Showing 30001 words to 33000 words out of 163788 words
Chapter 11 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
yadda zanyi, yace yau to kiyi idan ba haka ba zanfara biyoki gida,
tace abunda yakamata kenan domin nima nafara gajia dayawon zuwa gurin ka saboda Baffa mlm yasamun ido sosai, tsaki ado yayi tareda cewa kibarni Da wannan tsohon" bafullacen zanyi maganin shi, tace yauwa dadai yafi kam domin yana takura mun sosai sannan tafito ta tafi gida.
_*Nikam nace to ALLAH ya shirya*_
*******
Su *Deeya* kam basu suka dawo gida basai karfe 3:30pm na yamma duk da sungaji amma haka sukayi wanka suka shirya suka tafi islamiyya, domin su basa wasa da karatu.
Sai karfe 6:00pm sannan suka dawo daga islamiyya, uniform suka cire sai suka sa riga da siket iridaya na wata atamfa, bulu me ratsin yalo basu daura dan kwalin kayan ba saidai suka dora wani bulun gyale me duwatsu akai, dinki kayan yai masu kyau sosai kasan cewar yadan kamasu kadan,
Bayan sun gama sai suka dauko siyayyar da sukayo zama sukayi kamar yadda suka sabayi, suka cire man shafawa sabulai daba turare da kayan kwalliya suma daban kayan kwalama suma duk daban har da pads dasuke amfani dashi idan period yazo shima sun core shi daban,
Wanda tun lokacin da suka fara al'ada, shine dasu kaje siyayya sai a karasa wanda zaya sauka pads din saboda tsabar kunya, ๐ saidai *Harees* ne ya daukar masu kuma har yanzu idan sunje siyayyar shine yake daukar masu pads din,
Bayan sun gama cirewa sun ajiye kowani agurin zaman shi sai suka kwashi _chocolates da sweets biscuits_ kun rabin Wanda suka siyo, zasu fita sai *Feeya* tace sweet *Deeya* ayi rige-rigen zuwa gurin Hajiyarmu, tace Oyo muyi ayoma sedi redi gooooo suka fita falon kasa da gudu,
lokaci guda suka fajikin Hajiya amma sai *Deeya* tace yeeee! narigaki *Feeya* tace to sarki ojoro ai tare muka iso KO" Hajiyarmu?..tace "eh amma dai ku daina gujegujen nan haka,
sukace to Hajiyarmu tareda sauka saman kafet suka zube _chocolate's da sweets da biscuits_ din, gani yawan _chocolate's da sweets da biscuits_ kala-kala yasa Hajiya zaro ido tace yanzu duk yaza kuyi da wannan tarkacen?..
sukace sha zasu yi tace lallai yaran nan da sauran ku, kunga baruwana da shirme kubani su duk nan, ba musu suka kwasa suka mika mata saidai sunata turo baki, guda biyar-biyar ta basu tace ya ishe su haka ba ruwanta da shirmen su sai idan zasuyi al'ada sai suyi tafaman fadin cikin su naciyo,
sannan ta tashi takwashi sauran tanufi sama tabar sunan zaune suna turo bakim
Sai kuma suka fara yiwa junansu gwalo daga nan kuma sai suka fara jifan junan su dasu sweets din
suna dariya,
*Deeya* Ce tajefi *Feeya* dawani _chocolate_ saidai tuni *Feeya* ta kauce majifar tana dariya, daidai lokacin da *Habeeb* yashiga wanda ga dukkan alama dawo warsu kenan,
Sai jifan yasame shi a kirji wanda kallo daya zakai mashi ka fahimci ran shi abace yake, ganin hakan yasa *Feeya* ta haye sama da gudu cike da tsoro, dasauri itama *Deeya* zata gudu yadaka mata tsawa aikam ta tsaya cak! yayinda jikinta yadauki rawa Cikin bacin rai yace?...
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart ce๐น
[7/2, 11:46 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
2โฃ2โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Ke! Ina wasa dake ne?... Kai ta girgiza ciki da tsananin tsoro, cikin abinda baifi secod ba ya'isa gaban ta wanda har saida suka ji numfashin juna tareda daddadan kamshi turaran su wanda ya daki hancin su alokacin guda, musamman *Habeeb* dayaji kamshi turaran ta har cikin kwakwalwar shi wanda yahaifar mashi da faduwar gaba me tsanani,
da karfi yarintse ido sai kuma yabude aikam tuni sunyi jajir haka ne yasa tayi saurin jada baya kadan, cike da tsoro ta kalle shi abunda tagani akwayar idon shi, yasa taji gabanta yafadi musamman data tuna da abunda tayi masa jiya, Cikin bacin ran yace shine kika jefeni dan baki da kunya ko?..
Cikin tsanani tsoro tace kayi hak.... ta kasa karasa wa sakamakon yatsun shi biyu dayasa yakama bakinta, yamatse aikam tuni taji wani irin rad'ad'en zafi ya bakunce ta wanda yasa hawaye suka fara ambaliya akan kyakkyawar fuskarta,
ahankali tadaga hannun biyu tana bashi hakuri๐domin babu bakin magana,
fuska ya daure๐ก tareda cewa aidama nace zan kamaki shine jiya kikai mun rashin kunya har da murgud'a mun wannan bakin saboda kin rainani KO?...yakarashe fadi tareda sake matse bakin.
gaba daya jikinta yadauki rawa saboda zafin data sakeji yaratsa ta, Cikin tsawa yace dalla daina kallo na, ahankali ta lumshe idonun ta masu daukeda zara-zaran gashi yayinda hawaye suka sake zubowa, tsaki yayi tareda kauda kan shi gefe yace idan kika sake murgud'a mun wannan bakin me Kama da gidan tsutsa saina sa wuka nayanke shi, sannan yasaki bakin tareda cewa bace mun agurin nan kona tattakaki, aikam tuni tahaye sama dagudu tana sakin kukan shagwaba.
Saman kun shin yafada tareda dafa kanshi sai kuma ya rufe ido ahankali yafirta yah ilahee, can kuma sai yasaki tsaki mtww tareda cewa nikam nagaji! da wannan abubuwan nagaji!! nagajiiiiiiii yakarashe fadi dakarfi, Hajiya dake tsaye akan shi tun lokacin da *Deeya* tashiga ita kuma tafito don taji dalilin dayasa mata ya' kuka, tace dame kagaji?.. dasauri yabude idanun shi Da sukayi jajir ya zuba su akan ta, tace nace dame kagaji?... shuru yayi ba tareda yace komai ba sai dai kallon ta kawai dayake yi da jajayen idon shi, zama tayi kusada shi tareda cewa idan har akan "Murjanatu kake furta kallamar gajiya to kayi maza kafurta istigifari saboda ka sabi ubangijin ka domin shi ya jarabeka da auren ta,
idon ya lumshe tareda furta Astagafurullah! astagafurullah!! astagafurullah!!!
tace yauwa. saidai meyasa idan an bata maka rai sai kazo nima ka bata mun rai, a miliyon ya bude ido cike da tsanani tsoro yake kallon ta me kunshe da tambaya?.., aikam tuni tabashi amsa da cewa tabbas bacin ran *"Sadeeya* da *"Safeeya* shine bacin raina, aduk lokacin da ransu yabaci inajinshi har cikin raina don haka banason abunda kakeyi masu" musamman hali dubuna, wanda narasa abunda yasa kake saurin sata kuka gaskiya kadaina banaso.
Idon yarintse yayinda yake jin wani irin abu yana yawo akahon zuciyar shi wanda yarasa kome ne ne, ahankali yafurta kiyi hakuri zan kiyaye saidai aduk lokacin da raina yabaci ina shigo wa nan ne domin naji sanyi araina, amma sai su kuma su sake bata mun rai wanda hakan ne yakesa nakeyi masu abunda suma ransu yake baci wanda bansa hakan yana bata maki rai ba, don haka ki gafarce ni sannan yatashi yafita.
Bin bayan shi tayi da kallo harya fita sannan tayi ajiyar zuciya ahankali tamike jiki bakwari, tanufi sama zuciyarta cike da tsanani tausayin halinda yake ciki.
*****
Dakin su *Deeya* tashiga har alokacin *Deeya* tana kuka yayinfa *Feeya* ke lallashin ta, zama Hajiya tayi agefen gado dasauri suka matsa kusada ita suka dora kansu acinyarta Cikin shagwaba *Deeya* tace Hajiyarmu kinga har yanzu bakina yana mun zafi, ahankali tasa hannun asama leben da haryayi ja abuga fara, Cikin sanyi murya tace sannu hali dubuna kiyi hakuri da halin "Hamman din Ku, amma kuma meyasa kukeyi masa rashin kunya bana hana kuna ba?...
tace nifa ban masa rashin kunya ba naje jifan sweet *Feeya* ne shine nasa meshi bansani ba, kuma nace yayi hakuri shine ya matse mun baki ta kareshi fadi tareda turo dan mitsitsin bakin, murmushi Hajiya tayi tace to yi hakuri hali dubu na, amma kuma kuringa kula da yanayin dayake shigowa, kunga wani lokaci yana shigowa ne ranshi abace sai Ku kuma kusake bata mashi rai, wanda banajin dadi haka kamar yadda banaji dadin abunda yake maku, ku kiyaye banason kunayi mashi rashin kunya kunji ko?...suka Ce to sannan ta tashi tafita.
*******
*Habeeb* kam rai bace yanufi part din shi direct toilet yanufa Bayan yayi wanka sai yadauro alwala yafito daure da tawul akugun shi, daya kuma ahannun shi yana goge Kai bai Shafa maiba saboda yajiyo kiran sallah don haka turaruka yafesa sannan yasa boxes tareda saka brown din jallabiya, sannan yafita zuwa masallaci.
dakyar *Habeeb* ya'iya tsaya wa akai sallar isha'i dashi saboda wani irin azababben yinwa dayakeji, don haka ko doguwar addu'ar daya keyi bai tsaya yayi ba to balle kuma daukar karatun da sukeyi bayan isha'i duk Ranan asabar da lahadi, *Harees* yana kallon fitar shi daga masallaci shima yai sauri tashi yabi bayan sa, yace lafiya naga ka fito yau ba zakayi karatun bane?.. dakyar yafurta zanje nadawo ne yace "OK tareda koma wa cikin masallacin shikuma yawuce.
part dinsu lnna yanufa da sallama yashiga lnna tana nad'e abun sallah ta amsa zama yayi a kushin tareda cewa lnna sannu da gida, tace yauwa *Habeebu* sannu da dawowa agalabaice yace yauwa lnna don Allah idan akwai abinci ataimaka mun dashi amma kafin nan idan akwa ruwan zafi a fara bani tukun, tace to *Habeebu* duk akwai bari na kawo maka yace to lnna nagode.
*Habeeb* baibar part din lnna ba saida yaci abinci ya koshi sannan yafita, koda yafito su Baffa suna fito wa daga masallaci don haka sai kawai yanufi part din shi, domin dai yasan yarasa karatun yau, dakin shi yanufa yahau kwamfuta yafara gudanar da aikinsa ba tare daya kalli inda *Jana* take ba, kasan cewar tunda yashiga take bin shi tana bashi hakuri wanda zaya iyacewa shine karona farko datayi masa laifi yanuna bacin rai shine tabashi hakuri,
ganin zata dame shi yasa yace yaji tafita tabashi guri zayayi aiki ne sannan tafita tsaki yayi mtww tareda cigaba da aikin shi.
****๐๐*****
Yau Monday kuma ayau nesu *Deeya* zasu fara rubuta NECO don haka koda sukayi sallah basu koma bacci ba, kodama basu saba da hakan ba Bayan su yi karatun alqur'ani sai sukayi wanka suka shirya Cikin uniform suka fito basu tsaya karin kumallo ba kasan cewar sun tashi da azumin litini, don haka saidai kawai suka sallami Hajiya da Abba ida sukai masu fatan alkhairi,
Sannan suka fita part dinsu lnna suka shiga nan ma fatan alkhairi su kai masu, sannan suka fito suka shiga part din *Habeeb*.
direct dakin *Habeeb* suka shiga dake nan kasa yana tsaye gaban madubi sanye yake da wata dakakkiyar shadda sky blue, kamshi turaran shi duk yacika dakin, yana kokarin saka hulla yaji sallamar su amsa wa yayi ba tareda yajuya ya kalle suba, cikin sanyi murya sukace Hamman *Habeeb* ina kwana?..
yace kun tashi lafiya, cike da mamaki sukace lafiya lau domin bai taba yimasu haka ba, hakan ne yasa sucewa Hamman *Habeeb* yau zamu fara jarabawa, yace to madallah sai amaida hankali cike da zumud'in sukace to *Deeya* Ce yar daukan magana tace to Hamman *Habeeb* ai ba kayi mana addu'a ba, dasauri yajuyo ya kalle ta,
itakuma tayi saurin ta dukar dakai kasa tana wasa da hannun ta yayinda kirjinta yake bugawa, fuska hade yace to aisai ku zauna KO a tsaye za'ayi addu'a?... zama sukayi shima yazauna sanna yafara kwararo masu addu'a sun amsawa, bayan sun shafa yace to Allah yabada sa'a sukace ameen sannan suka fita.
*****๐๐****
Kwance tashi asarar me rai gashi har lokacin zabe yazo anyi kuma Cikin nasara *Habeeb* yalashe zabe, kuma ayau ne Jumma'a aka rantsar dashi anbashi office dinshi da gidan dazai zauna yanzu haka ranan Monday zaya fara aiki, dawowar su kenan daga abuja don haka, yau gidan Alh Hashim soro cike yakeda yan'uwa da abokan arziki masu ta ya su murna,
"Aban garen su *Deeya* kuma tuni sun gama jarabawar su dukka daga neco har weac yanzu haka ma gobe asabar zasu yi send4t walima, shiyasa sun kasa zama sai shirye-shirye suke don haka duk fuskar wanda ka kalla agidan dauke take da fari ciki, musamman *Deeya* da *Feeya* bakinsu kamar gonar audiga don farin ciki, Hajiya tasa anyi masu gyaran jiki kamar wasu amare ga fulawa da akai masu ahannu da kafa kai yan biyun Hajiya sunyi matukar kyau kamar kasa ce suka gudu.
******
Washegari
Tunda misalin karfe 7:30am su *Deeya* suka isa
Makaransu kasan cewar sune manyan dalibai kuma shugabanni koda karfe 10:00am tayi alfurqan
ta cika tabatse da mutane, dakuma manyan baki acikin har da gwamna da sanata wato *Habeeb* Hashim soro, su Adda Mamu da Adda Rahma sunzo dukkasu tareda yaran su,
Cikin nutsuwa ake gudanar da program me ban sha'awa da burgewa, musamman yadda dalibai keta zuba larabci da turanci gwanin sha'awa, sannu ahankali har aka gama liyafar. yayinda shugabar dalibai wato *Haleematus-sadeeya yusuf* da mate makiyarta *Safeeya Hashim* sune dalibai mafi hazaka akowani fanni shiyasa duk suka washe rabin kyaututtukan, wanda hakan ba karamin burge mutane sukayi ba,
Shi yasa ake ta daukar hoto dasu su Adda Mamu suna son suyi hoto dasu amma mutane sun hanna, *Habeeb* ma har zaya tafi sai *Harees* yace ya tsaya su dauki hoto dasu *Deeya*, shiyasa yatsaya saidai kuma sunfi minti talatin suna jiransu amma basuzo ba hakan ne yasa gaba daya ran *Habeeb* yabaci.
Cikin bacin ran *Habeeb* yace da *Harees* kaga mlm kana bata mun lokaci fa, ahankali yace kayi haku bari nakira su fuska ba annuri yanufi gurinsu da'alama shima ran nashi ya baci, *Harees* yana isa gurinsu wani kyakkyawa saurayi shima yana'isa dan kimani shekara ashirin da biyu, sanye yake da t-shirt fara da wando baki Cikin yanayi na gayu yace yamma ta don Allah inason muyi hoto,
har da *Feeya* za tace to sai tafasa sakamakon wani irin kalla da *Harees* ya watsa mata, dasauri ta daukar dakai kasa yayinda gaban take faduwa fuska daure yace mujen kuko?..Cikin sanyi murya su kace to tareda bin shi abaya, saidai kuma jiki su yai sanyi da ganin yanayin shi wanda hakan bai masu dadi ba domin basu taba ganin shi haka ba,
yayinda wannan saurayin yake binsu yana cewa pls babys ku tsaya muyi hoto mana, ko sauraren shi basu yi ba domin bacin ran dasu kagani a fuskar *Harees* duk ya daga masu hankali musamman *Feeya* suna karasawa gurin su Adda Mamu, shi kuma saurayi
yana kai hannun shi yariko academy gown din dake jiki *Deeya.*
Aikam Cikin tsanani bacin ran *Habeeb* ya sharara mashi wani irin mahaukacin marin dayasa shi kusan faduwa, dasauri abokan shi sukarike shi kasan cewar suna biye dashi abaya Cikin tsanani bacin ran saurayin yadago tareda cewa?...
*_Barkan mu da Jumma'a MASOYANA_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:46 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
2โฃ3โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Baki yasaki tareda zaro ido cike da tsoro saka makon ganin *Habeeb* kasan cewar shi din sanan ne, ga kuma wani irin azababben kwarjini da *Habeeb* din yaimasa wanda hakan ne yasashi kasayin magana,
Cike da bacin ran *Habeeb* yanuna shi da d'an yatsa tareda cewa Kai! tabbas Kaci darajar "mahaifin ka, amma badan haka ba dayau sai na KO" ya maka tarbiyya domin naga alama bakada ita, Cikin tsoro saurayin yace Sorry sir,
Da karfi *Habeeb* yace rufe mun _stupid mouth_ dinka agurin nan, kona sake watsa maka wani marin ni tsaranka ne Ina magana kana magana, dasauri yarufe๐คญ tareda girgiza Kai, yace "to nabaka bashi wannan idan kasake kuskure sake aikata haka KO?..
Na rantse sai nayi maka mummunan hukunci dasai kayi mamaki, Kai! hattara wlhy ba kasan kowane *Habeeb* bako?... Shikama dan saurayin nan duk ya tsorata da ganin yanayin *Habeeb* din, Cikin tsawa yace bace mun agurin nan stupid boy kawa,
Cikin sauri yamatsa shida abokan sa.
yayinda *Habeeb* ya watsama su *Deeya* wani irin firgetattace kallo dayasa ji kinsu yasake yadaukar rawa saboda tabar tsoro, tsawa yadoka masu Wanda yasa suka Kara tsoro ta, yace Ku kuma zaku wuce mutafi kosai na tattakaku agurin nan?..
Da sauri suka nufi inda motacin su yake yayinda *Hafeez* daketa wata masu harara tun dazu, yace aidama tattakasu kayi tunda su wawayen yarane ba tareda *Habeeb* yace komai ba, yabi bayansu rai bace yayinda *Harees* da *Hafeez* suma suka bisu, suma su Adda Mamu suka dafa masu baya,
Saidai sukam zuciyoyin su cike da mamaki fadan da *Habeeb* yayi duk dacewa "eh sunsan lallai saurayin bai kyauta ba, to amma kuma fadan da *Habeeb* din yayi yayiwa inji cewar su fa๐. haka dai suka nufi gurin motocin guda biyar ne ajere guda Adda mamu suka shiga da iyalanta, itama Adda Rahma haka guda kuma *Hafeez* ne da *Harees* da *Deeya* da *Feeya,* biyu kuma ta uban gayyace *Habeeb* yashiga daya escort din shi suka shiga daya, alokacin guda suka bar harabar makaranta dagu.
Shikam dan saurayin nan suna gefe shida abokansa suna kallon su harsu ka bar harabar school din, sannan ya sauke ajiyar zuciya dai-dai lokacin da naga me girma gwamna ya'isa gurin shi kafatar shi yadafa, tareda cewa Mustee my boy duk abinda yafaru nagani saidai banji dadin hakan ba, naso nakaraso naba hon BB soro hakuri amma nakasa saboda tsabar kunyar abunda ka aikata,
Wanda wannan din alama ce kanuna ta rashin tarbiyya kuma kasan inayi maka ita dai-dai gwargwado, to amma meyasa zakayi mun haka acikin mutane shi baka ganin hakan zaya iya zubar mun da mutunci a idon mutane?...
hawaye naga sun zubo akan kyakkyawar fuskarshi yace Dad kuskure ne amma bazan sake aikata haka ba kaji?...murmushi Dad yayi tareda cewa nayi my boy to kashare hawaye mana, yace to Dad nashare amma gaskiya inason yarinyar nan, baki Dad yabude cike da mamaki yace wacce acikin su?..yace *"Sadeeya* inason ta sosai pls Dad kayi wani abu kaji?..
dariya yayi tareda cewa kar kadamu my boy zanyi