Showing 15001 words to 18000 words out of 34919 words
Chapter 6 - AURE A YAU! Book Complete By Sadiya Abdurrazak.txt
a gidan suke wuni su ma, da an sayi kaya su kai masa idan ba na gari ba ne a saka masa a mota, a wunin ranar sau uku ta canza kaya, kawai saboda yin vedio, ita komai nata na media ne, hatta abinci kullum sai ta yi vedion sa ta saka a status, ga kuma ƙarya da take yi, idan ta yi sabon magani sai ta ce za ta fara gwadawa kafin ta fitar da shi, washegari sai ta zo status tana ba su labarin ƙarya ta ce mijinta ya ce kaza ya ce kaza, domin ta daɗe da yin block ɗinsa ta WhatsApp, tiktok dai yana kallon vedios ɗinta har ma ya bi comments ɗin mutane ya sha kayan takaici.
Dayake yau Alhamis ce yara suna gida da rana babu islamiyya, sai ta sa aka yi musu kwalliya, ta yi musu vedio suna riƙe da kayan suna bayanin a zo a siya, Yusuf dake zaune a office yana ƙarasa aiki don sun kusa tashi, abokinsa ya shigo ya zauna fuska babu walwala, Yusuf ya ce"Ya dai?"
Abokin ya ce"A gaskiya Yusuf kana cikin tsaka mai wuya, sam ba ka more aure ba, a ce mace ta zama 'yar media tana neman ta saka yaranka ma a ciki? Idan ita ba ka isa da ita ba ai ka isa da yaranka".
Ya gyara zama ya ce"'Yarka mace ce Yusuf za ta gurɓata mata tarbiyya a banza, kalli abin da ta yi posting yanzu".
Ya kunna vedion da ya yi saving ya miƙa masa wayar, wani baƙin ciki ya kama Yusuf, ganin Yusra riƙe da maganin maza tana cewa"A lokacin baya hankalina ya tashi saboda ina damuwa da son na samu ƙani, sai Momyna ta ce mini za ta share mini hawaye, wannan maganin shi ta nuna mini ta ce"Allah ne zai ba ni ƙani, sannan wannan maganin ne zai ba ni ƙani, cikin ikon Allah sai ga shi na samu ƙani silar wannan maganin, don haka ku zo ku siya man power domin kyautata soyayyarku da mazajenku".
Duk da ya san tsara mata aka yi amma abun ya tsorata shi, yadda har ta haddace, yarinya ƙarama 'yar shekara takwas a ce tana tallan maganin maza? Anya Zubaida tana da hankali kuwa?
Ya miƙa masa wayar, yana cewa"Amma ban gani a page ɗinta na tiktok ɗin ba, ina bibiyarta".
Abokin ya ɗan daburce kaɗan kafin ya ce"Za ta ɗora, ai dama sai ta fara sakawa a status".
Yusuf ya ƙanƙance ido ya ce"Ya aka yi ka sani?"
Gabansa ya ba da rass, tun da ba zai iya faɗa masa yana da lambar matarsa har suna fira, kuma yana siyan kayanta ba, ya ce"Matata ce take ba ni labari, yanzu ma ita ce ta turo min, take cewa sam bai dace ba".
"Ok" Kawai Yusuf ya ce ya cigaba da aikinsa amma ransa ya yi baƙi, a gurguje ya ƙarasa aikin, ya tattara komai ya bar companyn.
Sotari idan ya tashi gidan iyayensa yake tsayawa su gaisa har ya yi sallar magriba, sannan ya koma gida ya yi wanka ya ci abinci ya ɗauki mukullin shagon da yake siyar da kayan provition ya tafi, sai kuma dare zai dawo, amma yau sai ya zarto gida, yana shiga tsakar gidan yake jiyo shewar mata, a bakin shiga falon ya ga maza masu delivery suna zaune, suka yi masa sallama kawai ya ɗaga musu hannu, har zai shiga ya fasa, ya zagaya ya shiga ta vantilation, ya shige ɗakinsa ba tare da sun gan shi ba, zama ya yi shiru yana nazari, yanzu a ce rayuwa za ta tafi a haka, matarsa ta dinga abin da ta ga dama kuma ba shi da ikon hanawa? Tun tuni ya san ta yi block ɗinsa a whatsApp, shiru kawai ya yi mata saboda ba ya son fitina. Can dai jin an fara kiraye-kirayen magriba kuma matan ba su gama watsewa ba sai ya ɗauki waya ya kira ta, tana ɗagawa ya ce"Na shigo fa ina ɗakina ina jiranki".
"Ok" Kawai ta ce, ta katse kiran, ta cigaba da sabgarta, ganin za a shiga sallah sai ya yi alwala ya tafi masallaci, ana idarwa ya koma gidan, ana idarwa ya dawo, yanzu ta ƙofar falon ya shiga, ya tarar da mata uku sun baje suna ta fira, ga kuma wani matashi zaune yana ts liƙe kaya da gam, ita Zubaidan tana ware kaya da littafi a hannunta, ga kuma waya liƙe a kunnenta, daidai sanda ya shigo ta ji yana cewa "Alhaji kayanmu ingantattu ne, idan ka gwada za ka dawo mini da feedback". Ta gefen ido ya kalli yadda take ta washe baki, ta tattare doguwar rigarta ana ganin dogon wandon jikinta, fuska a murtuke ya ce"Zubaida ina jiranki". Ya shige ɗakinsa
Ranta ya ɓaci sosai, a ce a gaban mutanenta ya kira ta da sunanta gatsal babu wata soyayya? Ita da take gyaran aure take zuwa tana ƙaryar yadda mijinta yake riritata, shi ne zai zo ya yi mata magana haka fuska kamar kunun kanwa? Jikinta sai ya yi sanyi ta ce musu"Ina zuwa, bari na je na ji, dama ya faɗa mini sun yi faɗa da wani abokin aikinsa, bari na je na kwantar masa da hankali".
Ɗaya cikin matan ta ce"A'a ni kam kin ga tafiyata, C.E.O guda ta shiga rarrashin miji ai ba san sai gobe za a fito".
Duk suka saka dariya kowacce ta kwashi kayanta suka tafi.
Sai shi matashin da yake cewa"Idan na gama na je da su kawai ko?"
Ta ce"E ai duk ba cikin gari ne, a yau ma za ka iya kai wa ko'ina, sai da safe".
Daga haka ta shiga ɗakin nasa, zaune a bakin gado ta same shi, ta haɗe rai sosai ta ce"A gaskiya Yusuf ba na son irin abin da kake yi mini, ya ka san ina kan aikina za ka matsa mini da kira? Har ma ka zo gaban ƙawayena kana kirana ranka a ɓace? Me kake nufi ne?"
Ya ce"Nan gidana ne, ina da ikon shiga ko'ina ko da kuwa kina da baƙi, babu ruwana da baƙinki, kuma zan yi miki gargaɗin ƙarshe, kar na sake zuwa gidan nan na tarar da namiji a cikin gidana, duk wani ɗan iska iskancinsa ya dakata daga ƙofar gida, saboda ba ki dan kanki ba namiji har cikin ɗaki? Wannan wane irin jahilci ne?"
Ta ce"Duk wani namiji da za ka gani a gidan nan abokin kasuwancina ne, kuma tun da ka san da sana'ata ka kuma bar ni na yi to ido ne naka, babu ruwanka da waye zai shiga waye zai fita, sai dai ko idan zargina kake yi wannan sai ka yi bayani, kuma namiji da kake batun ya zo har ɗaki ƙanina ne, da babata da babar shi uwa ɗaya uba ɗaya suke, ka ga kuwa ba ka da ikon hana dangina shigowa gidana".
Ya ce"Gidanki ko nawa?"
Ta ce"Ai tun da ni ce matar gida ina da iko da shi, idan kana son goge kalmar gidana to sai dai ka sake ni".
Ya ce"Ina ba ki abinci ke da yaranki, ina yi muku sutura, ina biyan kuɗin makaranta, ina yi muku magani, komai na hidimar gidan nan ina yi daidai karfina, haka ne?"
Ta ce"Tun da ka ce daidai ƙarfinka zan iya yarda, don kuwa ni dai sana'ata ce take ɗauke mini sauran buƙatuna".
Ya ce"Ok! Zubaida daga yau idan kin yarda ni mijinki ne na soke wannan sana'ar taki, kada ki sake yi, kuma idan kika sake posting 'ya'yana a media ko da ba tallan kaya kika ba su ba za ki ga matakin da zan ɗauka, ai neman kudi ba hauka ba ne".
Ta yi wata dariyar rainin hankali ta ce"Amma dai ka san babu wanda ya isa ya hana ni sana'a ko?"
Ya ce"Ba zan sani ba sai na ga kin ƙi hanuwar tukunna, sannan za ki ga matakin da zan ɗauka".
Ta ce"To za mu ga wanda zai janye ƙudurinsa a tsakaninmu".
Ta fice daga ɗakin, shi kuma gidan iyayensa ya tafi. Kafin ma ya ƙarasa har wayar Zubaida ta riga shi zuwa, ya shiga ya tarar mahaifiyarsa tana waya da ita, wayar a hans free take don haka ya zauna yana saurara, daidai inda take kuka tana cewa"Mama ni idan zaman nan ba zai yiwu ba kawai ya sake ni, sai da ya ga na fara samun ɗauka zai ce na daina? 50-50 fa muke yi na ɗawainiyar gidan, sutura Indai mai tsada ce ta shiga mutane sai dai na yi wa kaina, idan wata ya yi nisa kuma ni ce nake ƙarasa cefanen gidan, ban da ma ba a son tone-tone wallahi idan kika ji abubuwan da yake mini sai kin yi mamaki, kamar ni kaɗai ce mai kasuwanci da aure? Abun nan fa a gida nake yi, akwai masu fita waje suna yawo gida-gida, kuma shi ne ya hana ni buɗe office ya ce na yi a gida, to a kan me zai ce wai kar namiji ya shigo masa gida? Ƙanina ne fa".
Takaici bai gama kama shi ba sai da ya ga Mama ta dage tana ta ba ta haƙuri, ita kuma tana sake ƙirkiro wasu zantukan, da haka dai har suka yi sallama ya yi shiru yana sauraronsu.
Sai da ta gama ya ce"Mama don girman Allah ki yi mini uzuri a wannan karon na haƙura da auren nan".
Mama ta ajiye wayar ta rafka salati sannan ta fara matsar ƙwalla, kafin ta ce "Innalillahi wa inna alaihi raji'un! Yusuf kai wane irin taurin kai ne da kai? A da ina tunanin zuciyar kakanka na wajen uba ka ɗakko, amma yanzu na lura ka ma dame shi ka shanye, kai wawan ina ne kidahumi? Sai ka ce ba ɗan zamani ba har ka dinga saka kanka a tukunya kana cewa matarka ta daina sana'a, to wallahi idan na sake jin makamanciyar maganar nan za ka sha mamakina, kuma ko bayan raina ban amince ka saki Zubaida ba, a zamanin nan za ka samu mace kamarta ne? Ban da iyayenta ba da tuni kana nan kana gararin dako a kasuwa ba? So kake a ce mana butulu?"
Ya ce"Amma Mama..."
Ta ɗaga masa hannu ta ce"Kar na ji komai, babu ruwanka da sana'arta, babu ruwanka da baƙinta kuma, amma fa sai idan na isa da kai".
Ta ƙare da faɗin"Ka tashi ka ba ni waje, kafin raina ya ƙara ɓaci".
Ya ce"Ki yi haƙuri Mama, shikenan ta cigaba, amma ta daina saka 'ya'yana, tallan maganin maza da take ba su, ba a san iya shekarun da vedios ɗin nan za su ɗauka ba, idan suka girma suka fahimci ma'anar kalaman da suka yi wane kallo za su yi mana ni da itan? Ita matata ce ba 'yata ba, tun da iyayenta sun yarda ta yi komai a media ba komai ba ne, kuma Allah Ya jarabce ni da zama da ita dole shikenan ta yi, amma su 'ya'yana ne, ni ne nake da ikon yin yadda na so da su ba kowa ba".
Mama ta saki ba ki ta ce"Au kenan dai a taƙaice gorin 'ya'ya kake yi mini ko?"
Ya ce"Ni ba haka nake nufi ba sai da safe".
Ya fice daga gidan ransa a ɓace, shagonsa ya nufa ya zauna ya fara ciniki, gabaɗaya zuciyarsa a jagule take, can kuma sai ya tashi ya rufe shagon, bisa shawarar zuciyarsa ya tsallaka kusa da su ya je ya sayi sabon layin mtn aka yi masa regester, ya tafi gida.
Haka ya tarar da falon kaca-kaca, da alama sun ci abincin dare bayan fitar tashi, firji ta buɗe ya ɗauki lemo ya shiga ɗakinsa, ya binciko wata waya ya saka layin a kai, ya jona ta a caji.
08028966015
[10/07, 5:56 am] Sadiya Abdulrazak: IMZEEDVENTURE
https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha!
Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo?
To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE!
Za ki sha mamaki! 🤩Muna da:
✅ Adashe na kayan kitchen
✅ Kayan yara sabbi da gonjo
✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau
📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253
📩 DM: WhatsApp
📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture
*AURE A YAU*
NA
*SADIYA ABDULRAZAK*
MARUBUCUYAR
Sandar dukan uwargida
Miji goma
Wani zaman
Zuciyar mace
Iya ruwa
Wani auren
Wutar ƙaiƙayi
Da walakin
Matar shige, dss
*First class writers association*
Page 6
Haka ya kwanta bai ci abinci ba, sai wajen ƙarfe ɗaya na dare ya farka da yunwa, a dole ya fito ya ci abincin, sai kuma ya kasa komawa baccin saboda yanayin da yake ciki na buƙatuwa, ya san idan ya je ya tunkari Zubaida ransa ne kawai zai ɓaci, amma babu yadda zai yi dole sai ya je ɗin, saboda yana jin yau ya kai ajin ƙarshe, ba zai cutar da kansa ba tun da dai yana da halal ɗinsa, don haka ya tafi ɗakin nata, ya tarar tana ta sharar bacci, ya hau gadon ya matsa kusa da ita, yana fara taɓa ta ta farka tana tsaki ta ce"Wai lafiya kuwa?"
Bai amsa ba, bai kuma sake ta duk ƙoƙarin fizgewa da take yi, rai a ɓace ta ce"Yusuf wai mene ne haka ne? Na fa gaji, sai ka ce ba ɗazu ka gama ci mini mutunci ba, shi ne yanzu za ka zo kana naniƙata, to kusanta ta ba naka ba ne tukunna, gara ma ka bari sai mun san inda matsayin auren namu yake".
Ya ce"Ban gane matsayin aurenmu ba".
Ta ce"Ƙwarai kuwa, domin ni dai ba zan zauna da mijin da zai hana ni sana'a ba, wallahi ko ina za a je ɗayan biyu ne, ko dai na cigaba da sana'ata ko kuma a haƙura da auren, sai ka auro mai zaman ɗumama maka kujera, wacce ko ɗan kunne sai ta ce ka siya mata".
"Ok" Kawai ya ce, ya cigaba da abin da yake yi mata, yana ta ƙoƙarin danne ɓacin ransa, kusan ƙarfi-ƙarfi ya saka mata ya samu ya rage abin da yake damunsa, ba don ya samu cikakkiyar gamsuwa ba, ya koma ɗakinsa ya yi wanka ya kwanta, yana tunani a kan shawarar da yanke, Allah Ya ga zuciyarsa shi ba zarginta yake yi ba, amma yadda ya ga tana waya da namiji ɗazu ya sa shi jin yana son sanin iyakarta kan mu'amala da abokan kasuwancinta maza, ya ga yaya take yi, wasu irin kalamai take yi musu, shiyasa ya yanke zai je mata da sabuwar lamba, da sunan customer, amma dai yana fargabar abin da zai tarar.
GIDAN HAMZA
Da safe bayan Hamza ya fita Saude ta shiga ɗakin Sahura tana dariya ta ce"Amma Sahura kin cuce ni, shekararmu nawa da mutumin nan bai taɓa kama ni da sata ba sai yanzu da kika zuga ni, Allah na ji kunya fa sosai".
Sahura ta yi dariya ta ce"To da na zuga ki na ce ki yi dole ne? Kuma wallahi rashin wayonki ne ya ja mana komai, ta ya ma kika bari ya kama ki?"
Saude ta ce"Hmm! Wallahi farkawa ya yi ina cikin zaɓen wanda zan ɗauka, ƙaddara dai kawai".
Sahura ta ce"Hamza kenan, ga tsoro ga daren kasuwa, ni kuwa idan ba ɗaure ni zai yi ba ina ji ina gani ta ya zan yarda ya ɗibar mini wake?"
Saude ta ce"Kin ga Sahura mu zuba masa ido kawai ya yi aurensa, ai jiki magayi, shi fa ƙarin auren ma bai karɓe shi ba, cikin waɗanda ya aura ke kaɗai ce kika iya zama, ke ma don a tsaye kike, amma mu zuba ido mu ga wacce zai auro".
Sahura ta ce"Ai Saude ina mamakin rashin kishinki, kamar wacce aka yi muku auren dole?"
Saude ta ce"Wallahi baƙincikinsa na tara kawai Sahura, shiyasa gabaɗaya ya fita daga raina, yanzu ne ma dai da ya canza hali soyayyar ta fara farfaɗowa, don haka ni babu ruwana da ƙarin aurensa".
Sahura ta ce"Ai shikenan Allah Ya sanya alkhairi".
Saude ta ce"To yanzu kika yi magana, kawai mu zama kurame mu zama makafi, mu ga abin da Allah zai yi, mu dai mun zama ɗuwawu a gidan nan dole a zauna da mu".
Tun daga ranar Hamza ya sake tsare gida, sam ba sa ganin walwalarsa, saboda wani haushinsu yake ji, don gani yake kawai su suka hana shirin aurensa sauri, tun da inda babu su ai da iya cikinsa zai dinga ciyarwa, da tuni ya gama haɗa lefen. Ba a fi sati biyu da wannan bidiri ba ya tara su a ɗakinsa, yana wani ɗaga kai sama yake cewa"Dama na tara ku ne saboda na yi muku bayani".
Sahura ta ce"Muna sauraronka"
Ya harare ta ta gefen ido, don azarɓaɓinta yana ba shi haushi, shi fa ji yake kamar ma ya sake ta, kawai dai don ya rasa ƙwaƙƙwaran dalilin yin sakin ne, tsakani da Allah shi auren jari ya so yi da ita, a zatonsa za ta sakar masa jakarta ne ta dinga rage masa hidimar gida, ta dinga gatale shi tana saka shi a ɗaki tana yi masa miyar kaza, sai ga shi ya ga saɓanin hakan, har gara Saude ya san a da yana sonta sosai, kuma yanzu ma wasu halayen nata na ƙeƙe da ƙeƙe kawai ya tsana, da kuma yadda idan tana da shi ba za ta taimaki gida ba, dole sai ya bayar za ta dafa da shi.
Ya yi gyaran murya yana ɗaga kafaɗa da bata rai ya ce"Dama ina so na sanar da ku zan ƙara aure, an saka rana yau, nan da wata biyu in sha Allah!".
Suka haɗa baki wajen faɗin"Allah Ya sanya alkhairi".
Ya ce"To don haka wancen ɗakin na ga kuna shiga shan iska, sai ku daina shiga, a nan Mardis za ta zauna in sha Allah".
Saude ta ce"Babu damuwa Allah Ya nuna mana".
Ya ce"To kuma ba na son fitina, ba na son wasu ƙananun kishi ko rigima, ba zan lamunta ba, aure dai babu wanda ya isa ya hana ni na yi, tun da da kuɗina zan yi, kuma gidana ne ina da ikon kawo duk wacce na ga dama".
Saude ta ce"To Hamza wannan kuma sai dai ka faɗawa Sahura, don ni dai ka