Showing 6001 words to 9000 words out of 21911 words
Chapter 3 - RAYUWAR ZAINAB Complete Book 1234 By Zainab Kabir Jaen.txt
ba tasa su Anty Asabe suka ta ya ta d'iban kayan, ta maidasu can.
Tun da ta dawo kullum sai sunyi waya da ancul aboki, sai dai kuma taki basa damar yazo ko sau d'aya sa bo da Hamma yana nan yayi nacin har ya gaji, gashi kullum sonta k'aruwa yake a zuciyarsa
Yau ya yanke shawarar ko taki ko taso sai yaje gidansu, dan yana kishirwar ganinta, ya shirya tsaf cikin dakakkiyar shaddarsa marun, kana ganinsa kaga had'ad'd'en matashi mai ji da ilimi, a marun d'in matarsa ya fita kai tsaye gidan su ya nufa.
Ita sam bata san da zuwansa ba, ta idar da sallah taji Anty Asabe tana cemata tazo b'akonta yazo, gabanta ne taji ya fad'i amma sai ta dake ta fita garden d'in gidan cikin natsuwa, tun daga nesa ya hangota blue black din hijabine a jikinta yayi mata kyau sosai abinka da farar fata, kafeta yai da ido har ta karaso tai masa sallama tare da jan daya daga cikin kujerun gurin ta zauna ta gaishe shi cike da girmamawa sannan ta ce "zuwa ba sanarwa kawai sai dai naji kazo kaga ko kwalliya banyi maka ba, murmushi yayi tare da fad'in "aike ko baki kwalliya ba kyau kike, dan nikam kin fimin kyau a haka abar k'auna.
Shiru suke cikin farin ciki da annashuwa duk da dai ita tana cikin tsoran kada Hamma ya zo ya taddashi bata san me zata ce masa ba Allah, Allah take yatafi aikuwa tana cikin wannan tunanin sai ga motocinsu sun shi go gida zumbur ta mik'e alamun tsoro suka bayyana a fuskarta amma dakewa tai a hankali yake fitowa daga motar idanunsa basu sauka a koina ba sai akan Zainab d'insa kuma zaune ita da wani duk da dai bai san abin da ake kira da kishi ba amma nan da nan ransa yai wani mugun baci yana cikin kakin sojojinsa cikin natsuwa yake tafiya ya karaso gurin ya ce "keee me kike anan, d'aure fuska tayi ta ce "bakona ne, ancul d'in mu ne, kuma shi nake sa ran zan aura, ita kanta tayi mamakin kanta data iya fadin maganar kallonta yake cikin bacin rai nan da nan idanunsa suka kada sukai ja cikin tsawa ya ce kafin na irga uku kibar gurin nan ai kafin ya karasa sa bo da tsorata tabar gurin shika ancul aboki tsayawa yai ganin ikon Allah daga gani wannan dai Yayan Zainab ne dan ga kamanan bare ya ce kishi ne, dan haka a ahankali ya ce "kayi hak'uri Yayanmu wallahi na tambayeta yafi saunawa ta barni nazo nagana da iyayenta amma taki yarda ni kaina banso nafara zuwa gurin ta ba tare da neman izini ba amma wallahi ba wai nazo da niyyar yaudarar ta bane ni aurenta zanyi.
Wani kallo Hamma yai mai tare da fad'in "okey ba matsala zan yi magana da iyayen mu ya ce "to yayanmu ngd,"
Barin gurin yayi kai tsaye part d'inta ya nufa yaje ya taddata tana ta rusa kuka kanta ya damko ya ce "da aurena akanki kike kula wani, ina amfanin iliminki? to yau shi ne jan kunne na farko kuma na k'arshe da zan miki wallahi na k'ara ganinki da wani, abin da zan miki bazai miki kyau ba ki bari in ba aurena akanki saiki kula kowane kare ko kina tunanin akwai wanda zai aureki bakida cikakken asalai ne? burina a kullum bai wuce naga na samo miki iyayenki ba na maidaki `Ya mai enci kamar kowa, amma ke wato soyayya ce a gabanki koh? ya ce ko kina tunanin shi saurayin naki zai aureki inyasa wacece ke? to wallahi ki nutsu kisan me yake miki ciwo......
Kuyi hakuri da wannan
Ina godiya agareku masoyana Allah ya bar kaunar
Inayi wa duk wani Dan kungiyar Royal Star fatan alkhairi.
Allah ya kara dauk'aka " kungiyarmu mai albarka.
#zainab kabir Jaen
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹Rayuwar Zainab❤🩹
Story & writing
By: Zainab Kabir Ja'en
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A}http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishadantarwa (R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi
Alkalaminmu yancin mu.
FREE BOOK📖📚
🅿️........1️⃣1️⃣
Ya saketa tare da barin gurin, kuka tasa mai cin rai, a yanzu Hamma ya tuna mata wace ce ita, ada ta shagala ta daina wannan tunanin, sam bata ga laifinsa ba, sa bo da a kalamansa ba abin da yayi karya, ita d'in mara asali ce, mara gata! shi yayi mata duk wani gata a rayuwarta, ko haka ya barta ba abin da zata ce masa tunda ya suturta, ya bata ilimin addini dana boko, to ita kuwa mai zai sa ta k'i mishi biyyaya! Tayi alk'awarin zata bauta masa har karshen rayuwarta, amma ta yaya? Tana mutukar son ancul aboki, kuma tasan ko ba dade ko ba jima Hamma sai ya saketa! Dan tasan bazai iya zama da ita ba, tashi tai ta d'auro alwala ta gabatar da sallar nafila tana addu'ar Allah ya baiyana mata iyayenta.
Shi kuwa a b'angarensa yana shiga daki ya fara farfashe kayan D'akin yana huci, zuciyar maza ta b'aci sai da yaga yafara jiwa kansa ciwo ya dakata, yana fad"in "why? Meyasa zata min haka? da aurena akanta ! Zuciyarsa ce ta ce mai "kai to me ye naka aciki tunda ba sonta kake"afili ya ce sa bo da kare mutuncin aurene badan haka ba ina ruwana da ita, d'ayar zuciyar kuma ta ce mai "ko dai ka fara sonta, tun da kaganta da wani kaji haushi," da karfi ya ce noooo bazai yuwu ba.
Wanka ya shiga ya shirya cikin k'ana nan kaya ya fita, motarsa ya nufa yabar gidan ya tafi gidansu abokinsa Kamal,yana zuwa Kamal ya ce "yau kaine a gidanmu Captain lafiya kuwa naga kamar ranka a b'ace?" murmushi yayi tare da fadin lafiyar kenan" Kamal ya ce no fad'a min gaskiya kodai-kodai....." harararnsa yayi ya ce kaga "Malam dakata ni mene had'ina da ita 'murmushi Kamal yai ya ce calm down abokina me ya faru ? "Ahankali ya labarta masa abin da yafaru, ya ce "ni ba wannan ne damuwata kaga akwai aurena akanta ba " numfashi kamal ya sauke ya ce "abokina naji abinda ya faru kuma gaskiya bata kyauta ba amma kaima da laifinka in kana sonta kawai ka rik'e matarka hannu biyu ba hujja bace, kace ta jira sanda ka saketa ta kula wani kuma inka lura Zainab yarin ya ce mai bukatar tallafin wani tunda ta rasa iyaye tana son wanda zai jata a jiki ya dinga fad'a mata gaskiya amma yanzu duk abin da yazo kanta shi zatayi, karkayi la'akari da cewa baka sonta,ka d'auketa kamar su Basmah zaka gani ba wanda zatayi shawara dashi sai kai wani gauran numfashi ya sauke, ya ce "abokina nagode da shawararka agareni kuma insha Allah zanyi aiki da ita" ya ce "bakomai abokina nima in ka saki inaso kaji Yayanmu "duka ya kai mai yana fad'in " ba kada dama wallahi Allah ya shiryeka, sun dade suna shira dan anan Captain yayi sallar isha'i
To tunda abin ya faru basu kara ganin juna ba, yau ta yanke shawarar zataje ta bashi hak'uri akan abin da ya faru.
Da sallama ta shiga dakin, yana zaune a falonsa, ya d'ago ya kalleta ya amsa sallamar, ta masa kyau sosai, cikin wata abaya take ammata ado da duwatsu har kasa tayi rolling da mayafinta ta tufke gashin kanta yai kamar tayi acuci, tayi kyau sosai, agefan k"afarsa da zauna ta ce "Hamma ina wuni," cikin sakin fuska ya ce "kin yini lafiya kanwata" tayi mamakin sunan da taji ya kirata dashi amma sai tace "lafiya kalau Hamma, "ya ce "masha Allah" ta sun kuyar da kai tare da fad'in "dama Hamma nazo ne in baka hak'uri akan abin da ya faru, dan Allah kayi hak'uri, sai ga hawaye yafara wanke mata fuska😭😭
"A hankali ya sakko ya durkusa a gabanta ya ce "daina kuka kinji kanwata na dad'e da yafe miki ya karasa fad'a yana goge mata hawayen daya b'ata mata fuska ya ce "daina kukan haka, ki daina b'atamin wannan kyakkywar fuskar taki kanji kanwata yimin murmushi, tai ta ce "to Hamma nagode.
Ya ce "mukulla kawance daga yau kin zama kanwar Captain " ta miko hannunta suka d'aura .
Tun daga ranar ya zamana ko da yaushe indai yana nan suna tare duk ranar week end sai sun fito yawo yanzu gaba d'aya ji suke basu da wata damuwa ita ce yanzu take kula da b'angarensa, cinsa da shansa wataran ma har wanki take mai gabada ta mai dashi dan gata, amma ita har zuciyarta tana yi mai ne a matsayin Yayanta ba wai don tana Matarsa ba, don ita mantawa take wai shi mijinta ne.
Kullum sai sunyi waya da ancul aboki idan ya ce mata zai zo sai tace ya bari Yayanta ya bashi dama a haka yake ta hak'uri
Wannan kenan ............✍️
Kuyi Hakuri da wannan
Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci
Ina yiwa duk wani Dan k"ungiyar royal star fatan alkhairi
Allah yakara daukaka k" ungiyarmu mai albarka
#Zainab Kabir Jaen
{@GARKUWAR ROYAL STAR}
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY & WRITING
BY:ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana,fadakarwa,ilimantarwa,dakuma nishadantarwa,(R.S.W.A)Ruwa Ka"dai ke maganin kishi.
*Alkalaminmu ƴancin mu.*
FREE BOOK📖📚
🅿️.....1️⃣2️⃣
........ Yau Uncle Aboki yacemata,shifah gaskiya yagaji,yau zaizo yasami Yayanta ya mishi magana, dan shi gaskiya yanason ganinta,Tarasa yanda za tayi da shi don gaskiya tana matukar son sa,amma bata son ɓacin ran Yayata,yace "kinyi shiru baki ban amsa ba,"tace "shikenan Allah yakawo ka lafiya", yace "zanzo karfe biyar nasan lokacin yadawo koh?," tace"eh yadawo,"yace"," toh Sweetyna kimin kwalliya mai kyau kinji abar kauna",murmushi tai,tace "toh abin kauna zanyi maka".
Karfe hudu dai dai a kofar Gidan nasu yai mai,horn ya yi,wani Soja yataso da sauri ya bude,yana ganinshi ya ganeshi,yace "barka da zuwa ranka ya dade", murmushi Uncle Aboki yay yace "barka dai,Dan Allah Captain yadawo gidane?," da sauri yace eh ranka yadade, yadade da dawowa ai", Uncle Aboki yace " toh Dan Allah kamin magana dashi,kacemasa ya yi bako," da sauri yace "toh bari namasa magana.
Wayar shi ce yaji tana kara da sauri yakara gurin ,tare da fadin " hello " a dayan ɓan garen sojan yace" Ranka ya Dade kana da bako yana dakin baki", a hankali yace "ina xuwa toh " ya fada tare da kashe wayar, tashi yay kai tsaye falon bakin ya nufa Sallam yay Uncle Aboki Ya amsa mai cikin girmamawa, suka gaisa sannan Captain yace "amma abokina ban ganeka ba?", "Ankul Aboki yace"da farko ni dai sunana Abubakar Abdullahi,Amma ana kirana da Uncle Aboki,ni Malamin Ƙanwarka ne Zainab Al'ameen, kuma magarnar gaskiya nazone kabani izini domin nafara zuwa wajanta zance,"nan take Captain yaganeshi wato wannan Malamin na sune daya taba ganinsu tare,tabbas shine sai yanzu yaganeshi!" Nan da nan ya hade rai kamar hadarin gabas yace "toh ni dai Zainab Ƙanwace a gurina kuma iyayen mu ba anan suke ba, Dan haka bani da damar yanke hukunci akanta!, " numfashi Uncle Aboki ya sauke tare da fadin" Yayanmu wallahi! Ina sonta Kuma aurenta zanyi Yayanmu Dan Allah kaban izini na fara zuwa gurinta Dan Allah, " shima Captain numfashin ya sauke, a ransa yana tunanin taya zai bawa wani kato damar zuwa wajan matarsa zance?, abinda bazai yuyu bane,afili kuma sai yace " bari in turo ma ita ta fadamaka gaskiya ya karasa fada yana mikewa, musabaha sukai Uncle Aboki yace" nagode Yayanmu", yace "no bakomai" .
Tana zaune agefan gadonta taji Sallamar sa, Amsawa tayi cikin sanyi murya tace "Hamma sannu da dawowa kayini lafiya "zama yai, ya amsa sallamar cikin murmushin da ya tsaya iya lab'b'ansa sannan yace ", kinyi bak'o kinsan da zuwansa?," sunkuyar da kanta tai k'asa Tace" eh Hamma nasan da zuwansa!,"kallonta yay yace mene hadinki dashi? ",Kanta akasa tace "dama Hamma sai kuma tayi shiru," yace "dama me", tace "Hamma Saurayina ne" tafada k'irjinta yana dukan uku uku, yace " Zainab kiji tsoran Mahaliccinki,kinsa nema akan nema Haramune koh?," ahankali ta d'aga kai alamun "eh", yace" amma meyasa kike kula wani Namijin alhalin kinsan dawani auren akan ki? To Ki nutsu kisan meyake miki ciwo, ni Zainab ina samun Iyayenki zan sauwake miki Aurena dake kanki ki auri duk Wanda kike so, amma yanzu, ba dai dai bane ki take k'a'idojin Ubangiji, kiji tsoran Allah, ki tuna cewa zaki mutu zaki koma ga mahaliccinki!".
Gaba daya jikinta yayi sanyi nan da nan hawaye ya wanke mata fuska a hankali tace "Allah na tuba Hamma kayi hakuri Dan Allah", a hankali yace ni na yafemiki Ƙanwata amma ki fada masa gaskiya kinji Ƙanwata ," tace "Toh Hammana insha Allah " yace "good" yana falon baki yana jiranki", Tace" toh Hamma".
Wannan kenan...............📝📝
Kuyi Haƙuri da wannan
Ina godiya Agareku masoyana, Allah ya bar zumunci.
Ina yiwa duk wani d'an Ƙungiyar Royal star fatan Alkhairi.
Allah yakara d'aukaka Ƙungiyarmu mai albarka.
#ZAINAB KABIR JAEN {@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY AND WRITTING
BY:ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writer's-Association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fa"dakarwa,ilimantarwa,dakuma nishad'antarwa(R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin k'ishi.
Alkalaminmu "yancin mu.
FREE BOOK📖📚.
🅿️.............1️⃣3️⃣
Zainab ce ta sunkuyar da k'ai tana goge hawaye, ta ce "To Hamma", Murmushi ya yi shi ma ya ce "Good tashi kije" tashi tayi jikinta a sanyaye ta nufi falon bakin, Sallama tayi a sanyaye, Uncle Aboki daya Dade yana jiranta da fara'arsa ya d`ago ya kalleta, ya ce "barka da zuwa abar kauna, tun dazu da Yayanmu ya tafi nake ta kallon hanya, shi ne kika shanyani ko?" ya fad'a kamar zai yi kuka, Zainab murmushi tayi ta ce "barka da zuwa Uncle", Mamaki ne ya kamashi rabon da ta kirasa da wannan sunan tun kafin su fara Soyayya da ita, danne mamakin nasa yayi suka gaisa sun d'an taba hira ba sosai ba, sannan Zainab ta ce "Uncle ina son magana da kai" "To abar kauna ina jinki" Cewar Uncle. Hawayenta ta goge, Sannan a hankali ta Zayyane masa labarinta tun daga sanda Baffah ya tsinceta har zuwa Aurenta da Hamma, sannan ta karasa da ce wa "Uncle Allah ya gani ina sonka kuma banyi haka da niyyar yaudararka ba, nasan ko ba dad'e ko ba jima Hamma zai sakeni shi yasa na karbi soyayyarka, sa bo da nasan kai ma zaka zame min gata koda Hamma ya sakeni," ta karashe tare da fashewa da matsanancin kuka! wata Uwar zufa ya goge haƙiƙa ko Mara lmani yaji labarin Zainab da gwagwarmayar da tasha a rayuwa dole ya Tausaya mata amma ya sani Hajiyarsa ba zata tab'a bari ya auri Zainab ba tunda batada asali to shi kam ya zai yi ke nan?, A hankali ya sauko ya durkusa agabanta ya ce "Zainab haƙiƙa kin ga rayuwa wanda duk mara lmani in yaji labarinki sai ya Tausaya miki! Amma kinyi kuskure da ki kayi soyayya da auren wani akanki ni Zainab masoyinki ne kuma ina nan ina jiranki duk sanda Hamma ya sauwake miki ni kuma a shirye nake na aureki", cikin kuka ta ce "na gode da soyayyarka agareni," sallama su ka yi ya tafi cike da tsananin begen juna, tashi tayi ta koma cikin gida zuciyarta na suyar rabuwa da Uncle din nata.
A bangaren Hamma kuma yana komawa part dinsa yaji zuciyarsa tana zafi, band'aki ya shiga ya sakarma kansa shower ko ya samu ya ji sauƙin abunda ya to kare masa zuciya , Amma lna ji yake kamar ana ƙara masa zafin zuciyar wanka yayi ya fito ya shirya cikin wata dakakkiyar blue din shaddah ta amshe shi abinka da farin mutum, wayoyinsa ya d'iba da makullin mota ya fito a falo ya ganta a zaune ta zabga tagumi kallo daya yayi mata ya d'auke kai ya cigaba da tafiya, da sauri ta taso ta karaso gabansa ta ce "Hamma fushi kake dani pls kayi hakuri kaji,?" cikin tsawa ya ce "ban hanya!" ya fada yana zaro mata ldanuwa ai kuwa ta tsorata da sauri ta matsa, shi kuwa gogan na kara cigaba da tafiyarsa kuka tasa, ita kuwa ya zatayi bazata iya jure Hamma ya yi fushi da ita ba ta shiga uku d'akinta ta Shiga ta yi wanka kanta ne taji yana mata ciwo ga wani irin sanyi da take ji, bargo taja ta lulluba kafin wani lokaci zazzabi ya rufeta.
Shi kuwa Captain ya na fita gidansu Kamal ya wuce, yana zuwa Kamal ya ce "abokina naga ranka a bace ko dai Madam din ce?" murmushin karfin hali yayi ya ce "kawai yanayi ne ya zo a haka, na zo ne mu tattauna akan batun neman iyayen yarinyar nan, numfasawa Kamal din yayi ya ce "abokina kawai za mu bada sanarwa ne a Gidan Television da Radio da Jaridu ko Allah zai sa mu dace, shi ma Captain Numfashi ya sauke ya ce "haka ne abokina gobe in Allah ya kaimu sai muje mu kuma bada sanarwar ko?".
Wannan ke nan .........📝📝
Kuyi haƙuri da wannan.
Ina godiya agareku masoyana Allah ya bar zumunci.
Ina yiwa duk wani d'an k"ungiyar Royal Star fatan alkhairi.
Allah ya kara daukaka k'ungiyarmu mai albarka.
#ZAINAB KABIR JA'EN
{@GARKUWAR ROYAL STAR}
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY & WRITING
BY: ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://wwwfacebook.com/royal-star-writer's-association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa, ilimantarwa, dakuma nishadantarwa.(R.S.W.A) Ruwa kadai ke maganin kishi.
Alk'alaminmu 'yancinmu.
FREE BOOK📖📚
🅿️..........1️⃣4️⃣
Sun dad'e suna fira, kafin daga bisani yayi masa sallama ya tafi, daya fito kai tsaye shopping ya wuce yayi mata, d'an gaba d'aya ya mance da sun yi fad'a kafin ya fito, yana shigowa Gidan part d'inta ya nufa da sallama ya shiga, amma yaji shiru ganin bata falo yasa ya nufi bedroom d'inta, ganinta yayi a k'udundune da blanket da murmushi dauke a fuskarsa ya haura saman gadon, ya janye blanket din wani hucin zafi yaji ya daki fuskarsa a kidime yace "kanwata me yake damunki? bakida lfy?me yasa baki fada