Showing 24001 words to 27000 words out of 35767 words

Chapter 9 - BEELAL BUK BOOK 1 BOOK COMPLETE BY MAMAN AFRAH.doc

da za su tafi na Beelal ne da ya cire shi ne aka bashi aron na Hameedar ya sanya, suka bar wannan Win a nan amma wai takalmin ta Wauka ko ajiyewa bata yi wai saboda shiririta takalmin ma take yiwa kuka tana kiransa da suna Beelal" Ta faWa tana kallon Hameeda da ta kwantar da kanta a kafaWar Baban nata sai faman ajiyar zuciya take yi.


"Allah sarki Hameedan Baba da ace ina nan suka tafi da sai sun tafi da ke saboda ba na son abinda zai saka ki a damuwa ba" Ya faWa yana shafa kanta.


"Ikon Allah to ai ka san dai da ace da dama babu yadda za a yi Fatima ta tafi ta barta saboda ita ma ko kaWan bata son raba Beelal da Hameeda yanzun ma dole ce ta sanya ta yi haka, kuma kwana biyu kaWai za su yi su dawo"


"Tun da kin ce haja shikenan amma kin san ko da ace wuni Waya za su yi dole ta shiga damuwa" Ya faWa yana kallon Mamar Hameeda da ke linke kayan wanki.

"Yaushe suka taf...


Sallamar da aka yi ne ya katse masa maganar da yake ?o?arin yi, a tare suka amsa mai sallamar ne ya shigo cikin gidan yana wani Waga kai tare da hura hanci.


"Sannu da zuwa Yaya" Ummar Hameeda ta fala cikin girmamawa.

Maimakon ya amsa sai ya maida kallonsa kan Wan uwansa ya ce

"Shin baka samu sa?ona ba Hamisu na ji ka shiru kokwa wannan ce ta hanaka zuwa " Ya faWa yana kallon Umma da ta sunkuyar da kai.


"Ka yi ha?uri Yaya wallahi shigowarsa gidan kenan tun da ya tafi gona da sanyin safiya sai yanzu ya dawo kuma ban kai ga faWa masa sa?on ba ka shigo, amma ka san da ace na faWa masa da tuni ya zo" Ta ce har lokacin kanta a ?asa saboda girmama wan mijin nata da take.

"Sannu ishashshiya da mai wato baki ma faWa masa ba saboda kin raina ni, kuma kina son rabani da Wan uwana"


"Haba Yaya ya za ka ce haka, baka ga yadda jikina ma yake ba ko kayan jikina ban kai ga canjawa ba, wallahi shigowata kenan" Cewar Baban Hameeda yana ta ?o?arin nunawa Yayan nasa gaskiyar matarsa.


"Ni kwa na ga ko kayanka baka kai ga canjawa ba amma ka iya Waukan ?ar gwal ka Worata a cinya kana wani shafa kanta kamar wanda ka samu jikin zomo" Ya faWa yana sanya hannu a babbar rigarsa yana kuma aikawa Hameeda wani mugun kallo dan ya tsani yarinyar a rayuwarsa, yana ji a ransa duk duniya babu wanda ya tsana sama da ita saboda tsallan baWaken da ta yi na dirowa duniya ta shiga tsakaninsa da gadon da yake so ya yi na Wan uwansa saboda jahilci irin nasa ba ma ya tunanin bai san gawar fari ba.

"Dama da ace ke namiji ce da tuni na daWe da aika ki lahira, to saboda ke mace ce kuma na san dai mace ba za ta samu gado ba kamar yadsa namiji zai yi babakere da gado ba amma duk da hakan kema ina jin tamkar in sha?eki in aika da ke inda ba a dawo wa" Ya faWi hakan a zuciyarsa har lokacin bai daina hararar yarinyar ba duk da a kan idanun mahaifanta duk da an ce wai mutuwa ma na tsoron idon mahaifi.




Shiru Baban Hameeda ya yi tare da sunkuyar da kansa ?asa ganin irin kallon tsanar da Wan uwan nasa ke jifan ?ar tasa Waya tilo wannan abu na bashi mamaki da Waure masa kai maimakon a ce ya samu irin wannan ?iyayyar daga wajen wasu amma sai gasho daga wajen Wan uwansa da yake da shi tilo a duniya yake samun ?in jininsa kuma masoyiyarsa ?arsa Hameeda wacce ita kaWai ya haifa ita kaWai kuma yake gani ya ji daWi, amma bai san mai ya sa Yayansa yake nuna mata ?iyayya haka ba duk da shi Win ma ba wai ya tsira bane yana nuna masa ?iyayyar daga shi har matarsa Hafisa amma yana jurewa sai yanzu kuma da Allah ya azurtashi da haihuwa bayan irin shekaru da ya Wauka yana neman haihuwa bai samu ba amma maimakon Yayansa ya?aunace ta ko dan shi ma bashi da Wa ko Waya amma sai ya Wauki karan tsana ya Wora mata "Wallahi Yaya na dawo ne na samu tana bu?atar kulawar saboda tana ta kuka a kan Beelal yaron nan na wajen Idrisu sun tafi Kano, ka san ta sha?u da yaron sosai shi ne nake lallashinta"


"Eh lallai fa a lallasheta, yaron wajen Idrisu ko yaron Fatima, Idrisun da ya ce ya bar mata yaron ta ri?e ita kaWai saboda nakasar da ke jikin yaron, ko ma ba haka ba yanzu ina Idrisun yake da kake danganta yaron da shi, mutumin da ya yi watsi da su kowa ya san yafi shekara ba Si zo garin nan ba kai sai dai ma an danganta da sama da shekara ba ya yi shekara biyu baya garin nan ka ga kuwa sai dai ka kira shi Wan Fatima ban da ma rashin hankali ku bar yarinya tana kusantar yaron da babu mai ?aunarsa duk garin nan daga uwarsa sai ku, yaro da ?afa kamar ta ?adangare duk a lan?washe hannu...

"Haka Allah ya halicceshi" Cewar Hameeda da ta Wago kan ta daga kafaWar mahaifinta.

Da sauri mahifin nata ya sanya hannu ya rufe mata baki.


"Barta ta faWa koya mata aka yi tarbiyar da uwarta ta bata kenan raina na gaba da yiwa na gaba rashin kunya, idan ka ga dama ka aika min buhun gero da na wake zan siyar in yi amfani da kuWin dama shi ne kiran da nake maka" Yana kai ?arshen maganar ya juya fuuu ya fice daga gidan ba tare da ya jira cewar kowa ba.





GabaWaya sai aka rasa mai cewa komai a cikinsu, Umma da ke ?o?arin yiwa Hameeda faWa a kan abin da ta yi duk da yarintar ta amma akwai bu?atar a nusar da ita faWawa babba magana haka duk da cewa dai dai ta faWa kuma Fatima ce ke kowa musu cewa idan ana tsokanar Beelal Win su faWi hakan. Baban Hameeda kwa mutuwar zaune ya yi jin bu?atar da Yayan nasa ya zo masa da ita, saboda sauransa gero da wake kowanne buhu WaiWai kuma shi ma niyya yake ya kai su kasuwa saboda yana so ya siyi taki saboda aikin gona da zai yi, amma babu yadda zai yi haka zai Wauka ya bashi saboda gudun magana da kuma son zama lafiya, in ya so ko rance ya yi ya kashe wutar gabansa.






_HAJIYA LA?IFA_


Tana ta faman gudu -gudu sauri-sauri ta iso Sangarenta cikin ikon Allah bata haWu da kowa ba, dan tsoronta Waya kar a ga fitarta ace wani mugun abu ta fita yi saboda hana haihuwar Hajiya Nuratu lafiya dan wannan yana cikin dalilin da ya sanya aka hana su fita daga gidan saboda kar wata ta je ta yi wani mugun ?ulli a kan cikin da Hajiya Nuratun ke Wauke da shi. Tana shigowa falon ta samu Nasira na ta kaiwa da komowa alamar tana cikin damuwar fitar da Hajiya LaWifa ta yi saboda matsala sannan tana tsoron tonuwar asirin nasu ma saboda wani dalili.

Ganin Hajiya LaWifa ya sanya ta taho wajenta tana son ?arin bayani.


"Hajiya ya na ganki haka? Ya kika dawo? Ko an ga Beelal Win" Ta jefa mata tambayar da son za?uwar jin amsar.

GyaWa mata kai ta yi tana ?o?arin bata amsa sai suka hango Fatima a mugun kiWime tana sakkowa daga saman benen tana haWa matakala bibbiyu. Da sauri Hajiyar ta nufeta ta kamata ganin duk ta rikice


"Yaya ki sakani na tafi neman Beelal, shin ya aka yi har aka barni nake bacci shin ina na samu dama da kwanciyar hankalin da bacci ya samu nasarar Waukana?" Ta faWa tana sakin kuka tare da ?o?arin ?wace kan ta daga ri?on da ?ar uwar tata ta mata.


"Ki kwantar da hankalinki Fatima b...

"Haba Yaya ta ya zan kwantar da hankalina bansan inda Beelal yake ba wallahi sai na fita koma me zai faru ya faru, in yaso daga can ma idan na samu Beelal Win mu koma inda muka fito hakan zai fi mana kwanciyar hankali" Ta katse Yayar tata cikin kuka da ?araji.


"Fatima ni kain???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a yanxu daga wajen nake har na fita domin tafiya nemansa Mai tsaron ?ofa ya sanar da ni ya samo shi, shi ne dalilin da na dawo domin ya sanar da ni yana tare da Beelal Win kuma baccin da ya Waukeki suma kika yi da kika farfaWo numfashinki ya dawo gangar jikinki shi ne kuma baccin ya Wauke ki muka kai ki Waki"


"Dan Allah da gaske an ga Beelal?" Ta faWa tana kallon Nasira dan ta tabbatar mata dan kar Yayar tata ta Soye mata dan hankalinta ya kwanta.


"Wallahian ganshi ni ma yanzu ta shigo nake tambayarta" Cewar Nasira har da murmushin farinciki.

Rungume Yayar tata ta yi, sannan ta sake ta ta je ta rungume Nasira saboda farinciki, dan yanzu ganin Nasira take kamar ?ar uwarsu saboda yadda ta rufa musu asiri kuma ta damu da damuwarsu.


_Mai tsaron ?ofa_


Yana bakin get da butarsa yana ta alwala da ba dan ya yi sallah yake yi ba dan dai kawai yana so kowa ya fice ya barsa aikuwa daga ya hango wani sai ya fara wankin fuska wani sa'in idan wani ya zo sai ya fara shafar kai, kowa zai fice daga cikin mazan masu aiki sai ya masa magana, sai da ya tabbatar kowa ya fice sannan ya dangwarar da butar. ?akinsa ya shiga ya Wakko wata babbar riga da yake shimfiWa da ita jakar kayan su Beelal Win ya sanya a ciki, Beelal dai kallonsa yake kawai dan har abincinya bashi amma ya ce masa ya ci abinci a gidan tsohuwar wannan. Sai danya sanya takalman Beelal Win da ke ajiye a inda ya sille, sai kuma ya ce


"Taso ka kwanta a kan rigar nan" Kallon rashin fahimta Beelal Win yake masa sai ya ce cikin in'innarsa.


"A ka zan yi bacci?"

"A'a a ciki zan kai ka wajen Mamarka"


"Mama?"


"Eh ?ulleka zan yi dan kar a ganka, ko da an ganmu za a Wauka ko kayan wanki ne, sauri zan yi kafin a fito daga sallah in kai ka"

Jin haka Beelal ya tashi ya kwanta a kan rigar haka Mai tsaron ?ofa ya ?ulle rigar da sauri ya le?o sai da ya tabbatar babu komai sannan ya sungumo Beelal haba wa ?afa me na ci bam baki ba, haka ya ringa zabga sauri gabaWaya a kiWime yake, yana tafiya addu'a tana ta kai kawo a bakinsa kamar zai ari baki.

Yana shiga part Win Hajiya LaWifa ya zuba a guje har sai da ya ga ya danganta da ?ofar falon.

"Assalamu alaiku" Ya faWa yana ta waiwayen bayansa, da hanzari suka taho su duka ukun Hajiya LaWifa kawai ya mi?awa ?ullin hannunsa bai jira komai ba ya kuya cikin sauri, su ma da suka karSa sai suka shige ciki ba ma su tsaya a falo ba sama suka haye da shi suna ta murna.




Da sauri har ana rige -rigen buWe rigar da Hajiya ta kunce ?ullin. Zabura Beelal ya yi yana kilkila dariya, su ma dariya suka shiga yi Fatima har da ?wallar farinciki.


"Mama kin ga an kawo ni a ?ulle?" Ya faWa cikin in'innarsa yana ri?e hannunta.

"Kamar kayan wanki ba" Ta faWa tana dariya. Rungumeta ya yi yana ta farinciki, sannan ya sake ta, ya rungume Hajiya LaWifa ya ce.


"Ammi na daWe ban ganki ba" Ya faWa yana rungumarta.


MAMAN AFRAH=?
?=??>?p?



d'?d'?d'?d'?d'?d'?


*BEELAL*



=ئ?=ئ?=ئ?=ئ?=ئ?=ئ?


NA



MAMAN AFRAH



FCW


Da sunan Allah mai rahma mai jin ?ai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.

*This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* =?
?=?
?=?
?

_Masoyana ina muku fatan alkairi a ko ina kuke, masu aiko min da sa?o ta hannun wasu na ftn alkairi sa?on ku na zuwa ina gdy, masu kirana a waya a kan labarin Beelal dk ngd muku. Tabbas na ji daWi kuma na godewa Allah da ya bani ikon rubuta labarin nan wanda wasu suka sanar mini hakan na faruwa sosai da sauran ?an uwansu wasu kuma ?a?ansu, ina fatan wanda suke aikata haka ga waWanda Allah ya tauye musu wani Sangare na halittar jikinsu ba dan baya son su ba sai dan haka yake so ya gansu saboda baiwa da kuma iko da ?udirarsa za su faWakantu su daina dan su ma basu da ikon canja halittar ubangiji._

2?? 3?? ?'?2?? 4??


"Ni ma na daWe ban ganka ba my son"


"To me yasa bakya zuwa?" Ya faWa cikin In'innarsa


"Bamu labarin inda Mai tsaron ?ofa ya kai ka" Cewar Fatima dan kawar da tambayar da ya yiwa Hajiya LaWifa.


Nan ya shiga basu labari tun daga zuwan da Alhaji Husaini ya yi, har dawowarsa da Mai tsaron ?ofa ya dawo fa shi. Sosai suka ji tausayin yaron, har da ?wallarsu jin irin marin da Alhajin ya masa ko tausayinsa bai ji ba bai kuma dubi ?an?antarsa ba kawai dan baya son ganin masu nakasa a ?ofar gidansa. Sannan sun jinjina tare da yabawa tsohuwar da ta taimaki Beelal ba tare da ?yara ko hantara ba kuma tare da ta ?yamaci nakasar da ke tare da shi ba, sun sanya mata albarka tare da fatan alkairi a gareta da kuma mata fatan yin kyakkyawan ?arshe da makoma mai kyau wannan shi ne addu'ar da suka mata kuma kowane Wan adam zai yi fatan dace da waWannan abubuwa.



Sun ci abinci suna aka kunnawa Beelal kallo a tv yake yi, yans kallon ?wallon ?afa domin Beelal akwai son ?wallo, duk da kasancewar ?afarsa Waya a lan?washe amma kuma wani lokacin ko ?wallon ledar sai ya sanya Mamarsa ta haWa masa yana bugawa da ?afar mai lafiya saboda kasancewarsa mutum mai ?aunar ?wallon ?afa (Ball) Dan har irin ?aramar nan ta roba garesa burinsa kullum a siya masa kayan ?an ball yake sawa a jikinsa.


"Ammi ina so a siya min kayan ?an ball" Ya faWa cikin in'innarsa ya katse musu hirar da suke yi.



"Aikuwa dole in sayi kayan ball ba ma kala Waya ba" Cewar Ammi tana murmushi, duk a lokacin suna kokawa junansu damuwarsu da halin da suke ciki dan Nasira ta daWe da komawa Sangarensu, ita Fatima rashin miji a kusa tsawon fin shekara ma ita kuma matsalar uwar mijinsu a kan rashin haihuwarta da bata sake ba sai tai ta kiranta juya.


"Allah saki a aljanna Ammi" Ya faWa cikin in'innarsa yana nuna farincikinsa a fili.


"Amin ya rabbi yarona"

"Wato ni ba a min addu'ar ba" Mama ta faWa tana kallonsa.

"Harda ke Mama" Ya faWa yana sanya hannun hagun Winsa mao lafiyar ya rufe fuska irin yana jin kunyar nan.

"BuWe idon" Cewar Mama tana dariya.

"Ammi ba fa balla kaeai nake so ba har da wa?a inaso" Ya faWa yana kallon Ammi.

"Inyeee lallai yaron nawa ka ce abu biyu kake so kenan?"

"Eh mana amma ai ni tun da ban iya magana ba, kuma ?afata Waya ce mai lafiya ba zan iya yin wa?ar ba ma in ana yi, kuma ba zan iya rawa ba in ana yi, balla ma da ?afa Waya nake gwadawa wataran sai ki ga na faWi, kuma ko a makaranta idan yara na wasa basa yi dani ko ball na ce zan shiga hana ni suke sai dai in yi ni kaWai ko mu yi da Hameeda" Ya faWa idanunsa na cikowa da ?walla. Tasowa Ammi ta yi ta dawo kujerar da yake zaune ta zauna a kuss da shi ta sanya hannu ta dafa kafaWarsa ta ce.


"Haba Beelal shi fa Allahn da ya halicceka ya fi kowa sonka yana sonka a haka a duk yadda ya halicci bawansa yana son sa da kuma ?aunarsa, dan mutane suna nuna maka kyama kar ka damu domin babu wano wanda zai iya canja maka halitta, kake dagewa da karatu na islamiya da boko kamar yadda na sanka"


Kai ya gyaWa mata alamar gamsuwa da bayaninta sai kuma ya ce.


"A islamiyarmu ma ranar nan Malamin mu zai karSi harda wai dan ya ce in karato shi ne kowa ?an ajin suke min dariya wai in'ina zan yi ta yi, haka ya ce sai ma karanta, wai dan na ce Am...am...amma yatasa'alun" Shi ne ya ?wala min bulala a kaina su kuma suke min dariya wai yelelo mai baki a lan?washe ban iya karatu ba, malamin namu ma gida ya korani sai Mama ce ta ce in yi ha?uri.




" Ya faWa cikin in'innarsa.


"Allah sarki ka ?ara ha?uri ka ji duk mai nema yana tare da samu anko ina yake a duniya, kuma komai zai wuce wata rana sai labari" Ta faWa tana jin wani mugun tausayin irin halin da yaron ya tsinci kansa a ciki, mutane basu da hankali da tunani wasu, ace Allah ya yi halittarsa shin kai wanene da zaka kusheta?


"Assalamu Alaikum" Nasira ta shigo falon Hajiya bakinta Wauke da sallama, da yake da Wan ?arfi ta yi kuma wurin na Wan amsa kuwwa sai sallamar tata ta katse musu maganar, jin Nasira na magana sai Hajiya ta sakko ?asa.

"Nasira lafiya dai, na ga yanzu tara ma ta wuce?"


"Eh Alhaji ne ya sanar a faWawa kowa yana taro a Sangaren Hajiya Nuratu kin san ta sauka"


"Kai ma sha Allah, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login