Showing 9001 words to 12000 words out of 34919 words

Chapter 4 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt

ai kuma shikenan sai dai mutuwa ta raba".

Don son kawar da zancen Maman Nawal ɗin ta ce"Don Allah idan kina buƙatar wani taimako ta fannin abinci ko mahaɗin girkin ki dinga faɗa mini, idan kika sake wuni ko kwana da yunwa ban yafe ba".

Sabila ta ce"Na gode maman Nawal, amma a sanina da ke ba kya yin wata sana'a, sannan ke ba mahaukaciya ba, ta ya za ki taimake ni? Kayan mijinki naki ne, amma ba ki da ikon rabawa, saboda haka na gode da niyyar taimakona, Allah Ya bar zumunci".

Maman Nawal ta ce"Zan tambaye shi kuma zai amince".

Ba ta jira cewar Sabila ba ta ɗauki wayarta ta kira shi, ta saka a hans free, yana ɗagawa ya ce"Gimbiyata uwargidana, ya dai ko kewata kike yi?"

Ta yi murmushin yaƙe ta ce"E to da kewar ma, dama magana nake so mu yi".

Ya ce"Ina sauraronki Babyna".

Ta ce"Akwai wata cikin maƙotanmu dake buƙatar taimako, da ƙyar suke cin abinci, shi ne nake so a ba ta kayan abinci, kuma sannan ta samu kwano a gidanmu kullum, zai yiwu?"

Ta yi murmushi mai sauti ya ce"Haba ranki ya daɗe, yanzu don wannan ne har kike neman izni? Me zai hana ya yiwu? Ki buɗe store ki ba ta komai da kika ga ya dace, idan ma duka za ki kwashe mata a yau zan aiko da wasu, sannan abinci idan tun safe har dare ne na amince miki ki dafa ki ba ta".

Ta ce"Godiya nake Alhaji".

Ya ce"Wannan girmanki ne sarauniyar mata".

Daga haka ta ajiye wayar, Sabila ta kura mata ido kafin ta ce"A zatona a yau ko jiya kuka samu matsalar da har kika zo kina kuka da iƙirarin rabuwa da mijinki, sai kuma na ji kun yi waya babu alamun hakan, don Allah me wannan nagartaccen mijin ya yi miki da zafi haka wanda kika kasa mantawa? Rabon da mijina ya sakaya sunana ya faɗa mini na soyayya tun ina amarya, ke kuwa me ya yi miki zafi Amina?"

Dariya ta yi, amma kana gani ka san ta takaici ce, ba ta bi ta kan zantukanta ba ta ce"Kin dai ji da kunnenki, da amincewar shi zan taimake ki, don haka za ki karɓa hankali kwance".

Ta tashi ta fita daga gidan tana cewa "Bari na dawo yanzu". Sabila ta bi ta da kallon mamaki, tana ta ayyana abubuwa da dama.

GIDAN YUSUF

Alarm ne ya tashe shi da asuba, ya yi wanka a gurguje, don jiya ya yi mafarkin da ya wajabta masa yin wankan, ya yi alwala ya fito ya buga ɗakin Zubaida, har sai da ta ce masa ta tashi, ya tafi masallacin unguwar tasu, da ya dawo ya kwanta ya cigaba da baccinsa, ita ma baccin ta koma, sai da yara suka tashi karafniyarsu ta tashe ta, ta duba agogo ta ga har ta makara, don bakwai da minti goma, ta fito da sauri ta shiga kitchen, ta ɗora ruwan shayi tun kafin ya tafasa ta juye, ta zuba a fulas ta haɗawa yaran nasu a kofuna, ta shafa musu mai suka zura unifom saboda ta san idan suka tsaya yin wanka lokaci zai ƙure, sai da suka yi zaman karyawar ta tuna babu biredi a gidan, ta nufi ɗakin nasa, fitowarsa daga wanka kenan yana shiryawa, ta ce"Babu biredia gidan fa".

Ta sani ya tsani ta ƙi faɗa masa abu ya ƙare sai a ƙurarren lokaci, shiyasa da ya yi kamar bai ji ta ba ba ta yi mamaki ba, don ta san dama dole zai ji haushi, ta sake cewa"Magana nake yi maka fa".

Ta ce"To me zan yi miki? Me kike so na ce? Sai yanzu bakwai da rabi za a siyo biredi? Har yaran nan su gama karyawa su tafi makaranta? Dole sai da biredi za a karya ne? Me ya hana ki yi wani abun?"

Sosai taɓa rai, kafin ta ce"Yanzu Yusuf ni kake faɗawa magana kawai saboda siyan biredi? Idan ka ce ba za ka siya ba ma kawai ai ya wadatar".

Bai kula ta ba, ta bar ɗakin tana ta ƙananun ƙunƙuni, ta ɗakko biskit ta ba su, ba su kai ga fara ci ba suka ji horn ɗin mai adaidaitasahun da yake kai su makaranta, don haka da hanzari suka karya tana ta azalzalarsu su yi sauri, suka gama ta raka su bakin get ta ga tafiyarsu, ɗakinta ta koma ta yi wanka ta shafe jikinta da humra masu ƙamshi da tsada, ta ɗakko wata dakakkiyar shadda ta saka, ta zauna a bakin gado ta fara chatting, tana jiran zuwan mai aikinta, ta gyara mata falon ta samu damar yin vedion da ta yi wa followers ɗinta alƙawari, na nuna musu sababbin kayan product ɗinta da za fitar a cikin satin nan.

Yusuf ya fito daga ɗakin ya tsaya yana kallon falon, har yanzu yana nan a yadda yake jiya da daddare, sai ma ƙarin kofunan da aka samu, ya san ko za su kai Azhar a haka Zubaida ba za ta gyara ba, dole sai lokacin da mai aikinta ta zo, kitchen ya shiga ya dafa indomi ya soya ƙwai biyu, a nan kitchen ɗin ta zauna ya ci, ya kora da ruwan shayi, ya shiga ɗakinta ya ce mata"Zan fita".

Ta ce"Ok".

Ya ce"Akwai komai?"

Ta ce"Ka duba ka gani mana".

"Ok" Kawai ya ce, ya fita yana cewa"Sai na dawo" Duk da ya san ba shi da matsayin da za ta ce masa ya dawo lafiya.

Bai jima da fita ba mai aikin ta zo, ta gaishe da Zubaida, ta fara gyaran falo ta ce mata"Kin ga Hafsa fara sama mini abin da zan ci pls, ki soya mini dankali".

Cikin ƙanƙanin lokaci ta soya mata, sannan ta fara gyara gidan, ta gama komai tsaf, gida ya ɗauki ƙamshi ya dawo hayyacinsa, Zubaida tana karyawa tana amsa waya kamar wata ministar, ta gama ta ɗakko wata babbar jaka, ta baje kaya a falo, sai da ta sake kallon kanta a mudubi ta ga yadda ta yi kyau sannan ta saita kayan aikinta, ta saita vedio ta fara ɗakko magungunan mata da na maza ɗaya bayan ɗaya tana bayaninsu, tana gamawa ta yi posting, nan da nan ta fara samun like da comments saboda tana da mabiya maza da yawa, da yawan comments ɗin mazan kuma duk yaba kyaunta suke yi, wasu ma kai tsaye suke cewa suna sonta, wannan ita ce sana'arta, wacce ta samu karɓuwa sosai take samun alkhairi da ita, ta sani Yusuf ba ya son tallata kaya a media da take yi, amma babu yadda zai yi da ita, tun da iyayenta sun ba ta goyon baya, kuma a ƙarƙashin mahaifinta yake, a nan yake samun rufin asiri, sannan ita 'yar lelen iyayenta ce, duk abin da take so suna goya mata baya, Yusuf yana aurenta ne kawai, amma ba shi da ikon saka ta da hanata, saboda yadda nashi iyayen suke rausar shi a duk sanda ya yunƙura don ɗaukar mataki.


08028966015
[08/07, 10:18 am] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture


*AURE A YAU*



NA
*SADIYA ABDULRAZAK*


*First class writers association*


Page 4


GIDAN HAMZA

Da safe Hamza ya tafi kasuwa hankali kwance, bai taɓa hasashen Sahura ta taɓa masa akwati ba. Ita kuwa Sahura bayan ya fita yara sun tafi makaranta ta fito da kayan nan, ta shiga ɗakin Saude, Saude ta"Yau tun safe na ga kamar akwai magana a bakinki".

Sahura ta ajiye kayan tana cewa"Ai yanzu ma a safiyar muke Saude, to kamar yadda na faɗa miki zan gudanar da bincike, jiya dai ga abin da bincikena ya samo, Hamza dai da gaske aure zai ƙara, lefe yake haɗawa a cikin ɗakinsa, saboda tsabar ya mayar da mu huhulahu, a cikin gidanmu zai haɗa lefe?"

Saude ta ce"Amma dai Sahura kina da ƙarfin hali, gidanmu ko gidansa?"

Ta ce"Mu ma ai gidanmu ne, tun da dai mu yanzu Hamza ko sakinmu ya yi sai dai ya fita ya bar mana gidan, don mun ci gida, ni fa ko haihuwa ɗaya na yi da miji na ci gida ya zama nawa, ballantana biyu".

Saude ta janyo ledar kayan tana cewa"A'a ni kam ko yau ya sake ni Ni gidan iyayena zan kwana".

Ta fito da leshin tana jinjina kai, sannan ta zazzage ledar kayan gwanjon suka fara ɗaga su, kayan bacci ne masu kyau, irin gwanjon nan giredi, da kuma wasu riga da wando da riga da siket na zaman tsakar gida haka, Sahura ta ce"Ai kuwa duk buduruwar da ya kai wa gwanjo a lefe ta yi asara, wannan rashin daraja har ina?"

Saude ta ce"To ai ta gode Allah idan babu kayan sata a ciki, sanda zai yi ƙarin aurensa na farko fa wani ango ne fa sabon aure ya dinga sato kayan lefen amaryarsa yana kawo masa yana siya, da kayan sata aka yi rabin lefen, ranar da asiri ya tonu na ga ikon Allah a gidan nan".

Ta kwashe da dariya ta ce"Ba za ki gane yanayin da Hamza ya shiga ba a ranar, Sahura na so dai a ce kina nan, amma na sha kallo na sha dariya".

Sahura ta ce"Oh! Allah mai iko, ashe dai Hamza ba yau ya fara rigima ba".

Saude ta ce"Yanzu ya za a yi da kayan nan? Rabawa za mu yi?"

Sahura ta ce"Ƙwarai kuwa, kowacce ta ɗauki wanda zai yi mata, les ɗin nan kuma nawa ne, idan ya so tun da yau za ki karɓi girki ke ma sai ki san dabarar da za ki yi ki ɗauki naki, akwai wani blue da na gani wallahi zai yi miki kyau sosai Saude".

Saude ta ce"In sha Allahu kuwa shi ɗin zan ɗauka, Allah Ya kai mu daren".

Nan suka baje kayan gwanjo aka raba, Sahura dai kayan bacci kawai ta ɗiba, saboda kayan sakawar duk tsayin ya yi mata kaɗan, duka Saude ce ta ɗiba, kowa ya adana nashi suka shiga sabgogin sana'arsu.

Dare ya yi Hamza ya dawo daga zance ya shiga ɗaki, Saude ta bi bayansa, har ya neme ta aka yi komai aka gama lafiya lau, ta yi luf kamar mai bacci, sai da ta tabbatar ya yi bacci ta sakko daga gadon, ta danna wayarta ta haska ta nufi wajen akwatin, ta buɗe ta fara ciro kaya, les ɗin saura guda uku, ga shi kuma duka sun yi mata kyau, hakan ya sa take ta ɗaga su ta rasa wanda za ta zaɓa, sai dai ta bi shawarar Sahura ta ɗauki blue, har ta rufe akwatin ta sake buɗewa ta zaro wata shadda copy, tana cikin haɗe su waje guda ƙarar ledar ya farkar da Hamza, shi a zatonsa ko ɓera ne ya shiga akwatin yake ta'adi, duk da ya san ba shi da ɓera a ɗakin, a gigice ya fara laluben wayarsa, don idan ɓera ya ragargaza masa kayan nan ya cuce shi, ya manta ya saka wayar a caji, yake ta lalubenta a gadon ya rasa, ya fara cewa"Innalillahi wa inna alaihi raji'un! Dukiyata, lefena, kayan Baby Mardis".

Saude ta daskare a wajen riƙe da kaya, ta kasa gaba ta kasa baya, kawai sai ta kwanta rungume da kayan. Hamza ya zare wayar daga caji ya kunna, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi ganin Saude kwance da kaya rungume a ƙirjinta, ya ce"Innalillahi wa inna alaihi raji'un! Saude! Saude me kike yi da kayan masu delivery? Kayan mutane ne fa da suke tara order ba sa karɓa da wuya, wallahi kayan mai delivery ne".

Saude ta yi luf kamar mai baccin gaske, amma zuciyarta bugu take yi kamar za ta fasa ƙirjinta ta fito, ita dai sata ba halinta ba ne, amma ga shi Sahura ta cuce ta ta sa ta yi, kuma abun bai karɓe ta an kama ta tun a karon farko.

Hamza ya fara zungurar ƙafarta yana kiran sunanta, ta yi kamar ba ta ji shi ba, sai da ya kai hannu ya fara jan shaddar, ta zabura ta sake ƙanƙame ta tana cewa"E mun ɗauka, mun ɗauki saƙonmu muna godiya, ba cewa ka yi ni less da shadda ba, Sahura kuma less?"

Hamza ya ɗan ji fargaba kaɗan, ganin yadda Saude take magana cikin bacci, kamar mai shafar aljanu, amma ya dake ya saka ƙarfi ya fizge kayan, Saude ta tashi zaune ta fara kalle-kalle tana cewa"Me ya kawo ni ƙasa ni da na ke kan gado?"

Hamza ya yi mata mugun kallo ya ce"Dubunki ce ta cika, uban me ya kawo ki kan akwatina?"

Ta ce"Kar ka sake ambatar ubana, ka san dai kai kaɗai ne kake faɗa mini haka ban ce ubanka ba ko? To ka kiyaye".

Ya ce"Na faɗa ɗin, me ya kawo ki kan kayana? Kenan ɗan hali za ki fara yi ko? Kayan mutane ne fa na kawo gobe zan saka su a mota a kai musu garuruwansu, shi ne za ki sata ki takaice ni ki kashe mini kasuwa?"

Ta ce"Ni fa mafarki na yi, wata tsohuwa ta zo tana faɗa mini wai na duba akwatin cikin ɗakin nan, zan ga ka fara yi mana tarun kayan sallah na kwashi rabona, kuma kawai sai na farka na gan ni a haka da kaya a hannu, don Allah me yake faruwa?"

Hamza ya yi mata mugun kallo ya ce"Amma dai kin san ba tsoron aljanu nake yi ba ko? To bulukiya ma ta ci malafar ubanta, ke dai dubunki ta cika yau na kana ki, kuma wallahi kayan nan a lissafe suke, ko tsinke ne babu a ciki ke ce".

Saude ta ce"Wallahi ban taɓa ɗaukar maka kaya ba, Hamza idan sata halina ce ai da tuni ka sani".

Ya zazzage kayan akwatin duka ya fara lissafawa, ya ce"Ina kayan cikin baƙar leda?"

Saude ta rasa bakin magana, don rigar jikinta ma ta gwanjon nasa ce, ya je ya kunna globe ɗaki ya gauraye ds haske, sai yanzu ya kalli rigar jikinta da kyau, tun da ɗazu duk bidirin da aka sha a duhu ne, Hamza ya lailayo wata ashar mai gunna ya maka, gane wannan rigar ta jikin Saude, abokinsa ne yake harkar buɗe dilar gwanjon a kasuwarsu, kuma shi ne ya ba shi shawarar ya haɗa har da su a cikin lefensa, don idan suka ji wanki fa guga ya saka su a leda a matsayin sababbi za a kalle su, kuma wannan rigar duk ta fi yi masa kyau a cikin kayan, yana ganinta ya hango yadda za ta yi kyau a jikin Mardiyya, sannan duk ta fi sauran tsada, don dubu ɗaya da ɗari biyar ya siyar masa da ita, saɓanin sauran da ba sa wuce ɗari bakwai dubu ɗaya, don haka ba zai manta da kalar rigar ba, sai ga ta a jikin Saude, wacce a idonsa ganinta ya yi kamar an saka wa ta macen biri kaya.

Kamar zai yi kuka ya ce"Saude! Wannan rigar ta jikinki fa? Saude haka za ki yi mini? Talata mini neman aure za ki yi? Rigar da na ajiye amaryata za ta saka a daren farko ita kika ɗauka kika saka?"

Sai ya nemi waje ya zauna ya ce"Na shiga uku ni Hamza, me yasa Allah Ya jarabce ni da mata biyu duka babu na ɗauka ne?"

Saude ta ce"Wai Hamza me kake nufi ne? Kenan sharri za ka ƙala mini? Na ce maka mafarki na yi". Ta juya ta ɗauki hijjabinta za ta bar dakin.

Ya zabura ya ce"Ubanki ke da mafarkin, wallahi dawowa za ki yi na lissafa kayan nan, ko riga ɗaya ce babu sai na siyar da keken ɗinkinki ko firji".

Ya gama duba kayan, ya fahimci less guda ɗaya ne babu, sai kuma duka kayan gwanjon, ya ce"Ina leshina?"

Ta ce"Wallahi ban ɗauka ba".

Ya ce"Na rantse da Allah idan ba ki fito mini da shi ba gobe zan ci kasuwar keken ɗinkinki".

Ta ce"Wallahi Hamza ban ɗauka ba, amma dai..." Sai kuma ta yi shiru, tana son faɗa masa Sahura ce ta ɗauka tana fargaba, ba ta so ta yi gulma.

Ya ce"Amma dai me?"

Ta ce"Wallahi ban ɗaukar maka ba".

Ya ce"Mu je dakin naki".

Ta wuce ya bi bayanta, suka shiga ita da kanta ta buɗe sif ɗin ya shiga bincikawa, bai yi nisa ba ya ga sauran kayan gwanjon, ya ce"Innalillahi wa inna alaihi raji'un! Gaskiya Saude kin raina ni, kin gama wulaƙanta ni wallahi, to maza fito da su".

Ta fito masa da su duka, ya ce"Ina leshi ina sauran kayan bacci?"

Ta ce"Wallahi ban ɗauka ba, su ne kawai".

Ya yi tsaki rai a ɓace ya nufi falo, kai tsaye wajen keken ɗinkinta ya yi, ya fara kici-kicin cire kan keken, da sauri ta ƙarasa ta ce"Haba Hamza idan na ɗauki leshin nan ai dai za ka gani ko?"

Ya ce"Kanki ake ji".

Ta ce"Wallahi ban ɗauka ba, amma na san wacce ta ɗauka dai, yana ɗakin Sahura, sauran kayan baccin ma suna wajenta".

Ya ce"Kutt! Kenan dai gungun ɓarayi na tara a gida nake ciyar da su? Duk zan yi maganinku".

Ya kwashi kayan ya fita, ya kai ɗakinsa, ya dawo ya shiga ɗakin Sahura, duk da yadda jikin Saude yake a sanyaye sai da ta fara dariya saboda tunawa da Sahura ta kai ɗinkin less ɗin ɗazu da rana.

Ya fara ƙwanƙwasa ƙofar yana haɗawa da kiran sunanta, ta zo ta buɗe tana cewa "Waye cikin daren nan? Hamza ki ɓatan kai ka yi?"

Ya ture ta ya shige ɗakin ya saka sakata, Sahura da ita ma rigar jikinta ta gwanjon ce ta janyo hijjabi ta saka tana cewa"A'a fa wallahi Hamza ba za ka yi haka da ni ba, yaushe ka fara satar kwana?"

Ya ce"Ke ba wannan ya kawo ni ba, maza ɗakko mini leshena da kika sata,kuma ki fito mini da kayan baccina, wannan ta jikin naki ma ba yafewa zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login