Showing 12001 words to 15000 words out of 35767 words

Chapter 5 - BEELAL BUK BOOK 1 BOOK COMPLETE BY MAMAN AFRAH.doc

nutsuwa a tsorace take.

Ledar su ta Wakko tare da kama hannun Beelal ta ce mu je ko?"

"Fatima ban da shi fa, ke kaWai za ki shigo" Cewar mai tsaron ?ofa.


Idanu Fatima ta zaro jin furucin mai tsaron ?ofa ta ce


"Kamar ya ban da shi?"


"Haba Fatima ya kike Sata lokaci akwai gagarumar matsala fa, tun da aka ce ki shigo shi ma ai za a shigo da shi"


"A'a ba zan taSa tafiya ina bar shi a nan ba, idan wani abun ya faru da shi fa?"


"Mai tsaron ?ofa wai ya na ji shiru, ka san fa haWarin da ke tattare da wannan kasadar da zan yi" Nasira ta faWa lokacin da ta le?o daga Wakin jin shiru ba?uwar ba ta shiga Wakin ba.

" Tana zuwa " Cewar mai tsaron ?ofa, lokacin da ya juya yana kallon Nasira kafin daga bisani ya maida hankalinsa kan Fatima da ta ?i shigowa.


"Babu abin da zai faru da shi ki taho kawai zan kula fa s...

?aran kiran da ya shigo wayar Mai tsaron ?ofa ne ya katse masa maganar.Ganin sunan Hajiya LaWifa ya gani da sauri ya Waga ya kara a kunnensa.

"Mai tsaron ?ofa sun taho ne?"Cewar Hajiya LaWifa.


"Yanzu za su taho Hajiya sai dai wai ba za ta iya tafiya ta barshi ba"

"Sa wayar a handsfree na mata magana"

Da sauri ya sanya wayar a handsfree

"Fatima ki yi ha?uri ki taho shi ma za a san yadda za a yi a shigo da shi" Muryar Hajiya LaWifa ta doki kunnen Fatima.

"To Yaya" Cewar Fatima ba dan ta so ba.

"Mama ki je ni ina nan, ni ma an ce za a shigo da ni" Beelal ya faWa cikin in,innarsa yana mai yin murmushi dan shi daWi yake ji an ce za su shiga gidan.


"To Beelal" Fatima ta faWa tana shafa kan sa, ?walla na cikowa da hawaye.Haka ta barshi tana ta wai wayensa har dai Mai tsaron ?ofa ya nuna mata Wakin da za ta shiga.

Tana shiga Nasira ta mi?a mata kayan dan har ta fitar da su daga leda gudun Sata
lokaci.Da mamaki Fatima take kallon kayan dan bata fahimta ba


"WaWannan kayan su za ki saka domin yin Sadda kama" Cewar Nasira tana juya mata baya dan ta sanya kayan.Haka Fatima ta yi sauri ta sanya kayan, tsaf kayan suka zauna a jikinta dan dama ba ?iba gareta ba dan wani ma sai ya yi zaton ba ta da aure.

Tana gama saka wa suka fito daga cikin Wakin, haka suka baro bakin get Win suka kama hanya kowacce na addu'ar isar su lafiya.

Fatima sai ?arewa gidan kallo take kamar ba shi ba, ga tarin motoci nan masu kyan gaske wasu kuma a lulluSe suke.Mamaki take a rant a cewa duk tarin dukiyar gidan nan amma babu kwanciyar hankali a cikinsa, tabbas arzi?i ba shi ne ban kwana da damuwa ko tashin hankali ba sau tari dai ka ga wanda bashi da cin yau bare na gobe ya fi wanda ke da tarin dukiya saSun kwanciyar hankali amma wasu sai suke ganin babu wanda ya kai mai kuWin samun waWannan abubuwan.Tun da yana da dukiya ai babu wani abu da zai rasa.

Sun Wan yi nisa da bakin get kaWan sai kuwa suka ga shugaban masu ban ruwan flowers a gabansu kamar wanda aka jefo shi.
???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?

"Nancy manyan ?asa fa gari baki Waya" Ya faWa yana washe baki.


"Akwai magana ne sauri nake, kai sai ka tare mutum kuma ni ina da abin yi ba yanzu muka gaisa ba"Ta faWa gabanta na faWuwa.


"Kinsan ba na gajiya da kallonki, dama ina can zaune ina jiran dawowarki sai kuma na hango kin ruSanya, ma'ana kun zama ku biyu ke da kika tafi ke kaWai" Ya ce yana ta ?o?arin ganin fuskar Fatima da ta janyo hijabin ya rufe fuskarta.

"Wayyo Allah Wazu na kuSuta yanzu kuma yana son kawo min cikas"Nasira ta faWa a zuciyar ta a fili kuma ta ce


"Eh a wajen get muka haWu da ita Hassana ce fa kamar baka gane ta ba"Ta ce tana wulwulga ido, tare da fatan Allah sa kar ya hango jirginta.

"Hassana fa kika ce? Hassanar kuma ciwon baki take ne da ta kasa min magana kin san ta fa da shegen surutu, amma ko zolata bata yi ba"Ya faWa yana washe baki.


"Ciwon ha?ori take kuma idanunta ma ciwo suke shi ya sa ra rufe fuskar"Ta ce tan Wan zungurin Fatima alamar su tafi tun kafin ya gano su.

"Ikon Allah sai na ga ta ?ara tsawo sannan ji ?afafunta jajir da su kamar wacce fa zo faga indiya"


"Cin man gyaWa ne ya mata yawa shi ne Wanya ta kama ta" Nasira ta faWa tana ?ara zungurin Fatima wacce ta ji?e jagaf da gumi saboda ruWewa sai addu'a take a zuciyar ta.

Haka suka tafi suka bar shi wajen yana ta mamakin yadda aka yi aka haihu a ragaya.


"Fatima ki rage sauri, mu tafi sannu -sannu dan kar a gan mu a zargemu kin san su gidan nan zargi bashi da wahala a wurinsu saboda tsabar rashin yarda" Cewar Nasira su ka ci gaba da tafiya.

Sun kusa kai wa part Win Hajiya LaWifa kawai sai suka hango Hajiya Mariya mahaifiyar mai gidan kuma sirika a wurin su Hajiya LaWifa, sanye take da doguwar riga mai adon duwatsu, kai da ganin rigar ka san ba ?aramin kuWi aka sanya wajen siya ba,ta Waura Wan kwalin rigar sai kuma ta yafa mayafi wanda ya shiga da rigar.Sai tabarau a fuskarta?an aikinta guda biyu suna take mata baya sai wata tafiyar ta?ama take tana hura hanci.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil idan matar nan ta gano mu yau ?aryarmu ta ?are"Cewar Nasira tana zare idanu.


"Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu ma ba za ta gan mu ba" Fatima ta faWa cikin raWa.

"Baki san matar nan ba wallahi, kawai mu bi jikin flowers mu Suya idan sun wuce sai mu fito tun da ba hanyar get suka nufa ba Sangaren sauran matan gidan za ta je" Nasira ta faWa tana Wan waiwaya inda za su Suya gabanta na lugude.




Cikin flowers suka shiga suka laSe, gabaWayan su a tsorace suke dan kar asirinsu ya tonu, gashi dole dai sai su Hajiya Mariyar sun wuce ta gaban flower da suka ratse suka Soye a ciki dan hanyar part Win Hajiya Nuratu suka nufa ita ce wacce ke da tsohon ciki a yanzu kuma ita ce ake ji da ita tamkar nama Waya a miya ake kuma tarairayarta kamar ?wai.Har Hajiya Mariya ta kusa gota flower kamar wanda aka dakatar da ita sai kawai ta tsaya a setin inda su Nasira suka laSe, aikuwa nan da nan zukatansu suka shiga lugude tamakar ana daka hatsi a turmi.Dan hatta numfashinsu sai da suka dakata da sha?a saboda suna ganin kamar idan ta jiyo za ta san da zaman su a cikin flowers Win.


Hajiya Mariya kwa fuska a haWe ta sanya hannu ta gyara zaman gilashin fuskarta, kafin cikin izza ta buWe baki ta ce.

"Nasira! Fito daga maSoyarki"

?irjin Nasira ne ya bada wani sautin dimm har wani fitsari ta ji yana ?o?arin ?wace mata, su kuma sauran ?an matan da ke yiwa Hajiyar aiki mamaki suke a ina Hajiya ta ga Nasira da har take mata magana amma ba su yi mamaki ba saboda sun san Hajiyar da idanu kamar na ?wan?walati shegen gani ne da ita.Nasira kwa jin Hajiyar ta ce ta fito duk da hankalinta a tashe yake sai ta sanya hannu da danne cinyar Fatima alamar kar ta tashi, tare da mata alama da hannu a kan bakinta alamar ta yi shiru.Dan ta san da ace Hajiya ta gan su dukansu cewa za ta yi su fito amma jin ita kaWai ta ambata sai ta Wan ji sanyi-sanyi a ranta.

Cikin sanyi jiki ta fito daga cikin maSoyar ta bar Fatima a ciki wacce ke tsugunne gabaWaya abin duniya ya isheta, ga tunanin ta bar Beelal a bakin get ga kuma tunanin wannan tsaka mai wuya da suke ciki dan ta fara hasashen da wuya su tsallake siraWi babban tashin hankalinta kuwa bai wuce halin da ?ar uwarta LaWifa za ta shiga idan har asirin nasu ya tonu.Nasira bake -bake ta yi a saitin wurin da ta fito, ta babbake dan kar a hango Fatima dan har rigar Fatima ta Wan le?o sai dai fatan kar Hajiya ko ?an rakiyarta ta su gani.Wurwurga ido ta shiga yi kana ganinta ka san bata da gaskiya da ma ?an magana sun ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake.

"Keee Nasira! Shin wai dodanniya kika Waukeni da duk lokacin da za mu haWa hanya da ke sai kin Suya ko kuma kike sinne kai, kai wani lokacin ma ina tahowa kike sauya hanya ko kin Wauka ba na sane da ke yanzu ma na hango shigarki maSoyarki wato ga aljana kin gani"

Wata bayyananiyar ajiyar zuciya Nasira ta sauke, wacce da Hajiya ta lura sai ta yi zaton al?awarin yanka Nasira aka yi aka fasa saboda irin ajiyar zuciyar da ta sauke mai ?arfi.


Idanu Nasira ta rufe tare da ware su cikin sauri tana ta ?o?ari harhaWa kalmomin da za ta yiwa Hajiyar bayani, dan ba ?aramin daWi ta ji ba jin Hajiya lokacin shigarta cikin flower ta ganta, bata hangosu suna tahowa ba, Allah ne ya rufi idanunta ba ta hango Fatima ba.

"Ba da ke nake magana ba" Cewar Hajiyar cikin Sacin rai.

"A'a ba haka bane Hajiya dan Allah ki yi ha?uri, kawai dai ina ratse miki hanya ne dan baki girma da kuma matsayi, saboda rumfa sha shirgi kike, sannan kuma sawun giwa ya taka na ra?umi ba na so mu ke haWa hanya da ke dan ba girma da matsayinki bane haWa hanya da mu Wiyan talakawa wanda muke samun mafaka daga arzi?i da Waukakar da Allah ya muku" Cewar Nasira cikin girmamawa.

Wani murmushi ne ya bi ta kan Sacin ran da ke kwance a kan fuskar Hajiyar har ha?oran makarta guda biyu da ke jikin manyan ha?oranta na gabasuka bayyana, wani daWi ne ya ziyarci ran Nasira dan ta lura ha?arta ta cimma ruwa da ma babu abin da Hajiya Mariya ke so sama da a koWa ta a wasa ta tamkar wu?a a wurin washi.

"Allah sarki ?ar nan ai ban san haka bane, jeki abinki ai da ma bin na gaba bin Allah"Ta faWa tare da juya wa ta kalli ?an aikin nan nata guda biyu ta ce

"To iyayen gulma da tsigudidi da baku san girmama na gaba ba saboda tarbiya bata isheku ba kuka tsatstsareni da ido"

Saurin sadda kan su ?asa suka yi dan sun san yanzun nan ran su in ya yi dubu zai Saci in ma ba a raba su da aikin su ba saboda korar ma'aikaci a gidan ba abu bane mai wahala.

"Godiya nake Hajiya Allah ?ara girma" Nasira ta faWa tana juyawa ta Wan fara tafiya domin barin wurin dan bin umarnin Hajiya Mariya, ganin idanunt basa wurin da Fatima ke Soye bare ta ankara da rigar Fatima da ta Wan fito.

Gaba ta yi cikin izza da ta?ama suka nufi Sangaren Hajiya Nuratu.Nasira ganin sun sha kwana ta dawo ta ce Fatima ta fito su tafi.Sai da suka shige get Win Sangaren Hajiya LaWifa sannan suka tsaya suna maida numfashi tamkar wanda suka yi tseran gudu.

"Mu yi sauri mu tafi cikin gidan Hajiya kar wata daga cikin ?an aikin Sangarenta su gan mu kin san kowa yana iya yin komai a kan kuWi, bar ganin ?an aikin Sangaren Hajiya LaWifa ne a ciki wallahi muddin suka gan mu sai sun faWa saboda irin tarin alherin da aka yi al?awari za a baowa wanda ya kawo cewa wani ba?o ya shigo gidan nan.Dan duk wanda kika gani a cikin gdn nan to mutanen gidan ne ko kuma masu yiwa mutanen gidan hidima amma bayan su ba a so kowane bare ya shigo cikin gidan nan"


"Saboda me??? Kuma menene dalilin su na yin hakan?" Fatima ta jefawa Nasira tambayar dan bata so t nunawa Nasira cewar ta san dalilin yin hakan duk da ba komai t sani ba dan ta lura abin yanzu ya zarce wanda ta sani.


"Ba mu da wani lokaci mu tafi kawai, za ki ji dukkan komai daga bakin ?ar uwarki" Nasira ta faWa tana kama hannun Fatima suka nufi cikin sashen Hajiya LaWifa.



Beelal tun da aka rufe get Win nan yaron ya tsaya abin tausayi, sai waige-waige yake dan Mai tsaron ?ofa ko ta kan sa bai bi ba saboda yana tsoro sannan yana jiran kiran Hajiya LaWifa ta bada umarnin yadda za a yi da yaron. A gefe Waya ma dai babbar rashin nutsuwar da ke tattare da shi rashin sanin su Nasira sun tsallake rijiya da baya ko kuma shin afka ciki. Tagumi Beelal Win ya zabga da hannunsa mai lafiyar yana ta tunanin halin da Mamarsa take ciki duk da yaro ne amma ya san dai Mamarsa na cikin wani hali dan yana jin irin wayar da ake bugowa Mai tsaron ?ofa da yadda ya ga duk hankalin kowa a tashe amma Mamarsa an tafi da ita. Yana nan tsaye sai ya hango wani kare ya fito daga cikin wani get da ke gaba da gidan da suka zo.Ganin karen ba?i??irin da jajayen idanu hakan ya sanya Beelal jin wani mugun tsoron karen gashi unguwar ta masu hannu da shuni ce babu kowa a layin kowa yana cikin gida, idanun Beelal ne suka kawo ruwa ganin karen kamar ma wurinsa ya nufo ga wata sar?a a ?afar karen da gani a Waure yake ya cire Waurin ya kamo gabansa.Kafin karen ya ?araso Beelal ya fara waiwayen wurin da zai shiga ya Soye saboda kar karen ya cutar da shi dan babu ?afar da zai ceci kan sa wajen gudu saboda yadda ?afar guda Waya take kamar a shanye sannan kuma a lan?washe.

Ganin babu wurin da zai fake hakan ya sanya ya matsa jikin get Win gidan da suka zo ya shiga bubbugawa dan ko Mai tsaron ?ofa zai kawo masa Wauki ya taimaka masa, bugun yake da hannun hagun Winsa mai lafiyar dan Wayan na daman shi ma a lan?washen yake. Mai tsaron ?ofa kwa yana jin bugun ?ofar kuma ya san Beelal ne ke bugawa, amma bai yi wani yin?urin buWewa ba, saboda bai san ya mai zai cewa yaron ba kuma yana gudun tonuwar asiri kar wani ya ga yaro a zargeshi da wani abu dan shi wallahi bai shirya rasa aikinsa ba wanda yake taimakonsa wurin taimakon iyaye da iyalansa.Dan haka mirsisi ya yi tusar ango amma a ransa tausayin yaron ne fal.

"A...a...bu...We...min...ga ...ga... ka...ka...re nannnn" Ya faWa da fashewa da wani kukan mai ban tausayi.

Jin kalamansa ya sanya Mai tsaro ?ofa nufo ?ofar da niyyar taimaka masa amma kuma sai ya hango Waya daga cikin ma'aikatan gidan ya nufo wurinsa hakan ya sanya ya dakata, amma a ransa ji yake kamar ya buWe ya Wakko yaron ko ma mai zai faru ya faru.

Beelal kwa da ke ta bugun ?ofa jin ba a buWe ba ya ce

"Wayyo Allah na" Cikin in'innarsa.

Cikin ikon Allah sai ya hango wasu samari guda biyu sun fito daga gidan da karen ya fito sun taho a guje, karen kuwa hangosu da ya yi sai ya fasa nufar wurin Beelal ya mi?e kwalyar layin a guje, samarin suka mara masa baya.Dur?ushewa Beelal ya yi a wurin yana maida numfashi har lokacin tsoro ne fal a cikin ransa dan ya mugun tsani kare. Yana a hakan ya hango samarin nan sun dawo da karen nan sun kamo shi, suna zuwa za su wuce sai idanunsu ya sauka a kan Beelal wanda ficewarsu Wazu basu lura da shi ba saboda hankalinsu na a kan karen nan.

"Kai ji wani yaro kyakkyawa da shi" ?ayan wanda ke ri?e da sar?ar da ke Waure a wuyan karen ya faWa.


"Kai wannan yaro kamar ba a Nigeri'a ba" Cewar Waya, yana juyawa ya sanya bakinsa a kunnen Wayan ya masa raWa.

"Baabaa yaron nan fa mu tafi fa shi Wakinmu da gani zai yi daWin harka ka dai gan shi ?arami babu zancen tonon asiri"

"Kuma fa wallahi ka kawo shawara, da ganinsa bashi da galihu, mu kuma da ma irinsu muke so wanda iyayensu ke wasarere da su" ?ayan ya faWa yana ?yal?yala dariyar mugunta.

" Eh ai in har iyaye basa kulawa da yaransu to fa gayu ba za su yi ?asa a gwiwa ba wajen kai musu farmaki wala mace ko namiji, dan mu ba fyaWen ?ananan yaran ba, ba kuma lalata ?a?a mazan ba" Cewar Wayan lokacin sun ?araso wurin Beelal da ke dur?ushe, yana ?ara tattakura ganin sun dawo da karen da ya firgitashi Wazu.


"Ikon Allah Baabaa ai nakasashshe ne" ?aya ya faWa yana ?walalo idanu waje.

"Dalla can kai fa gara ne, to ai ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba"

Dariya suka yi su duka sai Wayan ya ce

"?an yaro ya sunanka, kuma mai kake a nan baka san masu gidan nan su suka Waurewa jahilci tsantsa ba, basa son masu nakasa su raSe su ba amma ka zo ka zauna musu a ?ofar gida"


"Zo mu je gidan mu ka zauna mu baka biskit da alewa har da madara" Cewar wanda aka kira da suna Baabaa.

"Mamana ta faWa min kar in bi mutumin da ban sani ba, kuma kar wanda ya bani abu na karSa, kuma ko waye ya ce in buWe wandona ma kar na buWe kuma in faWa mata duk wanda ya yi hakan" Beelal ya faWa cikin in'innarsa yana kallon su.

" Kai! Ka ga uwa mai tunani ko? Wato duk da ta barka wasarere ashe ta bar maka makaman da za ka ya?i masu hali irin namu" Cewer Wayan yana kallon Waya.

"Gaskiya na sarawa matar nan ko da ba warin kaifin ba, wato dai tana faWawa yaronta idan masu satar yara za su yaudaresa da alewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login