Showing 9001 words to 12000 words out of 21911 words
Chapter 4 - RAYUWAR ZAINAB Complete Book 1234 By Zainab Kabir Jaen.txt
min ba? a tare ya jero mata tambayar, amma ko d'aya ba wadda ta iya amsa masa d'an gaba d'aya ta fara fita a hayyacinta, gaba d'aya ya nannadeta kai tsaye hospital ya kaita nan da nan likitoci suka rufa akanta, yana ganin wani Doctor ya fito ya nufe shi yana fad'in "Doctor me yake damunta? ta farfad'o?" Likitan ne yayi murmushi ya ce "karka damu typhoid ne ya ke damunta amma yanzu an mata allurai ta samu bacci nan da lokaci kankani zata tashi", cikin damuwa yace "to Doctor nagode, likitan ya ce "no ba komai nasa wata nurse ta kula da ita zaka iya tafiya yallab'ai" murmushi yayi ya ce "ba damuwa zan shigo goben", hannu ya mika mai su ka yi musabaha sannan ya fito daga Hospital din.
A wannan Daren gaba d'aya bacci yayi k'aura acikin idanuwansa, da asuba ya gabatar da sallarsa, akan dadduma bacci ya d'aukeshi bashi ya farka ba sai karfe goma ko break fast bai tsaya yayi ba ya shirya a gurguje, Hospital d'in ya fara zuwa ya dubata lokacin da ya shiga d'akin bacci take dan haka ya tafi akan zai dawo anjima, Kamal ya kira ya tambayeshi "Abokina kana gida?" A daya ɓangaren Kamal ya ce "E ina nan tun dazu nake jiranka," ya ce "wallahi Abokina bacci ne ya d'auke ni, kuma dana tashi sai da na biya ta Hospital na duba Madam bata da lafiya," cikin jimami Kamal ya ce "ayyah Abokina me ya sameta?" captain ne ya ce "typhoid ne wallahi" Kamal ya ce "ayyah Allah ya bata Lafiya in mun dawo ma je na dubata".
Wannan ke nan..........📝📝
Kuyi haƙuri da wannan.
Ina yiwa duk wani d'an k'ungiyarmu Royal star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci.
Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci.
Allah ya kara d'aukaka k'ungiyarmu mai albarka.
#ZAINAB KABIR J'AEN
{@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY & WRITING
BY:ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 {R.S.W.A}https://www.Facebook.com/Royal-star-writer's-Association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishadantarwa (R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi.
Alkalaminmu yancin mu.
FREE BOOK📖📚.
🅿️.............1️⃣6️⃣
............Yau ta yanke shawarar zata jira shi har zuwa sanda zai dawo, daan haka a falo ta zauna bayan ta gabatar da sallar isha'inta ta zauna akan doguwar kujera tana jiransa har ƙarfe 12 bai dawo ba wasa-wasa har barci ya fara ɗaukanta ba alamun sa, anan falon bacci ya ɗauke ta, shikwa a ɓangaransa bashi ya dawo ba sai ƙarfe 1:30 yana yin parking ɗin motar shi ya hango haske a falo mamaki ne ya kama shi kenan ba tai bacci ba falon ya shiga da sallama ɗauke a bakinsa ,hango ta yayi a kwance akan doguwar kujerar falon ƙarasa wa yayi gabanta ya tsugunna yana kallon ta shidai yasan ba son Yarinyar nan yake ba amma yana jinta acikin jiki da jininsa ji yake tamkar in babu ita bazai iya rayuwa ba yana jinta kamar ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya, ya yi wa kansa alƙawarin kulawa da ita har ƙarshen numfashinsa, gaba ɗaya ya ɗauke ta be sauƙe ta a ko ina ba sai akan gadon part ɗinsa, wanka yayi ya kwanta akan doguwar kujerar part ɗin nasa ,da asuba ita ta fara tashi mamaki ne ya kamata ganinta a ɗakin Hamma ita dai tasan a falo ta kwanta hango shi tayi akan kujera ta zuba masa ido wani irin son Hamma ne yake ratsata amma tasan ba zata taɓa samun shi ba saƙƙowa tayi daga kan gadon tashiga toilet ta ɗauro alwala.
A ɓangaren sa kuwa tunda ta tashi yasani ganin ta tada sallah yasa shima ya miƙe ya ɗauro alwala ya tafi masallaci kasan cewar yau bazai fita da wuri ba yasa bai dawo da wuri ba, ita kuma tana idar da sallah ta tashi ta gyara part ɗinsa tas sannan tasa turare kichin ta shiga ta haɗa musu break-fast shigowa yayi kichin ɗin ya same ta tana soya dankali da ƙwai a hankali yace" barka da aiki ƙanwata", murmushi tayi ta ce"barka dai Hamma" sannan ta tsugunna har ƙasa ta ce "Hamma ina kwana?" shima murmushin yayi yace "Lafiya ƙalau ƙanwata ya ƙarfin miki" ta ɗan shagwaɓe fuska tace"da sauƙi bayan kwana biyu kamanta dani" ,murmushi yayi sannan yace "waya faɗa miki ƙanwata?ke kin taɓa ganin inda mutum ya manta da ƙanwarsa? to ina tare dake aikine yamin yawa wallahi amma kullum kina raina ,turo baki tayi gaba bata kulashi ba marairaice murya yayi yace " please ƙanwata ki ya fema Yayanki kinji dan Allah kimin murmushi kona ji daɗi araina" ,murmushi tayi sannan tace"Hamma ni bakamin laifin komai bafa na ya femaka ma in kayi min" shima murmushin yayi sannan yace "to ƙanwata na gode na tana di gift ɗin dazan baki amma saikin gama aikin ki zan baki tace" to Hamma"yana zaune a kichin ɗin yana ta yata hira a haka har ta ƙarasa aikin sannan suka ɗiba suka jera a dining ,tace "Hamma bari inje part ɗina nashirya kajirani fa karka tafi" yace "to ƙanwata ina jiranki amma fa kiyi sauri kinga nakusa makara" tace"toh Hamma ganinan .........
Wannan kenan........📝📝
Kuyi haƙuri da wannan.
Inayiwa duk wani ɗan ƙungiyar Royal star fatan alkhairi Allah yabar zumunci.
Ina godiya a gareku masoyana Allah yabar zumunci.
Allah ya ƙara ɗaukaka ƙungiyar mu mai albarka.
#ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY & WRITING
BY: ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.}
http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fa"dakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad"antarwa.(R.S.W.A)Ruwa kadai ke maganin kishi.
Al"kalamin mu "yancin mu.
FREE BOOK📖📚.
🅿️................1️⃣5️⃣
Ba damuwa yanzu kana gida ne cewar captain, "a d'aya bangaren Kamal yace" eh ina gida ka karaso kad'aukeni dan bazan fita da motor ba, "captain ya ce" ok ba damuwa gani nan zuwa, ya fad'a yana katse kiran, "kai tsaye gidan su Kamal ya nufa, horn yayi gate man d'in gidan yazo ya bud'e mai yana fad'in "barka da zuwa Yallab'ai, "Captain ya kalleshi da murmushi ya ce, "yauwa Baba barka dai, an tashi lafiya, "Lafiya kalau" cewar Baba mai gadi bayan sun gaisa, "kai tsaye parking space d'in gidan ya nufa yayi parking din motarshi sannan ya shiga gidan, da Nadiya yafara cin karo kanwar Kamal, "da sauri ta ce " lah Mommy kinga Yaya Al'ameen yazo, Yaya Al'ameen sannu da zuwa, "murmushi yayi ya ce" yauwa k'anwata, sannan ya wuce suka gaisa da Mommy, sun dad'e suna shira sannan ya tashi ya ce " mom bari nak'arasa part d'in Kamal, "tace toh son kak'i kawo min matarka dai naganta koh?, "murmushi yayi ya ce "Mom zan kawo miki ita next week insha Allah, "murmushi ta yi ta ce Allah ya kaimu da rai da lafiya, "Ameen ya ce sannan ya k'arasa part d'in Kamal da yake shirin fitowa, "yace ka iso kenan?, to mu k'arasa, "ya ce na dad'e ai ina gurin Mommy muna fira, "Kamal ya ce" ok badamuwa mu wuce, "nan suka juyo suka nufi falon gidan, "Mommy su kai wa sallama sannan suka fito suka tafi gidan radio da jaridu gidan talabijin duk suka bada sanarwa, "sannan suka juyo suka nufi asibitin
zaune suka sameta tana shan tea, ya jiki sukai mata sannan suka nufi gurin Dector "kai tsaye office d'in Likitan suka shiga da sallama a bakin su, ya amsa da murmushi a fuskarsa sannan ya basu gurin zama suka zazzauna sannan suka gaisa captain ne ya ce" doctor ya jikin nata?, "murmushi Likitan ya yi sannan ya ce" jikinta da sauki yanzu ma zaku iya tafiya da ita, "captain ya ce" to Doctor badamuwa mun gode, "sannan ya basu sallama suka nufi gida, bayan ya sauke ta ya maida Kamal gida sannan ya dawo
A falo ya ganta kwance akan kujera doguwa, "ya k'araso kusa da ita ya ce " k'anwata ya jikin?, "ta ce da sauki Hammana, "ya ce masha Allah Mom d'in su Kamal tace tana so ta ganki insha Allah next week zan kai ki
Cikin muryarta, ta marasa lafiya ta ce" to Hamma Allah ya kaimu lokacin, "tashi yai ya nufi part d'insa, "itama b'angaren nata ta nufa, su Aunty Asabe da Baaba Kande ne suka shigo suka dubata, sun dad'e kafin suka tafi, "wanka tashiga sannan ta gabatar da sallar magariba
tun daga Wannan Rana ganin Hamma ya yi mata wuya dan da safe kafin ta tashi ya fita ba ya dawo wa sai wajan karfe sha d'aya lokacin kuma ta dad'e da yin barci, "aiki ne yayi masa yawa ga shi ta b'angaren cigiyar iyayenta da ya bayar, amma tana ransa gaba d'aya a wannan lokacin sai taji ta damu da rashin ganinsa.
Wannan kenan.........
Kuyi hakuri da wannan .
Inayiwa duk wani d'an k'ungiyar Royal star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci.
Ina godiya agareku masoyana Allah ya bar zumunci.
Allah yakara d'auka ka kungiyar mu mai albarka .
#ZAINAB KABIR JA'EN
{@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY & WRITING
BY:ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py _c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa.(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.
Al'kalamin mu 'yancin mu.
FREE BOOK 📖📚
🅿️................1️⃣7️⃣
Da sauri ta 'karasa part d'in nata ta shirya, sanda ta fito har ya gama shiryawa kallonsa tayi yayi kyau sosai a hankali ta bud'e baki tace "sorry Hamma na dade ko?" yace "a'a 'kanwata ba komai zauna muyi break fast sauri na ke yi" tace " to Hamma" tunda suka fara break din kowa ya yu shiru dan kowa da tunanin da yake, bayan sun kammalla ta d'ebe kwanunka ta kai kitchen sannan ta zo taraka shi har bakin motarsa ya tafi ita kuma ta koma cikin gidan, Hamidah ce ta kirata ta d'aga da murnarta tana fad'in "hello 'kawata wato kin manta dani kwana biyu ko?" a d'aya 'bangaren Hamidah ta ce "'yar rainin wayo ai ni fushi nake dake kuma yanzu ma sa'a ki ka ci na kiraki" marairaice fuska tayi kamar Hamidar na wurin tace "kai bloody me nayi miki kuma?" Hamidah tace "yaushe rabon da ki zo ki gaida Mamanmu?, yanzu ma gaba d'aya kin yada mu jiya da mu ka yi waya da sis Fatima tace ita ma rabon da kuyi waya harta manta" cikin sanyi murya tace "dan Allah sis kuyi ha'kuri kunsan koda yaushe kuna raina kuma in Allah ya yarda ina nan zan zo kin ji? Bestyna" cikin murna Hamidah tace "to my bloody sai kin zo" tace "insha Allah" sun dade suna waya kafin suyi sallama, bayan ta katse kiran ta tashi ta gyara gidan ta tafi ɓangaren su Mama Kande acan ta yini suna aikace aikacen su kamar yanda suka saba, bayan sun yi sallar magariba Anty Asabe tace "ni kuwa 'kanwata kinga yanda kika koma? ki fada min gaskiya mene tsakanin ki da yalla'bai na fara zargin wani abu!, Da farko ya d'aukeki daga 'bangaren masu aiki ya mai dake part ďin kusa da nasa sannan kuma ya hanaki kula saurayinki mene dalili? ki fadan gaskiya 'kanwata babu 'boye-'boye a tsaninmu ke 'kanwata ce", sunkuyar da kai tayi tace "a zahirin gaskiya na boye muku wani 'bangare a labarina nan ta bata labarinta har zuwa aurenta da Hamma har i zuwa kawo yanzu, murmushi Anty Asabe tayi tace "Alhamdullilah amma na ji daďin wannan auren naku dan wallahi kunyi matu'kar dacewa Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi Allah ya bayyana miki iyayenki Allah kuma ya dai-daita tsakaninku" dariya tayi tace "kai Anty Asabe wannan murna haka to Allah ameen" nan suka cigaba da hirarsu cikin nishad'i dan har ga Allah suna jin junansu a rai.
A d'ayan ɓangaren Abbie ne zaune yana ta tunanin rayuwa, Basma ta shigo tace "Abbie hutawa kake yu anan?" ya ce "wallahi Basma tunanin y'ar uwarki nake yi yau shekaru sha tara ke nan amma har yau shiru babu ita babu dalilinta ga Ammin ku kullum ciki damuwa, ga wannan lallura dake damunta na rasa yanda zanyi kuma ni har yanzu ban fidda ran zan ganta ba, gaskiya Hajiya Falmata ta cuceni!nayi Dana sanin saninta Allah zai bi min ha'kina insha Allah" ya fad'a yana goge 'kwallar da ta taru a idonsa ita ma Basma haweyen daya wanke mata ta goge ta san iyayenta basu da wata damuwa da ta wuce 'batan yayarta kuma kullum inta kai goshinta 'kasa sai tayi addu'ar Allah ya bayyana ta iyayenta su huta cikin sanyi murya tace "Abbie insha Allah a jikina ina jin Allah ya kusa bayyana mana Anty Ummi" murmushi ya yi yace "Allah yasa 'yata" tace "yauwa Abbie dama ina son zuwa Nigeria wajan Hamma Al'ameen" yace "to amma ba yanzu ba" ta ce "to Abbie".
Su waye Al'ameen? ..........
Wannan ke nan.......✍️✍️
Kuyi haƙuri da wannan.
Ina yiwa duk wani d'an 'kungiyar Royal star fatan alkhairi Allah ya bar zumunci.
Ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci.
Allah ya 'kara d'aukaka k'ungiyarmu mai albarka.
Ina godiya a gareku takwarorina Ummu Raees, kakata, Mauncy, da dai sauransu.
#ZAINAB KABIR JA'EN
{@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: RAYUWAR ZAINAB COMMENT
PAGE 18
Masha'allah Hussain Allah y Sanya alkhairi y Bada zaman lpy t Bada zuri'a mai albarka🤲🏻🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Kaji illar kawayen banza su hure maki kunne su hanaki girmama uwayen mijinki dama shi kanshi mijin sannan Kuma m daga karshe su kashe maki aure y Allah ka kare mu daga sharrin gurbatattun abokanai 🤲🏻🤲🏻🙏🏼
Masha'allah Hassan kaikam k dace d mace Allah y Kara maku hakuri d juna Allah y Baku zuri'a mai albarka🤲🏻🥰💃🥰🥰🥰
Masha'allah Allah y raya al'ameen ga tafarkin tsira y kare shi d kariyar shi yasa mai jinkan iyayen shine🤲🏻🙏🏼
Kai gsky naji dadin wannan abun Hassan d hassana ga Kuma Hussain d Ussaina💃 Allah y Baku zaman lpy Kuma y baka iKon yin adalci a tsakanin matan ka🤲🏻💃💃💃
Hussaina Allah y sauke ki lpia🤲🏻🥰💖💖💖💖💖💖
Masha'allah
Garkuwar royal 🌟 Allah y Kara hazaka d basira d qarfin👀ya kare ki d sharrin masu sharri🤲🏻Kuma Allah y Kara daukaka d Nisan kwana🤲🏻🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Muna godiya sosai
Daga fateemah🥰🌹
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Tsokaci,,
dama mu mata abinda ke cutar mu kenan bakin kishi aduniyar nan mata mafi akasarinsu kishi sukasa alamarinsu yayinda su maxan daake kishin akansuma yawanci Bata tasu sukeba baxaki tsaya kiyi abinda yakawoki duniyaba saidai kibata lokacin ki abanxa akan wata aiyanzu kishin kwatar miji ake kema kixama sarauniya agurinsa bawai Kita shirmen kishi dawata ba wlh mata mukula mudawo haiyacinmu,,
Kunga irinta ai kamar masu Hali irinna hajiya falmata wlh akwai ire irensu harma da wainda suka fisu kiga mace aduniya batada abokiyar gaba samada kishiyarta yesss baace kada kiyi kishi ba kishi halal me ga kowacce mace kuma halittane Amma saikisan irin Wanda xakiyi
kiga mace tabata lokacin ta gabun malamai dasunan mallakar muji ko nakasa kishiya wlh wannan ba maslaha bace aikiyi tsaftataccen kishi tahanyar dawoda martabarki ga mijinki shine kawai
kainifa macen dadake biye biyen malamai wlh batakai maceba tunda bakisan yadda xaki kwaci kanki ahannun wataba saikin hada da xagon kasa wannan kinrako mata duniyane kamarsu hajiya falmata wlh sunyi asara akwai iri irensu dadama harma da wainda suka fisu aikata mummunan aiki duk abinda muke gani akarance karancenmu wlh akwai mata masu aikata mafiyinsa axahiri kuma karshensu Dana sani da nadama
Kalubale garemu Mata ☹️☹️☹️
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤🩹RAYUWAR ZAINAB❤🩹
STORY & WRITING
BY:ZAINAB KABIR JA'EN
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 {R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c
Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.
Al'kalaminmu 'yancin mu.
FREE BOOK📖📚.
🅿️..................1️⃣9️⃣
Yau cikin Usaina ya cika wata tara da sati biyu, a ranar ta tashi da matsanan cin ciwon mara, aka d'auketa a ka kaita hospitalspital nan likitoci suka tabbatar da haihuwa ce, nan aka rufu a kanta, ba'a fi minti ashirin ba ta haifi santaleliyar 'Yarta mace farinciki a wajan a halinta ba'a magana, ana wajan Usaina ana ta yimata sannu da barka ana juyowa wajan jaririya aka ga babu ita babu dalilinta, tashin hankali a wajan a halin nan ba'a cewa komai tun ana d'aukar abin wasa yazamana abin ya koma gaske, daga likitoci har i zuwa ma'aikatan gurin kowa yana cikin tashin hankali, nan aka shigar da report wajan 'yan sanda bincike ake ta ko'ina har rufe asibitin a kayi amma ina
da Alhaji Hussain yaga abin ya'ki 'karewa ya hakura ya fauwalawa Allah, Usaina ta rame sosai, hawan jini yakamata da k'yar aka dinga kar'bo mata rubutun dangana ta hak'ura, amma har yanzu bata koma yanda take daba.
A 'bangaren Hajiya Falmata koda tasamu nasarar d'auke jaririyar kai tsaye wata 'kawarta ta kaiwa ajiya kafin tasamu abin ya lafa taje ta jefar da Yarinyar duk abinda ake ko a jikinta dan ko jaje bata yiwa Uwar Yarinyar ba a cewar ta ita ba abinda ya shafeta bane.
Bayan abin ya lafa ta tambaye shi kan zataje saro kayayyaki ya barta nan ta d'au Yarinyar taje wani daji a Yankin jigawa mai gatari ta yarda ita ba tausayi ko kad'an a ranta, ita dai burinta ta samu burinta ya cika bayan ta dawo sai ta fito da wani salo na shiga jikin Usaina sa bo da taji sirrinta, Allah yasa ita Usainar bame surutu bace barin ma da Yarinyar ta ta 'bata shi yasa bata samu yanda take so ba.
Bayan 'batan 'Yar tasu sai da Hajiya Usaina tayi shekara hud'u sannan ta samu wani cikin, wannan karon 'kasar waje Abbie ya fitar da ita da yaga tana da cikin saida ta haihu 'yarta Basma ta girma sannan ta dawo Nigeria Hajiya Falmata ba'kin ciki kamar ya kashe ta. bayan shekara biyu ta kuma samun ciki haba Hajiya Falmata kamar tayi hauka wannan karon nan ba'kin cikin ta kasa 'buya yayi.
Kun san yaro ba hankali Basma ce ta tafi 'bangaren Hajiya Falmata aikwa