Showing 27001 words to 30000 words out of 163788 words

Chapter 10 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

amsa, yace kinga bashi nazo yi ba yanzu dai fadamun dan'uwana yana ciki...?


wani dariyar tayi me cike da reni wayo tace bansa niba kai kaji, wai dan'uwashi koma meye hadin kifi da kaska Oho! kaga mlm idan zaka jeka nemi dan'uwa kaje ka neme shi can, amma banan ba domin dai mijina ba dan'uwan ka bane ehee!,


yace Allah ko...? tace kwarai yace haka ne saidai kuma dadin abun koda akaga zabuwa dazanta akagan ta, ma'ana koda kika ganmu tareki ka gan'mu don haka kuma baki'isa Kira bamu ba kinji,


cikin masifa tace ban dai ga dama ba wlhy, yace aitunda baki ganta tun farko ba toh" ko yanzu bazaki taba ganin taba har'abada, dai-dai lokacin da *Habeeb* yabudo labule sanye yake da jallabiyya fara kallo daya zakai masa ka fahimci daga bacci yatashi, da'alama hayaniyar su ce ta ta dashi sannan ga duk kam alama ransa bace yake,


ido suka hada da *Harees* yasaki labulen yakoma ciki yayinda *Harees* yabi bayan *Habeeb* din yana zabgama *Jana* harara,


itama hararan tabi shi dashi har tana hadawa da cewa banza kawai maye๐Ÿ˜›.




Dan karamin falone me kyan gaske babu wani tarkace yana dauke ne daga t.v bago sai set din kushin, can gefe kuma tebur ne guda biyu kowa ne dauke da computer, sai agogon bango shikenan.


Zama sukayi suna fuskantar juna yayinda *Habeeb* ya watsama *Harees* wani irin kallo Cikin tsanani bacin ran yace"...?






*_Don Allah kuyi hakuri da rashin ganin posting din akan lokacin munyi buki yar'uwa ta ne._*






Muje zuwa




A




*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Sadeeya)




Tareda






โœ๐Ÿฝ




๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


2โƒฃ0โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_








Wai nayi maka katanga da gida na ne..? Murmushi *Harees* yayi tareda girgiza Kai alamar "a ah, *Habeeb* yace toh" meyasa kake mun haka ne eye...?


Dariya *Harees* yayi tareda cewa yi hakuri nabari, tsaki *Habeeb* yayi tareda cewa dalla mlm aiba ba tun yau kake fadin ka bari ba amma baka bari din ba, so ni nagaji da jin haka don haka saika cigaba da yi saidai bazan fasa gaya maka ba, tabbas kanada aiki idan har sai kajira *"Jana* ta amsa maka sallama sannan zaka ringa shigowa,




murmushi yayi yace insha'allahu daga yau nabari Cikin bacin ran yace "a ah kar kabari kaji, saidai fa kasani wlhy kwanan nan zanyi maku bura'uba daga Kai har "ita domin kuna shiga hakki na baiyuwa sai Ina Cikin bacci na ku dameni da shegen surutun iskanci, ya karashe fadi tareda jan tsaki,




shikam *Harees* dariya yake sosai yayinda *Habeeb* keta hararan shi yace "OK cigaba dayin dariya ka gani idan ban dauki mataki akan iskancin da kukeyi mun ba, kuma ka sani sarai zan'iya dauka KO..?




Cikin dariya *Harees* yace tabbas nasan zaka iya yanzu dai kayi hakuri nayi maka alkawarin, bazan sake biyewa *Jana* ba musamman a iri wannan lokacin dake baccin ka me cikeda daddadan mafarkinnn..




Da sauri *Habeeb* yace mafarkin wa...? *Harees* yana dariya yace ummmmh...kodai abar kaza cikin gashita kawai, tsaki *Habeeb* yayi tareda cewa kaidai kasani, *Harees* yace kaima kasani.




Yanzu dai ba wannan nan ba yakake ya kuma gajiyar kamfen..? yace lafiya gajiya kam akwaita sai kuma na yau da gobe, yace yau da goben ina za'aje...? yace yau liman katagun da kafin liman zamuje, gobe sai muje huturu da gudun fulani dama su sukayi saura,




yace "OK toh" Allah yabamu nasara yace ameen, saidai yau ma bazan samu zuwa ba saida gobe insha'allahu, dasauri yace jiya mafa bakaje ba yauma kuma bazaka jeba to" Ina zakaje...?




yace yi hakuri kasan jiya munyi tiyata dayawa shiyasa, yau kuma zankai mutane na Shopping ne kasan jiya bamu samu zuwa ba saboda me Daraja ta batada lafiya,


toh" shine Zan kaisu yanzu so kozaka rakamu...? ya karashe fadi cike da zolaya,


hararan shi *Habeeb* yayi tareda tashi yana cewa kasan aina saba rakaku so dole kafadi haka, kaga mlm ni zan shiga nayi wanka kafin mutane sunyi yawa domin najiyo hayaniya alamar sun fara taruwa so sai mun hadu anjima,


mikewa shima *Harees* din yayi yana cewa "OK sai kun dawo *Habeeb* yace "ok tareda shiga daki, shi kuma *Harees* yafita.




*Jana* tana nan inda take don haka KO" kallon inda take *Harees* baiyi ba yafita, saidai itace tabi bayan shi da harara tareda cewa maye kawai to" umma ta gaida ashsha,
Koda *Harees* yafita! ya'iske mutane harsun fara taruwa a harabar gidan part din su *Sadeeya* yanufa.


**********


Yan biyu kam sai misalin karfe 10:30am suka tashi brush su kayi sannan suka karya kumallo,


bayan sun gama su kayi wanka suka shirya cikin wata haddiyar doguwar rigar material, marrow color sai aka man na mata black din flowers awuyan rigan da kuma hannu rigan sai sukayi rolling da bakin gyale, kasan cewar su farare sai shirin yaima su kyau zasu fito kenan,
sai su kaji sallama *Harees* zaya shiga dakin.




jin muryar shiyasa *Feeya* tayi saurin boyewa akuryar gado, domin wani irin kunyar shi takeji musamman ma yanzu dayake kiranta me Darajar shi,


*Deeya* Ce ta amsa sallama tana cewa Hamman *Harees* ina kwana.. yace lafiya Queen of beauty, kun tashi lafiya..? tace lafiya qalau yace masha'allah toh" kun shirya kenan ko...? tace "eh, yace "ok amma ina me Daraja ta..yafadi yana duban dakin,


Cikin kun she dariya *Deeya* ta muna masa rigar *Feeya* da tafito gurin saurin boye wa, Cikin zola kuma tace Hamman *Harees* ai my sweet *Feeya* tace mutafi kawai wai yau ba zata jeba,


yace au haka tace"...? tace "eh yace "OK to ke mutafi kawai sai mufara zuwa gidan su "Mamu da gidan "Rahma sannan gidan "zakiyya, sai kuma yace kai!..amma yau zamu sha yawo har da gidan su little feena fa zamu,




tace yauwa Hamman *Harees* toh" mutafi yace "OK, Da sauri *Feeya* tafito tana cewa kai! my sweet *Feeya* yaushe na fadi haka..? dariya sukayi gaba daya,




ahankali *Harees* ya matsa kusada ita cikin sanyi murya yace toh" amma ai kince ba zakije bako...? cike da shagwaba tace "a ah nifa bance ba tafadi, tareda hararan *Deeya* dakeyi mata gwalo,


Yace hmm! wato kwalliyar ce bakiso nagani ko...? kanta yana kasa batace kamai ba saidai wasa da yatsunta datake tana murmushi, cikin rada yace toh" yajiki..? batareda ta kallo shiba tace naji sauki, yace nima naji sauki dariya tayi still bata kalleshi ba murmushi yayi tareda cewa kinfayi kyau sosai me Daraja ta, bari muyi selfee da sauri ta daga kai aikam tuni ya kashe ta da hoto,


dariya sukayi dukkan su sannan yace oyo mutafin ku suka bishi abaya yayinda *Feeya* take cewa *Deeya* keko...? aizan rama sukai ma lnna sallama tace masu sai sun dawo itama zata shiga gurin Hajiya sannan suka fita.




Motoci da mashina da Mutane ne cike aharabar gidan 'yan zuwa kamfe, wanda cikin lokaci kankani suka cika gurin, dakyar su *Sadeeya* suka ra'ba sukafi ta daga gidan saka makon mutane dake tafaman kai gaisuwa sukeyi gurin *Harees*.




*Habeeb* kam cikin lokaci kankani yai wanka yashirya yafito cikin wani ratsetsen yadi dark bulu me shara-shara domin har anagani farar vest din shi, saiya saka hula meratsin fari da bulu kasan cewar aikin rigar ma an ratsashi da farin zare sai yasa farin takalmi, gaskiya dressing din yayi masa kyau sosai,


Sai faman kamshi turaruka yake, wayoyin sa da wallet yakwasa dake saman durowar gefen gado tareda key motar da zaya shiga, cikin sauri yafita daga dakin.


jin takun tafiyar sa tareda kamshin turaran shi sune su kasa *Jana* sauri tashi tsaye tayi tana jiran fitowar sa, da saurin ta tari gaban shi cak! yatsaya tareda watsa mata wani irin kallon dayasa taja baya dasauri,
yace lafiya zaki tare mun hanya bakiji mutane awaje suna jirana bane...?


tace dama zanje gidansu Shafa ne, tsaki yayi tareda kallon ta sama da kasa, yace toh" ban yadda ba idan kuma har kika fita ba da izinina ba kamar yanda ki kasaba toh"keda Allah, sannan yabi ta gefenta yafita abun shi
Cikin takun kasaita.


Mutane naganin fito warshi suka taso Cikin sakin fuska ya tare su da gaisuwa yayinda direban sa yakarbi key
yabude masa tashiga, cikin kankani lokaci muten suka shiga motoci masu mashin suma suka hau dama tuni me gadi ya bude masu kofa sukayi tafita har suka gama sannan ya mai da kofa yarfe.




Itakam *Jana* *Habeeb* yana fita tasaki Dariya tareda cewa hmm! BB smart kenan aidole yau saina dangana kaina da Ado idan ba haka ba gaskiya akwai matsala


_*Nikam nace toh"Allah Kai mana tsari da matsala kowa ce iri ce ameen*_


Sannan ta hayewa sama dakyar ma take taka matakalar tana sakin nishi.


*****
Saida lnna ta tabbatar mutane sun watse aharabar gidan sannan tafito tashiga part din Hajiya, sai faman sallama lnna keta zubawa amma shuru ba amsa, hakan ne yasa tashiga,


mamaki ne yakama lnna ganin Hajiya zaune amma bata amsa sallamar ba, zama lnna tayi kusada ita tareda ta bata tace Hajiyar su *KYAUTA* lafiya...?


Ajiyar zuciya tayi tace hmm! lafiya qalau lnnan *Hafeez* yaushe kika shigo..? lnna tace a ah babu lafiya kam tunda ina tayin sallama baki amsa ba, tabbas *Hafeezee* na yafadi gaskiya da yace" kina cikin damuwa shin meke faru wane..?


Murmushi Hajiya tayi tareda cewa Kai! Inna *"Hafeez* bakomai kawai dai shirmen *Hafeez* ne, lnna tace "a ah Hajiyar su *KYAUTA* *Hafeezee* na baiyi shirme ba, domin kuwa alamunki yanu na kina Cikin damuwa don haka idan har zan'iya sani toh" ki fadamun kila inada shawarar dazan baki.


Hajiya tace hmm! dama dai ba komai bane yakeda muna illa irin abubuwan dasuke ta *FARUWA* tsakanin "Hamman su *"Sadeeya* da matar shi abun yanada muna sosai,


Inna tace tabbas nima abun yanada muna, saidai ba damuwa ce abunda yaka mata murin gayi ba, addu'a ita ce" mafita, shikuma *"Habeebu* ya cigaba da yin hakuri ita kuma Murjanatu" nasiha za'a cigaba da yimata tareda muna mata abubuwan daya kamata taringa yiwa mijinta,


wanda tasan su sarai amma kuma lalaci Da son
*Zuciya* sun hana ta aikata wa, Hajiya tace tabbas kuwa sune suka hana ta aikata wa, dai-dai lokacin da su kajiyo karar jiniya lnna tace Alhamdulillahi yau su Alh sun dawo dawuri, Hajiya tace "eh dama yace sanmako zasuyo
tace Allah sarki gashi ko har sun iso, tace "eh fa.


lnna tace toh" Hajiya abunda za'ayi kenan,tace toh"Allah yasa adace tace ameen. dai-dai lokacin Abba yashiga falon da sallama suka lnna ta gaidashi tareda mikewa tayi ma Hajiya sallama tafita.


Cikin son nan da ake cewa baya tsufa saidai masoyan ta su tsufa, Hajiya da Abba suka hada ido sukayi ma juna lallausan murmushi tace sannu da dawowa, yace yauwa tareda Kama hannun ta kamar yadda yasa ba suka nufi dakin shi cikin sanyin murya yace ya' akayi ne Hajiyarmu naga damuwa afuskar ki muje ki fadamun menene yafaru,


dai-dai lokacin da su kashi ga dakin ta taimaka mashi ya cire babbar rigar shi, hannun ta Yakama suka zauna a gefe gado yace fadamun mene damuwar...? tace kahuta mana tukun, yace aihutun ba zayayi dadi ba tun da ki na cikin damuwa,


Murmushi tayi
tace aiba wata damuwa bace dama dai akan abunda keta faruwa ne tsakanin Hamman yaran nan da matar shi, murmushi yayi yace toh" bana ce ki ringa yi masu addu'a ba...?


tace Ina yi amma abun ne yafara da muna sosai, yace karki damu da hakan kedai kawai ki cigaba dayi mashi addu'a komai zaiyi dai-dai ne insha'allahu,


saidai nasha fada maki auren Na" ALLAH da "Murjanatu kaddara Ne wanda yaka mata kigane hakan, kuma shi duk abunda kikaji ankira kaddara, toh" ana nufin jarabta wace duk wanda Allah ya jarabceshi da'ita tofa bashi da ikon yayema kashi harsai ubangiji ya yaye masa ita, koba haka bane..?


Ajiyar zuciya tayi tareda cewa hakane toh"Allah yaye masa yace ameen tareda tashi yana cewa Zoki hada mun ruwan wanka, tace toh"
Amma dai yanzu lokaci yayi da ya kamata a bashi
matar shi ko...?, dasauri yajuwo ya kalle ta Cikin tsanani mamaki yace...?








_Kut! ๐Ÿ˜ณ dama ashe *Habeeb* yanada wata matar ,amma yake cin kwakwa agurin *Jana*_,tab! ๐Ÿค”
_nasan dai me karatu zaya ce toh" wacece wannan matar KO"...? ๐Ÿ˜€ toh."_




Muje zuwa




A


*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda




โœ๐Ÿฝ




๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน
[7/2, 11:46 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


2โƒฃ1โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_








Me ki kace"?..tace nace ne yanzu kam lokaci yayi da yaka mata abashi matar" shi, kaga idan bai jidadi gurin wannan ba to" zayaji agurin waccan" domin na tabbatar bazasu taba taruwa su zama daya ba KO?...


Dasauri yadawo kusa da ita ya zauna Cikin tsanani farin ciki ya rike mata hannun ta sannan yace Alhamdulillahi!, abunda nadad'e ina jira ki fada kenan da bakin ki sai gashi yau kin fada din wanda baka ramin dadi naji dajin haka ba, kuma tabbas maganar ki gaskiya ce dakika Ce",


idan "baiji dadi gurin "wannan ba to zaiji agurin "waccan hakane, dama amfani auren mace fiye da daya kenan idan wannan ta kuntata maka waccan zata faran tamaka, don haka yanzu kifada mun da wani lokaci kikaga ya kamata abashi matar shi?...


tace umm to idan ba damuwa abarshi zuwa alokacin dana fada maka kwana kin baya, yace to ba damuwa haka din ma shine dai-dai Allah yanuna mana lokacin lafiya tace ameen.


yamike yana cewa wai yau Ina yan "biyun ki ne?... banji duriyar su" ba ko suna part din Baffan su ne?... tace sun tafi siyayya tareda "Hamman dinsu" *Harees* daga can kuma zasuje gidajen yanninsu" yace ah! lallai yau za'asha yawo to ita *Safeeya* taji sauki kenan?... tace "eh taji yace to Allah yakara sauki yakuma dawo dasu" lafiya tace ameen.



Koda lnna ta koma part dinsu ta'iske Baffa yadawo, _kasan cewar akwai wayandan ke daukar karatu agurin shi duk ranan asabar da lahadi,_


bayan ya zauna sai yake tambayar lnna tasamu shiga gurin Hajiya kuwa?... tace "eh yace to me yake da mun Hajiyar?.. nan ta kefada ma shi akan abubuwan dake faruwa tsakanin *"Habeeb* ne da "matar shi,


Baffa yace tabbas abubuwan Da "Murjanatu takeyi babu dadi Wanda dole ne ya damu mutane musamman yawon da takeyi ba tareda izinin "mijinta ba, saidai kawai a ita yimata addu'a shirya lnna tace to Allah ya shirya ta yace ameen,


tace yanzu kam lokaci yayi daza a bashi matar shi ko?.. murmushi yayi tareda tashi yace yau zamu sakeyin maganar da "Alh sannan yanufi daki.




********
*Jana* kam wanka tayi ta shirya sannan tazari key mota tafito Junior yana biye da'ita yana fadi Aunty *Jana,* zanbiki, _suma aunty suke kiranta kamar yadda sukaji su" *Sadeeya* nakiran ta,_


Cikin fada tace to bazanje dakai ba yaro sai shegen nacin tsiya dalla gafara kawuce katafi part din Hajiyar ku, fuska Junior ya kwabe kamar zayayi kuka tareda juyawa zai wuce sai kuma yajuyo yace Aunty *Jana* to ki siyo mun _chocolate da ice cream_ kinji?..


tace to da gudu yanufi part din yana tsallen murna, ita kuma tashiga mota tafita bata tsaya ko'ina ba sai unguwar ilela akofar wani dan madai-daicin gida naga tayi fakin, sannan tafito ta kulle motar tanufi cikin gidan wanda yake dauke da falo guda da dakuna biyu.


Ado ne kwance atsakiyar falon dagashi sai gajeren wando yayi sha yakoshi, ganita yasa yatashi dasauri yanufeta tamkar mayunwacin Zaki itama haka domin tuni tayi jifa da Jakarta tareda gyalen ta, gani nayi yana kokarin rabata da suturan jikinta yasa nai saurin fita ina furta au'zubillahi.


*_KE DUNIYA ina ZAKI da MU?.. wai shin meke damun wasu matan ne?...ace da AUREN KI kike aikata ZINA?... Wa'eeyazubillahi! wannan wani irin MASIFA CE haka?..., shin mazajan kune basa gamsar daku shine kuke bin mazan TITI?...shin ke ba mace bace?... bakisan yadda zaki koyar da mijinki yadda zaya ringa gamsar dake bane?... dole sai wasu mazan ne zasu gamsar dake?...KO" dayake na tabbatar wasu ba rashin gamsar dasu bane mazajan su" basayi, tsabar jarabace DA suka sama kanku, kai kaji wani komawa baya wai harda kudi wasu suke ba abokin facikancin nasu Wa'eeyazubillahi! da kudin Ku da Auren Ku kuke aikata ZINA innalilahi, wlhy duk macen datake aikata ZINA especially matan Auren to ta tuba tadaina idan kuma bata daina ba to tabbatar da cewa AZABA ME tsananin GIRMA tana nan tana jiranta ranan gobe KIYAMA, Allah kashirya masu aikata hakan ka, wayanda basu aikata wa ubangiji ka karesu ameen._*


Saidai su *Jana* suka dauki tsawon wani lokaci suna aikata masha'arsu, sannan suka sararawa Kansu sannan ta maida suturan ta, tadauki gyalen ta tayafa tareda daukar Jakarta tabude taciro bandir din kudi yan dari biyar-biyar tamiwa ado,


fuska daukeda farin ciki yakarba tareda cewa godiya nake me zakina, badan keba da yanzu Ina can agidan yari kuma gidan nan daki kasiya mun naji dadin sa kwarar kinga gashi Ina rayuwa ta hankali kwance, shiyasa nake rokon Allah yabarni dake *Jana* domin kina shayar dani farin ciki,


_Sata sukayi shida abokanshi sai aka kama su" shine tayi ta cuku-cuku harta fitar da shi, sai kuma gidan dayake suka koreshi shine tasiya mashi wannan gidan,_


tace hmm ainima rokon danakeyi kullum kenan Allah yabarmu tare yanzu dai Zan tafi sai nadawo, yace to amman don Allah kar kisake yin kwana biyu nan da bakizo ba jinayi kamar zan mutu, tace haka nan nimafa naji kamar Zan mutu saboda rashin jinka ajikina amma karka damu zansan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login