Showing 9001 words to 12000 words out of 35767 words

Chapter 4 - BEELAL BUK BOOK 1 BOOK COMPLETE BY MAMAN AFRAH.doc

tafi ke kaWai" Ya ce yana ta ?o?arin ganin fuskar Fatima da ta janyo hijabin ya rufe fuskarta.

"Wayyo Allah Wazu na kuSuta yanzu kuma yana son kawo min cikas"Nasira ta faWa a zuciyar ta a fili kuma ta ce


"Eh a wajen get muka haWu da ita Hassana ce fa kamar baka gane ta ba"Ta ce tana wulwulga ido, tare da fatan Allah sa kar ya hango jirginta.

"Hassana fa kika ce? Hassanar kuma ciwon baki take ne da ta kasa min magana kin san ta fa da shegen surutu, amma ko zolata bata yi ba"Ya faWa yana washe baki.


"Ciwon ha?ori take kuma idanunta ma ciwo suke shi ya sa ra rufe fuskar"Ta ce tan Wan zungurin Fatima alamar su tafi tun kafin ya gano su.

"Ikon Allah sai na ga ta ?ara tsawo sannan ji ?afafunta jajir da su kamar wacce fa zo faga indiya"


"Cin man gyaWa ne ya mata yawa shi ne Wanya ta kama ta" Nasira ta faWa tana ?ara zungurin Fatima wacce ta ji?e jagaf da gumi saboda ruWewa sai addu'a take a zuciyar ta.

Haka suka tafi suka bar shi wajen yana ta mamakin yadda aka yi aka haihu a ragaya.


"Fatima ki rage sauri, mu tafi sannu -sannu dan kar a gan mu a zargemu kin san su gidan nan zargi bashi da wahala a wurinsu saboda tsabar rashin yarda" Cewar Nasira su ka ci gaba da tafiya.

Sun kusa kai wa part Win Hajiya LaWifa kawai sai suka hango Hajiya Mariya mahaifiyar mai gidan kuma sirika a wurin su Hajiya LaWifa, sanye take da doguwar riga mai adon duwatsu, kai da ganin rigar ka san ba ?aramin kuWi aka sanya wajen siya ba,ta Waura Wan kwalin rigar sai kuma ta yafa mayafi wanda ya shiga da rigar.Sai tabarau a fuskarta?an aikinta guda biyu suna take mata baya sai wata tafiyar ta?ama take tana hura hanci.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil idan matar nan ta gano mu yau ?aryarmu ta ?are"Cewar Nasira tana zare idanu.


"Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu ma ba za ta gan mu ba" Fatima ta faWa cikin raWa.

"Baki san matar nan ba wallahi, kawai mu bi jikin flowers mu Suya idan sun wuce sai mu fito tun da ba hanyar get suka nufa ba Sangaren sauran matan gidan za ta je" Nasira ta faWa tana Wan waiwaya inda za su Suya gabanta na lugude.




Cikin flowers suka shiga suka laSe, gabaWayan su a tsorace suke dan kar asirinsu ya tonu, gashi dole dai sai su Hajiya Mariyar sun wuce ta gaban flower da suka ratse suka Soye a ciki dan hanyar part Win Hajiya Nuratu suka nufa ita ce wacce ke da tsohon ciki a yanzu kuma ita ce ake ji da ita tamkar nama Waya a miya ake kuma tarairayarta kamar ?wai.Har Hajiya Mariya ta kusa gota flower kamar wanda aka dakatar da ita sai kawai ta tsaya a setin inda su Nasira suka laSe, aikuwa nan da nan zukatansu suka shiga lugude tamakar ana daka hatsi a turmi.Dan hatta numfashinsu sai da suka dakata da sha?a saboda suna ganin kamar idan ta jiyo za ta san da zaman su a cikin flowers Win.


Hajiya Mariya kwa fuska a haWe ta sanya hannu ta gyara zaman gilashin fuskarta, kafin cikin izza ta buWe baki ta ce.

"Nasira! Fito daga maSoyarki"

?irjin Nasira ne ya bada wani sautin dimm har wani fitsari ta ji yana ?o?arin ?wace mata, su kuma sauran ?an matan da ke yiwa Hajiyar aiki mamaki suke a ina Hajiya ta ga Nasira da har take mata magana amma ba su yi mamaki ba saboda sun san Hajiyar da idanu kamar na ?wan?walati shegen gani ne da ita.Nasira kwa jin Hajiyar ta ce ta fito duk da hankalinta a tashe yake sai ta sanya hannu da danne cinyar Fatima alamar kar ta tashi, tare da mata alama da hannu a kan bakinta alamar ta yi shiru.Dan ta san da ace Hajiya ta gan su dukansu cewa za ta yi su fito amma jin ita kaWai ta ambata sai ta Wan ji sanyi-sanyi a ranta.

Cikin sanyi jiki ta fito daga cikin maSoyar ta bar Fatima a ciki wacce ke tsugunne gabaWaya abin duniya ya isheta, ga tunanin ta bar Beelal a bakin get ga kuma tunanin wannan tsaka mai wuya da suke ciki dan ta fara hasashen da wuya su tsallake siraWi babban tashin hankalinta kuwa bai wuce halin da ?ar uwarta LaWifa za ta shiga idan har asirin nasu ya tonu.Nasira bake -bake ta yi a saitin wurin da ta fito, ta babbake dan kar a hango Fatima dan har rigar Fatima ta Wan le?o sai dai fatan kar Hajiya ko ?an rakiyarta ta su gani.Wurwurga ido ta shiga yi kana ganinta ka san bata da gaskiya da ma ?an magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake.

"Keee Nasira! Shin wai dodanniya kika Waukeni da duk lokacin da za mu haWa hanya da ke sai kin Suya ko kuma kike sinne kai, kai wani lokacin ma ina tahowa kike sauya hanya ko kin Wauka ba na sane da ke yanzu ma na hango shigarki maSoyarki wato ga aljana kin gani"

Wata bayyananiyar ajiyar zuciya Nasira ta sauke, wacce da Hajiya ta lura sai ta yi zaton al?awarin yanka Nasira aka yi aka fasa saboda irin ajiyar zuciyar da ta sauke mai ?arfi.


Idanu Nasira ta rufe tare da ware su cikin sauri tana ta ?o?ari harhaWa kalmomin da za ta yiwa Hajiyar bayani, dan ba ?aramin daWi ta ji ba jin Hajiya lokacin shigarta cikin flower ta ganta, bata hangosu suna tahowa ba, Allah ne ya rufi idanunta ba ta hango Fatima ba.

"Ba da ke nake magana ba" Cewar Hajiyar cikin Sacin rai.

"A'a ba haka bane Hajiya dan Allah ki yi ha?uri, kawai dai ina ratse miki hanya ne dan baki girma da kuma matsayi, saboda rumfa sha shirgi kike, sannan kuma sawun giwa ya taka na ra?umi ba na so mu ke haWa hanya da ke dan ba girma da matsayinki bane haWa hanya da mu Wiyan talakawa wanda muke samun mafaka daga arzi?i da Waukakar da Allah ya muku" Cewar Nasira cikin girmamawa.

Wani murmushi ne ya bi ta kan Sacin ran da ke kwance a kan fuskar Hajiyar har ha?oran makarta guda biyu da ke jikin manyan ha?oranta na gabasuka bayyana, wani daWi ne ya ziyarci ran Nasira dan ta lura ha?arta ta cimma ruwa da ma babu abin da Hajiya Mariya ke so sama da a koWa ta a wasa ta tamkar wu?a a wurin washi.

"Allah sarki ?ar nan ai ban san haka bane, jeki abinki ai da ma bin na gaba bin Allah"Ta faWa tare da juya wa ta kalli ?an aikin nan nata guda biyu ta ce

"To iyayen gulma da tsigudidi da baku san girmama na gaba ba saboda tarbiya bata isheku ba kuka tsatstsareni da ido"

Saurin sadda kan su ?asa suka yi dan sun san yanzun nan ran su in ya yi dubu zai Saci in ma ba a raba su da aikin su ba saboda korar ma'aikaci a gidan ba abu bane mai wahala.

"Godiya nake Hajiya Allah ?ara girma" Nasira ta faWa tana juyawa ta Wan fara tafiya domin barin wurin dan bin umarnin Hajiya Mariya, ganin idanunt basa wurin da Fatima ke Soye bare ta ankara da rigar Fatima da ta Wan fito.

Gaba ta yi cikin izza da ta?ama suka nufi Sangaren Hajiya Nuratu.Nasira ganin sun sha kwana ta dawo ta ce Fatima ta fito su tafi.Sai da suka shige get Win Sangaren Hajiya LaWifa sannan suka tsaya suna maida numfashi tamkar wanda suka yi tseran gudu.

"Mu yi sauri mu tafi cikin gidan Hajiya kar wata daga cikin ?an aikin Sangarenta su gan mu kin san kowa yana iya yin komai a kan kuWi, bar ganin ?an aikin Sangaren Hajiya LaWifa ne a ciki wallahi muddin suka gan mu sai sun faWa saboda irin tarin alherin da aka yi al?awari za a baowa wanda ya kawo cewa wani ba?o ya shigo gidan nan.Dan duk wanda kika gani a cikin gdn nan to mutanen gidan ne ko kuma masu yiwa mutanen gidan hidima amma bayan su ba a so kowane bare ya shigo cikin gidan nan"


"Saboda me??? Kuma menene dalilin su na yin hakan?" Fatima ta jefawa Nasira tambayar dan bata so t nunawa Nasira cewar ta san dalilin yin hakan duk da ba komai t sani ba dan ta lura abin yanzu ya zarce wanda ta sani.


"Ba mu da wani lokaci mu tafi kawai, za ki ji dukkan komai daga bakin ?ar uwarki" Nasira ta faWa tana kama hannun Fatima suka nufi cikin sashen Hajiya LaWifa.



Beelal tun da aka rufe get Win nan yaron ya tsaya abin tausayi, sai waige-waige yake dan Mai tsaron ?ofa ko ta kan sa bai bi ba saboda yana tsoro sannan yana jiran kiran Hajiya LaWifa ta bada umarnin yadda za a yi da yaron. A gefe Waya ma dai babbar rashin nutsuwar da ke tattare da shi rashin sanin su Nasira sun tsallake rijiya da baya ko kuma shin afka ciki. Tagumi Beelal Win ya zabga da hannunsa mai lafiyar yana ta tunanin halin da Mamarsa take ciki duk da yaro ne amma ya san dai Mamarsa na cikin wani hali dan yana jin irin wayar da ake bugowa Mai tsaron ?ofa da yadda ya ga duk hankalin kowa a tashe amma Mamarsa an tafi da ita. Yana nan tsaye sai ya hango wani kare ya fito daga cikin wani get da ke gaba da gidan da suka zo.Ganin karen ba?i??irin da jajayen idanu hakan ya sanya Beelal jin wani mugun tsoron karen gashi unguwar ta masu hannu da shuni ce babu kowa a layin kowa yana cikin gida, idanun Beelal ne suka kawo ruwa ganin karen kamar ma wurinsa ya nufo ga wata sar?a a ?afar karen da gani a Waure yake ya cire Waurin ya kamo gabansa.Kafin karen ya ?araso Beelal ya fara waiwayen wurin da zai shiga ya Soye saboda kar karen ya cutar da shi dan babu ?afar da zai ceci kan sa wajen gudu saboda yadda ?afar guda Waya take kamar a shanye sannan kuma a lan?washe.

Ganin babu wurin da zai fake hakan ya sanya ya matsa jikin get Win gidan da suka zo ya shiga bubbugawa dan ko Mai tsaron ?ofa zai kawo masa Wauki ya taimaka masa, bugun yake da hannun hagun Winsa mai lafiyar dan Wayan na daman shi ma a lan?washen yake. Mai tsaron ?ofa kwa yana jin bugun ?ofar kuma ya san Beelal ne ke bugawa, amma bai yi wani yin?urin buWewa ba, saboda bai san ya mai zai cewa yaron ba kuma yana gudun tonuwar asiri kar wani ya ga yaro a zargeshi da wani abu dan shi wallahi bai shirya rasa aikinsa ba wanda yake taimakonsa wurin taimakon iyaye da iyalansa.Dan haka mirsisi ya yi tusar ango amma a ransa tausayin yaron ne fal.

"A...a...bu...We...min...ga ...ga... ka...ka...re nannnn" Ya faWa da fashewa da wani kukan mai ban tausayi.

Jin kalamansa ya sanya Mai tsaro ?ofa nufo ?ofar da niyyar taimaka masa amma kuma sai ya hango Waya daga cikin ma'aikatan gidan ya nufo wurinsa hakan ya sanya ya dakata, amma a ransa ji yake kamar ya buWe ya Wakko yaron ko ma mai zai faru ya faru.

Beelal kwa da ke ta bugun ?ofa jin ba a buWe ba ya ce

"Wayyo Allah na" Cikin in'innarsa.

Cikin ikon Allah sai ya hango wasu samari guda biyu sun fito daga gidan da karen ya fito sun taho a guje, karen kuwa hangosu da ya yi sai ya fasa nufar wurin Beelal ya mi?e kwalyar layin a guje, samarin suka mara masa baya.Dur?ushewa Beelal ya yi a wurin yana maida numfashi har lokacin tsoro ne fal a cikin ransa dan ya mugun tsani kare. Yana a hakan ya hango samarin nan sun dawo da karen nan sun kamo shi, suna zuwa za su wuce sai idanunsu ya sauka a kan Beelal wanda ficewarsu Wazu basu lura da shi ba saboda hankalinsu na a kan karen nan.

"Kai ji wani yaro kyakkyawa da shi" ?ayan wanda ke ri?e da sar?ar da ke Waure a wuyan karen ya faWa.


"Kai wannan yaro kamar ba a Nigeri'a ba" Cewar Waya, yana juyawa ya sanya bakinsa a kunnen Wayan ya masa raWa.

"Baabaa yaron nan fa mu tafi fa shi Wakinmu da gani zai yi daWin harka ka dai gan shi ?arami babu zancen tonon asiri"

"Kuma fa wallahi ka kawo shawara, da ganinsa bashi da galihu, mu kuma da ma irinsu muke so wanda iyayensu ke wasarere da su" ?ayan ya faWa yana ?yal?yala dariyar mugunta.

" Eh ai in har iyaye basa kulawa da yaransu to fa gayu ba za su yi ?asa a gwiwa ba wajen kai musu farmaki wala mace ko namiji, dan mu ba fyaWen ?ananan yaran ba, ba kuma lalata ?a?a mazan ba" Cewar Wayan lokacin sun ?araso wurin Beelal da ke dur?ushe, yana ?ara tattakura ganin sun dawo da karen da ya firgitashi Wazu.


"Ikon Allah Baabaa ai nakasashshe ne" ?aya ya faWa yana ?walalo idanu waje.

"Dalla can kai fa gara ne, to ai ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba"

Dariya suka yi su duka sai Wayan ya ce

"?an yaro ya sunanka, kuma mai kake a nan baka san masu gidan nan su suka Waurewa jahilci tsantsa ba, basa son masu nakasa su raSe su ba amma ka zo ka zauna musu a ?ofar gida"


"Zo mu je gidan mu ka zauna mu baka biskit da alewa har da madara" Cewar wanda aka kira da suna Baabaa.

"Mamana ta faWa min kar in bi mutumin da ban sani ba, kuma kar wanda ya bani abu na karSa, kuma ko waye ya ce in buWe wandona ma kar na buWe kuma in faWa mata duk wanda ya yi hakan" Beelal ya faWa cikin in'innarsa yana kallon su.

" Kai! Ka ga uwa mai tunani ko? Wato duk da ta barka wasarere ashe ta bar maka makaman da za ka ya?i masu hali irin namu" Cewer Wayan yana kallon Waya.

"Gaskiya na sarawa matar nan ko da ba warin kaifin ba, wato dai tana faWawa yaronta idan masu satar yara za su yaudaresa da alewa da biskit kar ya karSa, ka san wasu yaran idan aka ce mu je cikin gidan can in baka alewa tuni za su bika saboda shegen kwaWai, sannan ta faWa masa kar ya cire wanda wato saboda irinmu masu lalata yara maza idan mun ce cire wanda mu fitar maka ciji sai su fidda amma ka ji ta koya masa darasi"


"Eh mana gashi kuma ?arami amma ya iya haddace abubuwa kuma ga nakasa magana ma ba ya iya yin ta"

Motocin gidan Alhaji Husaini Ado mai kuWi da suka hango sun karyo layin a sukwane, hakan ne ya basu damar cikawa rigarsu iska ba tare da sun samu damar cewa yaron nan ya bar wajen ba ga motocin gidan nan, saboda sanin halinsa na ?in nakasashshe.

Beelal kuwa ganin sun juya da sauri sun bar wurin sai hankalinsa ya kwanta dan shi ba maganarsu ba ma yake tsoro karen da ke hannunsu yana wani dalalo harshensa yawu na zuba shi ne abin da ke bashi tsoro.Hango wasu rantsattsun motoci guda uku sun shigo layin su ne suka matu?ar Waukewa Beelal hankali saboda kyawunsu da kuma yanayin yadda suke fafara gudu tamkar tamkar motar ?an kwana-kwana za ta kashe gobara.Baki sake yake kallon motocin.

Alhaji Husaini Ado mai kuWi ne kishingiWe a cikin motar da ke tsakiya yana Wan bin layin anguwar da kallo yana Wan sakin tsaki jefi-jefi.Hango wani yaro dur?ushe a ?ofar gidansa abin ya bala'in Waga masa hankali, cikin sauri ya mi?e zaune tare da daidaita zamansa kan mazaunansa dan da a ringishe yake.Idanunsa ne suk sauka a kan hannun Beelal marar lafiyar da ke lan?washe, kafin idanunsa su gama tantance abin da ya gani suka ?arasa kan lan?washashshiyar ?afar Beelal.Wani uban ashar ya yi tare da yiwa direban motar wata uwar tsawar da ta sanya ya ja wani uban birki da ?arfi...



MMN AFRAH=?
?>?p?=??



d'?d'?d'?d'?d'?d'?



*BEELAL*


=ئ?=ئ?=ئ?=ئ?=ئ?=ئ?



NA



MAMAN AFRAH



FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Da sunan Allah mai rahma mai jin ?ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.


*This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* =?
?=?
?=?
?

Page 1?? 1?? ?'?1?? 2??



Waigawa Nasira ta yi hagu da dama ta ga babu kowa, shi ma mai tsaron ?ofar waige-waigen yake kamar yadda ita ma take yi.Sai da ta tabbatar ba kowa sannan ta ce.


"Mai tsaron ?ofa Hajiya LaWifa ce ta...


"Yanzu ta kirani ta faWa min komai" Ya katse ta daga maganar da take son faWa masa.

"Yawwa to ina ba?uwar take?" Ta tambayeshi cikin raWa-raWa dan shi kaWai ta gan shi kuma ma duk fa babu kowa dole ta yi takatsan tsan saboda tsaro amma akwai tsoron ma.


"Ki shiga cikin Wakina ga ta nan zuwa" Ya faWa yana kallon Nasira, cikin sauri ta yi wuf ta faWa Wakin mai tsaron ?ofa da ke kusa da get Win ba tare da kowa ya gan ta ba.


?ofar ya kama da hannunsa ya Wan buWe ?ofar da yake mayar da ?ofar ya yi ya kara dan kar wani ya zo bazata ya gan su.Yana buWewa ya le?a kan sa sai da ya tabbatar babu kowa a wajen sannan ya ce


"Fatima shigo ta zo" Ya faWa a hankalin.

"To" Cewar Fatima dan gabaWaya ma bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login