Showing 69001 words to 72000 words out of 163788 words

Chapter 24 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

ma meson zuciya KO?.. Kai tsaye *Deeya* tace "eh mana idan ba son zuciya ba Da rashin sanin muhimmancin sallama ba, aida daki kazo sai kice Assalamu'alaikum *Sadeeya* yajikin mijin mu yanzu yana Ina ne?..


kinga ni kuma sai nafada maki inda yake, amma dazuwa kince wai keeeee! sai kace wata yarki to aiko" yarki "Lili mama banji kina kiran ta Keeeeee! ba balle nida ba yarki ba, sannan kince wai Ina mijin ki kum...




katseta *Jana* tayi dacewa Keeeeee! dalla banason maganar banza tambayar kinayi Ina mijina?..hararan ta *Deeya* tayi zuciyar ta cike da jin haushin ta musamman data tuna abubuwan datayi tamata a Abuja, tsaki tayi tareda cewa bansani ba.




Cike da bacin rai *Jana* takai hannun zata mari *Deeya,* aikam cikin zafin nama *Deeyar* tarike hannun ta, tareda yarfar dashi Cikin tsanani bacin rai tanuna tada yatsa tace karki farashi wlhy ainan ba Abuja bane kokin manta ne natuna maki?...to nan din Bauchi ne tafadi tana nuna kasa da yatsa, so saiki ki kula domin bazan sake daukar abinda kikai mani a Abuja ba wlhy,




Sannan ta nufi hanyar office din *Harees,* yayinda tabar *Jana* baki sake Cike da mamakin *Deeya* tsaki tayi tareda cewa kai! Lallai ma yarinyar nan kin rainani wato nikike fadawa wannan maganar KO?... zaki sani ne ai inda muka hadu, sannan ta juya tanufi gurin motar ta tashiga taja tabar harabar asibitin ran ta bace.




Tsaki *Deeya* tayi kasan cewar tana kallon tafiyar ta, sannan tace umma ta gaida assha, juyawa tayi takoma bakin emergency room din ta cigaba safa da marwa tareda addu'ar Allah yaba Hmm *Habeeb*.



Likitoci sun dauki tsawon lokaci suna fama kafinsu samu numfashi *Habeeb,* yadawo inda daga karshe sukai masa alluran barci sannan aka kaishi dakin Hutu na musamman domin yana bukatar Hutu, kasan cewar sungano tsabar damuwa ce tareda wani abun dayasa aran sa wanda ta dalilin hakan ne jinin sa yahau sosai.




*Harees* ne yafara fitowa daga room din Dasauri *Deeya* ta tare shi tana cewa Hmm *Harees* ina Hmm *"Habeeb* din yajikin sa??? ransa bace yace ki biyo ni, ba musu tabi bayan sa saidai jikinta yai sanyi daganin yanayin sa hakan ne yasa gaban ta faduwa.




Office din yahadu sosai sanyi ac da daddad'an kamshi ke tashi acikin sa, bayan sun zauna sai yaciro wayar sa yakira Hajiya Cikin hikima yafada mata abunda yasamu *Habeeb* din, sannan yace mata anyi masa alluran barci wanda zaya iyakai wa tsawon wani lokaci bai farka ba saidai babu damuwa insha'allahu normal zaya farfad'o,




tace" to Allah yabashi lafiya amma yaduba mata lafiya hadi dubun ta domin itama tana bukatar ganin Likita, murmushi yayi tareda kallon *Deeya* wacce kanta ke duke tana tunanin halin da Hmm *Habeeb,* yake cikin.




yace to Hajiyar mu dasauri tadago kai jin yace" Hajiya cikin sanyi murya tace Hmm *Harees* pls bani "Hajiyar Mu inyi magana da'ita", harara ya watsama ta wanda yasa tashiga taitayin ta, bayan yagama waya da Hajiya sannan yakira Baffa da Baffansu yafada masu *Habeeb* bayada lafiya da ganan kuma sai yafara kiran layin yan'uwa daya bayan daya, yana fada masu cewa *Habeeb* bashi da lafiya yanzu haka yana asibiti ankwantar dashi amma dasauki bayan yagama fada masu sannan ya kashe wayar.




Kallon *Deeya* *Harees* yake me dauke da harara kauda kai tayi tareda turo baki, Cikin yanayin tana shagwaba tace kai Hmm *Harees* sai faman harara ta kakeyi, yace na harare ki Queen of beauty nan gaba ma ba hararan ki zanyi ba zane kizanyi da bulala,




ido tazaro cike da tsoro tace to me nayi?...tsaki yayi mtww! tareda cewa to meye ma ba kiyi ba ummh! haba Queen of beauty meyasa kike haka ne wai ke bakisan irin son da Dan'uwa yake maki bako?.. to bari infada maki abun da bakisa niba "Dan'uwa yana *SONKI* fiye da yadda yake son kasa,




Cikin sanyi murya tace to ainima inason sa dasauri yace karya ne baki son sa" tace Allah inason shi, yace to meyasa kike so "yasake ki?.. tace to ai bada gaske nake yi ba fa, hararan ta yayi yace to inda yasake ki kuma fa?...shuru tayi.




Yace yanzu tsakanin kida Allah kina son "shi?.. dasauri tace "eh yace kinyin alkawari zaki koma gidan "sa tace "eh amma dai ba Abuja ba, yace to shikenan tashi mutafi gida tace "a ah ina nan har sai yafarka yanzu ma muje ka kai ni naga "shi,




yace a ah! sai anjima tace pls yace kiyi hakuri har zuwa anjima yanzu anyi masa alluran barci ne yana bukara hutu, so tashi muje ki kinga ma sai ki taho masa da abun zayaci idan yatashi kinji?..jiki asanyaye tace to badan tasoba ta tashi suka tafi gida saidai *ZUCIYAR* ta cike da son ganin *Habeeb* din.




******
*Jana* kam tana fita daga asibiti Unguwar su "Ado tanufa ranta bace akan abinda *Deeya* tayi mata ta, saidai kuma kodata isa din bata iskeshi ba, don haka sai ranta yakara baci takira layinsa yafi a'irga amman bai jeba, har zata tafi sai gashi yadawo abige yayi sha yai tatul,




yana ganin ta yasaki murmushi cikin maye yace *Jana* ta nayi miss dinki sosai fa itama murmushi tayi, tareda cewa nima haka ina ta kiran layin ka bana samu meyasa mu wayar kane?.. dariya yayi yace na siyar da ita nasha kodeeeee! yakarasa fadi tareda jan kalmar karshe sosai, sannan yace amma zaki sake siyamun wata ko?..




tace "eh yace yauwa *Jana* ta mu shiga ciki ki bani zumarki na lasa, tace kasha dai son ranka adona yace to shikenan muje sannan suka shiga cikin gidan sa, ba tareda bata lokaci ba suka fara fatali da kayan jikinsu,




*_Ni ko ganin haka yasa na'ari na kare๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€inafurta Wa'eyazubillah! Allah kashri yamu ameen._*




*_Asibitin_* har misalin karfe 5:00pm *Habeeb* bai yafarka ba alokacin kam *Deeya* taci kuka har ta gaji saboda ganin *Habeeb* bai farkaba, kwance take akan cinyar adda Mamu kasan cewar duk sun zo tana, saifaman lalla shin ta Adda Mamu take.




Dasauri *Haress* yafito daga office dinsa yanufi dakin da *Habeeb* yake kwance, yayinda wani nurse yake biyu dashi wanda shine yaje yafada masa *Habeeb* din yafarka,




Koda suka shiga dakin yafarka amma sai faman surutai yakeyi, dasauri *Harees* ya'isa gurin shi yafara bashi taimakon da yadace, sannu ahankali yadawo normal ido ya tsuwara *Haress* din yayi da bakin sa ke anbato salati, can kuma sai yai shuru tareda lumshe kyawawan idon sa ahankali yafara tunanin abunda yafaru,




Can sai yabud'e idon tareda kokarin tashi, dasauri *Haress* ya kamashi yatashi yasa masa filo don ya jin dadin gina, ya nace masa sannu bai amsa ba saidai yace Ina *"Leemah* ta?.. Cike da mamaki *Harees* yace Ina Ce maka sannu ka nace mun Ina *Leemah* kar?..




Kai tsaye yace "ita nakeson gani. yace to muda bakasan gani ai sai kasa akore mu daga Bauchi, kaga malam tashin na taimaka maka kashiga toilet kayi wanka da brush, sannan ka dauro alwala kazo kayi sallah la'asar sannan ka samu abunda zakaci, kuma su "Baffa zasu fara shigo wasu gaida kai sannan ita *"Leemarta* ka data damu mutane da kuka sai kace ba ita ce tayi sanadin zuwan ka asibiti ba.




Bayan yayi wanka yafito saye da jallabiyya kasan cewar an kawo masa, bai iske *Harees* saidai dadduma ashinfid'e so hawa kawai yayi yafara gaba tareda salla yana idar da sallah sai yakoma bakin gado ya zauna tareda yajingi ya lumshe ido, domin baya jin karfi jikinsa ga wata irin mahaukaciyar yinwa da yakeji.




Sallamar su Baffa ne yasashi bude ido har zaya sauko sai Baffa yace a ah yi *Habeebu* zaman ka, nan dai sukai masa su yajiki cikin girmama wa yace dasauki basu dade'ba suka fito.




*Jana* ce tanufi dakin zata shiga (kasan cewar dasuka gama bad'alar su saita dawo asibitin) sai *Deeya* tayi sauri tadauki basket din dake dauke da kulan abincin tashige dakin abinta, har *Janan* zatabi ta sai *Harees* yace tayi hakuri har *Deeya* tafito sai tashiga saboda ba'ason adamesa da hayaniya, ba dan tasoba takoma gefe tana haransa.




Bakinta daukeda sallama tashiga aciki ya amsa don haka bataji ba basket dinta'ajiye,
sannan tanufi gurin sa, kallo daya yai mata yakauda kai tareda lumshe ido yana jin wani irin *SONTA* yana ratsa jinin sa,




still yanzu ma sanye take da abaya saidai wannan din brown color ne me stones farare sai tayi rolling, sai zuba kamshi take tayi kyau sosai fuskar nan fayau koda taci kuka hakan bai sa ta canja ba,




Cikin cool voice dinta tace sannu Hmm *Habeeb* yaji ki?..banza yayi da'ita saida tafadi haka har sau uku amma bai amsa ba, sai kawai ta fashe da kuka me cike da shagwaba, Dasauri yabude idon tareda cewa
meye?..




itama banza tayi dashi, ido yarintse yana jin ku kanta har cikin ransa ahankali yabude idon aikam har sunyi jajir tsura mata suyayi, sannan yahad'e fuska yace ke bakisan yadda mutun yakejin kukan ki aran sa bako???...bata tanka ba, saidai ta cigaba da kukan ta me cike da sangarta Cikin tsawa yace?....








*_Adadin comments adadin typing gaskiya_*๐Ÿ˜€






Muje zuwa




A


*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)






Tareda






โœ๐Ÿพ






๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ




4โƒฃ4โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






_NOT EDITS_






"Wai keeee wannan kukan daki keyi na mene haka eyeee?.. shin *Leemah* kinsan yadda nake jin kukan ki acikin *ZUCIYATA* kuwa?... nace menene kinyi banza dani, so idan bazaki fada mun abinda yasaki kuka ba to Ina rokon ki kiyi shuru domin kukan ki yana kona mun *ZUCIYATA* matuka.




Tsayar da kukan tayi tareda tsura mashi kyawawan idanun ta dake tsiyayar hawaye, shidin ma kallon ta yake da idanu wan sa masu rikita ta, yayinda yakeji wani irin sonta yan azabtar da *RUHIN* sa, kauda kai tayi tareda turo baki sannan tace to bakai bane nace maka sannu yajiki shine ka kyaleni.




Tsaki yayi mtww! tareda barin kallon ta sannan yace to Ina ruwanki dani eyeee keda ki kace baki sona to meye na tambayar ya jikina?...Dasauri tace nibace bana sonka ba yace kince mana tunda kince sai na sake ki, tace to aikai kace baka sona shi yasa nace ka sake ni, Dasauri yace da yaushe nace ba nason ki?... shuru tayi batace komai ba,




Cikin sanyi muryar yace nasan bakida amsar tambaya nan *Leemah* ta, domin nidai da bakina ban taba cewa bana *SONKI* ba idan har ma nace to tabbas bana cikin hayyaci na, amma nasan *ZUCIYATA* bayan "Hajiyar Mu babu macen danake so irin ki sai KO "Lili mama, amma sai ki tafadin banason kum...yakasa karasa wa saboda ganin tana kokarin cigaba da kukan fuska ya daure tareda cewa to meye kuma?..




"Baki ta turo tareda goge hawaye da bayan hannu sannan tace to aini ma inason ka sosai fa, yace to shine kike; tacewa sai na sakeki?..tace "eh saboda abinda kukai mani ne kai da Aunty *"Jana* yace to ainace kiyi hakuri kuma "itama nace kar tasake yimaki haka kinji?..shuru tayi.




yace pls *Leemah* ta to kiyi hakuri kinji yafidi tareda kama kunnu wan shi, tace to aina tun-tuni na hakura yace yauwa *Leemah* shiyasa nake sonki saboda bakida riko murmushi tayi Sannan tace to yajiki?..idon shi k'uri akan ta yace naji asauki musamman ma dana ganki; saidai inajin yinwa sosai *Leemah* ta me kika kawo mun ummh?..




ba tareda ta kalle shi ba tace abinci, yace yauwa Allah yasa jagwalgwalon nan ne me dadi ai bata san lokacin da dariya yawace mata ba, tace Kai Hmm *Habeeb* shi kakeson ci?.. ido ya lumshe wani irin sanyi ne yaji yama-maye zuciyar sa yayinda yaji gaba daya damuwar sa tayaye domin yanzu kuma kam yasan babu maganar *SAKI* tsakanin su, ahankali yabude idon tareda zubasu akan baby beauty fice dinta me cike da kuruciya, wani irin *SONTA* ne ke fisgar shi a kowani lokaci da kowani minti dake tafiya da kowani sakon,




lallausan murmushi ya saki tareda cewa "eh shinake son naci I hope shiki kai mun?.. tace "eh tareda nunafar inda ta ajiye basket din.


Wani dan karamin flas me tsawo tadauko tabud'e tadauki cup ta tsiyayo hadadd'en coffee me zafi tasa spoon Sannan tamika masa, kin karba yayi cike da tsoro tace pls Hmm *Habeeb* kafara shan coffee sannan kaci alalan kwai din kaji?..,




fuska ya yamutsa tareda cewa to ai banda lafiya kinga ma hannuna yaimun tsami, bazan iyasha da shiba pls kid'an taimaka ki banida hannun ki kinji *Leemah* ta?..




Dasauri tace ayya sowee Hmm *Habeeb* dina Bari na baka kaji tafadi tareda zama kusa dashi, tana fifita coffeen sai data tabbatar ya rage zafi sannan tafara bashi a baki, yana sha amma idon Sa nakan ta.




Saida ya shanye coffee sannan tazuba masa alalan tareda farfesun kayan ciki me romo wanda yasha kayan yaji kamshi sai tashi yake, yanaci yana zuba sanyi itakam sai dariya take masa wanda yake sake sashi nishadi sosai, haka taci gaba da bashi saida ta tabbatar ya ko shi sannan ta kyaleshi bayan ta bashi wani hadadden kunun zakin aya, daga nan kuma suka fara fira da'alama sun manta da mutanan dake wane suna jiransu.




*****
Shuru *Deeya* ba tafito ba hakan ne yasa *Haress* shiga dakin, fira ya'iske su nayi abinsu gwanin sha'awa wanda kallo daya zakai masu ka fahimci suna matukar kaunar juna su, sosai suke fira su sai dariya suke da'alama sun manta da kowa da komai sai kan su,




Cike da mamaki *Harees* ya kalle su, yace eyeee lallaima ku din nan koma dai nace Queen of beauty, wato ana can anajiran kifito su shigo su gaida Dan'uwa shine ki ka zauna kunata soyewa ko?..cike da kunya tace kai Hmm *Harees,* yace to karya nafada?.. tace to ai shine fa yace" na bashi abinci a baki hannun sa yana ciwo,




Murmushi *Habeeb* yayi tareda hararan shi yace to basa ido ina ruwan ka da soyewar Mu?..yace da ruwana kaida baka da lafiya mene na tsaya wa soyayya, yace soyayya kam ai sai munje gida ko *Leemah* ta?.. Murmushi tayi tareda rufe fuska da tafin hannun sannan ta gyada kai alamar "eh, yace yauwa don haka saika sallameni domin ni tuni naji sauki,




yace aiba ka isa ba malam sai kayi sati daya tukun na dasauri *Habeeb* yace tabdijam wane zayai sati asibiti?..yace kai kaga bari nace su shigo su gaida kai, don naga alama kun manta dasu" yafadi tareda fita.



*Deeya* tana gani su Adda mamu sun shiga tayi saurin mike wa, zatabar bakin gadon aikam dasauri *Habeeb* yamai da'ita tareda watsa mata wani irin kallon dayasa ta nutsuwa, da gudu Lili taje gurin *Habeeb* tayaye jikin sa tareda fadin Daddy nawai baka da la'iya inji Aunty *Feeya*?.. yace "eh, tace to ina ema tiwo?.. yace kaina ne amma yanzu ya daina, cike da tausayi tace soweee Daddy na kalka chake en tiwon kai kaga Aunty *Deeya* tana ta kuka,




Dariya akayi gaba daya dakin shikam *Habeeb* murmushi yayi tareda kallon *Deeya,* wacce kanta ke kasa cike da jin kunyar tonatan da Lili tayi, Cikin sanyi murya yace to Lilin Daddy Junior yace Daddy sorry yace yauwa, nan dai yan'uwa sukai ta gaida shi daya bayan daya yana amsawa.




*Jana* kam gaba daya hankalin ta yana kansu *Deeya* itada *Habeeb,* sai kallon su take me cikeda tsana jitake kamar taje ta shak'e *Deeya* don bakin cikin ganin ta zaune kusada *Habeeb.*




*_Bayan kwana biyu_*
******
"Ayau lahadi kuma ayaune *Harees* ya sallami *Habeeb* daga asibiti kasan cewar tuni yaji sauki sosai tamkar bashi ba har da yar ki ba yayi, acikin kwana biyu nan kuma wani irin shakuwa ce sosai tashiga tsanani sa *Deeya* da,
yayinda itakuma *Jana* aduk lokacin data shirya tafito daga gida dasaunan zuwa asibiti gaida *Habeeb* saita fara zuwa gurin *Ado tukun sun gama bad'alar su tukun sannan tanufi asibitin.




*_Allah kashirya matan auren dasuke aikata ZINA da AUREN SU ameen._*




Gaba daya familiy sun hadu a babban falon part din Abba kasan cewar yaune ranan dasu ke family meeting, bayan Baffa yabude taro da addu'a kamar yadda aka saba sai Abba yafara magana indaya yanke hukunci cewa nan da sati biyu *Deeya* zata koma dakinta lokacin *Habeeb* yasake samun sauki sosai, kowa yayi fari ciki dajin haka musamman *Habeeb* da yaji kamar yajawo sati biyun kusa bayan an gama sai aka tambayi kowa idan yanada magana yayi wayan da suke dashi sunyi sannan akayi addu'a kowa yatashi yafita.






*Habeeb* da *Harees* ne tsaye a harabar gidan inda *Harees* yake cewa da *Habeeb* Dan'uwa amma dai ba gobe zaka koma bako?..yace "a ah saidai jibi insha'allahu, yace to Allah yakaimu yace ameen nan dai suka da'n tattauna akan al'amuran yauda kullum sanna kowa yanufi part dinsa.




*Washegari Yakama Monday*
*******
Kuma ayaune su *Deeya* zasu fara zuwa school da misalin karfe 9:00AM, *Deeya* CE tafito cikin shirin tana zuwa school din sanye take da riga da siket na wani tsadadden less blue yanada zanan flowers fari, dinki rigar have gown ne yadan kamata ta sama siket din kuma me tsaga ta baya ne saidai kuma ba ko wane zaya game akwai tsaga ta bayan ba, ya kuma fito mata da sherp dinta sosai.




Sannan tasa wani tsadaddan passion din sarka da dan kun'ne da zobe da awarwaro masu asalin kyau duk farare saidai suna da ratsin blue, bayan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi sannan ta kashe daurin dankwali saita dauko gyale fari me flowers blue, tayafa sai tasa takalmi sannan ta rataya jaka fari gaskiya tayi kyau sosai, mirror ta kalla sai tayi dariya domin ta san tahadu matuka Cikin cool voice dinta tace wannan kwalliyar ta Hmm *Habeeb* dina ce.




Sannan tafito zaune ta iske Baffa da lnna (kasan cewa nan part dinta kwana), cikin ladabi tareda tsantsar kaunar iyayan nata ta zauna tsaki yar su kamar yadda tasa ba, cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login