Showing 27001 words to 30000 words out of 257774 words
Chapter 10 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt
gani ba...
Take taji wani b’angare na zuciyarta na raya mata, karki janye k’udirinki, kar Ki d’agawa d’aya daga cikinsu k’afa.. Ruin them all, expose them and take them down.... Ta k’arashe tana mai goge ragowar hawayen da suka zubo mata, sallaman Umaima ya sanyata saurin mik’ewa had’ida saita kanta kaman babu abinda Ke wakana...
“Ke Wai baki gajjiya da zaman d’aki...Kinga taso mu tafi b’angaren Giwa d’iyanin muci dinner a cen....” Umaima ta fad’i daga nan yanda take tsaye...
Saida ta d’an rausayar da idanunta kana tace “Yo naga dai gidan sarauta ai zaman d’aki da kulle ya gada ko ba haka ba... Kinga dama ke nake jira muje na duba jikin Zahra, tana raina tin d’azu...”
Umaima ta d’an girgiza kai kurum tana mai janyo hannunta tana fad’in “Iyanin Ki amsa kiran Ya Mahmood..!”
Saida k’irjinta ya buga jin tace ta amsa kiran Mahmood, harga Allah ta mance Wai yana kiranta... Banda guntun gulma mai zai mata, yaji da abubuwan da suke gabansa, tabbas da ace yasan wacece ita da kuma k’udirin da ya kawota wannan masarauta ko mai irin sunananta bazaiso ji ba balle ya buk’aci ganinta...
Wani tapkeken parlor suka soma shiga, babu kowa cikinsa sai manya manyan standing ac daketa faman aikinsu suna huro ni’imtaccen sanyi... Hotuna ne a jere a parlorn sahu sahu na ahalin Sarki AbdulJabbar mai rasuwa....
Muhibbah tai k’uriwa hoton da yake daga center... Yaran Sarkin ne su duka hud’u cikin hoton, dukansu cikin shiga irinta mulki da sarauta, k’asaitaccen murmushi irinta ‘ya’yan sarauta kwance saman fuskokinsu, idanunta suka waiga gefe kad’an nan ta hango wani hoton, su duka hud’u amma wannan suna yarane masu k’ananun shekaru wanda tsaf ta gane fuskokinsu domin kaw sanin da tai masu kenan....Tai K’uri tana duban hoton zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri....Ji take tamkar ta rarumi koma minene ta tarwatsa hoton dashi, so take ta finciko hoton daga ma’ajiyinsa ta zane fuskokinsu tai masu lamba mai muni wanda suma har abada bazai shafe daga tarihin rayuwarsu ba kaman yanda sukaima nata rayuwarta lamba...Take ta dunk’ule hannayenta duka biyu tana mai ci gaba da sakin huci a hankali....
Sam bata ko kula da Umaima da ta fice ta wani k’ofar tana amsa kira a waya ba...
Waige waige ta soma sanda ta tabbata babu kowa cikin parlorn sai ita kad’ai saiko na’urorin nasara.... Nan ta hangi matakalan haurawa bene daga gefe, ta soma takawa a hankali ta nufi benen dikda tsananin bugu da k’irjinta keyi, ita kanta ta sani abinda takeyi abune mai matuk’ar had’arin gaske....
Abinka da gini irinta sarauta nan ta hangi dogon corridor da yake open, ga k’ofofi birjit iyaka ganinka.... Ta rasa ta wane k’ofar zata soma bi, lumshe idanunta tai tana ambato Allah da neman taimakonsa, Ta bud’e idanunta a hankali tana jin k’warin gwiwa na zuwa mata... Cen ta hangi wani k’ofa da yake daga center, zuciyarta tafi amintar da tabi wannan k’ofa... A hankali cikin sand’a had’ida d’an sauri ta nufi k’ofan, ta d’an tura a hankali tana lek’awa, shima d’in wani hamshak’in parlor ne maiji da tsari... Tabbas ana baza mulki a wannan gida, Ta fad’i haka cikin zuciyarta.... Cikin sand’a ta kutsa Kai cikin parlorn, saidai shigarta Keda wuya Ta soma sauraron wasu muryoyi.... Tai saurin k’arasawa yanda take sauraron maganan, tabbas muryar Giwa ce dan bazata tab’a mance wannan azzalumin murya a dodon kunnenta ba, tana iya sauraro muryan d’aya daga cikin yaranta suna tattaunawa saidai bazatace ga wanene suke maganan ba cikin yaran nata dan gaba d’aya yaran murya kala guda Ke garesu, na Mahmood ne kad’ai ta d’an banbanta dan dik ya fisu gwab’in murya mai cikeda k’warjini... Hakan ya tabbatar mata da d’aya daga Cikin k’annensa Giwa ke tattaunawa....
Bataji gaba d’aya abinda suke tattaunawa akai ba amma tabbas taji Giwa na basa umarnin aiwatar da wani abu.... Jin kaman ana k’ok’arin tab’a k’ofa ya sanyata saurin sad’ad’owa ta fito k’irjinta na tsananin bugu.... Sauri sauri ta nufo dogon open corridor d’in nan tana tafe tana waigawa baya bata ankara ba saiji tai ta bige mutum ta fad’o cikin jikinsa....
SameenaAleeyou 📚
[6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*013*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ido cikin ido suke duban juna itada Yazeed, ga tsananin bugu da k’irjinta keyi, tamkar ta tsatta ma wannan fuskar tasa miyau haka takeji... Shiko sosai ya had’e rai yanai mata wane irin duba.. K’aran tafiyar mutane da suka soma jiyowa ya sanya tsoro ya kuma bayyana a fuskar Muhibbah tai k’ok’arin sa kai zata rab’a ta gefen Yazeed saidai tuni ya fizgota sun shige tsakankanin gini hakan yai daidai da d’aukewar wutan lantarki...K’irjinta yaci gaba da bugawa, duhu ya soma shigowa dan haka kana iya ganin mutum amma duru duru, tana iya hango Farin fuskan Yazeed cikin duhun yanai mata alamu da tai shiru....
Zuciyarta taci gaba da tsinkewa sanda taji tafiyar yana nufosu sosai, tai saurin rintse idanunta a hankali yayinda Yazeed yaci gaba da k’are mata kallo from head to toe dan tsaf yana iya ganinta cikin duhun nan dashike shi Allah yayisa mai idon kallon mata...
Giwa ce da Jakadiya suka taho zasu shige wani k’ofar, saida suka d’an tsaya kusan yanda Yazeed da Muhibbah Ke lab’e suna tatauna wasu al’amararsu da suka shafi cikin gidan
Muhibbah najin sanda suka ci gaba da tafiya suka shige wata k’ofar ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali...
Suna shigewa Muhibbah tai saurin matsawa baya tana sakin huci a hankali, lokaci guda take k’ok’arin saka kai zata shige dan ko takan Yazeed bata kuma bi ba tamkar wani babu abinda ya faru...Yazeed da ya kafeta da mayun idanunsa yana k’are mata kallo saurin tare gabanta yai da hannunsa guda kana yace “And just where do you think you are going..? Fad’a min zakiyi mai kikazo yi nan... Wacece Ke....? mai ya kawoki wajen nan..?!”
Banda bugu babu abinda k’irjinta keyi, tsananin tsanarsa ne kwance cikin idanunta, bata d’ago fuskarta ba har lokacin saima bugu da k’irjinta Ke ci gaba da yi..
Mamaki ya cika Yazeed ganin tai masa banza kaman bataji abinda yake fad’i ba.... Wacece ita...? Yai tambayar a zuciyarsa... Ga duhu da ya gauraye wajen saiko hasken walk’iya dake haskawa lokaci zuwa lokaci...
A hankali yake k’ok’arin mik’a hannunsa da niyyan d’ago fuskarta... K’irjinta yaci gaba da bugawa, zuciyarta naci gaba da mata zafi.... K’iris ya rage hannunsa bai sauk’a samar fuskarta ba wayarsa dake aljihun wandonsa ya d’auki ruri... Yai saurin mik’a hannu ya ciro wayar hasken wayar ya haske fuskarsa tarau, tai saurin karkatar da fuskarta sabida tsananin k’yank’yaninsa da ya sauk’o mata dikda Uban gayun dake jikinsa....
A yayinda hankalinsa ya ya karkata kan wayar salulansa Muhibbah ta hangi fad’uwan abu mai kamada sark’a ta mata daga aljihun nasa... Tana ganin sanda ya d’aga wayar yana mai juya baya, hakan ya bata daman silalewa tai saurin d’aukar sarkar tana mai sakar masa muguwar kallo kana ta juya cikin sauri ta fice daga wajen k’irjinta sai bugu yake tamkar ana iza mata guduma....
Sauri sauri ta nufo k’asa zuciyarta bata daina tsinkewa ba, dik wani motsin da zatai sai taji tamkar yanzu ne suka bangaji juna ita da Yazeed, uwa uba hannunta da takeji tamkar ba a jikinta yake ba har yanzu... Ji take tamkar ta guntile hannun ta jefar idan ta tuna sanda ya fizgo hannun nata suka b’oye... Takai dubanta ga hannun nata, sai lokacin ta tina ashe akwai sark’a rik’e a hannun nata... Idan bata b’ata gani ba wannan design d’in jewelry d’in irinsa ta gani a kunnen Rahima yau da safe da suka had’u a k’ofar Bayi...Toh kodai nata ne..? Ya akai yazo hannun Yazeed..? Tambayar dataji na tasowa daga k’asar zuciyarta... Ta saki murmushi a hankali dan ko babu komai ta sami wani abin...
Sanda ta sauk’o k’asa ta tadda kuyangi da dama wannan karon sai kai komo suke, dik wanda tazo giftawa cikin Kuyangin sai sun risina Sun gaidata, itama har ta koya daga wajensu Umaima saidai ta jinjina masu kai murmushi saman fuskarta alamun amsawa... Tana tafe cikin kantamemen parlorn mai tsawo da fad’in gaske ta hango Umaima tsaye daga waje ta cikin glass d’in sliding door.... Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali kana ta nufi k’ofar da take hango Umaima, saidai tana isa jikin k’ofar ta hango Fu’ad zaune saman wasu kujeru na shak’atawa yayi zama irinta masu mulki k’afafu d’aya bisa d’aya, da alama magana sukeda Umaimar...
Fu’ad ya murmusa kad’an kana yace “Kawai tambayarki nake, a ina kika samota...?”
Umaima ta murmusa kad’an itama kana tace “Prince F kenan, ai abin ne ya bani mamaki, naga friends d’ina da dama sukan Zo Masarautar nan, baka tab’a tambayar koda sunayensu ba dikda cewa su sukan damu da zancen Princes d’in Masarautar nan... Kaga kuwa bazakaga laifina ba dan na tambaya kodai kodai....?” Ta k’arashe da sigar zolaya tana kashe masa idanu...
Ya murmusa a hankali kana yace “I can’t deny that she’s kind of.... Beautiful...!” Ya k’arashe yana alamu da hannayensa tamkar wani mai describing irin kyaun da ya hango tattareda ita....
Umaima tai murmushi mai d’an sauti wannan karon kana tace “Prince F kenan kaidai kawai ka nad’ani matsayin campaign director d’inka dan Muhibbah k’anwarmu ce tinda k’anwar Ansar ce...”
“Muhibbah..!” Ya nanata sunan a hankali kana yace “Beloved..!” Yana maganan yana jinjina kai lokaci guda yaci gaba da fad’in “Ta dace da sunanta.....!”
Sabon bugun zuciya ne ya sauk’arwa Muhibbah tai saurin jada baya tana maida numfashi a hankali had’ida lumshe idanunta, wayoyin kanta suna k’ok’arin kwancewa... Anya zata iya k’arasa abinda ta fara... Wata zuciya taceda ita “Ke Saudatu what have you gotten yourself into...?”
Take kuma taji wani b’angare na zuciyar nata na fad’i mata “Toh mahaifinki fah... Ta yaya zaki San asalin abinda ya samesa idan baki dawo ba...? Sannan mahaifiyarki da kika rasa fah.... Dik uk’uba da masifa da kika shiga a baya fah...? Shikenan sunci banza suna rayuwarsu cikin jin dad’i da zaluntar wasu al’umman... Saudatu zaki iya... Zaki iya abinda kika riga kika fara... Tabbas zaki iya...!!”
Da wannan shawari na zuciyarta taji natsuwa na zuwa mata a hankali... Ta waiga gefe ta hangi wata Kuyanga zata shige... K’arasawa tai gareta ta tareta tana tambayarta ko ina d’akin Zahra yake....?
Kuyangar ta nuna mata wani b’angare nan cikin parlorn da shima benen za’a d’ale kana tace “Ta nan ne Rankishi dad’e...” Tai mata nuni da b’angaren benen dake kallon hagu, dashike irin babban matakalan nan ne mai kunne biyu d’aya na kallon b’angaren dama yanda ta sauk’o bada jimawa ba saman d’ayan na kallon b’angaren hagu...
Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Muje ki nuna min....”
Kuyangar ta d’an d’ago tana dubanta kana ta kuma sadda idanunta tana fad’in “Kiyi hak’uri Rankishi dad’e bana d’aya daga cikin amintattun dake haurawa d’akin Gimbiya Zahra’u... Amma idan kika haura d’akin nata a nan yake...”
Jinjina mata kai Muhibbah tai kana tace “Kina iya tafiya..”
Kuyangar ta jinjina kai alamun amsawa kana Muhibbah ta nufi benen kaman yanda Kuyangar ta sanar da ita...
Matsakaicin wajene mai kyaun gaske Shima, Muhibbah ta tsaya daga parlorn tana k’arema wajen kallo, tabbas sai a b’adda mutum b’att ba’aji d’uriyarsa ba a gida irin wannan... D’akuna guda biyu ta hango nan ta nufi d’akin dake daga gefen dama.. Ta d’anyi knocking a hankali sallama saman bakinta... Jin ba’a amsata ba ya sanyata d’an tura k’ofar a hankali... Nan ta hangota kwance saman royal bed da akai ma d’akin ado dashi wanda yake d’an tsurut a tsakiyar d’akin sabida girma da d’akin kedashi... Tai K’uri tana duban yarinyar dake baccinta hankali kwance... Ta tsinci kanta tana mai sakin murmushi, lokaci guda ta shigo d’akin had’ida tura k’ofar a hankali kaman mai tsoron kada ta tasheta...
Muhibbah ta k’araso gaban gadon tana k’arewa Zahra kallo k’aunar yarinyar na kuma shigarta, batasan dalili ba amma dik tsanar da taiwa mahaifin yarinyar bata hango tsanar tattareda yarinyar saima k’aunarta da takeji na shigarta a hankali musamman dataji cewa ta rasa mahaifiyarta, kaman yanda itama ta rasa mahaifiyarta sannan a kusan shekaru irinta Zahran Ta rasa nata mahaifiyar itama... Janyo bargo tai ta rufawa Zahra kasancewar anyi ruwa garin ya d’anyi sanyi kana ta d’auki remote control d’in AC ta rage mata... Lokaci guda ta zauna a gefenta tana dubanta...
A hankali Zahra ke bud’e idanunta har ta bud’esu tarau tana duban Muhibbah dake sakar mata murmushi...
Zahra Ta mik’e sosai ta zauna murmushi saman fuskarta...Kafin ta sami zarafin magana Muhibbah tace da ita “How are you feeling now...?”
Yarinyar ta d’anyi mata K’uri murmushin bai bar fuskarta ba kana tace “Much better...”
Muhibbah ta d’an jinjina kai alamun rashin sabo kana tace “Akwai yanda ke maki ciwo kuma...?”
Kanta ta kuma girgizawa alamun a’a...
“Kin sha maganinki na dare...?”
Take annurin fuskar yarinyar ya d’an d’auke alamun basu shiri da magani...
Muhibbah takai dubanta ga yanda magungunan Ke aje bisa ruwa a gefe, kana ta isa ta d’auko...
Zahra tai raurau kana tace “Paa ke sakani nasha dole... Banson drugs...”
Gefe da ita Muhibbah ta zauna kana tace “Let me teach you something...” Tai maganan tana mai b’alle maganin kana tace “Oya close your eyes now and open your mouth... Just think of your favorite candy, kiyi tunanin shi kike sha... There....!” Ta k’arashe tana mai saka maganin bakin Zahra...
Dik yanda Muhibbah tace Zahra tai hakan takeyi, a haka har Ta ida bata magungunan.... Su duka biyun fuskokinsu ya cika da annuri...
Tsaye yai nan jikin k’ofa yana dubansu... It’s been a while since he saw his daughter as happy as she’s right now, akwai wani murmushi da takeyi wanda tun bayan rasuwar mahaifiyarta bai kuma hangowa a fuskarta ba sai yau.... So yake budurwar da suke tareda Zahra ta juyo yaga fuskarta don bayanta kawai yake hangowa amma sai bugu k’irjinsa keyi a hankali lokaci guda yana hango tsananin Farin ciki dake tattareda d’iyar tasa...
Yai k’asaitaccen murmushi a hankali, bazaiso wani abu ya gifta tsakanin wannan Farin ciki da Zahra Ke ciki ba... A hankali yasa kai kaman zai juya, saidai tuni Zahra ta hangosa... Ta d’an bud’e murya had’ida kiran sunansa...
Dummm!!! Haka k’irjin Muhibbah ya buga...
Zahra taci gaba da fad’in “Paa ka shigo ku gaisa da Aunty Muhibbah...!”
A hakali yake takowa cikin d’akin, cikin takunsa mai cikeda charisma yayinda zuciyar Muhibbah yaci gaba da bugawa da sauri da sauri cikin sakanni... Sai murza sark’ar dake hannunta take ba tareda ta iya koda motsa wuyarta ba balle tai tinanin juyowa....
Tana jin sanda Zahra Ke furta “Aunty Hibbah meet my Paa...!”
Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, bugun zuciyarta ya k’aru.. Batasan ta yanda zata soma juyawa tai idanu hud’u da wannan azzalumi ba and act like nothing ever happened.... Tana tsaka da tinanin ne sallaman Umaima ya katsesu....
Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali...
SameenaAleeyou📚
[6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*014*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Umaima ta shigo tana mai fad’ad’a murmushinta “Yaya barka da shigowa...” Ta fad’i cikeda risinawa...
Jinjina mata kai yai daidai sanda wayar salulansa ta d’auki ruri, abokinsa Turaki ne mai kiran... Dan haka kai tsaye ya juya ya fice daga d’akin...
Muhibbah ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida bud’e lumsassun idanunta... Umaima ta k’araso tana fad’in “Sorry na barki ke kad’ai a parlor Prince F ya rikeni da hira, ashe kin hauro nan...”
Muhibbah ta rausayar da idanu kana tace “Eh mana, kin barni ni kad’ai salon naje na b’ata a wannan k’atoton gidan... Allah yasa ban shige wani wajen ba nai karo da d’akin patient d’ita...”
Umaima da Zahra suka d’anyi tak’aitaccen dariya a tare cikeda jin dad’i kasancewa da juna Umaima na fad’in “Kar ki damu babu wanda zai saceki cikin Masarautar nan...”
Suka kuma darawa a tare
Rahima dake lab’e jikin k’ofa k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi ganin wannan mayyar k’awar Umaimar mai bak’in shishigin tsiya tareda Zahra... Allah ya gani bata k’aunar yarinyar nan.. Bata iya shiga ba sai juyawa da tai zuciyarta na mata zafi...
A b’angaren Yarima Mahmood kaw tinda Turaki ya sanar dashi isowarsa bai kuma dawowa d’akin Zahra ba dan tini ya samu Ubandoma ma na jiransa daga waje, yasan isowar Turakin zai sanar dashi..
Hakan sai yafi wa Muhibbah dan harga Allah batajin tayi shirin fuskantar babba cikin azzulaman ‘ya’yan sarki AbdulJabbar a yau bayan karon da tai da Yazeed da kuma zancen Fu’ad da Umaima da ta sinkaya...
Dik surutun da Umaima da Zahra keyi da alama hankalinta bai taredasu... Tafi bada mahimmanci ga duban k’ofa kaman mai jiran shigowar wani... Cikin zuciyarta take sak’awa, tinda ba Yazeed bane ba kuma Fu’ad bane Giwa Ke tattaunawa da, tabbas da Jamal kenan take tattaunawar, a shi take bada umarnin zartar da wani abu... Mai kenan..? Meye take umartan Jamal yai da wannan kakkausar murya irin haka...? Idan bata b’ata ji ba kaman taji Giwa na cewa kaje ka duba ka gani ko har yanzu na raye... Wannan statement shi take ta nanatawa cikin zuciyarta har lokacinda sukai karo da Yazeed.... Waye Giwa take bada umarnin aje a duba ko Yana nan a raye... Could it be mahaifinta ne...? Kardai Abbanta ne tsawon shekarun nan yana cikin Masarautar nan basu kashe shi ba...? Ya zama dole tabi bayan Jamal taga yanda Giwa ta aikesa...?! Bata ida tinanin ba taji Umaima na dungurinta tana fad’in “Hibbah Wai ina kika tafi munata tambayarki...?”
K’ok’arin saita kanta Muhibbah tai kana tace “Kinsan na baro wayata cen sashen bak’i kuma munyi da Mummy zata kirani toh ko shakka babu nasan tana kan nemata yanzu haka....”
Umaima ta d’an girgiza kai tace “A’a Gaskiya bai kamata ki k’yale Mummy taita kiranki no response ba, zatai tinanin ko wani abin ne ya sameki... Kinsan iyaye da nuna damuwarsu musamman idan sun tura yara makaranta... Ki tashi kije ki d’au wayarki gaskiya...”
Murmusawa Muhibbah tai kana tace “Toh shikenan ga patient d’ina na barta hannunki amana...”
Suka murmusa gaba d’aya kana Muhibbah ta mik’e ta fice Zahra na labartawa Umaima yanda Muhibbah ta bata magani cikin dad’in rai ba tareda taji d’acin maganin ba...
**
Gimbiya Zeenat ce hankice a parlornta na alfarma, bayi guda biyu sai aikin tausan k’afafunta dake bisan manyan pillows na sarauta suke... Shigowar Raheema fuska a tamke yasa Gimbiya Zeenat umartan kuyangin nata da su fice su basu waje... Babu musu kuyangin suka mik’e sukai kaman yanda uwar gijiyar tasu ta umarta...
Raheema ta zauna saman kujera sai cika take....
Aunty Zeenat ta d’ago tanai mata wani irin duba kana tace “Ke