Showing 21001 words to 21911 words out of 21911 words
Chapter 8 - RAYUWAR ZAINAB Complete Book 1234 By Zainab Kabir Jaen.txt
ba wanda ya kula kowa, kuka take ta rerawa dan a gaskiya ta sha'ku da su Ammi a haka suka isa gidan, ga ba d'aya gidan ya canza mata anyi masa gyara sosai gidan suka shiga kowa 'bangarensa ya nufa mamaki ne ya cikata ganin komai na d'akin sabo ne akwatuna tagani saiti-saiti, wajan set haud'u sunyi kyau sosai a ranta ta ce "kenan Hamma yayi min lefe?" Murmushi tayi sannan ta shiga wanka ta shirya cikin kayan bacci masu kyau tabi lafiyar gado tai kwanciyar ta.
Washe gari ta tashi ta gabatar da ayyu kanta sannan tayi wanka tai simple make up d'in ta falo ta fito a zaune ta tar dashi yana danna computer 'karasawa tayi ta ce "ina kwana Hamma" kallon ta yayi tayi masa kyau amma cikin had'e rai ya ce "lafiya" ya cigaba da abinda yake abin ya k'ona mata rai amma sai ta dake ta ce "Hamma ga break fast d'inka fa tun d'azu na gama" k'ara b'ata rai yayi yace "ni fa na k'oshi tun d'azu nayi break fast d'ina" kallon sa tayi na wani lokaci sannan ta ce "shikenan" ranta yayi bala'in 'baci ita bata san me tayi masa ba yake mata wannan wulak'ancin amma ba komai zata jure bar ya sakko, tashi tayi ta koma part d'inta break fast d'in da ba tayi ba kenan.
To yau kusan watansu d'aya a haka bayacin abincinta kuma baya kulata gaisuwa ce kawai take had'a su, Basma ta kira ta fad'a mata halin da take ciki tana kuka tace "Basma na gaji da wula'kancin da Hamma yake min wallahi Basma yanzu baya sona kwata-kwata, nagaji-nagaji Basma!" ta k'arasa cikin kuka da k'yar Basma ta rarrasheta ta dena kuka ta ce "ni wallahi Anty laifinki nake gani a ce har yanzu kin kasa shawo kan Mijinki ni wallahi yanzu nida Mijina zaman mu muke lafiya in akace miki ba auren soyyaya mukai ba bazaki yarda ba duk abinda nake so shi yake min yasiyamin fa sabuwar mota inna fara fita zanzo gidan lki sai na nuna miki dan Allah Anty kiyi iya bakin k'ok'arinki nasan ki" ta 'karashe da zolaya, murmushi Zainab tayi ta ce "kai wannan Yarinya bakida kunya wato Mijina ko ke mai miji" dariya sukayi gaba d'aya sannan sukai sallama ha'kik'a tayi d'amarar shawo kan Mijinta ta kowace hanya tashi tayi ta nufi falo a zaune ta hango shi a kan kujera yana waya da alama daga wajan aikin sa yake kiran, bata lura ba kawai taji tayi sufa da 'bawon ayaba nan kuwa ta fad'i a k'asa war was k'arar data k'walla ita ta juyo da hankalinsa kansa bai san ya akayi ba kawai ya gansa a gabanta gaba d'aya narkewa mai tayi sai kuka take yana bata ha'kuri, hijabi ya d'akomata yayi hospital da ita tundaga ranar yake kula da'ita sosai duk ta narke masa ta 'kara tabbatar da son da Hamma yake mata domin yanzu baya barinta tayi kowane irin aiki, harta warke yanzu zamansu suke lafiya duk fushinnan Hamma ya dena ya rungumi matarsa suna zaman zu lafiya cike da so da 'kaunar juna.
Bayan shekara ashirin
Wata ham shak'iyar mata na gani a zaune daka ka ganta kasan hutu da jin dad'i ya ratsata, wata Yarinya naga tafito wadda bazata wuce shekaru sha bakwai a duniya ba ta nufo matar tana kuka ta ce "Momma kinga YQya Ashman ya k'wacemin waya ko" Ashman dake fitowa ya ce "wallahi Mommah Yarinyar nan tunda aka bata waya yanzu bata karatun arzi'ki shiyasa na 'kwace" sai a lokacin na k'arewa matar kallo bakowa bace face Zainab yanzu ta zama wata Hajiya gata tayi kyau in ka kalleta baza kace ta haifi su Ashman ba kallon shi tayi ta ce "haba Yaya babba kayi ha'kuri ka maida mata wayar ta in naga bata karatu da kaina zan kwace kaji Babana" cewa yayi "to Momma ta" ya mi'ka mata wayar bayan ya tafi Zainab tayi wa d'iyar tata fad'a sosai akan karatu sannan ta ce "taje ta kira mata papi a lambu" ta ce "to Momma" yaran Zainab had'u, Ashman ne babba wanda yaci sunan Abbu sai Aisha wadda taci sunan nanne ana kiranta da Ashna, sai 'yan biyun ta Hasana da Usaina sukuma ana kiransu da Ammi k'arama da Mommy k'arama yaran sun tashi cikin kulawa sosai BQba kande tana zaune a tare dasu Anty Asabe tayi aure yanzu Yaranta biyar hakama Fatima ita ta auri Kamal Abokin Hamma Hamida kuma d'an Uwansu ta aura ko wacce tana da yara biyu, Basma ma Yaranta hud'u tana zaune da mijinta Lafiya yanzu wannan family suna zaune cikin farin ciki da annashuwa sun mance duk wata damuwa Hamma ne ya shigo ya tadda ta a zaune ya zo ya zauna a kusa da ita ya ce "Amarya ta" dariya tayi ta ce "kai Hubby ka ganni tsofai-tsofai dani kace min Amarya har na kusa jikoki" dariya yayi ya ce " 'Yan matana ai bakya tsufa har yanzu ganin ki nake kamar Yarinya" dariya suka sa dukkan su cikin farin ciki da nishad'i
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
A yau na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai suna rayuwar Zainab ina fatan abinda muka fad'a dai-dai Allah ya bamu ikon amfani dashi abinda muka yi kuskure Allah ka gafarta mana ina godiya a gareku masoyana Allah ya bar zumunci.
Mu had'u a sabon littafina mai suna ❤🩹RASHIN MAHAIFIYA❤🩹
Na gode
#ZAINAB KABIR JA'EN
{@GARKUWAR ROYAL STAR}.