zan ɗibi waken suya na kuɗin leshina".
Ai yana fita da daka tsalle ta bi bayansa, don kuwa jiya aka kawo mata buhu ɗaya ko farkawa ba ta yi ba, kamar yadda ya kwasa a guje ita ma haka da gudun suka ƙarasa kofar kitchen ɗin, ya ɓata rai ya ce"Ki matsa".
Ta ce"A kan me zan matsa? Na ce a bar shi s bakacin na sallah na, tun da na riga na kai ɗinki".
Ya shiga ɗakinsa ya ajiye kayan, ya dawo, ya tarar Sahura ta babbake ta tare ƙofar shiga kitchen, da ƙyar ya ture ta ya shiga, a tare suka shiga, shi ya fara rarraba ido, ita kuwa da ta san ma'ajiyar buhunta ta yi kansa ta kwanta, ya ƙarasa ya dauki wani bokiti ya matso yana cewa"Matsa na ɗibi waken nan? Nawa ne kwano ɗaya?"
Sahura ta ce"Hamza ko me za mu yi ban da sana'ata s ciki".
Ya ce"Ni ba sana'ata kuka taɓa ba? Kayan me delivery ne fa".
Ta ce"To je ka dai gobe zan karɓo maka leshinka".
Ya ce"Wallahi ƙarya kike yi, a yau za ki ba ni abuna".
Ta kwanta a kan buhu ta yi bake-bake, ya yi iya yinsa ya kasa ɓanɓare ta daga buhun nan, da ya ga da gaske ba za ta saki ba sai ya fara jan ƙafafuwanta, ganin zai ci galaba a kanta ya da ta sakin wani gigitaccen ƙaran da ba shi ba hatta Saude da ke laɓe tana leƙensu dai da ta tsorata, ta ɗago daga kan buhun taba cewa"Zo ka ɗiba! Zo ka ɗiba, wallahi idan ka taɓa waken goɗiyarmu sai mun mayar da hannuwanka duka biyun kan mazaunanka! Zo ka ɗiba!".
Hamza ya fara baya-baya a tsorace, amma bai fita daga kitchen ɗin ba, don yana son nuna jarumta ko kaɗan ce, Sahura ta fara takowa wajensa a hankali, cikin taku ɗaya-ɗaya, duk taku ɗaya da ta yi shi ma sai ya yi taku ɗaya yana matsawa baya, yana ta muzurai da cewa"Yau ko tsamiya ce a kanki sai kin biya ni leshina, sanda ina yaro babu kalar hatsabibancin da ban yi ba, har kwana na sha yi a kan bishiyar kuka, na yi mafici fa tunfafiya".
Sahura ta yi kwanta-kwanta, ta shammace shi kamar mage za ta kama ɓera, ta yi wuf ta wawaso ƙafafunsa, sai ga shi ta yi sama da shi cak, Hamza ya daddage ya kurma ihu yana cewa"Saude! Saude! Innalillahi wa inna alaihi raji'un! Wa innahu bismillahi".
Sahura ta fito da shi tsakar gidan tana cewa "Tsamiyar za mu kai ka ka kwana a can".
Hamza cikin tashin hankali ta samu ya diro ƙasa, bai yi wata-wata ba ya faɗa ɗakinka, ya banke ƙofa ya danna sakata, Sahura ta ƙarasa ɗakin ta buga kofar da ƙarfi tana cewa"Ka fito ka karɓi leshinka mana!".
Ya ce"Na bar miki ki riƙe a bakacin kayan sallarki, yanzu saura takalmi da mayafi".
Saude kuwa dariya ta kusa ƙulle mata ciki, ta fito ta ce"Amma Sahura kin raina mijinki wallahi, kar fa wataran ki da zuciyarsa ta buga".
Sahura ta ce"Ai ba ki da wayo shiyasa kika ba shi kayansa, wallahi kaya sun zo kenan, kuma idan bai kwashe su daga gidan nan ba ba zan fasa zara ba, ai raini ne ma ya zo ya dinga haɗawa kishiya kayan lefe a gidanmu".
Saude ta ce"Da safe ma ƙarasa zancen".
Kowacce ta shige ɗaki, shi kuwa Hamza zama ya yi ya zuba tagumi, har yanzu ƙirjinsa bai daina bugawa da sauri ba, saboda fargaba da tashin hankalin da ya shiga, mamaki yake yi yana tunanin dama tana da aljanu amma ba su taɓa tashi ba? Wata zuciyar ta ce masa 'Haba babu mamaki shiyasa a baya ta taɓa ɗaga ka ta daka a cikin ruwan tsami, wannan ma aikin jinnu ne".
A hankali ya ce"Allah ga Hamza, Allah ka zama gatana, ka sani sunna nake son ɗabbaƙawa a ƙarin auren nan, Allah ka kaɗe mini fitinar gidana kafin auren da bayan auren".
Washegari da safe ya haɗe duka kayan a akwatin, da Sahura ta shigo kawo masa abun karyawa bai tada zancen jiya ba, ita ma ba ta tada ba, yana gama karyawa ya ja akwatinsa ya bar gidan da ita.
GIDAN SUNUSI
Komai na kayan abincin da suke da shi a gidan sai da maman Nawal ta ɗibar wa Sabila, kuma masu yawa wanda zai kai musu wata biyu ko fi, sannan ta ba ta dubu biyar ta siyan gawayi, Sabila ta dinga godiya har da ƙwallarta, Maman Nawal ta ce"To ba wannan ba, yanzu sai ki nemi inda za ki ɓoye kayan nan, kar ma ki faɗa masa, don ƙarasa kashe masa matacciyar zuciyarsa za ki yi, ki ja bakinki ki yi shiru, idan ya ba ki ki dafa, ranar da bai ba ki ba sai ki ɗiba a wannan ɗin ki dafa, kuma wallahi Indai namiji zai iya fita ya bar ki babu abinci, ya dawo ya gane cewa kin nema kun ci, ko ma har ki ajiye masa to shikenan kin kashe kanki, kin ce ya nemi waje ya kwanta, don ya daina nemowa, duk ranar da bai ba ki ba ko yunwa za ta yi masa lahani kar ki dafa ki ba shi".
Sabila ta yi shiru tana nazari, a ganinta ya za a yi ta ƙi nuna masa kayan arziƙin nan? Ai ko don ya ga girma da mutuncin maƙocinsa ya dace ta nuna masa, kuma ita dai ba ta jin za ta iya yin girki ta hana shi abinci, amma a zahiri sai ta nuna ta ɗauki shawararta, ta ce"To shikenan maman Nawal na gode sosai".
Ta yi girkinta wadatacce, har kifi ta siya ta saka a har miyar, sannan maman Nawal ta aiko mata wanda ta dafa, da daddare da ya dawo ta kawo masa abinci, farar shinkafa da doya, ga miya ta ji kifi, ya buɗe ya fara ci yana yi yaba danna waya, ta yi zaton zai tambaye ta inda aka samu, tun da ta san dai ya sani dubu daya da dari biyar ba za ta isa wannan girkin ba, sai da ya gama cin abincin tsaf zai tashi, ta ce"Baban Amal".
Ya kalle ta ba tare da ya amsa ba.
Ta ce"Ka ga an yi girkin da ya fi ƙarfin kuɗin da ka bayar amma ba ka tambaye ni inda na samu ba".
Ya ce"To ina ruwana? Me ya hana ki yi daidai na karfina? Ko na ce ki yi mini ciko ne? Ok don kin cika kuɗi kin canza girki shi ne kika titsiye ni za ki goranta mini?"
Ta ce"Wallahi sam ba da wannan manufar ba ne, abun arziƙi ne fa ya same mu, bari ka gani".
Ta shiga kitchen ta fara ɗebo kayan abincin, ta zube su duka a gabanta, ta ɗora kuɗin gawayin a kai ta ce"Ka ga kyautar kayan nan aka ba mu, har da kuɗi wai na dinga siyan gawayi".
Ya haɗe rai sosai ya ce"Uban waye ya ba ki wannan kayan?"
Ta ce"Haba baban Amal abun ba na faɗa ba ne, nan maƙotanmu ne fa, wannan matar maman Nawal da take shigo mini, kuma mijinta ne ya ce a bamu".
Ya haɗe gira sosai ya ce"A kan me? Ina ruwansa da gidana da zai ba ki abinci? Ok kenan zuwa kike kina tona mini asiri kina cewa ba na ba ki abinci ko? Ke wallahi sai na ji ma mene ne haɗinki da shi da zai ba ki abinci, ƙanin ubanki ne?"
Wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, ta ji kamar za ta mutu don takaici, a tsawace ya ce"Na ce ƙanin ubanki ne?"
Ta girgiza kai alamar a'a, hawaye ya sakko mata.
Ya ce"To gobe ki tabbata kin mayar musu, ba na son taimakonsu".
Ya fice daga gidan, ita kuma ta zauna ta kifa kanta da gwiwa ta fara kuka, yaran duk jikinsu ya yi sanyi irin yadda suka saba idan uban nasu yana yi mata tijara.
08028966015
[09/07, 4:08 pm] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture
*AURE A YAU*
NA
*SADIYA ABDULRAZAK*
*First class writers association*
Page 5
Haka Sabila ta dinga komai a sanyaye har yara suka yi bacci, ita ma ta kwanta, tana tunanin yadda za ta iya mayar da kayan abincin da shi ma ya san suna buƙatarsa, ita sam ba ta yi zaton zai ce haka ba, tun da ai taimakonsa aka yi, ƙarfe goma ya dawo gidan, lokacin bacci ya fara ɗaukarta, ta zo ta buɗe masa ya shigo, ta koma ɗaki ta kwanta, shi kuma ya zauna a bakin gadon, har ta ɗan yi mamaki tun da ta ga ba danna waya yake yi ba, idan ya yi irin zaman nan ta san akwai abin da yake damunsa, ko kuma ba shi da ko sisi, inda da ne da za ta yi masa magana ta tambaye shi mene ne, amma yanzu da yake tana jin haushin shi sai ta yi banza da shi, ya yi wajen minti biyar a haka har bacci ya fara ɗaukarta, can dai ya ce"Sabila".
Ta ce"Na'am"
Ya ce"Nawa ne kuɗin gawayin da kika ce sun ba ki?"
Ta ce"Dubu biyar ce".
Ya ce"To ɗan ba ni dubu uku mana".
Ta ce"Kuma tun da mayarwa zan yi ai bai kamata na taɓa kuɗin ba".
Ya ce"Bar shi ma kawai ba sai kin mayar ba".
Ta ce"To".
Ta ɗora da faɗin"Ni a ganina ai taimakonka ma aka yi, kuma babu kyau mayar da hannun kyauta baya".
Ya ce"Ke dalla ba na son iyayi, ni ɗakko min na wuce kawai".
Ta tashi ta ɗakko kuɗin tana cewa"Amma fa gawayi ta ce na siya da kuɗin, kuma zan dinga siyan biskit ɗin makarantar yaran nan".
Ya haɗe gira ya ce"Ok kenan don ta ba ki kuɗi ita ce za ta tsara miki yadda za ki kashe? Kenan ma ita ce mijinki ita za ta fara tafiyar da gidan".
Ta ce "Ba haka ba ne ba wallahi".
Ya ce"To ba ni, idan kuma ba za ki ba ni ba ki faɗa mini, duka na ce ki ba ni? Ban da ma ba ni da kuɗi ke kin isa na tambaye ki wani abu?"
Ta zari dubu ukun ta ba shi, ta mayar da dubu biyu ta ajiye, ya fice daga gidan, kai tsaye gidan su Karime ya tafi, don dama daga can yake, ya je zance ta tambaye shi dubu biyar, ya mata babu cash bari ya je ya ciro, saboda dubu biyar din ce a jikinsa, kuma ba ya so ya yi ƙaraf, shi ne ya je ya ba ta, shi kuma ya tsira da ukun, ya san za tq ishe shi gobe tun da dai ba shi da wani case ɗin cefane.
Karime wata bazawara ce, wacce ake yi mata laƙabi da Karime 'yar arufta, aurenta huɗu, duka babu wanda take zaman wata uku, kuma dama kafin auren ma ta daɗe a gida ta zama babbar buduruwa, amma dayake tana da ɗan jiki ƙarami ba a fiya ganin girmanta ba, sai dai idan ka kalli fuskarta da kyau za ka lura ba yarinya ba ce, kowa a unguwar nan da kewaye an shaida Karime cikakkiyar 'yar arufta ce ta gaske, domin ta iya tarar aradu da ka, tun tana ƙaramarta kowa ya santa wajen faɗa da masifa, sanda ta zama buduruwa kuwa ta yi tashen tara samari saboda ta ƙware a yaudara, da iya cin kuɗin samari, rashin haƙurinta da rashin kunya shi yake hana ta zaman aure, saboda ita sam ba ta ɗaukar rainin hankalin namiji, mijinta na ƙarshe da suka rabu, sai da suka yiwa juna jina-jina har da kwanciya a asibiti, don ice ya mammaka mata, bayan ta gama suyar naman sallah, a kan rabon naman aka yi faɗa, ita kuwa ta caka masa almakashi a cinyarsa, ta jefe shi da murfin tukunya ta fasa masa goshi.
Yanzu kuma ta ƙware wajen cutar zawarawan da suke zuwa wajenta, a zahiri za ka yi mata kallon mara kamun kai, sai dai duk ɗan iskan da ya matso kusa da ita zai gane ba haka abun yake ba, domin za ta yi ta ci maka kuɗi ne da sunan za ta amince maka, har ka gaji ka gane ka tafi, aure kawai take son yi, saboda ta gaji da zaman haka, Allah Ya yi ta cikin mata masu yawan buƙatuwa, kuma mijinta na farko hariji ne, ya yi mata sabo mai wuya, duk sauran mazan da ta aura sam ba su gamsar da ita ba, shiyasa yanzu ta maƙalewa Sunusi tun da ta ga matashi ne mai jini a jika, take kyautata zaton za ta samu yadda take so su dinga cin uwar sabada.
Shi kuwa Sunusi tsakaninsa da Allah yake sonta, yana ta tanadin aurenta, don adashi ya shiga a kasuwarsu, yake yin zubi duk wata, ɗauka tana zuwa kansa sai dai kawai ya yi wuf da 'yar arufta, shi dai yanzu da a ce ta tambaye shi kuɗi ta rasa ya ji kunya, gara a ce Sabila da yaran su kwana da yunwa, kullum idan zai je zance akwai ledarta ta tsaraba, haka kawai take yi masa waya ta ce ya kawo mata abu mai gishiri, idan ta ce haka nama take nufi, kaza, tsire balangu ko kifi, idan ta ce mai suga kuwa ya san kayan sanyi take nufi, kuma ba ta shan lemo mai araha saboda ba ta son gas, sai dai ta siyo mata yogurt zundumemi ki da kuwa bashi ne sai ya ciwo.
Washegari da safe ta dafa indomi da shayi suka karya ta raka yara makaranta ta dawo, ya tashi ya yi wanka ta kawo masa nasa, ya buɗe indomin yana ɗan haɗe fuska ya ce"Ba na ga da ƙwai a kayan nan ba?"
Ta ce"E akwai".
Ya ce"To me ya hana ki soyawa?"
Ta ce"Wai da barinsa na yi sai gobe sai na soya doya da shi ko dankali".
Ya yi tsaki ya ce"Ɗan soya min guda biyu".
Ta ce"To".
Ta je ta kunna gawayin ta soya, kafin ta gama har ma ya gama karyawar, ta ajiye masa ya cinye ya tafi kasuwarsa. Tun daga nan kuma ya naɗe hannu, bai sake ba ta ko naira biyar ba, kwana biyu dubu biyun hannunta ta ƙare, saboda kullum tana siyan ruwa na ɗari biyu, tana siyan gawayin ɗari biyu kuma ta siyawa yara biskit ɗin zuwa makaranta, yau da daddare yana cin abinci take ce masa "Baban Amal kuɗin hannuna sun ƙare, babu ma gawayin da za a yi amfani da shi gobe, kuma akwai siyan ruwa, da biskit ɗin yaran nan".
Ya yi shiru kamar bai ji ta, wannan halinsa ne, ta yi masa magana ya share ta, abun yana ɓata mata rai sosai, sai da ya gama ya tashi zai fita ta ce"Ina yi maka magana, ba na so gobe yaran nan su yi latti".
Ya ciro ɗari biyu a aljihunsa ya cilla mata yana cewa"Ki je ki siyo".
Ta ce"Amma da daren nan? Na za ta za ka taho da shi ne".
Ya ce"To ki bar shi gari ya waye mana, ni yaronki ne da za ki aike ni?"
Ya fita daga gidan, yaran sun yi bacci, ba za ta tashe su su tafi siyan gawayi ba, sannan kuma ba ta son fita ta bar su su kaɗai a gidan, don haka ta haƙura dai washegari da sassafe ta fita ta siyo, yara sun tafi makaranta shi ma ya gama komai zai fita ta ce"Yau fa sai ka ba da kuɗin cefane, kayan kayan miyan da ta haɗs mana da shi sun ƙare, kuma na faɗa maka sai sn sayi ruwa, biskit ɗin yara ma bashi na karɓa".
Ya ce"Su ma sauran sai ki ci bashin".
Ta ce"Shi ma mai shagon don dai mun saba da shi ne, amma ba zan iya zuwa wajen mai kayan miya cin bashi ba".
Ya ce"To ni dai haka na tashi babu ko sisi, ki ɗibi kayan abincin ki siyar mana, ko taliya biyu kika kaiwa mai shagon ya siya ai za ki samu na cefanen".
Mamaki ya kama ta, saboda ita ba ta san Sunusi yana zarar kayan abincin yana siyarwa ba, ta ce"Na siyar da abincin fa ka ce?"
Ya yi tsaki ta ce"Zancen kike so". Ya fice daga gidan.
Ta zauna tana ta mamakin halinsa, haka ta karɓi bashin barkono ta dafa shinkafa da wake, da zai dawo ya dawo da kayan miya mai yawa, tun da dama sana'arsa ce, tun daga ranar kuwa bai sake ba ta kuɗin cefanen ba, sai dai ɗari biyun siyan gawayi, shi kansa mai ruwa bashi yake ta zubawa ana yi mata lissafi.
GIDAN YUSUF
Zubaida wuni ta yi da waya, manyan mata 'yan gayu da 'yan ƙarya ana ta saka order kaya, ga masu adaidaita sahunta nan