Showing 111001 words to 114000 words out of 163788 words
Chapter 38 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
gaba, Don har ana hango lallausan suman dake kwance luffff afaffad'an kirjinsa rigar iya guiwa take.
*Deeya* Ce naga tashigo dakin bakinta dauke da slm sanye take da kayan bacci farare irin masu tasushin nan, riga me guntu hannun da wando iya guiwa kanta saye dawata hula me gara, gurin *Habeeb* tanufa kwanta wa tayi a bayan sa tareda tura hannun ta duka biyu acikin kirjin sa ahankali tafara wasa da lallausan suman dake kwance lufff, kirjinsa sannan ta dora kanta akafad'arsa,
Ahankali tafara goga fuskarta asajen sa, cikin cool voice din me dadi wacce ke cike da bacci tace Hmm na sannu da aiki.
Cikin sarkakk'iyar murya yace yauwa *Leemah* ta aina gama dai-dai lokacin da yakarasa kulle computer, yatashi tareda juyota gaban sa yace *Leemah* ta bakiyi bacci ba?... tace "eh yace why?.. baki ta turo tareda cewa to bakai bane kasa bamun da kwanciya anan takareshe fadi tareda d'an dukan sa akirji.
Murmushi yayi me Cike da shaukin kaunar ta yace to am sorry *Leemah* ta, zomuje ki kwanta a nan din dama kuma aikirjin naki ne, dai-dai lokacin da yadagata yana fadin yauwa mujema kiji wani labari me dad'i.
Tsaki yar gado yazaunar da'ita shi kuma yana tsaye sai yace kinaji KO?..Kai ta gyada alamar "eh, yace" wata beautiful Lady ce mijinta zanyi Making Love da'ita, idon tazaro tareda cewa Kai! Hmm na taya akayi to kai kasani?..,
yace hmmm kedai tsaya kiji, dama already shi Mijin yayanta harma tana kiransa Hmm dinta kamar yadda kike kirana, lokacin da zaya fara making Love da'ita kinsan me tace"?.. tace a ah.
Kan gadon yahau yakwanta kansa yana kan filo sannan yace kina kallona?..kaita gyada masa alamar "eh aranta kuma tana fadin toshi Hmm na taya akai yasan abinda yafaru tsakanin mata da miji?..,
ido taga ya lumshe tareda fara jujjuya Kansa akan filon, sai kuma taji yafara fadin wayyo "Inna ta wayyo "Baffa na wayyo Hajiyar mu pls my sweet *Feeya* kuzo kiceceni Hmm *Habeeb* zaya kashe ni, sannan yabud'e idon yana mata dariya me Cike da zolaya.
itakam baki da hanci ta bud'e tana kallon sa cike da mamaki wato da'ita yako?..,aikam dasauri tahaye ruwan cikin sa tareda daukar filo tana dukan shi Cike da shagwaba tace Hmm na Dani kake fa...cikin dariya yace "eh dake nake koba haka kikace ba?. yakareshe fadi tareda kashe mata ido daya.
Baki ta turo sannan tace to aida gaske ne kakusa kashe ni, murmushi tayi tareda rike hannun ta yakarb'e filon datake dukansa dashi yaijifa dashi sannan yace, *Leemah* ta idan na kasheki to narayu dawa?.. tace ah! ga "Aunty *Jana* nan, had'e fuska yayi.
Aaikam dasauri ta waske da fadin Lah! aikai manaji abunda ka fadi ranan cike da zumud'in sonji abinda yafad'a aranan, yace mata me nafad'a *Leemah* ta gaya mun kinji"?..cikin da zolaya tace cewa kayi wayyo *Leemah* ta wayyo my Honey inason ki u are so sweet *Leemah* ta pls don't left me kinji?.. if u left me l will die l will die *Leemah* ta Kuma kanata maimaita wa.
Dariya yake sosai sannan yajawo ta ya rungume sai kuma ya mirginata takoma kasa shi kuma yana saman ta mean yai mata runfa, cike da shaukin kaunar ta yace Allah da gaske ne *Leemah* ta idan kika bar ni mutuwa zanyi domin kaunarki ma had'in rayuwata ne,
Sannan kuma ked'in aita dabance *Leemah*, domin kina dauke da wata irin ni'ima me dad'i dasauri tace kai Hmm na sai kace nid'i wata sweet ce ko honey, yace ai kinfi sweet da zuma.
Pls *Leemah* ta taimaka mun manayi abin nan dayasa naketa zuba maki subad'i, ido tazaro cike da tsoro tace wayyo Hmm na abin nan fa akwai zafi sosai, yace l promise u yau bazaki jizafi ba har zata sakeyin magana ya had'e bakin su.
_Nikam ganin haka yasa nafece ๐๐ปโโdomin bazan iya ganin abun nan ba lol_.
*_Bayan sati biyu_*
*****
Duk yadda *Jana* taso fita Don ta aikata mugun nufin ta, abin yagagara domin duk *Habeeb* yabi yatoshe hanyar hatta da bakin get yace" idan tasake zuwa ba tareda izinin shiba abakin auren ta, ita kuma idan akwai abunda ta tsana arayuwata to be wuce rabuwa da *Habeeb* ba.
_Nikam nace rabuwa ta nawa kuma KO readas_?
Don haka dole ta hakura gashi dai babu rashin ci babu rashin sha, amma tayi wani irin mugun ramewa tayi dubu tamkar ba *Jana* ba kasan cewar abubuwan sunyi mata yawa musamman rashin samun abun nan๐ da batayi.
Kasan cewar tuni ta fahimci *Habeeb* da *Deeya* sunayin abin, hakan ne yasata sake shiga wani irin ya nayi, domin bataga fuska ba balle tace itama aimata abin asalima yanzu wani irin mugun tsoron sa take ji data gashi sai taji gaban yafadi gawani azababben kwarjini dayake mata wanda kotasoyi masa magana akan abubuwan dayake ta wayanda suke mugun kona mata rai sai takasa,
gashi itaba ma'abociya ibada ba balle tayi kokarin kai kukanta ga Allah ba don yaimata maganin matsalarta saidai ma tasake tura kanta ga halaka, wato ta cigaba da biyama kanta bukata kamar yadda tasa ba.
Aban garen *Habeeb* da *Deeya* kam cikin sati biyun nan kuwa sun murji amarcin su son ransu, wanda ta dalilin hakan ne shak'uwa me karfi yasake shiga tsakanin su, idan kaga su sunyi kyau sunyi kiba musamman *Habeeb* da ya kasan ce yanzu bashi da wata matsala, daga b'angaren cikin sa har shimfid'ar sa, yana samun yadda yake so agurin *Leemarsa* wanda hakan ne yasata sake samun wani irin matsayi me girma a ZUCIYAR sa.
****
Yau lahadi kuma yaune *Habeeb* zaya koma gurin aiki, kamar kullum idan suka tashi sai sun shiga part by part sun gaida iyayan su, KO yanzu masun shiga sun gaida su tareda sallamar su akan zaya koma gurin aiki.
Ahankali suke tafiya tamkar marasa lafiya makale suke dajuna kamar zasu shiga jikin juna *Habeeb* da *Deeya* kenan, sanye yake dawani blue suit me a sakin kyau da tsada wanda yasake fito masa Da kyausa da kwarjinsa.
Ita kuma tana sanye dawani blue material wanda tayi masa dinkin riga da siket, dinkin yad'an kama jikinta kad'an don haka yai mata kyau sosai saita kashe daurin zahra buhari sosai tayi kyau fuskarta sai wani annuri yake fitarwa, hannun ta rikeda _briefcase_ dinsa sunyi kyau sosai saidai kallo daya zakai masu ka fahimci sam basusan rabuwa dajuna.
Saida suka isa dai-dai bakin kofar fita babban falo sannan suka tsaya, jantayayi ya rungume tsam akirjinsa yana jin SONTA da kaunar suna ratsa jini da bargon sa, yayinda yakeji kamar karya tafi yabar ta cikin sanyi murya *Habeeb* yace *Leemah* ta l will miss u so muรงhhh!,
ahankali tace me twooo Hmm na pls come back soon kaji?..yace l will Insha'allah *Leemah* ta kiyi mun addu'a kinji, ahankali tace Allah yakareka dakare warsa yabaka abinda kaje nema na alkhairi, ya kuma dawo mana dakai lafiya yace ameen *Leemah* ta nagode Allah yaimaki albarka pls ki kulamun dakaki kinji?.,
Tace to ni maka kula mun da kan ka sosai pls karka kula kowace "mace idanka kula wata" Allah babu ruwa na dakai takareshe fadi tareda turo pink mouth dinta, dariya yayi cike da shaukin kaunarta yakama bakin ya tsotsa sosai sannan,
yace karki damu *Leemah* ta ai babu macen datake da matsayin da zan kulata, yace oya we started our sing sake kwantarda kanta tayi akirjinsa yayinda hannun ta daya yake shafa lallausan sajensa, shikam sai lumshe ido yake domin yana matukar son haka ahankali tafara fadin.
_Zan rayu dakai zan mutu dakai abadan Dani dakai zamu zauna, idan nace ni; ina nufin kai" idan nace kai Ina nufin ni;_
Ahankali shima yace _zan rayu dake! zan mutu dake! abadan dani; dake! zamu zauna idan nace ni; ina nufin ke! idan nace ke! ina nufin ni_;
Dariya sukayi gaba daya sannan suka daga wa juna babbar yatsa, tareda fadin yessss! sannan yakarbi jakar yana fadi byeee *Leemah* ta itama tace byeee Hmm na sannan yanufi gurin mota,
Dasauri Saminu yazo yakarbi jakar tareda bud'e masa kofar motar yashiga tareda sa jakar sannan ya rufe, sannan yaje yashiga tasu motar suka fita daga harabar gidan da gudu abuja tayi Kira, to mu kam sai muce asauka lafiya *Habee-Leemat*.
Jiki bakwari *Deeya* tajuya zuwa cikin gida kamar zatayi kuka zuciyar ta cike dakewar Hmm dinta, takai tsakiyar falo kawai sai taga *Jana* k'idis agabanta Wanda hakan ba karami tsora ta da razanata yayiba,
gawani irin muguwar fad'uwa da gaban ta yayi dasauri tafara karan to addu'ar neman tsari, sannan ta kalli *Jana* wacce ke tsaye rik'e da k'ugu sai cika take tana ba tsewa, tareda watsama *Deeya* harara.
Tsaki *Deeya* tayi tareda watsa mata wani mugun kallo domin yanzu wani irin haushin ta takeji wanda tarasa dalilin dayasa takejin haka, _nikam nace kishine๐_ cikin had'e fuska *Deeya* tace...
*_Tau fa ๐ณsaida Habeeb yatafi ๐คto ko wata wainar kuma za'atoya tsakanin Deeya da Jana Oho!_*
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_ (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐พ
๐นMeenart๐น
[11/9, 10:06 PM] My Ameena: ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐ ๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
6โฃ1โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
_NOT EDITS_
Lafiya zaki tare mun hanya?..cikin masifa *Jana* tace antare maki hanyar dan ubanki, ido *Deeya* tazaro cike da mamaki jin yadda *Jana* ta k'unduma mata zagi, cikin bala'in dayake cinta tace dan ubanki natare hanyar kiyi abinda zaki shegiya aljana tunda aka likawa "mijina ke shikenan narasa gane kansa saboda asirin da shegen uban....
takasa karasawa saboda kyakkyawan marin da *Deeya* tazuba mata, Wanda ya gigita yasata rike kumatu cike da kwantena kwantena na mamaki take kallon *Deeya*.
Cikin tsananin bacin rai *Deeyar* ta nunata da yatsa tareda fadin duk abinda zaki fad'a kifad'a akaina zan iya dauka, amman banda "iyayena domin "sud'in mutane ne masu matukar kima da daraja agurin, Don haka bazan taba yadda wani mahaluki yaci musu mutunci inaji da gani banyi magana ba, wlhy bazan yadda ba KO kad'an kinji.
Cikin masifa *Jana* tace kutumar uba ni kika Mara?..cikin bacin rai *Deeya* tace "eh domin kigane iyayena ba abokanan wasan ki bane, inafatan kin fahimta ai?.
Cikin masifa *Jana* tace kan uba tunda kika mareni yau sai nayi maki dukan tsiya agidan nan,
Gaban *Deeya* ne yafad'di jin zancen duka, amma sai bata nunaba asalima tsaki tayi tareda kokarin bita gefen ta zata wuci still kirjinta yana dukan uku, cikin wani irin mahaukacin masifa *Jana* ta finciko *Deeya* tareda cewa dun ubanki dawo ke har kin iyasa ki mareni, sannan ki wuce tab!.yariyan baki isaba wlhy ai yau sai na lahiri yafikin jin dadi agidan nan.
Wani irin razanannen tsawa *Deeya* ta dokawa *Jana* tareda fadin dalla gafara mlm sakar mun riga ki naji ko?.., aikam dasauri *Jana* tasaki rigar cike da razana jikinta har yana kerrrrrrrma! lokaci daya kuma sai tsoron *Deeya* yad'arsu mata gawani irin mugun kwarjini datayi mata,
*Deeya* kam ita tayi tsawar amma saida tsawar tabata mugun tsoro wanda tayi mamaki har tana fadi aranta wai itace ta doka wannan tsawar haka?.., ranta amatukar bace yayinda kirjinta yake cigaba da matsanancin bugawa,
ta kalli *Jana* tareda nuna kanta da yatsa tace kinga nayi maki kama da wacce zaki taba fatar jikinta?..
Shuru *Jana* tayi takasa cewa komai domin gaba daya *Deeya* tayi mata kwarjini gawani mugun tsoron ta da yakamata, tsaki *Deeyar* tayi tareda fadin mlm kije kinemi wacce zakiyiwa dukan tsiya amma bani ba domin tab'ani dai-dai yakeda samun matsala arayuwarki, tana kaiwa nan tawuce sama zuwa dakinta hankalita kwance abinta.
Yayinda tabar *Jana* tsaye sake da baki da hanci, zama tayi akan kushin jabar tareda tura hannu ta acikin wannan uban attachment din da batasa lokacin cire shi ba,
abu sai tashin tsami yake mtsww kai Allah dai yarabu da kazaman mata ameen.
Wani irin iska me zafi tafesar daga bakin ta tana hura hanci rainta amatukar bace tace kan uba ai wlhy tunda kikayi kuskure marina yarinya sai naci ubanki agidan nan, KO bayau ba dama *BB* kike takama dashi to yawuce Don haka kwanan nan zakigane kuren ki tadan dad'e tana sakawa da warware wa, can saita tashi ta nufi sama buguzun-buguzun.
*Deeya* kam tana shiga daki tayi sauri ta kulle kofa taje ta zauna agefen gado tareda dafa kirjinta tana sauke numfashi kamar wacce tayi tseren gudu, sannan tad'aga hannun ta tana kallon kyakkyawa tafin hannun ta me dauke da zanen fulawa ja, cike da tsoro tace kai! yau nice namari "Aunty *Jana* har da yimata tsawa Kai!...amman nimafa naji tsoron tsawar nan.
Can kuma sai ta kyalkyace da dariya saka makon tunowa da reaction din da *Jana* tashiga lokacin da tayi mata tsawa, cikin dariya tace Kai! Ashe nima dai *BOSS* Ce, can kuma sai tamike zumbur tareda cewa Kai! wlhy bari nazo na bar gidan nan kar tayi mun duka kamar yadda ta fada tunda taga Hmm na baya nan, kafi azo aceceni naji jiki.
tana fadin haka ne tareda daukar gyalen ta yafa sannan tadauki wayar ta dake kan gado da jakarta da kuma hand out sannan tabude kofar ahankali, gaban ta yana d'an faduwa kadan tafita tareda kulle kofar ta sauka kasa atunananin ta zataga *Janar* saidai kuma bata ganta ba, Don haka tasaki ajiyar zuciya tareda fita dasauri.
******
*Deeya* Da tafita kai tsaye part din *Feeya* tanufa kwance ta'iske *Feeyar* hannun ta rikeda hand out tana karanta wa, _kasan cewa ranan Monday zasu fara jarabawa shiyasa itama *Deeya* ta dauko Nata don tayi karatun,_
Ahankali *Feeya* ta tashi daga kwance kasan cewar cikin ta yafara girma, murmushi tayi tareda ajiye hand out din tana kokarin daura dankwali, *Deeya* ta ajiye jakarta akan table tareda yaye gyalen kanta fuskarta dauke da murmushi.
Tace sannun da hutawa me ciki hararanta *Feeya* tayi tareda fadin bana son iskanci fa, ba me ciki ba walla me Kai! Cike da zolaya *Deeya* tace to me kai yakike ya my unborn baby?..tace kedai ki kasani tace kefa?..
tace bansani ba Allah my sweet *Deeya* kin cika shegen tsoka, dariya *Deeya* tayi tareda zaunawa tafadin aike kinsan tsokana ajinina yake, itama dariyar tayi tareda fadin aikam nafi kowa sanin hakan.
*Deeya* tace hmm ke kinsan abunda yafaru yanzu kuwa?..tace "a ah saikin fada nan *Deeya* fada mata abunda yafaru tsakanin ta da "Aunty *Jana*, dariya sukai sosai saida sukai me isarsu sannan suka tsaya.
*Feeya* tace kinyi mun dai-dai my sweet *Deeya* aigara da kika yimata haka, kinsan ita batasan darajar iyayenta ba shiyasa Kai! amma fa kinyi na miji kokari dakika mari wannan shad'ikar tace hmm ai kedai bari ni kaina saida nayi mamaki kain....karar wayar tane yakatseta dasauri taciro daga jakarta *Habeeb* ne yakirata video call ganin hakan ne yasata fadi Oh! my sweet Hmm I love u l miss u so muchhhh!, ta kareshe fadi dayin dariya.
Shima dariyar yayi me cike da sonta da kaunar ta sannan yace miss u two my honey *Leemah,* and Love u more than Love me Dear, cike da farin ciki tace nagode Habibina to yakake ya hanyar?... yace to gani nan dai hanya kuma gamunan a kanta tace Allah yatsare yace ameen kina Ina ne?...
tace gurin my sweet *Feeya* yace Oh! my *Leemah* shine kikafito?.. me makon kiboye mun kanki um?..cike da shagwaba tace to sowee my Hmm Allah daka tafi gidan babu dadi shiyasa nazo nan kaga tun ba'aje ko'ina ba nafara kewarka KO?..., pls nidai ka dawo dawuri kaji?..
murmushi yayi me kayatarwa tareda shafa suman kanshi yace, hmm Allah *Leemah* ta nima tun bamu fita bauchi ba kewarki tafara kamani sosai, tace kagani ko tozaka dawo dawurin?.. cike da shaukin KAUNAR ta yace karki damu *Leemah* ta zan dawo very soon kinji?..
tace to nan suka taba fira sannan sukai sallama, bayan yaimata gargadin ta maida hankali tayi karatu sosai tunda taga jarabawa zasuyi, tace to tareda zuba masa addu'ar tsari.
Daga nan kuma suka cigaba da fira itada *Feeya* can kuma sai ko wacce tafara karatu saida misalin karfe 4:30pm sannan tako gida part dinsu tashiga bata dad'e ba tafito tashiga part din Hajiya nan kam sai bayan isha'i sannan tafito ta nufi part dinsu dasauri tashige daki ta kulle.
_Nikam nace Kai!๐ *Leemar* *Habeeb* tun yanzu shiga bacci ko dai kina tsoron kar *Jana* ta suburbud'a kine?_ ๐.
*_Bayan kwana hudu_*
*****
Tun ranan da *Deeya* tamari *Jana* basu sake hadu wa ba domin kuwa tuni suka kulla wasan yar buya, duk yadda *Jana* ta so su hadu *Deeya* Don tayi mata illa kamar yadda take qudirtawa azuciyarta, Allah bai nufa ba domin *Deeya* tana rigata tashi sannan ta riga ta kwanciya.
Idan sukaje school suka dawo sai su yada zango gidan *Feeya* idanta ta so kuma sai tashiga part dinsu lnna ko tashiga part din Hajiya, sai bayan sallar isha'i sannan ta nufi part dinsu idan kuma tashiga bata iske *Jana,* Don haka sai tashige daki abinta,
Waya kuma tsakanin ta da *Habeeb* kullu yisuke suna zuba soyayya abinsu wacce take Kara masu shak'uwa da kaunar juna.
*****
Yau alhamis tunda ta tashi takejin aranta yau duk yadda zatayi sai taje gurin Shafa da Adonta, saida ta tabbatar *Deeya* tafita zuwa school ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ja,
tayafa gyale ja sannan ta dauki wata yar karamar jar jakar sarka da yankune sai tadauki pos da key motar ta data dade ba tashiga ba sannan tafito, tanufi ma'jiyar motocin motar duk tayi kura amma haka tashiga kafin takai bakin get saita fara kuka wanda kana ganin shi zaka ga ne na karya ne, tana isa get din ta tsaya tareda sauke glassa sannan kara sautin kukan sosai.
Dasauri baba megadin yafito
yana gani tana kuka yace subhalallahi! Hajiya lafiya?..., cike da kukan kissa tace wlhy yanzu aka kirani aka fadamun ankai "Mamana asibiti batada lafiya, yace assha
Allah yabata lafiya yafadi tareda bude mata get tafita saida ta hau kan titi sannan tasaki dariya tace bazan megadi sannan takarwa motar gudu.
_Nikam nace ai ita ce banza๐ lamba daya