Showing 171001 words to 174000 words out of 257774 words

Chapter 58 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt

abinda Ke damunki ne..?!”

Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali tace “Paa it’s about Aunty Muhibbah.. Do you remember her..?!”

Gyara zamansa sosai yai jin ta ambaci Muhibbah yace “What about her.?!”

Zahra ta d’an kuma muskutawa tace “Paa why’s everyone so curious about her this days.. First it was you, and now...Grandma ta kirani asking questions about her.. Paa I believe she’s a good person... But Maiyasa zata bani mayafi tace na bawa Jakadiya ta yafa..!”

Zuciyarsa Ta kuma tsinkewa, ya aje spoon d’in da yake juyawa cikin mug yana mai kuma tsareta da idanu... Sosai ya gyara zamansa yace “Tell me everything Zahra... Ta bawa Jakadiya mayafi, kuma ma Ke ta bayar tace ki baiwa Jakadiya..?!”

Zahra Ta jinjina kai tace “You remember that day..? Ranan da nace maka ita ta had’a gaba d’aya plans d’inta tace min I should trust her..!”

Mahmood ya jinjina kai yace “I remember..!”

Zahra taci gaba da fad’in “Paa the truth is that ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya ta saka, idan har Jakadiya ta yafa toh Babu halin ta bini Mu fita tare kaman yanda ka umarta kace Jakadiya tamin rakiya...! Toh na bata wanann mayafin Ta yafa muka had’uda Uncle Jamal yace zai assigning wata Hadima Ta min rakiya sabida Jakadiya zatai masa wani aikin...! Toh sai nace masa he shouldn’t bordered zan sami wata cikin Hadimaina tamin rakiya... Paa believe me I didn’t know an hana Hadiman cikin Masarautar nan yafa mayafi mai kyau... It was never my intention na cutar da Jakadiya... A dalilin wannan mayafin nayiwa Jakadiya Duka an ji mata ciwo Paa... All because of me..!” Ta k’arashe cikin rawar murya....

Sosai ya fad’a duniyar tunani, kenan Ta kuma tabbata Muhibbah tanada agenda d’inta cikin Masarautar nan... Why’s she connected to almost everything that’s been happening...? Farko rayuwarsa da Zahra, Raheema da Yazeed.. Taswiran da Baba Wambai ya basa wanda ya tsinci makamancinsa hannunta...Yanzu kuma harda Jakadiya da Jamal..? And if Jakadiya is somehow involved Toh Giwa ma might also be involved tinda yasan matsayin Jakadiya wajen Giwa... Kuma idan hakan Ta kasance zai iya yuwa tasan wani abu gameda ciwon Fu’ad tinda zuwansu asibiti shida Turaki nurse guda ya tabbatar masu cewa matar data shigo da Zahra Ta jima sosai cikin d’akin Fu’ad tana dubasa...Who are you Muhibbah...?! Mai kika shigo yi cikin Masarautar nan..?! Maiyasa kike neman ki tarwatsa ahalinmu..Duk abubuwan da suka faru, everything is pointing directly to you ne... What exactly do want from our family..?!

Har Zahra Ta fice bai fahimci Ta fice ba, sosai yai nisa a duniyar tunani... Idan Muhibbah tanada alak’a da duk abubuwan dake faruwa cikin Masarautar Toh ya zama dole yayi taka tsan tsan dan da alama bata shigo Masarautar ba saida Ta shirya... Babu wanda zai iya tunk’aran masarauta mai girma irin nasu yanda tayi ba tareda shiri ba... Shi mamaki ma abin ya soma basa... Sauri sauri ya haura sama ya kunna na’uran computer d’in yana duban abinda take a daidai lokacin...

Kuangin ne suka shigo nata da abin kari... Ta d’auki fork bayan sun fice tana k’ok’arin bud’e lock d’in k’ofa dashi...
Yayi K’uri yana dubanta yanda take dage k’arfinta gaba d’aya wajen ganin Ta bud’e k’ofar...


Cikin zuciyarta take furta “I really need to escape kafin Giwa ko d’aya daga cikin azzaluman yaranta su cimmani... Nasan mutanen da Abbah yace na taimaka masu suna b’oye cikin Masarautar nan... I need to escape kafin su cimmani..!” Ta k’arashe tana mai kuma dage k’arfinta, saidai abinka da k’ofa mai aminci ko gizau bai ba... Saima karyewa da cokalin yayi... Cikeda takaici tayi jifa da cokalin ta koma cikin d’akin ta zauna dirshan tana kuka mai tsuma zuciya...

**

Huci kurum Jamal yake fitarwa yana mai furta “I knew it.. Since from the beginning ban yarda da yarinyar nan ba Maami... But tinda ita d’in k’awar Umama ce komai yazo cikin sauk’i... Kamota bazai mana wahala ba... Umaima zata sanar damu yanda take rayuwa and believe Maami zan kawo miki ita har nan kiyi yanda kike so da ita... Kiyi gunduwa gunduwa da ita idan kina so... I promise I’d bring her here..!” Ya k’arashe yana mai kuma fitar da huci...

Giwa Ta jinjina kai tace “Na tabbata yarinyar nan koma su waye suka turota ta riga ta gama mana b’arna cikin Masarautar nan... Kuma da alama bata Zo ba saida Ta shirya... Amma zatayi nadama da danasanin sanin wannan masarauta da tayi balle har tayi gangancin shigowa cikinta... Mun gama da wanda suka fita balle ita k’aramar alhaki...


SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*




*66*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Zuwa safiya an samu Ansar ya d’an zama stable saidai har lokacin hawaye basu daina zubowa daga k’uncinsa ba... Cikin zuban hawaye ya kuma duban Mommy yace “Alfarma d’aya zaki min Mommy....! Ki sanar dani su waye suka nemi auren Muhibbah..? Ma waye aka aurar da ita..?!”

Cikin kwantar da kai hawaye na gangaro mata tace “Ansar I’ve no idea they are..! Kuma bana tsammanin shi kansa Yawale yasan daga wata duniya suke...!”

Ansar ya kuma dubanta da tsananin mamaki yana girgiza kansa, ya kasa yarda k’iyayyan da Yawale yakewa Muhibbah har yakai wannan matakin, abinda ko wa mak’iyinka bazakayi ba..! Kan mai zai aurartaga mutanen da babu wanda yasan daga inda suke...

Ya sauk’e wane irin nannauyan ajiyan zuciya yace “Mommy this cant be possible... Dole a nemo Muhibbah kuma dole a warware wannan auren muguntar da akai mata... Yau d’in nan basai gobe ba zan shigar da Yawale k’ara... Wllhi sai na d’auresa kodai ya fito min da Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci...

Mommy kanta dubansa kurum take dan bata tab’a ganin d’an nata cikin yanayi makamancin wannan ba..!

Muryar Hameedah dake gefe tana hawaye suka sinkayo tana fad’in “Baffah ya aurar da Muhibbah ne ga wasu Buzaye... Wanda shi kansa baisan daga Duniyar da suke ba..! Nasan Baffah bai kyauta ba amma dan Allah kayi hak’uri Yaya Ansar kar ka shigar dashi k’ara zai zame min abin gori ne daga cikin gidanmu har izuwa mutanen unguwa... Hamma Ansar nasan baka sona ka aureni... Dole akayi maka, dan Allah naci darajan ‘yan uwantaka... Kada ka tozartani a idon duniya....!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata....

Tausayin yarinyar dasu kansu gaba d’aya duk sai ya kuma rufe Mommy, tasan yarinyar batada laifi mahaifinta ya jawo mata halinda Ta tsinci kanta ciki... Mommy batakaiga magana ba suka sinkayo muryar Ansar yana furta “Bak’in Buzaye..!” Sai yayi Burki ya kuma furta BAK’ON BUZU..!!” Idan bai mance ba Muhibbah ta basa labarin yanda akaita binciken wanene Bak’on Buzu a masarauta...! Duk yanda akayi Wani ne daga Masarautar yazo ya aureta cikin yanayin shiga na b’adda kamanni...! Zasu halak’ata a wannan Masarautar muddin suka fahimci wacece ita... No no bazai bari hakan Ta kasance ba...! He needs to save her..!

Su Mommy gani kawai sukai ya hau fincike igiyar drip yana shirin dirowa daga saman gado...

Mommy ta isa ta rik’esa gam tana fad’in “Ansar lafiya kake...! Ina zaka a haka..?!”

Bai daina fincika ba yake fad’in “Mommy I need to go..! Muhibbah needs me Mommy... Mommy I need to save her... Her life is in great danger...! Mommy rayuwar Muhibbah na cikin had’ari mai munin gaske..!” Ya k’arashe yana mai zira takalmansa...

Mommy da Hameedar duk sun rikice, a rikice Mommy dake rik’eda Ansar ta dubi Hameedah tace maza ta fice ta kirawo likita...
Taci gaba da fad’in “No Ansar bazan Barka ka fice a haka ba...! Ka natsu ayi komai a sannu, bakada lafiya, Maiyasa zaka fincike drip...!”

B’anb’anre hannunsa daga rik’onda Mommy tai masa yana mai furta “Mommy Wai kin mance ne.. This is my profession..! I’m also a medical Dr... Mommy I know what I’m doing... Please let me go...!”

Mommy na hawaye take girgiza masa kai tana furta “No Ansar I can’t let you go... I just can’t...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana...

Girgiza kai shima yake yana hawaye yake furta “Mommy I’m sorry... But I’m going... Ki min fatan nasara kawai... Na tafi ko na mutu ko nayi rai... But I must go..!” Yana ida fad’in haka yasa kai cikin sauri... Mommy na kuka sosai tana k’walla masa kira... Cak ya tsaya ya juyo yana duban mahaifiyarsa... Lokaci guda ya dawo da baya ya rungumeta sosai yace “I love you Mommy.. Please forgive me...!” Daga haka Ansar bai kuma tsayawa wata wata ba yasa kai ya fice cikin sauri...

Mommy na kuka tana kiran sunansa inaa ko juyowa baiba ya fice a d’ari...!

**
MASARAUTA

Koda Zuhra ta fito zata tafi sai taji ta lek’a Raheema taga ya ta kwana dan bataji alamun d’uriyarta ba, wata zuciya tace ina ruwanki sabuwar amaryace k’ila baccin huce gajiyan biki take... Hakan yasa bata kuma bi takan Raheemah ba ta janyo ‘ya’yanta suka nufo downstairs... Saidai tana k’ok’arin sauk’a taji kaman k’aran fashewan abu daga d’akin Yazeed... Ta d’aga idanu tana duban d’akin... Sai kuma ta dubi Hadimarta tace “Hindu fita da yaran ina nan tafe..!”

Babu musu Hadimar tayi yanda tace...
Sauri sauri Zuhra ta koma upstairs ta d’an ja ta tsaya jikin k’ofan d’akin Yazeed zuciyarta na bugawa... Wata zuciya tace idan kikaga abinda zai dameki fah..? Take b’angare na zuciyarta Ta bata amsa da fad’in “Mijin K’warai akema kishi... Toh idan kikaga abinda bai dace ba fah..?! Tai shiru tana tinanin abinyi... Tasan halin Yazeed tsaf zai iya kulle Raheema yayi tafiyarsa ba tareda taci koda abinci bane... Maiyuwa ya kulleta ne ma yayi tafiyarsa tinda ba da jimawa ba taji ficewar motarsa...
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na kuka nanata mata “Ina ruwanki, Ke naki a wanne idanma wani abin yayi mata... Ai sunfi kusa a halin yanzu...!” Dikda irin wannan batu da zuciyarta Ke mata hakan bai hanata d’an bubbuga k’ofan ba.. Kaman sautin mutum takeji amma muryar bai fita... Hakan yasata saurin murd’a handle amma da alama an kulle k’ofar... Sauri sauri ta isa ma’ajiyan spare keys na gidan Ta d’auko key d’in d’akin ta bud’e... Can jikin gado ta hango Raheema d’aure ta gama jigata ta galabaita.... Raheema na hango Zuhra ta kuma fashewa da kuka hawaye na ci gaba da gangaro mata...

Shaye da tsananin mamaki Zuhra Ke dubanta irin d’aurinda yayiwa Raheema wanda ko ita bai mata irin wannan... Ta isa da sauri ta b’alle sellotape d’in da ya manne bakin Raheemah dashi... Tai wani irin jan numfashi had’ida shak’an iska... Sauri sauri Zuhra ke kwance hawaye basu daina zubowa daga idanun Raheema ba...

Bayan ta gama kwanceta ne ta mik’e da zummar tafiya dan da alama ko idanu Raheemar ta kasa d’agowa su had’a...

Ji tayi Raheema ta rik’o hannunta guda tana kuka sosai, cikin muryar kuka take furta “Zuhra na gode... Na gode..! Dukda ban cancanci taimako a gareki ba amma kika zab’i ki taimakeni... Hak’ik’a ke d’in kinada zuciya mai kyau... Nasan nan cancanci yafiya daga gareki ba kuma banaso nati taking advantage d’in kyakkyawan zuciyarki na nemi tafiyarki dan nasan babu wacce zan mata abinda na miki ta yafe min... Amma hakan bazai hana na rok’i gafararki ba k’awata... Zuhra dan Allah Ki yafe min..! Kiji taisayina karki tafi ki barni da hakkinki... Ki yafe min dan Allah..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya ga rawan d’ari na zazzab’i da jikinta keyi...

A hankali Zuhra Ta juyo tana duban Raheemah hawaye kwance saman fuskarta itama... Lokaci guda take furta “Shi taimako ana yinsa ne a lokacinda ka Keda halin taimakawa... Kar kayi la’akari da ma wa zaka taimaka... Ka tuna cewa waye yayi umarni da ayi taimako... Idan zakayi taimako kayi Dan Allah domin ladanka na wajensa..So kar kiji mamaki dan na taimaka miki...!” Ta d’anyi fasali kana taci gaba da fad’in “Raheemah kin min zalunci mafi muni... Na aminta dake kinci amanata! Kinyi amfani da kusancin dake tsakaninmu kin yaudareni... Amma tun kafin aje ko ina ga sakayya kin fara gani, Allah yasa hakan ya zamto wa’azi gareki da masu halayya irin naki... Ina kuma miki fatan Allah ya kawo miki sauk’i cikin rayuwar da kike fuskanta... Ni na yafe miki Raheemah, bazan tafi da k’ulli cikin zuciyata ba... Na yafeki duniya da lahira.. Ina kuma fatan Allah ya yafe miki..!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka...

Rungumeta Raheemah tayi tana kuka sosai, su duka biyun suna kuka sosai mai tab’a zuciya... Cikin kuka Raheemah Ke fad’in “Na gode..! Na gode k’awata..! Na gode miki..! Allah Ubangiji ya canza miki rayuwarki da abinda yafi zama alkhairi a gareki...! Thank you my friend..!”

Murmushi Zuhra Ta sakar mata kana tace “Allah sada mu da alkhairi Raheemah... Goodbye..!”

Raheemah tai tsaye tana duban Zuhrar kaman wanda bazasu sake gamuwa ba, kodashike ta tafi kenan bazata kuma dawowa Masarautar ba a cewar Zuhra, idan Yazeed bai aika mata takardan sakinta ba Alk’ali ne zai rabasu...!

Zuhra na fitowa ta tadda Motar da aka turo daga masarautarsu domin ya kwashesu ya iso... Hakan yasa tuni dogari ya fito ya fara loda kayansu a k’aruwar motar ta alfarma... Haka Hadimanta na cikin Masarautar sukaita kukan tafiyarta domin kaw zasuyi kewarta, Hadimarta d’aya tak da tazo da ita daga Masarautarsu mai suna Hindu kawai ta d’auka.. Amma duk Hadiman Masarautarsu Yazeed bata d’auki ko guda ba...

Motarsu na shirin tashi Yazeed ya iso yana faman cika, cikin huci ya nufo Zuhra zai damk’ota Dogarin ya tare gabansa yana fad’in “Hattara Yarima..! Umarnin mai Martaba ne yace a dawo da Gimbiya Zuhriyya Gida..!”

Yazeed bai daina huci ba yake fad’in “Toh sai mai idan Mai Martaba ne yace a maidata gida..! Shi yake aurenta ko ni nake aurenta..?!”

Ya maidoda dubansaga Zuhra wacce ta cika tai fam yace “Kisa aniya ki fito min da yarana daga motar nan dan babu yanda zaki kaimin yara..!”

Zuhra ta murmusa tace “Na gaba ya riga yayi gaba Yazeed.. Na baya kuwa sai labari..! Ai na fad’a maka k’afata k’afan yarana.. Ka gaya min ma waye zan damk’a amanan tarbiyan yarana cikin Masarautar nan...? Dan haka I’m leaving with my kids..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin shigewa mota...
Yazeed yayi saurin rik’ota yana sakin huci yake furta “No.. Wllhi bazan barki ki tafi min da yara ba..! They’re my children, ‘ya’yana ne they belong here and no where else.. Nan shine mahaifansu..!”

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “K’warai babu yanda zaki tafi dasu Rankidad’e..! Idan zaki tafi Ke kina iya tafiya amma yara zasu tsaya a gidan mahaifinsu...!”

A fusace Yazeed ya juyo yana watsama Waziri mugun kallo lokaci guda yake furta “And who gave you the right to interfere..?!” Yayi maganan cikeda takaicin Waziri dan ya gane nufin Waziri tinda yasan yanzu yaran jikokinsa ne shiyasa bazaiso a fita dasu daga cikin Masarautar ba...

Abu kaman wasa labari ya soma karad’e Fada Gimbiya Zeenat zata tafi da yaranta Yarima Yazeed ya doge ya hana... Babu shiri Giwa ta lek’o ta Samanta tana kallon wannan drama..

Zuhra bata kuma bi takan Yazeed ko Waziri ba Ta bud’e mota ta shige abinta taceda Driver su tafi..!

Ai Yazeed bai bari Driver d’in ya soma tafiya ba ya finciki k’ofar driver d’in ya saka duka hannayensa biyu ya cakumo driver d’in yayi jifa dashi waje ya shige cikin motar... Kaman mai tab’in hankali yake furta “So kike ki tafi fine..! Zamu tafi gaba d’aya..! Zamu mutu gaba d’aya kinga shikenan jin huta...

Sanin rashin hankalin Yazeed yasa Zuhra soma girgiza kai tana duban yaranta dake daga bayan jeep d’in Hadimar Ta rungumesu sai kuka suke... Cikin rawar murya Zuhra Ke furta “Yazeed no please...! Yazeed akwai yaranmu cikin motar nan..! Don’t please Yazeed..!!”

Inaaa ko Sauraronta bai ba ya finciki motar kaman mahaukaci suka fice daga cikin Masarautar... A d’ari Giwa ta sauk’o k’asa tana fad’ida Waziri maza yabi bayan Yazeed dan tasan haukansa komai ka iya faruwa...

Zuhra na kuka tana fad’in yayi hak’uri ko dan yaransu ya tsaya, Ta amince bazata tafi ba.. Amma inaa Yazeed balbala gudu kurum yake saman kwalata yana mai ci gaba da sakin huci wanda da ganin kasan ta ko wane b’angare na rayuwarsa bai masa dad’i... Cikin huci yake furta “No Zuhra I cannot be a loser..! I can’t be a loser.. I’m Prince Yazeed AbdulJabbar... Idan bazan zama Champion ba bazan zama loser ba... We’ll die together... No one is leaving me.. Not you nor our children..!!”

Kuka take tana furta “Yazeed please..!”

Cikin daka tsawa ya juyo yace da ita “Shut up..! Shut the hell up..!!!” Daidai sanda k’aruwa motar trailer ta dososu daga d’aya length d’in wanda sam Yazeed baima kula da zuwanta ba... Ji kake gau motocin sun had’a, motar da suke ciki ta fettu gefe ta had’uda jikin bishiya...

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un...!
**

Duk wannan buduri da ake cikin Masarautar Mahmood baida labari yana nan gaban na’uransa yana ci gaba da hasko masa ita, hannayensa rik’eda Taswiran yana kuma gathering duk abubuwan da ya sani gameda ita cikin kwanyarsa, zuciyarsa naci gaba da bugawa yake furtawa a fili “I need to confront her to end all this..!”

Yana tsaka da wannan tinanin ita kaw Muhibbah dake daga can nata b’angaren itama sak’e sak’en yanda zatai ta fice daga kurkukun da aka ajeta take, tinda b’alla k’ofa bazai working ba she needs to come up with something as soon as possible..! Take tinanin ciwo yazo mata, idan tayi ciwon K’arya tasan dole Kuyangin su bud’e k’ofa, idan kuma suka bud’e zasuyi tinanin taimaka mata harm su tafi kiran iyayen gidansu ita kuma sai tayi amfani da daman ta gudu kafin su cimmata...!

Da wannan tinanin ta soma tamke cikinta ta isa jikin k’ofa da k’yar tana bubbugawa tana fad’in taimako..! Taimaki..! A taimaketa..!!

Kasancewar babu Kuyangin wajen yasa babu wanda ya jita... Bata fasa kame cikinta tana sakin k’ara had’ida ambaton a taimaka mata ba...

Daga nan yanda yake kallonta hankali tashe ya mik’e yana kuma duban yanda take murk’usoso alamun batada lafiya... Bai wata wata ba ya fice ya nufi b’angaren nata hannayensa rik’eda Zanen guda biyu....

Cikin sauri ya bud’e k’ofar ya hangota nan kwance Ta rik’e cikinta sosai....

Cak ya tsaya yana sauk’e haki a hankali yayinda itama ta tsaya cak da rik’e cikin nata tana dubansa idanu waje... Su duka biyun duban juna suke, jiri ne taji yana neman d’ibanta da gaske bada wasa ba... Tana gab da silalewa k’asa Mahmood ya k’araso a d’ari yayi jifa da takardun dake hannun nasa ya isa gareta ya tallafota ta fad’o cikin jikinsa...

Tsananin mamaki ya hanata katab’us saima juya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login