Showing 18001 words to 21000 words out of 21911 words

Chapter 7 - RAYUWAR ZAINAB Complete Book 1234 By Zainab Kabir Jaen.txt

15 Nov 2025

1226

gab ake da rasa ransa a dena barinshi shi kad'ai saboda babu bu'katar ya dinga tinani" Kamal ne yace "insha Allah likita zamuyi iya bakin 'ko'kari muga mun kiyaye"likitan yace " yasamu barci yanzu zuwa anjima zai farka saika Shiga ka ganshi" Kamal yace "to likita na gode sosai".



A daya 'bangaren Amarya sai shirye-shirye suke yi ita da su Basma ta sanar dasu Fatima da Hamida suma sun zo gidan su na Adamawan,kwana biyu jin ta take ba tajin dad'i kwata-kwata sai taji ranta yana 'baci ga yawan fad'uwa da gabanta keyi tana ta dai yin addu'a,Basma ce ta shigo tace "Anty ga Yaya Aboki yazo"kallon ta tayi tace "da gaske kike koda wasa?" Basma ce tace "wallahi Anty da gaske yana falon ba'ki" tace "bai fad'amin zai zo ba wallahi gani nan ya kyauta" a gurguje ta shirya duk da dama a shirye take amma saida aka 'kara gyarawa,da sallama ta shiga d'akin ba'kin a zaune ta tarda shi yana danna Waya yana ganin ta ya saki murmushi yace "my shine kika barni inata jiranki ko" cikin shagwa'ba tace"to Hubby ba kaine baka fad'a min zaka zo ba" yace "sorry matar wallahi jinayi kawai ina son ganin matata shiyasa na taho" tace "humm hubby kamar kasan nima nayi kewarka" yace "da gaske? "Tace eh hubby" yace "yauwa tawan mene tsare-tsaren da zakuyi a bikin kinga fa yanzu saura sati uku,ni dai tsare-tsarena shine Abokina Musaddik ya had'a mana dinner,nima kuma akwai dinner da zanyi sannan ga party za'a yi Indian day ma amma shi sai an d'aura aure da daddare sannan Momma ma ta had'a nata partyn" zaro ido tayi tace"wai hubby kana nufin duk wanna partyn da za'ayi nima in yi wani ai sun isa mu dai anan walima zamu yi sai kuma kamu shikenan Wanda ka lissafa ai sun isa" murmushi yayi yace "shikenan matar jibi za'a kawo lefe fa" tace "to hubby" sun sha soyyayar su sannan ya tafi,ita kuma ta cigaba da shirye-shiryen ta mai gyaran jiki Mommy ta d'auko Basma tace "itama sai an mata" dan haka tare ake yi musu ta janza sosai dama kuma ga shi tana amfani da malato soup din Anty lady da body scrub gaba d'aya ta canja sosai kamar ba ita ba, an kawo lefe na gani na fad'a a kwatuna set uku ne sannan ga fridge lefen dai sai dai hassada amma sunyi kyau.



A 'bangaren Hamma kuma tunda aka Sallamo shi daga asibiti yana tare da Kamal Sam Kamal baya barin shi da damuwa ya dan rage damuwa yanzu jikin nashi Alhamdulillah har sun koma aiki shida Kamal duk labarin bikin ana fad'a masa da bikin ya rage. Sati d'aya ya tafi shida Kamal,kwanan sa biyu da zuwa amma ko sau d'aya bai hadu da ita ba ranar dinner cewa yayi "shi fa baza shiba" Kamal ba yanda bai yi dashi ba ya'ki zuwa,Mommy ce takira shi tace "Son na fahimci kana cikin damuwa ka dubi yanda ka rame" murmushi yayi yace "Mom na d'an yi rashin lafiya ne shiyasa kikaga na rame amma bayan haka ba abinda ke damuna" tasan 'karya yayi mata amma sai ta 'kyaleshi saboda ba taso ta matsa mishi, ranar partyn da Ammi ta had'a ne yaje sanda yaga Zainab da Ancul Aboki ji yayi wani abu ya tokare masa 'kirji numfashin sa yana neman d'auke wa da 'kyar ya lalla'ba ya bar gurin Kamal sai gani yayi bayanan da haka gida yadawo ya tar dashi a kwance ya dafe saitin zuciyar shi Kamal yace "wato Captain ka za'bi ka kashe kanka to kasani wallahi ka mutu a wannan halin daidai kake da wanda ya kashe kansa tunda nayi-nayi ka bari a sanar da Iyayenku a halin da kake ciki ka'ki bazan tsaya in zuba ido ina kallo ka mutu ba"kallon shi yayi yace " please ka mi'ko min maganina" tashi yayi ya d'auko mai ya d'ago shi ya bashi sannan bacci ya d'auke shi, zuba masa ido Kamal yayi tausayin Abokin nashi duk ya cika shi yarasa ta yanda zai 'bullowa lamarin.





Ana gobe d'aurin aure 'Yan uwan na nesa dana kusa duk sun zo ana ta shagali da daddare kowa shirin tafiya dinner yake yi shi kuwa Hamma Al'ameen yana kwance ciwon shi yana neman tashi domin ya sadda'kar daya rasa Zainab d'insa da suka had'u da shi daga tace"Hamma ina wuni"ko jiran ya masa ma ba tayi ba tayi gaba,Kamal ne ya shigo yace "Abokina ka tashi mu fita tunda bazamu partyn yau ba" shiru yaji ya kuma magana yaji shiru 'karasa yayi yace "wai kana nufin har kayi bacci?" Amma me yana ta"bashi yaga yayi lagab alamun ba numfashi a jikin shi wani ihu yasa Wanda ya karad'e gidan da gudu kowa ya 'karaso part d'in Kamal ne yake jijjigashi yana fad'in "Abokina in da wasa kake ka tashi bazaka mutu ta sanadiyyar soyayya ba katashi! " da gudu Ammi da Mommy suka rufu a kanshi suna kuka Zainab ce 'karshen shigowa tana shigowa taji Ammi tana cewa "Yarona ya za'a yi ka mutu ka barmu dan Allah ka tashi" ai tana jin haka ta yanke jiki ta fad'i a gurin sumammiya.


Tur'kashi ya zata kaga

Kuyi ha'kuri da wannan



Wannan kenan........✍️✍️


#ZAINAB KABIR JA'EN

{GARKUWAR ROYAL STAR🌟}
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹



STORY&WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN


🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c




Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.



Al'kalaminmu 'yancin mu.



🅿️...................2️⃣8️⃣.




____________________K'arar fad'uwar Mutum da akaji shiya tabbatar da zuwanta, gaba d'aya aka d'auke su akayi hospital dasu,kowa a gidan kuka yake yi dan ganinsu shi ke nan su Hamma sun mutu, likitoci sunyi iya 'kokarinsu domin su dawo da numfashin Hamma amma abin ya gagara sun dai tabbatar da yana raye, ita kuma awarta d'aya ta farfad'o kuka takeyi sosai tana fad'in "dan Allah Hamma karka mutu ka barni wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba!" da 'kyar aka lallasheta,Ancul Aboki ma yazo gurin tun sanda aka sanar dashi abinda ke faruwa, Kamal ne ya sanar dasu irin halin da Captain yake ciki tun farkon rashin lafiyarshi har yanzu kowa tausayin shi ya cika zuciyar shi Mommy ce ta rarrafa gaban Ancul Aboki tari'ke 'karfarshi tana fad'in "dan Allah ka taimaki Yarona ka ceto rayuwarshi na rok'eka, shi kad'ai muka mallaka a duniya dan Allah" ta k'arasa tare da fashewa da wani ma tsanancin kuka mai ban tausayi, numfashi Uncle Aboki ya sauk'e tare da fad'in "Mommy kiyi ha'kuri ki dena kuka indai nine na barma Captain matarshi,sa bo da na fahimci cewa suna 'kaunar junansu" ya share hawayen daya gangaro masa a idonsa dan shi Allah ya gani yana son Zainab, kowa hamdala yayi a gurin Abbu ne yayi magana tare da fad'in "Yarona ba' abinda zamu ce maka sai Allah yasaka da alkhairi kuma ina ro'kon alfarma ka akan zanyi hukunci a kanka kamar d'an dana haifa zan had'a auren ka da Basma 'kanwar Zainab,Ancul Aboki ya rasa me zaice ma wannan mutane masu karamci kawai saiya zube a gaban Abbu ya ce "Abbu nagode da karamcinku a gareni Allah yasa haka shi ne yafi. "alkhairi"ameen kowa ya amsa a gurin.

Gurin Likita Abbu da Abbie suka tafi domin tattauna yanda za'ai nan likitan ya ce "Alhaji ni a ganina a fitar dashi 'kasar America ko a can Allah zaisa a dace" Abbie ne ya ce "yanda kace Likita sai a shirya fita dashi d'in" ya ce "toh Alhaji insha Allah."




Rana bata 'karya sai dai Uwar d'iya taji kunya, a ranar 9/2/1999 aka d'aura auren Captain Al'ameen Hassan da Amaryar Zainab Hussain akan sadaki dubu d'ari wanda Abbie ne ya wakilice shi, sanan aka d'aura auren Abubakar Abdullahi(Ancul Aboki) da zan kad'e d'iyar Amaryar sa Basma Hussain wadda ita sai a yau tasan da batun auren taci kuka amma ba yanda zatayi dole ta ha'kura tayima iyayenta biyyaya shagalin biki kuma an bari sai Hamma ya samu Lafiya.


Washe garin d'aurin auren jirginsu ya d'aga zuwa America ita da Hamma kai tsaye a babban asibitin garin suka sauka ita take kula dashi da duk abinda yake bu'kata kafin ayimai aiki in andace shi ke nan, kullum suna waya da K'anwarta Basma tana 'kara kwantar mata da hankali suna waya dasu Ammi ma da su Abbie kowa fatan samun nasara yake musu.



Yau ce ranar da takama za'a yima Hamma aiki duk familyn nan sun hallara a America kowa fatan samu nasara yake yi ranar da azumi Zainab ta tashi sai addu'a ake tayi masa sunsa a Nigeria anata yi mai sauka da addu'aoi a masallatai sai dai fatan samun nasara.






Wannan kenan..........✍️✍️




Kuyi ha'kuri da wannan.



#ZAINAB KABIR JA'EN

{GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹



STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN



🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c




Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.


*Al'kalaminmu 'yancin mu.*




🅿️..................2️⃣9️⃣.




__________________To cikin ikon Allah an yi mai aiki cikin nasara Likitoci sun tabbatar da cewa yana tashi zai tashi cikin 'koshin lafiya,amma zai samu sati d'aya kafin ya farfad'o, nan aka ci gaba da bashi kulawa ta musamman tana zaune a gefansa hawaye take ta sharewa a ranta tana tunanin lallai duniya ba'a bakin komai take ba, kalli Hamma a kwance kamar matacce "Allah ina ro'konka kabawa Hamma lafiya" hannunsa ne taga yana motsi da sauri ta 'karasa ganshi lokacin su Abbie duk basa nan suna hotel d'in da suka sauk'a a hankali yake bud'e ido duk da sun masa nauyi, haske ne yayi masa yawa dan haka ya kara maida su ya rufe da gudu ta fita ta kira Likita a tare suka shigo a hankali ya kuma bud'e idon nasa a kanta ya sauk'e su tarame tayi duhu kamar ba'ita nan abinda ya faru yafara dawo mai aka ana i gobe d'aurin auren ta ya sameta yake cemata "ta temake shi tace bata son auren nan wallahi in ba ita bazai iya rayuwa ba" nan ta bud'i Baki tace ni wallahi Hamma in fad'a maka kwata-kwata babu sonka a raina soyyayar dana kemaka ta Yaya da K'anwa ne dan haka kaga babu batun soyyaya"yace "shikenan na gode" 'kwa'kwalwarsa ce take zai yana masa hakan dan haka ya juyar da kansa daga barin kallon ta dan zuwa yanzu yasan tazama mallakin wani shin mema take yi a gurinsa wani haushinta yaji yana ji ko ganinta baya son yi,da sauri da 'karaso gurin nasa tace "Hamma ka tashi alhamdulillah Allah na gode maka" kallon ta yayi sannan ya saukar da idonsa 'kasa a hankali cikin sanyin murya tace "dan Allah Hamma kamin magana kaji" cikin muryarsa dabata fita yace "me kikeyi anan gurin ina mijinki?" "Bawani bane mijinta face kai" Ammi ce take fad'a lokacin da suke shigowa, ha'ki'ka badan Ammi ce yaji tana fad'a ba bazai ta'ba yarda ba hakan yana nufin Zainab matarshi shi aka aurawa "garin yaya hakan ya faru?" Yun'kurin tashi yake yi Kamal ya 'karasa ya d'agoshi yana fad'in "to mijin Zainab 'karshe dai kayi likimo an aura maka ita sai kawarke ai" dariya kowa yasa a d'akin nan aka fara yimasa ya jiki yana amsawa "da sau'ki" to satin sa d'aya ya warware sosai saidai abinda ba'a rasa ba,a 'bangaren Zainab kuwa ta fahimci Hamma share ta kawai yake yi in yana shira yana dariya daya ganta sai ya had'e rai abin yana damunta sosai amma sai ta bayar da ko fushi yake da ita.


Yauce ranar da'aka sallamesu dan haka gaba d'aya jirginsu ya d'aga zuwa Nigeria kwannan su biyu da dawowa kowa ya warware gajiya Abbu ya yata rasu harda Ancul Aboki da Kamal dan yanzu Kamal tazama d'aya daga cikin wannan familyn suna ganin bazasu iya 'boye masa duk wani abu daya shafesu ba, bayan an bud'e taro da addu'a sannan Abbu yafara jawabai kamar haka "to abinda ya tara mu anan shine magana ce akan batun auren ku da yanda abubuwa suka faru da farko dai wannan Yaro Abubakar babu abinda zamu cemaka sai Allah yasaka maka da alkhairi ya kuma had'a kanku kaida matar ka domin kayi abinda ba kowa ne zai iya ba kayi ceton rai Allah yasaka maka da alkhairi" "Ameen" kowa ya amsa a gurin sannan Abbu ya cigaba "to bisa yanda abubuwa suka faru mun tsaida satin sama kowa zai tare da matar sa ke kuma Basma yanda muka sanki mai biyyaya karkiga had'a auren ki a kayi kice zaki wulakanta mijinki kimasa biyyaya" tace "insha Allah Abbu zan kasance mai biyyaya a gareku" yace "to Allah yai muku albarka ya baku zuri'a d'ayyiba" aka amsa da amin bayan an watse kowa ya kama gabansa Hamma ya samu Ancul Aboki yayi masa godiya bisa karamcinsa a gareshi sannan yayi mishi fatan alkhairi a auren shi sannan ya tafi.


To tundaga ranar Zainab bata 'kara ganin Hamma ba saida ta tambayi Basma take shaida mata ai yakoma Kano sai ana saura kwana biyu tariyar su zai dawo hawaye ta share sannan tace "sis bakya ganin yanzu Hamma ya dena sona" dafata Basma tayi sannan tace "haba Anty ai ke zaki bada labarin son da Hamma yake miki kawai dai inaga ko fushi yake ta abin da kikayimasa a baya amma wallahi Hamma bazai iya dena sonki ba" sai a lokacin taji zuciyar ta samu sau'ki amma tasan yanda zata 'bullo masa.



Wannan kenan.......✍️✍️



Kuyi ha'kuri da wannan.



#ZAINAB KABIR JA'EN

{GARKUWAR ROYAL STAR🌟}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: Rawa d girgiza💃💃💃 zanyi gabanki in daddara😁😁 kai naji dadin feginan wlh sosai hamma ashe dai kaine mijinta har abada sai dai muce Allah y bada xaman lpy mai daurewa. Allah y kara basira d karfin ido👀
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹


STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN


🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/?ref_c


Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.


Al'kalaminmu 'yancin mu.



🅿️............3️⃣0️⃣.




___________________To yau tun safe aka hada-hada a gidan sa bo da yau ne ranar da za'ayi walima, Amare su tare a gidajensu, su Hamida da Fatima duk sun zo, haka itama Basma ta gayyato 'kawayenta domin yanzu sun sasanta kansu ita da mijinta, kowa a gidan murna yake Basma ce ta kira Zainab take cewa "Anty Zainab Hamma fa yazo tun jiya kun had'u?" Murmushi tayi wanda yafi kama da ya'ke ta ce "a-a nasan dai yazo amma bamu had'u ba, ki rabu dashi fushi yake yi kuma zai sakko ne" murmushi Basma tayi sannan ta ce "haka ne kam Anty, Ancul Aboki ya ce " yana gaisheki" mantawa nai ban fad'a miki ba" duka ta kai mata ta ce "wato Ancul Aboki ko ba Mijina ko Hubbyna" dariya tayi ta ce "kai Antyna" murmushi tayi ta ce "ai gaskiya ce Yarin ya ta girma" duk dariya suka sa a dai-dai lokacin Hamma yazo wucewa domin zashi ya gaida Ammi had'a baki sukai suna fad'in " Hamma ina kwana" murmushi yayi ya ce "lafiya kalau Basma kintashi lafiya?" ta ce "lafiya kalau Hamma ance min jiya kazo zamu mu gaida ka kuma a kace ka fita kaida Yaya Kamal" ya ce "haka ne K'anwata mun je duba wani companyn su Abbie ne anan" ta ce "to Hamma Allah ya temaka a gaidamin da Yaya Kamal kafin mu had'u" ya ce "to zaiji" sannan ya wuce idon Zainab ya cika da k'walla wato yanaji tana gaishe shi amma ya shareta shi ke nan, Basma ce ta dafata ta ce "kiyi ha'kuri Antyna nasan be kyauta ba amma ki rabu dashi kisan yanda zakiyi ki shawo kan mijinki kar kice kema zaki d'au zafi kinji" ta ce "to K'anwata na gode" murmushi tayi ta ce " ba komai Anty bari in k'ara inje in d'auko mana kayan mu a part d'in Mommy mu mai dashi part d'in mu tun kan mutane su cika" ta ce "to K'anwata" Basma ta zame mata wani 'bangaren na rayuwar ta ta wuce iya K'anwa agareta ta zama K'awa kuma 'Yar Uwa, part d'in su ta wuce tana har had'a musu kayan su.



To da misalin karfe biyar na yamma harabar gida na gani a cike da mutane kowa ka ganshi farin ciki yake yi waige-waige nakeyi inga ta inda zan hango Angwaye da Amare amma ban gansu ba har na k'osa da zanyi tafiya ta kamar ance in kalli gefena nan na hangi Amaren suna tahowa ana ta watsa musu furanni haba ai saida na kusa sumewa sa bo da yanda naga sun had'u shigar indiyawa sukai Amaren cikin ja da adon milk sari Angwayen kuma cikin jar Riga da milk colour d'in wado zo kuga kyau idan akace muku ba indiyawa ne agurin ba bazaku ta'ba yarda ba, wajan zaman da aka tanadarwa Amaren da Angwayen nan suka nufa suka zauna har lokacin ba'a dena zuba musu furen ba, bayan sun zauna Malaman da aka gayyato domin suyi lecture suka fara can na hango tawagar Zainab fans da Hamma suma sun iso k'ar kashin jagorancu Ummu Rae'es da takwarorin Zee nan na basu gurin zama na gabatar musu da abinci suka zauna suka fara kwasa guri yayi guri domin 'Yan Uwa na kusa dana nesa duk sunzo Ancul Aboki ma 'Yan uwan shi duk sunzo wa'azi ake me ratsa jiki kowa a gurin jikinsa yayi sanyi su Basma kam harda kuka.


Bayan an gama aka gabatar da abubuwan ta bawa kowa yai yayi hani an sannan a aka watse Abbu ne yakirasu tayi musu nasiha sannan kowa Mijinta ya d'auke ta a mota ya tafi da ita sai dai muce Allah ya basu zaman Lafiya.



Wannan kenan........✍️✍️




Kuyi ha'kuri da wannan.


#ZAINAB KABIR JA'EN

{GARKUWAR ROYAL STAR🌟}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹


STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN


🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟. http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-101607075594165/ref_c




Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.



Al'kalaminmu 'yancin mu.




🅿️............3️⃣1️⃣.



_________________Tunda suka tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login