Showing 3001 words to 6000 words out of 35767 words

Chapter 2 - BEELAL BUK BOOK 1 BOOK COMPLETE BY MAMAN AFRAH.doc

girma da abun ya ransu.Wani murmushin ya?e na maye gurbin damuwar da ta so bayyana a fuskata na ?arasa kan tabarmar da yake zaune na zauna tare da dafa kafaWarsa na ce


"Eh Ummar Hameeda na son mu haka Babanka ma yana son mu, kuma rashin zuwansa ai hakan ba yana nufin ba ya son mu bane aiyuka ne suke masa yawa amma zai dawo kwanan nan"

"Amma ai ya daWe bai zo ba kuma ko ya zo ba ya kawo mana komai, ba ya siyo min alewa ko abin wasa kuma ba ya so in ke zuwa kusa da shi korata yake, ya ce tafi ka bani wuri ni ba na gane maganarka kuma ba na so kake zuwa kusa da ni" Ya faWa cikin in,innaa idanunsa na cikowa da ?wallar.

Daker na danne hawaye da ke barazanar zubowa daga idanuna, wani tausayin yaron ya rufeni ashe komai yana ?wal?walwarsa dama yara basu da mantuwa yanzu rabon Babansa da garin nan kusan shekara biyu amma bai manta abin da yake masa ba amma dole a matsayina na uwa in yi abin da zan kawar masa da abim daga ransa.Dariya na yi har ha?orana suka bayyana, Beelal kawai tsayawa ya yi yana kallona na ce


"Kaima dai Beelal da wani abu kake, ashe baka san wasa ba, ai Babanka wasa yake maka amma ya fi ?aunarka fiye da kowa, kuma kaya da ba ya siyo maka kuWi ne babu a hannunsa shi ya sa"


Shiru ya Wan yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce.

"Amma ina ganin kuWi a hannunsa kuma...


"Ya isa haka bana son jin komai, tashi mu je na maka alwala na cire maka kayan makarantar sai a sanya wasu ka yi sallah kafin nan na haWa abincin" Ta faWa dan kawar da zancen saboda ita tana fashin sallah.




MMN AFRAH>?p?=?
?=??


*BEELAL*



NA



MAMAN AFRAH



FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Da sunan Allah mai rahma mai jin ?ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.


Page 5?? ?'?6??



Misalin ?arfe biyu na dare ne zaune take a kan katifa, ta kasa bacci gabaWaya tunanin yayarta ya tsaya mata a rai, duk da ta san Yayarta na cikin rashin jin daWin zaman auren da take ta dalilin sirikarta, saboda mummunan ?uduri da sirikarta ta take da shi na jahilci da duhun kai.Amma dai ta san duk halin da Yayarta take tana zuwa ta gansu amma yanzu ta rasa gane dalilin da yasa ta Wauki lokaci mai tsawo ba ta ziyarcesuba.Tabbas in har ba wata gagarumar matsala Yayarta take ciki ba to da tuni ta zo.Dole ne ma ta ziyarci Yayarta duk ta halin ?a?a sai ta yiwa Kano dirar mikiya duk da ta kwana da sanin cewa hakan zai iya zama matsala ga ?ar uwarta amma wajibi ne ka gaida mai gasheka, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke irin ta wanda ya daWe yana tunani da nazari, a ?arshe kuma ya samo mafita, tashi ta yi ta Wakko wata farar leda a cikin wani kwano ta dawo ta zauna ta kunce ledar, memory card ne a ciki ta fito da shi.


"Kai zan siyar na ziyarci ?ar uwata domin sanin halin da take ciki rayuwa ko mutuwa, na siyar da wayar da ta siya mun wacce muke gaisawa na siya mana abubuwan bu?ata kuma sim Win ya faWi gashi ban haddace numberta ba bare na ari waya na san halin da take ciki" Ta faWi hakan a zuciyarta tana maida memoryn ta ?ulle ta sanya a ?asan filonta da nufi siyar da shi gobe ta samu kuWin mota.


Abin rufa ta sanya ta rufe Beelal da ke ta bacci cikin kwanciyar hankali, idanu ta kafeshi da su tana rayawa a ranta cewar ba za ta barshi a wurin Ummar Hameeda ba da shi za ta tafi duk da irin gargaWin da aka mata na zuwa gidan Yayarta ta da Beelal Win, shekaru biyar da suka wuce da ta je da shi ita ma yun waccen lokacin bata sake ziyartar Par uwarta ta ba. Wannan dalilin ne ya sanya basa zuwa sai dai ita Yayar ta zo saboda son samun zaman lafiyar Yayarta ta a gidan aurenta amma wannan karon da shi za ta je dan kwata-kwata ba ta so Beelal yake ji a ransa cewa ba Waya yake da kowa ba dan ko kaWan ba ta so ta ce ya zauna a gidan su Hameeda dan zai ga ba a je da shi ba gashi yana yawan tambayarta Amminsa bata zo ba ta kawo masa alewa da kayan daWi ba.Da safe za ta je ta siyar da memoryn a yau Win nan za su tafi Kano da wannan ?udurin a ranta bacci ya yi awon gaba da ita.


Da sassafe ta tashi ta shiga haWa musu kayansu, Beelal sai murna yake za su je Kano,saboda yana son ganin Yayar Mamarsa Hajiya LaWifa garin nan sauran na jiya ta haWa musu suka ci da ?arago, bayan sun yi wanka sun shirya ta fito ri?e da hannun Beelal Win dan dama ranar asabar ce babu makaranta dan haka shagon da mai siyar da waya ta nufa ta kai masa ya siyi memoryn 1200 ya bata kuWinta daga nan gidan su Hameeda suka je suka musu sallama daker aka raba Hameeda da Beelal dan cewa ta yi sai ta bi su haka ta rin?a kuka dan naira hamsin Win da Fatima ta bata ma jifa ta yi da ita tana ta bori a dole sai ta bi su, to itama Fatima dan babu yadda za ta yi, dan gudun matsala, amma da har ita za su tafi tun da duka-duka kwana biyu za su yi.


Suna zuwa gida jakar kayansu kawai ta Wauka suka hau machine domin ya kaisu Kazaure su shiga motar Kano domin a Mazari suke ?auyen kazauren ne, naira Wari ta bashi suna zuwa kwa suka samu mota saura mutum biyu su cika suna shiga wani mutumi ma ya zo dan haka babu Sata lokaci motarsu ta tashi.


Suna sauka a Kano, ta biya Wari bakwai ne kuWin mota, Wan sahu suka samu G.R.A Fatima ta ce dan haka Wari uku ya bu?ata kafin su ?arasa ?ofar tafkeken get Win gidan ta ce Wan sahun ya ajiye su, fitowa suka yi daga cikin adaidaitan suka shiga bin layin da kallo Beelal baki ya ?i rufuwa sai murna yake yana ?arewa haWaWWun gidajen kallo.Hannunsa Fatima ta kama suka fara tafiya domin ?arasawa ?ofar har cikin ranta ta ji daWi ganin yadda Beelal Win ke matu?ar murna sai dai kuma tana jin muguwar fargaba ta irin tarSar da za su samu daga mutanen gidan.Ita sai a lokacin ma ta ji a ranta dama basu taho ba saboda kwata-kwata ba ta son a sanya ?ar uwarta a damuwa amma dai ta sanya a ranta koma menene zai faru sai dai ya faru dan shau?in son ganin ?ar uwarta ya danne komai ciki kwa har da fargabar da ke cikin rai da zuciyarta.


A jikin get Win suka tsaya ajiye jakar kayan nasu ta yi ta sanya hannu ta shiga ?wan?wasa ?ofar a hankali sai da ta yi kusan sau huWu sannan wani ?aton mutum dogo ba?i da alama shi ne mai gadin ya buWe ?aramar ?ofar tare da tsayawa yana ?are musu kallo fuskarsa ko alama rahma babu ya haWe rai tamkar wanda aka faWawa sa?on mutuwa.


"Ikon Allah sun canja mai gadi kenan" Fatima ta faWi hakan a ranta.

"Ya aka yi ne, nan gidan ba a zuwa bara" Ya faWa yana musu kallon raini.


"Ba bara muke ba" Fatima ta faWa cikin jin wani Waci a ranta, wato dai talaka shi ba komai bane a wajen wasu masu kuWin, suna ganin bashi da galihu sun manta cewa su ma ba su suka baiwa kan su kuWin ba? Kuma Allahn da ya basu bai manta da talakawan ba daga ganin su sai ya danganasu da bara.


"To mai kuke in ba bara ba kin tashi kin Wakko nakasashshe dan ki fi samun sadaka to su wannan gidan ba a musu bara" Cewar mai gadin yana wani kallonsu tamkar wanda ya yi tozali da abin ?yama.

Hawaye ne a take suka shiga gangarowa kamar an buWe famfo daga idanun Beelal jin an kirashi da nakasashshe.Ganin hawaye na zuba a idanunsa hakan ya sanya Fatima jin gabaWaya tausayinsa ya kamata, baki ta buWe da niyyar yin magana sai ta ji Beelal Win ya ce


"Haka Allah ya halicceni idan kuma za ka gyara min to" Beelal Win ya faWa cikin in,innarsa.

Kallon kallo aka shiga da mai gadi da Fatima, amma ita gabanta na dukan uku-uku dan tana gudun mai gadin ya wula?antasu ko ma ya hana su shiga gidan gabaWaya.


"Allah sarki yaro ka yi ha?uri ka ji, babu wanda ya isa ya canja halittar ubangiji, hali ne dai kawai irin na Wan adam" Mai gadin ya faWa cikin sanyin murya dan sai ta ga gabaWaya jikinsa ya yi sanyi.


"Na ha?ura, domin Mamana ta faWa mun Allah yana tare da masu ha?uri" Beelal Win ya faWa cikin in,innarsa sai dai lokaci guda murmushi ya maye gurbin zubar hawayensa.Sosai Fatima ta ji daWi har wata ?wallar farinciki ta ciko idanunta ganin murmushi a fuskar Beelal.



"Baiwar Allah, ki daure ku tafi daga nan da gaske masu gidan basa son a musu bara " Ya faWa yana sanya hannu a aljihunsa ya fito da naira Wari ya mi?awa Beelal.

"Mu fa ba bara muke ba, wurin Ammi na muka zo gidan nan" Beelal ya faWa yana maida hannunsa mai lafiyar baya alamar ba zai karSi kuWin da mai gadin ke mi?o masa ba.


"Eh ba bara muke ba na zo wajen Hajiya LaWifa ne kuma ?ar uwata ce" Fatima ta faWa tana kallon mai gadin da ke kallonta baki sake jin wai wajen ?ar uwarta ta zo a wannan haWaWWen gidan, bare ma kuma ya san mutanen gidan sun tsani nakasashshe hakan ne ma ya sanya basa son a musu bara.


"Ka sanar da ita ?anwarta ce Fatima daga Mazari, ?auyen Kazaure" Muryar Fatima ta katse masa tunani.

Shiru ya Wan yi yana nazari kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya sanya hannu a aljihunsa ya fito da wayarsa, ya shiga nemo sunan Hajiya LaWifa saboda ya san ita mace ce mai sau?in hali ba kamar sauran matan gidan ba,sai da ta kusa katsewa sannan aka Wauka.

"Assalamu alaikum" Muryar Hajiya LaWifa ta doki kunnen Beelal da Fatima saboda wayar a handsfree aka sanya ta.


Amsa sallamar mai gadin ya yi sannan ya ce

"Hajiya kina da ba?i"

"Ba?i kuma?" Ta tambaya da mamaki a muryarta saboda ita dai ta san ba su yi da kowa zai zo ba, bare ma yanzu gidan nan nasu da ba kowa ake son ya shiga ba, ita ba ta so ma ace ana nemanta saboda gudun matsala.

"Eh ta ce wai sunanta Fatima daga Mazari ?auyen Kazaure"

"Fatima kuma? " Ta tambaya kana jin muryarta ka san hankalinta ya tashi.


"Eh ai ta ce ?anwarki ce"Ya faWa yana kallon Fatimar.

"Innalillahi wa inna ialaihir raji'un na shigesu" Ta faWa a zuciyarta a fili kuma ta ce

"Ita kaWai ce?"


wannan tambayar da ta yi ta Wagawa Fatima hankali hakan ya sanya ta yi saurin maida kallonta kan Beelal da ke jingine da jikin get Win.

"Ita da Wanta" Ya faWa kamar mai jin tsoro, dan ya san dokar gidan ta ?in nakasashshe, kuma ya san dai tun da ?ar uwarta ce ba za ta kasa sanin yaron yana da nakasa ba.


" Kar dai ita da Beelal?" Ta faWa hankalinta a tsananin tashe, dan ta san shikenan yau kuma sai abin da hali ya yi domin ta shiga gagarumar matsala...






MMN AFRAH=?
?>?p?=??




*BILAL*



NA



MAMAN AFRAH



FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Da sunan Allah mai rahma mai jin ?ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.



Page 7?? ?'?8??


Cikin tashin hankali ta mi?e tsaye ?irjinta na dukan tara-tara dan yadda take ji ya fi ?arfin dukan uku-uku.Ba ta san ma ta katse wayar ba saboda ruWewa da firgicin da ta tsinci kan ta a ciki, tana ta rayawa a ranta cewa yau sai dai Allah ya fitar da ita amma tana cikin tashin hankali da damuwar da babu iyaka.


"Haba Fatima ya aka yi kika taho ba tare da kin sanar mini ba, haba ?ar uwata tabbas na san kin kasa samun nutsuwa na rashin zuwana, shi yasa kika zo duk da ni ma hankalina ba a kwance yake ba na rashin samun wayarki amma zuwanki wajena tamkar ki tsomani a tafashashshen ruwan zafi ne saboda tashin hankalin da zan shiga dalilin hakan, gashi babban tashin hankalin ma kika taho da Beelal bayan kin san irin muguwar tsanar da suka yiwa nakasa" Hajiya LaWifa ta faWa a fili tsoro na bayyana ?arara a fuskarta, zarya ta fara tana ta son ta samo mafita dan kwata-kwata ma bata san ta yadda za su shigo gidan ba tsoronta Waya ma a ce wani ya gan su to fa ta shiga uku tsundum!


?aran wayarta ne ya dawo da ita daga zaucewa da faWar magangaun da take, tana dubawa ta ga sunan mai tsaron ?ofa Saro -Saro kamar yadda ta rubuta.Tsabar ruWewa ma sai ta kasa Waga wayar har kiran ya katse, yana katsewa wani ya sake shigowa ?aran da wayar take yi haWe suke da bugun da zuciyarta ke yi.Haka dai ta yi ta maza ta Waga wayar ta kara a kunne hannunta har karkarwa yake jikinta sanyi ?alau.



"Hajiya suna nan fa a tsaye kuma da na ji kiran ya katse na Wauka ma za ki sake kira" Ya ce cikin girmamawa.


"Mai...mai tsaron ?ofa ka taimaka min kar kowa ya gan su, ina zuwa akwai abin da zan yi" Ta faWa kamar za ta fashe da kuka kai da jin muryarta ka san tana cikin damuwa fargaba haWe da tashin hankali.

Jin muryarta kaWai ya sanya jikin Fatima yin sanyi tabbas ko da ace ba ta ga Yayarta ba jin muryarta kaWai ta san tana cikin wani hali, a halin yanzu ji take kamar ta kama Beelal su koma inda suka fito, sai dai ba halin yin hakan domin ko kuWin motar komawar basu da shi.



"To Hajiya in sha Allah babu wanda zai gan su, daga waje ma suke ko cikin get Win ban shigo da su ba" Ya faWa yana waiwaya bayansa yana ?arewa gidan kallo dan tabbatar da babu wanda ya taho ko kuma wanda ya hango su.


"Yawwa ina zuwa bari zan kira ka" Ta faWa a hankali kamar mai raWa -raWa ta yanke kiran tana kalle -kalle a falon nata dan gaskata babu wanda yake jin ta, duk da ta san ita kaWai ce.


Hajiya LaWifa na kashe wayar ta tafi da sauri ta buWe labulen window ta le?o ?asa da yake a sama take sai ta shiga ?arewa ko ina na gidan kallo.Babu kowa domin kowa yana can part Winsa kuma kowacce ?an aikinta na Sangarenta dan haka sai da ta tabbatar babu kowa ta saki labulen sannan ta dawo cikin falon nata.Cikin sauri ta sakko falon ?asa babu kowa a falon sai ?aran AC da TV suna ta aiki dama Nasira ta bari tana canja labulayen falon.Wayar Nasira ta shiga kira ringing Win wayar na bugawa da bugun da zuciyarta ke yi, bugu Waya biyu a na uku ta Waga.


"Assalamu alaikum Hajiya barka da warhaka"Nasira ta faWa cikin girmamawa.

"Nasira ki buWe kunnenki ki ji abin da zan faWa miki Hajiya ta faWa a maimakon amsuwar sallamar, dan ita burinta kawai ta san yadda za a yi da su Fatima ba tare da wani ya gan su ba dan ko kaWan ma ba ta fatan hakan.


"Ina jinki Hajiya"


"Ki Wakko kayanki na aiki set Waya ki saka a cikin leda ki zo Sangarena yanzu -yanzu" Cewar Hajiya LaWifa har lokacin a firgice take dan ta san matsawar labarin nan ya kai kunnen sirikarta to babu tantama wata?ila ma a yau Win nan a warware igiyoyin aurenta.



"Hajiya kayan aikina kuma?" Nasira ta tambaya cike da mamaki, dan a iya saninta dai Hajiya bata taSa bu?atar hakan ba.


"Haba Nasira haka na faWa kamar yadda kika ji, ki yi sauri ki zo yanzu kuma kar ki bari kowa ya gani"


"Toh Hajiya gani nan zuwa" Cewar Nasira ba dan ta gamsu da abin da uwar Wakin nata ta faWa ba, dan gabaWaya mamaki ya gama cika mata rai da zuciya.

Cikin sauri Hajiya LaWifa ta katse wayar tana sauke ?ar ?aramar ajiyar zuciya, dan tana ganin ta Wan fara samun mafita duk da ba a kai ga inda gizo ke sa?ar ba.

Nasira kuwa ganin Hajiya ta katse kiran ta saka wayar a cikin aljihun rigarta ta aiki dan uniform ne da su gabaWaya ?an aikin sai dai kowace matar gidan ?an aikinta da ban sannan kalar uniform Win ?an aikinta da ban, kayan ?an aikin Hajiya LaWifa blue ne riga da wando sai dai rigar har gwiwa ake musu da aljihuna a jikinta sai Wan karamin hijabi iya kafaWa amma hijabin ja ne.

Lokar kayanta ta buWe ta Wakko uniform Win, dan uniform Win aikin yawa garesu ana kuma sassake musu haka ta Wakko a wanke tas a goge dan Hajiya LaWifa ba ta son ?azanta kwata-kwata hakan ya sanya suke gyara kayansu tas gwanin sha'awa.A leda ta sanya ta fito daga Wakin, ma'aikatan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login