Showing 159001 words to 162000 words out of 257774 words

Chapter 54 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt

hasalima a kod’e fuskar tata take irin na wanda yaci kuka harda sauran busassun hawaye a fuskar nata... Dogayen bak’ak’en gashin idanunta da sukayi marfi wa manyan idanun nata duk sun shige cikin juna alamu kuka taci sosai, idanunsa suka sauk’o kan labb’anta masu d’an duhu kad’an wanda kaman an zane k’arshensu da liner... A hankali ya lumshe idanunsa yana mai k’ok’arin janye fuskarsa daga barin dubanta, nan idanunsa suka sauk’a kan hannunta da yasha zanen flowers na lalle dunk’ule da wata ‘yar takarda... Yai K’uri yana duban hannun nata... Duk wannan bacci da take takardan na nan mak’ale cikin hannunta bai fad’i ba... Daga gani ba rik’on wasa taiwa takardan ba...
Mahmood yakai hannunsa yana k’ok’arin bud’e hannun nata dake dunk’ule da takardar...

A hankali ya warware hannun nata har ya ciro takardan... Gabansa ya buga kikaci guda sanda ya warware takardan... Zanen ginin gidan sarautar nan ya gani... Take mafarkin da yayi da ita tana guduwa da zanen ya shiga dawo masa... Ikon Allah..! Wato dai mafarkinsa ta tabbata gaskiya... Yarinyar nan tanada wani agenda d’inta cikin gidan...! Toh ya akai irin zanen da Wambai ya basa ya fad’o hannunta... Mai takeyi da zanen..? Kuma a ina Ta samu..?! Tambayoyin da suka tsaya masa a rai har suka isa masarauta...

Lokacinda suka hankulan d’aukacin jama’an Masarautar naga hidindimun bikukuna da ake sannan wata labari da d’umi d’umi ta iso Masarautar cewa auren Raheemah dai ba da Mahmood aka d’aura ba da K’aninsa Yazeed aka d’aura...

Wannan hargitsi yasa har Mahmood ya ciccib’i amaryarsa ya shige da ita sashen da ya tanada na musamman Don ajeta ciki...

Yana fitowa ya tadda Barde da Turaki har sun sauya shiga suma, take ya kuma jaddada masu cewa babu wanda zaisan batun aurensa da Muhibbah..!
Barde ya jinjina kai cikeda risinawa yana mai tabbatar masa amincinsa garesa...!

Mahmood ya jinjina kai yace “Ina Kuyangin dana ce ka ware mun su...?!”

Barde ya kuma risinawa yace “Allah shi baka yawan rai suna nan waje suna jiran umarninka...!”

Nan ma jinjina kai yayi yace “Kasan sashen da na ajeta ai..?!”

Barde ya jinjina kai yace “K’warai Rankaidad’e...!”

Mahmood ya kuma daidaita tsayuwarsa yace “Akai Kuyangin wajen, aikinsu kenan su dinga kula da ita, kama daga abinda zataci zuwa komai na buk’atarta... Koda wasa kada a bari ta lek’o koda k’ofa ne har sai idan ni ne na umarta..!”

Barde ya kuma risinawa yace “An gama Allah shi taimakeka...! Jaaa zamaninka dogon Sarki mai dogon zamani..!” Ya gama kirariwa Ubangidan nasa kana ya mik’e ya fice...

Barde na ficewa Turaki da har lokacin bai daina sakin murmushi a hankali ba yace “Rankaidad’e ango yanzu haka za’ai hidimar nan bazaai shelan auren mai Martaba cikin Fada ba..! Ko Haka zaka tare ne bazaka bari ahalin Fada su shaida ba..!” Ya k’arashe cikin sigan zolaya yana sosa kai...

Wani irin duba kurum Mahmood d’in ya aika masa, Turaki yai murmushi da tafi kama da yak’e yace “Tuba nake Allah shi taimakeka...!!”

Girgiza kai kurum Mahmood d’in yayi yace “Kanada gaggawa Turaki... Sau nawa zan ce maka Ina buk’atarta cikin Masarautar nan shiyasa na aurota kafin su aurarta ga wani... Idan amfaninta ya k’are a cikin Masarautar nan zan sawwak’e mata taje ta auri wanda take so.. Babu wani abu da zai shiga taakanina da ita.. Hakan yasa na killaceta b’angare guda..! Ka fahimta..?!”

Turaki ya jinjina kai yana mai k’ok’arin matse dariyarsa dan ko babu komai gaban Sarki yake... Shidai yanzu hankalinsa ya kwanta tinda bai aurarta ga wani cikin Masarautar ba ya aurawa kansa, yasan daga baya zai yarda da batunsa cewa sonta yake... Sallama Turaki yai masa dan shi kam ba baisan auren Raheema da Yazeed Mahmood ya umarta a d’aura ba... Hakan yasa baibi takan ahalin masaeautar ba yai tafiyarsa gida dan huta gajjiya daga baya yazo yayiwa Jamal murnan aure...

**
Yazeed dake zaune spot d’insu shida abokansa su Zayyad suna kuma kid’asa dan ya sanar dasu daga yau ya zama Sarki, sabida ana d’aura auren Mahmood zai d’auki matarsa su koma Spain... Abokan sai kuma haukatasa suke suna duk’awa gabansa suna fad’in Allah shi taimakeka Rankaidad’e Mai Martaba Sarki Mai talakawa...!
Zayyad ne ya koma gefe yana amsa waya da alama labarin ta iso masa da d’umi d’uminta... Dama a ido ne suke nuawa Yazeed suna sonsa cikin zuciyarsu kuwa har kullum downfall d’insa suke son gani shiyasa duk abotan da ba’a gina cikin tsoron Allah ba ka guji irin wannan abota da wad’annan miyagun abokai wanda zasu kaika su baroka...
Babu shiri Zayyad ya k’araso yana labarta masu labarin da yaji...

Tamkar sauk’an aradu haka Yazeed yaji abun, ya mik’e ya cakumo Zayyad yana fad’in “K’arya kake... K’arya kake Zayyad Mahmood ne ya auri Raheema kuma d’aukanta zai su tafi Spain ni ne nan zan zama Sarki..!!”

Zayyad ya finciki wuyarsa daga hannun Yazeed yana furta “Ka zaci zan maka k’arya ne haka kawai, ai taimakonku yayi daga kai har Raheemar ya aura maku juna yanzu sai kuyi wanda babu zunubi sai Lada Your Highness ko ya kukace guys..?!” Ya k’arashe yana duban sauran abokan...
Gaba d’aya suka tuntsure da dariya suna jinjina k’arfin hali irin na Mahmood, kuma abinda Mahmood d’in yayi sosai ya burgesu... Sai dariya sukewa Yazeed suna fad’in karfa ya zama loser da gaske... Mahmood ya d’arasa a ko ina... Da alama sarautar nan bazai tab’a gadanta ba...

Huci kurum Yazeed yake yana ayyanawa cikin zuciyarsa Wai Yayansa Mahmood ya aura masa Raheema... Kenan shi bai aureta ba ya aura masa, kenan shirinsu ya b’aci, Mahmood bazai koma can k’asar Spain ba... Waima sabida tsaban wulak’anci da bai aureta ba shine bari ya aura masa... Who does he think he is da zai dinga yin abu gaba gad’i ba tareda neman izinin kowa ba... Lallai ma Mahmood ya wuce iyakarsa.. Waye ya basa daman deciding ma rayuwarsa... Wllhi ya taro fad’an da bazai iya, yau sai ya shayar dashi mamaki ya nuna masa bai isa dashi ba...! Fuuu ya mik’e yai ficewarsa...

Zayyad yasha gabansa yace “Your Highness the bill waye zai settling bills...?!”

Rai b’ace Yazeed ya ciro card d’insa ya mik’awa Zayyad zai fice Zayyad yace “No Your Highness, na sani ko empty account ka bani, ai jira zakai a duba a gani...!”

Shi dai Yazeed bai iya cewa komai ba sai tururi da yake...

Aiko ana zuwa wajen biyan Kud’i kati yak’iyi saima nuna declined da yakeyi...

Yazeed da mamaki yake dubansa kenan an rufe katinsa bazai samu access to family account d’insu na cikin Fada ba... Gashi d’aya account d’insa babu kud’i ciki kwanakin baya abokan sunyi duping d’insa ba tareda saninsa ba suka kwashe miliyoyin dake ciki... Zuciyar Yazeed kaman zata tsage ta fito waje... Lallai Mahmood ya gama raina masa wayo... Toh wllhi yau sai anyita ta k’are koda zasu raba zumunta ne na har abada...!

Yana ficewa abokan suka bisa da kallo suka fashe da dariya Zayyad na fad’in “Idan talauci Ta cinyesa ya kawo min SUV d’in nan na saya a wulak’ance dan nasan za’a kai wannan stage d’in dama ni ita nake hari..!”
Sauran abokan suka kuma kwashewa da dariya d’ayan na fad’in shi kuma Ford d’in Yazeed d’in zai saya idan an karya mata farashi..!
Haka suka dinga aibata Yazeed suna fad’in yanda suke tsananin son ganin k’arahensa a tsiyance...

**
Da tsananin mamaki Giwa take duban Waziri da alama da matarsa ya gama waya yana sanar da ita amfani kawai yakeda Giwa tinda ta gama aminta dashi idan suka kawar da Mahmood shi kuma bazai bari Yazeed ya d’ale karaga ba kaman yanda Giwa taci buri... Zaisan yanda zai ya kawar da Yazeed sarauta ya zamto nasu...!

Yau saiga hawaye na fitowa daga idanun Giwa jin irin bak’in cin amana da Waziri ya tasamma yi mata....

Giwa na hawaye take furta “Ni zaka cuta Shayibu... Ka rasa wa zaka cuta saini... Kana ikirarin kashe d’ah na dan ka d’ale karaga.. Bayan duk fad’i tashin da mukayi tare ashe cin dunduniyata kake ban sani ba... Shayibu ka bani mamaki.. Ni Turai zaka cuta..!”

Waziri na muzurai yake furta “Baki fahimceni bane Rankidad’e, kinsan halinku mata saida dabara... Ta tab’a kamani ina waya dakene shine nai mata wayo nace da ita munafuntarki nake don na sami yardarki... Idan ba ya haka ba bazan tab’a shawo kanta ba da yanzu tuntuni ta jima da fallasamu.. Amma kema Kinsan bazan tab’a cin amanarki ba Giwata..!”

Giwa ta katsesa da fad’in “Rufe mun baki munafukin banza munafukin wofi, bayan d’an da kake k’ok’arin ganin k’arahen nasa ma D’anka ne..! Yazeed d’anka ne ba d’an AbdulJabbar ba.. Idan ka kasheshi ka kashe d’anka da hannunka ne..!!”

Muryar Yazeed suka sinkayo yana fad’in “Maami...!! Mai nakeji.... Mai nake jin kina cewa..?! Wannan mutumin... Shine mahaifina..!!!?” Ya k’arashe hannunsa na tsananin rawa yana nuna Waziri...

Giwa da batasan da shigowar Yazeed ba dafeda k’irji take dubansa yanda yake wani irin tururi da huci jikinsa sai karkarwa yake yana nuna Waziri... Shi kansa Waziri da yaji batun a bazata idanu waje yake duban Giwa yana duban Yazeed....

Yazeed da jijiyoyinsa suka firfito waje tsalle yayi ya shak’o wuyan Giwa yana fad’in “Answer me..!! Tell me the truth... Waye mahaifina... Kuma karkice min wannan k’ask’antaccen mutumin shine mahaifina... Dan nayi imani sai na hak’a rami na banka maku wuta dukanku biyu kun mutu..!! Ki amsa min Maami... Kice min Abbah na mai Martaba shine mahaifina ba wanann wulak’antaccen mutumin ba..! Ki amsa min Turai..!!!”

*MUHIBBAH*




*62*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Giwa taji damk’a irin wanda bata tab’aji ba sai muzurai take idanunta na kuma firfitowa waje, Ji take kaman ranta zai fice daga cikin jikinta sabida tsaban azaba don wane irin damk’a Yazeed yai mata irinta wanda ransa Ke tsananin k’una... Ganin Yazeed dai kashe Giwa yake k’ok’arin yi yasa Waziri Saurin k’arasawa yana k’ok’arin ceton Giwa daga hannun Yazeed... Wawan naushin da ya kaiwa Waziri saida ya zaunar dashi har k’asa Waziri ya rik’e cikinsa yana murk’usoson azaba a wajen abinka da wanda shekaru ya ja tsufa ya sauk’o masa, zai wahala idan naushin da Yazeed yai masa bai targard’a masa wani k’ashi ba....

Yazeed bai saki Giwa ba yana hawaye yake dubanta yanda take k’ifk’if da ido tana neman tsira daga azaban da take ciki... Hawaye na zubo masa yayi wurgi da Giwa Ta koma gefe, bai daina huci ba yake nunata da yatsa yana fad’in “Kin cuceni kin zalunceni, Allah da kikayi sanadin zuwana duniya, da na zamto d’an wannan mutumin gwara ba’a haifeni ba..!! Ki tashi ki sanar dani komai da bakinki..! Ki tashi nace..!!” Ya k’arashe yana kuma finciko Giwa da har lokacin bata daina haki tana sosa wuyanta yanda Yazeed ya shak’eta ba...
Shar shar da hawaye Yazeed Ke kuka yana kuma jijjiga Giwa yake fad’in “Talk to me..! Tell me everything..! Ki fad’a min ya akai wannan k’ask’antaccen mutumin ya zamto mahaifina..!!!”
Ya k’arashe hawayen k’unan rai na tsartowa daga idanunsa da ya koma jazir...

Giwa na hawaye take furta “Yazeed ka yafe min, wllhi bada son raina bane... Duk abinda nayi dominku nayi kaida ‘yanuwanka... Yazeed ka yarda dani, wllhi sabida ku nayi komai...!”

Cikin daka tsawa hawaye basu daina zuba masa ba ya kuma fad’in “Ki gaya min ta ina kika taimakeni bayan kin sameni Ta haramtacciyar hanya... Hanyar da ko sarautar da nake da buri tsawon rayuwata banida gadonta... How could you do this to me Giwa..! How could you..?!!” Ya k’arashe yana mai kuma jijjigata hawaye naci gaba da zuba masa....

Cikin kuka Yazeed yaci gaba da fad’in “Now I get it... Shiyasa kika fifita Mahmood sama dani sabida Mahmood shine d’an AbdulJabbar ni kuma d’an wannan k’ask’antaccen mutumin... That’s why kika dage sai Mahmood ne zai sarauta... Yanzu na fahimci komai..!”

Katsesa Giwa tai da fad’in “No Yazeed ka saurareni ba haka bane..!”

Cikin huci ya katseta “Then how..! Yaya ne...? Bakida wani dalili da ya wuce wannan..!”

Giwa ta katsesa da fad’in “Mahmood shine babban mak’iyina a duniyar nan... Mahmood shine ya hanani rawar gaban hantsi... Mahmood shine ya zame min ciwon ido... Banida buri da ya wuce na kawar dashi a doron k’asa..!!!” Ta k’arashe tana sakin huci tamkar wata zakanya...

Izuwa lokacin da tsananin mamaki Yazeed ke dubanta cikin tsananin sanyin jiki.. Ya shiga girgiza kai alamun ya kasa aminta da abinda yakeji Wai mahaifiya zata tsani d’anta haka..!

“Maami shin Mahmood ba shine d’ah mafi soyuwa a gareki ba..?!”

Muryar Waziri ya sinkayo yana fad’in “Yazeed Mahmood ba d’an mahaifiyarka bane..!”

Cikin tsananin shock Yazeed ke k’ok’arin juyowa yana duban Waziri da yayi maganar.... Waziri ya jinjina masa kai alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “Mahmood d’an Baiwa ce, Baiwar da sukaci amanar mahaifiyarka itada AbdulJabbar bayan mahaifiyarka Ta basa kyautanta a matsayin tukwici...!!”

Girgiza kai Yazeed keyi kana ya kuma karkatowa yana duban Giwa cikin rashin fahimtar abindake wakana... “Mai...Mai yake cewa Maami...? Ki min bayani.. Shin abinda mutumin nan yake fad’i gaskiya ne..? Ba kece kika haifi Mahmood ba...?!”

Giwa ta jinjina masa kai hawaye na zubo mata “K’warai Yazeed kaman yanda kaji Waziri yace Mahmood shine product na cin amanata da Baiwata Izzatu da kuma mijina AbdulJabbar sukayi... Shiyasa naci alk’awarin maidashi nawa dan na d’au fansata akansa... Duk yanda Kaga na k’agu ya d’ale karaga ba sabida komai bane sai don malami na ya sanar dani wanda duk ya fara sarauta cikinku bazai k’argo ba zai mutu.. Kaga idan Mahmood ya d’ale yayi guntun zamaninsa sai kai ka d’ale ka jima kana mulkin ka wannan shine tanadin da nayi maka... Wannan shine dalilin da yasa kaga na dage Mahmood ya soma d’ale karaga dan ya tafi ya bamu waje mu kafa mulkinmu da zuri’armu..!!”

Yazeed ya zauna dirshan a k’asa yana nanata kalaman mahaifiyar tasa cikin kwanyarsa... Ganin yayi shiru yana nazari yasa Giwa kamo hannayensa tana fad’in “Yazeed ina matuk’ar k’aunarka duk wannan fad’i tashi da nuna ina son Mahmood a fili dukda kasheni da hakan yake can k’asar zuciyata wa kai nake da ‘yanuwanka mu samu mu kawar da Bare d’an Baiwa cikinmu..!”

Jajayen idanunsa ya d’ago yana dubanta kana yace “Koda ace shi d’an Baiwa ce but at least he carries my father’s blood, yana d’aukeda jinin AbdulJabbar na Yawo a b’argonsa... But what about me... Bana d’aukeda jininsa sai na wannan k’ask’antaccen mutumin kwarto mai bin matan mutane... Now I get it... Ashe ga yanda nayi gado..!!” Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushinsa yana aikawa Waziri jahilar kallo... Lokaci guda ya maidoda dubansaga Giwa ya tsime sosai yana mai ci gaba da fad’in “Su kuma ‘yan uwana waye mahaifinsu tinda naga alama k’aryace zalla cikin rayuwar ahalinki... Baki haifi Mahmood ba kikac kin haifa.. AbdulJabbar bai haifeni ba kikace ya haifa.. Toh su kuma Jamal da Yazeed fah...? Naki ne ko suma satansu kikayi... Ko kuwa dai suma wannan mutumin shine mahaifin nasu.. Kodai ma akwai wani wanda bamu sani ba..?! Talk kimin magana Giwa..! Ki bud’e baki ki amsa min tambayoyi na..!!” Ya k’arashe yana mai firfito da idanunsa waje tamkar zai kuma shak’ota....

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “Fad’a mana Turai... Jamal da Fu’ad suma ‘ya’yana ne...?!”

Giwa Ta d’ago tana dubansu, ta kalli wannan ta kalli wancan, ta had’iyi miyau da k’yar sai kuma ta soma fad’in “Banida tabbas akan Jamal, Don a lokacin na shiga rud’ani... Amma Fu’ad d’an AbdulJabbar ne... Shi kad’ai ne jininsa cikin yarana guda uku...!!”

Yazeed na sakin huci yake aika mata wulak’antaccen kallo, lokaci guda yake jinjina kai yana fad’in “No wonder mahaifinmu yafi son Mahmood da Fu’ad ashe yanaji a jikinsa sune jininsa na asali, no wonder sukafi kamanceceniya Ta fuskar halitta ashe sud’in sune ‘yan uwan juna...!”

Ya mik’e sosai yana ci gaba da fitar da huci yake fad’in “Now that I learned banida wata alak’a ta jini da d’an Baiwa Mahmood I won’t have mercy on him... I’ll not spare him...! Now more than ever I’ve every right to the throne sabida D’an Baiwa bai gaji sarauta ba...!”

Giwa tai saurin katsesa da fad’in “Karka d’auki mataki yanzu Don idan Mahmood ya san cewa banice na haifesa ba shirinmu zai lalace akansa...!!”

Cikin k’unan rai Yazeed yace “To hell with your plans Giwa..!! Do you think I care...?! My life is ruined...! Kin lalata rayuwana da kika bari wanann mutumin ya zamto mahaifina..! Kin cuceni da baki bari na fito a tsatson Abbah ba... I don’t give a damn idan Mahmood yasan cewa shi d’an Baiwa ce..!!”

Giwa na girgiza kai take fad’in “Idan ka sanar dashi yanzu shikenan bazai d’ale karaga ya mutu ba.. Kaga idan ka d’ale kaine zaka mutu ni kuma bazan juri rasaka ba d’ah na..!!” Ta k’arashe tana rau rau da idanu..

Shiru yayi yana dubanta tamkar mai nazari har lokacin bai daina sakin huci ba... Suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “K’warai d’ah na sarauta takace amma ka bari har mu kawar maka da Mahmood..!”

A fusace Yazeed ya katsesa da fad’in “Don’t you dare call me your son ever again..! I’m not your Son.. I’m my Father’s Son..! I’m Yazeed AbdulJabbar Mahmood...! You’re not my father and you’ll never be..Get that through your this empty skull of yours..!” Ya k’arashe yana mai bubbuga rawanin Waziri

Giwa Ta had’iyi miyau da k’yar sai kuma tace “Yazeed ka basa girma ko d’an kad’an ne tunda yanzu kasan komai...!”

Shu’umar murmushinsa yayi yana watsa masu wulak’antaccen kallo dukansu biyu sai kuma yace “Ai kun zubar da girmanku tun lokacin da kuka zab’i ku haifoni Ta wannan hanya... Thai man is not my father, zan fad’a kuma zan nanata... I might carry his blood but har abada bazai tab’a zama mahaifina ba... My Father is dead.. Mai Martaba AbdulJabbar shine mahaifina, and Ni ya fi dacewa na gajesa ba Mahmood d’an Baiwa ba k’ask’antacciya ba...! I’d never allow d’an Baiwa jinin Bauta ya mulki Masarautar nan ba..!!” Ya k’arashe yana mai watsa masu muguwar kallo lokaci guda yasa kai ya fice daga d’akin kaman zai tashi sama zuciyarsa naci gaba da suya...
**
K’AUYEN GALAMBI

Ubandoma yai jigum yana duban Baba Nomau yanda yake had’a wani ruwan magani cikin sabon goran da suka ciro daga daji suka fafeta.... Ubandoma ya d’an gyara zama yace “Yanzu Baba Wai kana nufin dama ba yanke harshenta matar nan akayi ba..?!”

Baba Nomau ya murmusa yace “Ubandoma kenan, matsafa babu abinda bazasu iya yi ba kai dai muyi addu’an Allah ya shiga tsakaninmu da mugu.... Ba yanke harshenta sukayi ba saidai sun d’aure harshen nata ne da muggan bak’ak’en

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login