Showing 12001 words to 15000 words out of 21911 words

Chapter 5 - RAYUWAR ZAINAB Complete Book 1234 By Zainab Kabir Jaen.txt

15 Nov 2025

1228

nan tace shegiya gwara da kikazo 'Yar uwarki sa ce ta nayi na yar ke kuma kashe ki zanyi shegu a halin tsiya, d'agowar da za tayi taga Alhaji Hussain a tsaye yana kallonta idon sa yayi jawur cikin rauni yace" Falmata me nayi miki? me Usaina tayi miki? kika raba mu da farincikin mu!nan ya zube a kan gwiwoyinsa yana kuka mai cin rai, hankalinta yayi matu'kar tashi ta rasa mai zata yi kuka tasa tana fad'in Alhaji kayi ha'kuri ka rufamin asiri, "wani irin duka ya kaimata sai da yayi mata jina-jina sannan yasa 'yan sanda suka kamata yau kimanin shekara ashirin amma har yanzu tana kurkuku.


Hajiya Usaina da taji labarin ba 'karamin kuka tayi ba ta yiwa Falmata Allah ya isa yafi a 'kirga.


Bayan Basma ta haifi yara uku Yasmeen, Intisar,da Hanan, amma har yanzu suna kulafacin 'Yarsu su suna fatan Allah ya bayyana ta.


Mommy kuma tunda ga kan Al'ameen bata 'kara haihuwa ba dan haka duk wata soyayya suka tattara ta a Kansa.


CIGABAN LABARI.....




Wannan kenan........✍️✍️




Kuyi ha'kuri da wannan.



Ina godiya agareku masoyana Allah yabar zumunci.


Ina yiwa duk wani d'an 'kungiyar Royal star fatan alkhairi Allah yabar zumunci.


Ina godiya agareku rayuwar zainab fans.


Allah ya'kara d'aukaka kungiyar mu mai Albarka.



#ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: tofah kardai daga haihuwar ya aga Babu kamar wata allura 🤔🤔🤔🤔🤔



kaiii gaskiya dasa hannu barina Kira Yan kato da gora 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️


gaskiya hajiya falmata kiguji karshenki takan San duniya kiraba ya da mahaifiyar ta wannan kayan xunubin har ina😥😥😥


karshenta kenan dama gidan kurkukun anyi mummunan karshe dman karshen masu Hali irin nata kenan masu San duniya
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: tofah kardai daga haihuwar ya aga Babu kamar wata allura 🤔🤔🤔🤔🤔



kaiii gaskiya dasa hannu barina Kira Yan kato da gora 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️


gaskiya hajiya falmata kiguji karshenki takan San duniya kiraba ya da mahaifiyar ta wannan kayan xunubin har ina😥😥😥


karshenta kenan dama gidan kurkukun anyi mummunan karshe dman karshen masu Hali irin nata kenan masu San duniya
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹




STORY&WRITING


BY:ZAINAB KABIR JA'EN



🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 {R.S.W.A} http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref_c



Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa.
(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.


Al'kalaminmu 'yancin mu.


FREE BOOK📖📚.



🅿️...............2️⃣0️⃣



Tun daga ranar basu ƙara had'uwa da Hamma ba, yau da wuri ya dawo a falo ya same ta tana kallon Indian fim, murmushi yayi yace"sannu da hutawa" ita ma murmushi tayi tace "yauwa sannu Hamma ka dawo lafiya?" yace"lafiya ƙalau ƙanwata bari inje in watsa ruwa kema ki shirya za muje gidan su Kamal" da murnar ta tace"to Hamma" d'akinta ta shiga ta shirya cikin wata blue black d'in shadda ta yafa mata milk colour d'in mayafi, tayi kyau sosai kamar ka sace abinka da farar fata.


Da ta fito Hamma tagani yana shirin fitowa kallon-kallo suka fara yiwa junansu domin kuwa shima shaddar daya sa kalar ta tace sak kamar sun had'a baki, murmushi suka sakar ma junansu sannan Hamma yace"shine kika sa irin kayana ko?" murmushi tayi ta shagwa'be fuska tace"kai Hamma ko kuma kai kasa irin kayana ba" dariya yayi yace"to naji mutafi yamma tanayi" nan suka jera suka nufi mota haba wa duk inda kake neman da cewa kaga wannan ma'aurata kasan sun kai dan sunyi bala'in da cewa,a zuciyata nace Allah Ubangiji ya 'kara had'a kawunansu, yau ba da sojan daya tafi daga shi sai Zainab gidansu Kamal suka nufa kai tsaye bayan sun isa suka shiga Mommy suka tarar a zaune Nadiya tana yanke mata farce, da murna Nadiya ta tari Zainab tana mata oyoyo nan suka gaisa da Mommy da yaya Kamal, Nadiya ta janye ta sukai part d'inta Kamal ma suka tafi part d'insa shida Captain ,hira sosai Nadiya da Zainab suka yi nan danan suka saba, basu suka bar gidan ba sai bayan magariba da al'kawarin Nadiya zata ziyarci Zainab ita ma.


A gajiye suka dawo dan haka kowa ɓangaren shi ya nufa, basu 'kara had'uwa ba sai washe gari, nan yake sanar mata yana so zaije ya gaida su Ammi shi tace "nima hamma zan bika please" "yace to ba damuwa insha Allah zaki" "tace to Hamma na gode"

A 'DAYA BANGAREN

Abbie ne zaune yana karanta jarida kawai yaga NASA cigiyar wata Yarinya da hoton ta tana 'karama da kuma hoton ta na yanzu kawai sai ya tsinci kansa da karanta labarin Yarinya mi'kewa yayi yana fad'in"Ummina ce ita ce wallhi ita ce!" Ammi ya ƙira ya nuna mata nan take ta yanki jiki ta faɗi.


Yanzu muka fara

Shin su Abbie zasu samu damar had'uwa da d'iyar su kuwa?

Shin Zainab ce Yarinyar da suka ga labarinta a jaridar?.


Shin Hamma zai kar'bi Zainab a matsayin abokiyar rayuwar shi?.


Shin ina labarin Ancul Aboki?.


Shin in Zainab ta had'u da Iyayenta ya Hamma zaiji sanda yasa Ammin sa ce Mahaifiyarta?.


Wannan amsoshin suna tattare a cikin wannan littafi namu mai albarka.


Wannan kenan✍️✍️✍️

Kuyi ha'kuri da wannan.


Ina godiya agareku masoya rayuwar zainab.


#ZAINAB KABIR JA'EN {@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: toh fa su hamma wato anga xee taxama mutum andaina kyararta da hantararta dacin xalinta ko wato kaga tayi fresh Takoma mace harda wani kanne ido kk😏😏 toko xamu amsheka saimun wahalarda Kai kaji abinda mukaji 😡


garadai kafita da ita taga gari garima yaganta kotayi kasuwa tunda Kai kace dibarmata lokaci kayi kafin aga iyayen ta yakamata kabarta ta sakata ta wala taxama mace Mai yanci itama😍😍😍

Masha Allah xee xee wahala takusa Yanke Miki insha Allahu ubangiji yabaiyanar wa iyyayenki ke kema kiji dadin iyaye ahayye xanaxo Bari inshafa hoda warrrrrrrrr💃💃💃💃💃💃💃💃💃
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹




STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN



🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref_c


Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, da kuma nishad'antarwa. (R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.


Al'kalaminmu 'yancin mu.


FREE BOOK📖📚.



🅿️...................2️⃣1️⃣.



Kiran sunan ta yake cikin tashin hankali "Usaina ki tashi dan Allah", ruwa ya d'ebo ya yayyafa Mata nan taja wani dogon numfashi sannan ta bud'e idonta a hankali,da sauri ta tashi tana fad'in"ina 'Yata take tana ina,"number da akasa in anji labarin iyayenta a kira ita sukai ta kira amma switch off tashin hankali nan Abbie yace su shirya gobe za su tafi Nigeria,nan da nan kuwa suka shirya suka d'unguma sai garin Adamawa,Alhaji Hassan ma shi da Iyalin sa duk sun zo dan Alhaji Hussain ya kira shi ya fad'a mai yanda ake ciki,Hamma lokacin baya Nigeria ya d'anyi tafiya zuwa Germany domin duba wasu company d'inshi na can,dan haka bai san wainar da ake toyawa ba.



Yauce ranar da Hamma zai dawo dan haka tun safe ake gyare_gyaren gidan sun shirya Abinci kala-kala ita dasu Anty Asabe ko'ina na gidan tas dashi 'kamshine kawai ke tashi, part d'inta ta koma domin ta shirya don yanzu tasan sun kusa Ƙarasowa,cikin wata farar Abaya ta shirya wadda taji stones ta tifke gashin kanta da ribbon fari tayi rolling d'in Mayafin rigar,Tubarakallah zo kuga had'uwa tayi kyau ma tuka flat shoe tasa ta fito,Ƙarar durar motocin su da taji ya tabbatar mata da isowar su dan haka ta tafi falo ta tsaya tana jiran shigowar sa

Yana shigowa falon ya ganta a tsaye sai murmushi take ware hannuwan sa yayi alamun ta taho aikuwa da gudu ta taho ta rungume shi tana yi masa sannu da zuwa jakar hannunshi ta kar'ba ta ajiye mai sannan ya nufi part d'inshi ya watsa Ruwa sannan ya fito ta gabatar masa da abinci, sannan tasa aka kaima sojojin gidan nasu .


Wannan kenan.......✍️✍️


Kuyi hakuri da wannan banajin dad'ine ina kwance da 'kyar na lalla'ba nai muku wannan ina barar addu'ar Ku.


#ZAINAB KABIR JA'EN.
{@GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹



STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN



🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟{R.S.W.A} http://www Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref=py_c


Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fadakarwa,ilimantarwa, dakuma nishad'antarwa.(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin 'kishi.


Al'kalamin mu 'yancin mu.



FREE BOOk📖📚



🅿️......................1️⃣8️⃣

________________________
Waye captain Al'ameen?
________________________


Al'ameen Hassan d'a ne a gurin Alhaji Hassan , d'a guda d'aya da iyayenshi suka mallaka a duniya shi yasa duk wani gata suka bashi, Mahaifinshi d'an asalin garin Adamawa ne su biyu iyayen su suka Haifa shida 'kaninsa Alhaji Hussain tagwayene su,tun tasowar su komai tare suke yi sun shaku sosai, in d'aya ba shida lafiya to d'aya ma sai ya kamu, a haka har suka girma sunyi karatu mai zurfi inda suka karanci 'bangaren kasuwanci, iyayensu suka basu jari, a hankali kasuwancin su ya bun'kasa Alhaji Hussain ne yazo Kano yi musu sare-sare nan ya had'u da Falmata soyyaya ce ta kullu a tsakaninsu har sukai alkawarin aure,


Sanda ya sanar da iyayenshi cewa sukai ya bari Yayanshi ya nemo shima amma sai ya dage ba yanda suka iya haka suka yarda nan akai biki, da farko Falmata ta nuna baruwanta daga baya da ta had'u da 'kawaye yan duniya ta goge sai ta dawo tafi kafin kowa shekarar su biyar bata ta'ba haihuwa ba,gaba daya Alhaji Hussain damuwa tayi mai yawa na yanda Falmata ta koma bata ganin kowa da gashi, shi kanshi wataran tsoranta yake yi, a wannan halin Yayan shi ya tafi Turkey domin duba company su na can, a can ya had'u da Hassana 'Yar gidan wani hamsha 'kin mai kud'ice a haka suka 'kulla soyyaya mai 'karfi ba da dad'ewa ba a kai bikin su ya taho da ita Nigeria suna zaune lafiya da mijinta da danginsa kasan cewar ita maca ce mai hakuri,kowa yabonta yake ana haka ta samu ciki, zo ku ga murna a wajan Alhaji Hussain kamar matarshi akace tana da ciki kulawa take samu ta kowani 'bangare sai dai Sam basa shiri da Falmata sa bo da ita halinta bai mata ba.


Bayan cikin ta ya tsufah ta haifo san kacecen d'anta namiji, yaro ne kyakkyawa fari tas dashi da suna yazo yaron yaci suna Al'ameen wato sunan Kakanshi Mahaifinsu Alhaji Hussain duk wani gata na duniya yaron yana samu a gurin iyayenshi ta kowani bangare tun daga kanshi mommy bata 'kara haihuwa ba.


'Kanwar Mommy wato Ussaina ta tafi karatu shi yasa bata taba zuwa Nigeria ba saida Alhaji 'karami yayi shekara biyar a duniya sannan yazo gidan Yayarta ta dad'e a gidan sosai a wannan zaman da tayi suka fara soyyaya da Alhaji Hussain kowa yaji dad'in wannan lamari ,sanda Hajiya Falmata taji anyi bala'i na 'kin 'karawa ta wannan dalilin har saida Alhaji Hussain yayi mata saki d'aya ganin haka yasa ta saduda bawai dan ta hakura a zuciyarta ba ,anyi biki na kece raini a ka kai amarya d'akin ta tana zaune da mijinta lafiya, shekararta biyu ta samu ciki ganin wannan cikin ba 'karamin d'agawa Hajiya Falmata hankali yayi ba tayi al'kawari sai ta salwantar da cikin ta ko yaya dan haka tai ta 'kullawa da kwancewa nan ta yanke shawara in har aka haifi d'an ko 'Yar zata sa a yarda su taga ta tsiya tasan yanzu tana yin yun'kuri za'a kamata amma ta yake shawara yanzu jira kawai take Hussaina ta haihu ta ida aikinta.



Wannan kenan .....✍️✍️



Kuyi hakuri da wannan.



#ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹



STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN


🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟
http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/?ref_c

Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad`akarwa,ilimantarwa, da kuma nishad`antarwa.
(R.S.W.A)Ruwa kad`ai ke maganin `kishi.

Al`kalaminmu yancin mu.


FREE BOOK📖📚.




🅿️................2️⃣2️⃣



Bayan ya kammala cin abinci suka d'an ta'ba hira kafin daga bisani ya ce mata "zan tafi gidan su Kamal akwai maganar da zamu tattauna dashi. "murmushi tayi ta ce" kai Hamma ko hutawa ba kayi ba to ka gaidamin da Nadiya da Mommy, ya ce" to K'anwata insha Allah maganar ce mai mahimmaci kinji K'anwata amma ai bazan dad'e ba "murmushi tayi ta ce" to Hamma badamuwa adawo lafiya, "murmushi yayi ya ce"Allah yasa K'anwata. "kai tsaye gidan su Kamal ya nufa, yana zuwa yayi parking d'in motar shi a parking space na gidan, sananan ya shiga gidan nasu, "bakowa a falon dan haka ya samu d'aya daga kujerun falon ya zauna. number Kamal ya kira ya ce" ka k'araso part d'ina su Mom basa nan sun tafi biki, "ya ce ohk ganinan.




Yana k'arasa wa part d'in nashi ya ganshi a zaune yana aiki a laptop d'insa, "gefen gadon yasamu ya zauna sannan ya ce" Abokina aiki kakeyine?, idon Kamal yana kan aikin da yake ya ce "wallahi Abokina wasu file nake shigarwa nama kusa k'arasawa, "Captain ya ce" ohk badamuwa ka k'arasa sai muyi magana, rufe computer yayi ya ce" nagama ai, ya ce" dama na zo ne akan maganar iyayen Yarinyar nan Zainab har yanzu shiru fa akeji kana ganin anya kuwa zamu samu iyayenta nan kusa?, "numfashi Kamal ya sauke kafin ya ce" Abokina kar mu fidda rai da samun iyayen Zainab ni a jikina inajin cewa za'a ga iyayenta kasan shi abu irin wannan sai a hankali dole mu bi lamarin a sannu insha Allah zamu samu nasara, "shima numfashin ya sauke ya ce" Allah ya taimakemu burina inga iyayen Yarinyar nan in mika musu 'yarsu, "murmushi Kamal yayi ya ce" to ya maganar aurenka dake kanta?, "hararar shi yayi ya ce" bansani ba d'an raini wayo.



Fitowa suka yi suka tarar Mom harta dawo ita da Nadiya da murnar ta ta ce "lah Yaya Al'ameen Kaine a gidan namu ina wuni?, "murmushi yayi ya ce " lafiya k'alau k'anwata ya karatu?, ta ce" karatu alhamdulillah ina Anty Zainab?, "ya ce "Wallahi tana gida ta ce" tana gaisheki. ta ce" ina amsawa ka gaidamin da ita nima, ya ce" insha Allah sannan ta zauna suka gaisa da Mom kafin ya nufi gida.




Wannan kenan...............




Kuyi hakuri da wannan kunsan yanayi na rashin lafiya kawai dan kar ink'i yi muku typing ne amma banda lafiya.



#ZAINAB KABIR JA'EN
{@GARKUWAR ROYAL STAR}
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹



STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN


🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/ref_c



Marubuta masu aiki da fasaha da zallar ma'ana, fad'akarwa,ilimantarwa, da kuma nishad'antarwa.
(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi.



Al'kalaminmu 'yancin mu.



FREE BOOK📖📚.



🅿️...................2️⃣3️⃣.




………Bashi ya iso gida ba sai wajajan sallar isha'i, sanda ya shigo harta tafi part d'inta ta kwanta dan haka bata san sanda ya dawo ba.


Washe gari da asuba ta tashi tai ayyukanta ta tafi part d'insa ta gyara masa, a kwace ta tarda shi yana kwance amma idonsa biyu murmushi tayi sannan ta ce "barka da safiya Hamma har yanzu baka fita ba dama?" Tashi yayi zaune sannan ya ce "wallahi kuwa K'anwata ban tashi ba kin tashi lafiya?" "Lafiya Alhamdulillah Hammana" ya ce "toh masha Allah bari inje in watsa ruwa yau bana jin dad'i ne sosai kuma su Ammi sun zo Nigeria harda Mommy ma suna gidan Granny" ji tayi gabanta yayi wata mummunar fad'uwa, amma sai ta dake ta ce"da gaske Hamma kace mun fasa zuwa can d'in?" yace"eh K'anwata sai dai muje Adamawan amma ni gobe zanje in yaso ke ma tafi daga baya" ta ce "toh Hamma bari in had'a maka kayan" ya ce "toh" sannan ya shiga wanka ita kuma tana shirya masa kayansa a akwatinsa ta tafiya



Wayarsa ce take ta ringing dan haka da sauri ya fito ya d'aga oganshi ne daga gurin aiki dan haka cikin girmamawa ya d'aga ya ce"barka da wannan lokaci Ranka ya dad'e" a d'aya 'bangaren Ogan nasu yace "barka dai Captain Al'ameen,sannan ya cigaba da cewa dama nakiraka ne in sanar da kai akwai wani aiki daya tashi na ujila kuma kai akasa a kan tafiyar tafiyar one week ce kayi ha'kuri nasan ko gama hutawa bakai ba kasan aikin namu akwai wahalar" cikin muryarsa mai tsananin kwarjini ya ce "ba damuwa Oga insha Allah yanzu zan taho"sannan ya katse kiran kallon shi tayi ta ce " Hamma yanzu ka fasa zuwa gaida su Ammin?" zuwa yayi ya tsugunna a gabanta yace" 'kanwata aiki ne ya tashi na gaggawa tunda kika ga Oga ya sani a aikin to aikine me mahimmanci ya zanyi dole in ha'kura inya so inna dawo sai mu tafi tare koh?" Murmushi tayi duk ranta ba dad'i tace "toh Hamma"


A gaggauce ya shirya sai da tayi mai rakiya har bakin motar shi sannan ta koma gida, kai tsaye wajan su Anty Asabe ta wuce sukayi aikin su kamar yanda suka saba sannan suka samu ke'bewa da Anty Asabe, bayan sun zauna ta ce"Anty Asabe dama kayan nan na wajan Anty Lady nake so da mayuka da sabulai da kuma su dilka da turarrauka nawa duk sun 'kare" murmushi Anty Asabe tayi ta ce"ai kayan ne suna da kyau sosai baki da damuwa zan mata magana sai a aiko miki dashi har gida" "yauwa Anty Asabe shi yasa nake sonki" sun dad'e suna shira sannan ta kira Fatima da Hamida sun sha hira sannan ta tafi part d'in ta ta kwanta.


Kwanci tashi ba wuya
Yau takama satin Hamma d'aya da tafiya yaune ya kama ranar da zai dawo dan haka suka yi mai kayan tarba kamar yanda suka saba,kamar yanda yayi tsammani haka kwa ya tarar ita tafara tar bar shi.


Washe garin daya dawo kuwa suka d'aga Adamawa shida ita...

To fahhhhhhh




Wannan kenan.......✍️✍️



Kuyi ha'kuri da wannan....



#ZAINAB KABIR JA'EN {GARKUWAR ROYAL STAR🌟}.
11/16/22, 9:43 AM - GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟: ❤‍🩹RAYUWAR ZAINAB❤‍🩹



STORY & WRITING

BY:ZAINAB KABIR JA'EN

🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟 http://www.Facebook.com/Royal-star-writers-Association-10160707075594165/ref_c



Marubuta masu aiki da fasaha da zallar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login