Showing 30001 words to 33000 words out of 257774 words

Chapter 11 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt

kuma fah.. Wannan kumbure kumburen na minene... Ince kina cen kina kula da d’iyar mijinki... Meye kuma zaki shigo kina kumbura fuska..?”

Raheema ta d’an kuma tura baki gaba tana kuma tab’e fuska kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Aunty wata mayya ce ta shigo Masarautar nan take neman shige min hanci da k’udundune.... Wllhi bakiga yanda take rawar k’afa kan ahalin Masarautar nan ba musamman Zahra... Aunty tsoro nake kar wannan shegiyar yarinyar Zahra tasa mahaifinta ya auka wa soyayyar wannan mayyar tinda dama yarinyar bak’ar munafuka ce dan na lura tamkar bata k’aunar alak’ata data mahaifinta....!” Ta k’arashe tana kuma tura baki gaba...

Tsegege Gimbiya Zeenatu ke dubanta kana ta murmusa kad’an cikeda k’asaita sannan taci gaba da fad’in “Dad’ina dake Raheema wauta, Ke yanzu har akwai macen da zata baki tsoro akan Mahmood... Mutumin da matan ma basa gabansa, mutumin da har yanzu mutuwar matarsa bai gama ficewa daga jikinsa ba... Ni wannan wauta naki da yawa take Raheema saikace ba d’iyar Saraki kike ba, sam Bakida jarumta... Har yaushe zaki tsaya wata banza can Ta baki tsoro Yo ni ba don inason cimma burina wajen ganin kin auri Mahmood ba yaushe zan tsaya ina biyayyawa Giwa...Toh wllhi ki bud’e kunnuwarki da kyau ki saurareni... Idanma baki son Mahmood wannan Ke ta shafa iayakacin abinda na sani shine idan za’a kashe rai a Masarautar nan sai kin aure Mahmood dan yanda na zamto ‘yar kallo cikin Masarautar nan auren Mahmood da zakiyi shine zai dawo min da Martaba ta ya kuma d’aga darajata, don na tabbata da zaran Mahmood ya zama Sarki Ke kuma kin zamto matar Sarki Toh fah mulki ta dawo hannunmu sai yanda mukai da Giwa cikin Masarautar nan, da Sarki da Uwarsa dik zasu dawo k’ark’ashin mulkin mu....Tunda ban haifa Sarki ba don haka dole na zamto Sirkar Sarki, dole ta ko wanne hanya nasan yanda zanyi mulkin Masarautar nan Ta dawo gareni... Kuma hanya d’aya kenan tak shine ki auri Mahmood...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje...

Raheema tai shiru tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali, k’aunar Mahmood na kuma fizgarta, dik yanda za’ai bazata tab’a bari wata tazo Ta rusa mata Farin cikin data jima tana k’ok’arin ginawa ba koda kuwa wann shegiyar d’iyar tasa bataso.... Da wann tunanin ta mik’e ta nufi d’aki shiryawa dan zuwa ganin Yarima Mahmood...

**
Turaki ya kuma gyara zama yana mai kurb’an drink d’in dake rik’e hannunsa kana ya nusa kad’an yace “Toh yanzu what are you suggesting your Highness...?”

Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali kana yace “I don’t know Turaki... Is getting more complicated... Na rasa ta ina zan b’ullowa al’amarin... Waye zan fara tuhuma..? Ta ina zan fara bincikawa... Sannan waye zan yarda dashi cikin Masarautar nan...?”

Shiru ya d’an gifta tsakani kana Turaki ya d’an gyara zamansa had’ida fitowa daga cikin kujera sosai “A gaskiya your Highness ko ni ban goyi bayan ka amince da kowa cikin Masarautar nan ba... I’m sorry to say not even your brothers...It might sound ridiculous but gaskiyar kenan... Kuma kaman yanda Baba Wambai yace, if you really want to get to the bottom of all this, Toh fa sai ka zamto shugaba a Masarautar nan... Idan har kana tunanin mutuwar Matarka nada nasaba da mutuwar mahaifinka bazaka tab’a ganowa ba har sai ka zamto kaikeda mulkin Masarautar nan....”

Yarima Mahmood yai shiru yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida fuzar da fuci a hankali... Lokaci guda abubuwa da dama ke ziyartan kwanyarsa... Mafarkin da yai da ‘yan uwansa harma da mahaifiyarsa, Sannan Maiyasa Giwa take so ya auri k’anwar matar mahaifinsa... Maiyasa yake jin can k’asan zuciyarsa bai aminta da wannan had’i da suke k’ok’arin yi ba... Maiyasa yake jin abubuwa da dama basa tafiya daidai cikin Masarautar... Tabbas ya kamata ya saka zancen Baba Wambai a ma’auni, bai kamata ya k’yale Yazeed ya d’ale Karagar Mulkin ba har dai yanaso ya samo amsoshinsa....

Turaki yaci gaba da fad’in “Mai kake gudu cikin sarauta Mahmood... Kana tinanin sirrin da ka b’oyewa d’iyarka shekara da shekaru na iya bayyana ne... Is that what’s holding you back...?” Ya k’arashe cikeda kulawa...

Kaikaitowa yai wannan karon yanaima Turaki wani irin duba kana ya soma fad’i cikin karaji “She’s never going to find out.... I won’t allow that to happen... I’ll protect that from happening, no matter the cost..!!”

Shiru Turaki yai ba tareda ya kuma cewa komai ba dan yasan wanene abokin nasa idan ransa ya b’aci... Bai kuma kawo zancen ba sai ma shiru da yai yana karantar Mahmood d’in da ko ba’ace ba lissafi da sak’e sak’e yake cikin zuciyarsa... Turaki ya girgiza kai cikeda tausayin abokin nasa....

***

A nan yanda ta mak’ale take jiran fitowar Jamal, Ta kusan minti talatin mak’ale a nan wajen tana ganin masu kaiwa da komowa amma bataga koda k’yallin Yarima Jamal ba... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma lek’awa... Har saida ta cire rai bazataga giftawansa ba ta hango wani mutum sanye cikin bak’in kaya mai tsananin duhuwa ya nufo ta yanda take, baka iya hango fuskarsa don ya rufe da bak’ar hula mai yanayi da hular sanyi... Baka hango komai sai alamun mutum... Sosai k’irjinta ke tsananin bugu zuciyarta na tambayarta wanene wannan... Tana gani mutumin ya nufi wata hanya ga walk’iya da har yanzu akeyi had’ida tsawa mai k’arfin gaske... Take taji zuciyarta tana son ganin yanda wannan mutumi zai jesa... Lokaci guda ta sad’ad’o ta fito daga mab’oyar nata ta nufi mutumin cikin sand’a dikda cewa tafiyar mutumin yafi kama da sassarfa tamkar mai tafiya cikin iska dan har b’acewa ganinta yake.....

Dikda tsananin tsoro da ya ziyarci zuciyarta hakan bai hanata bin bayan wannan mutumin da bata iya hango komai nasa face bak’in tufafi....

Suna tafe ta hango mutumin ya tsaya cak tamkar wanda aka tsaida shi... Gabanta ya yanke ya fad’i tamkar an iza guduma, idanunta suka firfito waje... Juyowan da mutumin zai yayi daidai da shigewar Muhibbah cikin tsakankanin gini zuciyarta bata daina tsinkewa ba, lokaci guda ta rintse idanunta sanda taji tamkar takun mutumin ya nufota....




SameenaAleeyou📚
[6/8, 8:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*



*015*



*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*



Sosai take jin tafiyar na nufowa yanda take, banda karanto addu’o’i cikin zuciyarta bata iya komai, ta rintse idanunta a hankali tana jiran mai aukuwa ya auku.... Cak kuma sai taji tafiyar ta tsaya, tai saurin bud’e idanunta dake rintse k’irjinta naci gaba da bugu... A hankali ta d’an fito da kanta tana lek’en hanyar, bataga kowa ba sai wasu mage guda biyu suna cin abinci daga gefe.... Allah ya gani tsikar jikinta yai matuk’ar tashi da ganin wad’anann Magen dikda gasu farare ne k’al gwanin ban sha’awa.... Ta kuma lumshe idanunta a hankali tana karanto addu’a na neman tsari, Allah yasa ita d’in ma’abociyar zikirin safiya da maraice ne wanda dik d’an adam idan yai rik’o dasu Allah yayi alk’awarin karesa daga dikkan wani abin cutarwa saidai kuma idan k’addararka ce toh sai ya cimmaka....
Tabbas wannan mutumi mai bak’in tufafi ya b’acewa ganinta, batasan Ta yanda ya nufa ba dan haka dole ta hak’ura da bin bayansa, gashi bataga Jamal ba mak’asudin b’uyarta a wajen... Babu yanda ta iya haka ta nufi masauk’i tana ci gaba da sak’e sak’e cikin zuciyarta lokaci guda tana juya sark’ar data d’auka daga wajen Yazeed....

Tana isa d’aki ta d’au wayarta, Aiko nan ta iske missed calls d’in Ansar kusan guda biyar... Ta d’an lumshe idanunta had’ida bud’esu, lokaci guda tana fuzar da huci a hankali... Kaman jiran isowarta yake nan wayar taci gaba da ruri....
Ta d’auka a hankali sallama saman bakinta...
Cikeda tashin hankali Ansar ke fad’in “Hibbah where have you been, I’ve been trying to reach you since ... Tell me akwai wani abu ne..? Are you okay... How are things there...?!” A jere yaita jero mata tambayar cikin tsananin damuwa...

Shafe fuskarta tai a hankali kana tace “Relax please Ansar..Just calm down... Babu abinda ya sameni, idan kajini shiru Ina aiwatar da abinda ya kawoni ne kafin lokaci ya k’ure min.... And please I want to ask you this favor... Dan Allah ka daina yawan kirana on and on, someone might get suspicious of me, especially Umaima ta yarda dani sosai banso na breaking trust d’inta da take dashi akaina... She really is a good person banso taga kaman na yaudareta ne ko wani abu mai kama da haka... Kuma kaima yin hakan ka iya shafar alak’arku...Please Doc ka rage yawan kirana...You don’t need to worry about me, I can take care of myself...!”Ta k’arashe Murya fal damuwa...

Fuzar da fuci yai a hankali kana ya soma fad’in “Seriously Hibbah...! Cewa kike na rage yawan kiranki bayan nasan abinda kikeyi abu ne mai matuk’ar had’arin gaske... And you’re even telling me kar na damu dake zaki iya kula da kanki...? Kema kinsan bazan tab’a yin haka ba... Idan bakiso naci gaba da kiranki on and on, then always keep me updated... I need to know everything that’s going on with you there...!”

D’an rausayar da idanu tai kana tace “Alright fine... Kana so ka sani..?” Lokaci guda Ta soma sanar dashi abubuwan da suka faru tiryan tiryan a d’an shigowarta gidan da tai....Saidai tin bata gama bashi labarin abubuwan data gani ba ya mik’e daga zaunen da yake yana mai furta “No Muhibbah, you’re not pushing through with your plans... You know what..? This is over... Park your things gobe gobe zanzo na d’aukeki mu dawo gida... Bazan iya barinki tsakankanin wad’annan Animals d’in kici gaba da rayuwa ba... Who knows, wa yasan abinda zasu miki...?!” Ya k’arashe cikin tsananin k’unan rai...

A d’an tsawace itama ta soma fad’in “Do you really think I like it here... Kana tunanin Ina jin dad’in zama cikin wad’annan azzaluman ne...? Do you think it’s easy for me facing them bayan dik abinda sukai min...? This isn’t easy for me.... Each time idan naga fuskokinsu sai na tuna wancan lokacin... So please idan bazaka ci gaba da k’arfafa min gwiwa ba ka daina sarar min da gwiwa...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka....

Cikin sanyin jiki Ansar ke furta “I’m sorry... Ba nufi na ba kenan Muhibbah.... Na damu dake ne Muhibbah, you know how much I love you right...? So please kar kiga laifina dan na nuna damuwata, Kawai gangan jikina ne a nan but gaba d’aya zuciyata da ruhina suna taredake Muhibbah.... I’m sorry I made you feel that way...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Tsaye ta mik’e had’ida dafe kanta kad’an tana mai furta “Ansar shiyasa banso sanar dakai ba, ya kamata ka gane da da yanzu ba d’aya bane... Babban kuskuren da sukai shine da suka barni da rai... Allah bazai kuma basu daman cutar dani ba... Kuma yanzu da na tabbata akwai abubuwa da dama da suke rufe cikin Masarautar bazan tafi ba Ansar har sai nakai mak’uran bincikena da yardar Allah... Kawai kaci gaba da min addu’a kaji...!”

Shiru yai tamkar mai nazari kana ya fuzar da fuci a hankali “Shikenan... Amma ki sani ba wai dan inaso ba na k’yaleki cikin Masarautar nan sai don Babu yanda na iya ne.... I love you so much Muhibbah... And ina kewarki sosai..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Jiki a matuk’ar sanyaye tace dashi “Ka gaisar min da Mummy, nima ina kewarku sosai... Sai mun sake magana...!”
Sukai sallama su duka biyun jikkunansu matuk’ar sanyaye...

Mik’ewa tai ta soma zarya a d’akin tana tunani abinyi gaba... Ta d’auko sark’ar tana ci gaba da juyawa... Tabbas ya kamata Washe gari juma’a takai ziyara k’ofar Yarima Yazeed.... Da wannan tunanin ta bud’e drawer ta linke sark’ar cikin k’aramar farar k’yalle kana ta fad’a bathroom ta d’auro alwala...
**

Yauma da salati saman bakinsa ya bud’e idanu daga baccin da yake mai cikeda mafarkai marassa dad’i... Tabbas abin ya soma damunsa sosai, hardai zai kwanta toh sai yayi marfkin wani abin k’i.... Yau mafarkin nasa gameda Ja’afar ne... Ja’afar bawa d’ah ga sarkin dawakai na cikin masarautarsu...
Kaman yanda ya gani cikin baccin nasa, Shida Ja’afar suna tafe cikin Bargan dawakan mahaifinsa su duka biyu Sun saka kaya irinta mulki da sarauta iri guda babu abinda ya raba, kwatsam abokan gaba suka far masu... A tare suka zaro takubbansu domin yak’an abokan gaban nan.... Cikin abokan gaban d’aya yayo kan Mahmood da takwabi saidai tuni Ja’afar ya tare masa saran kana ya mik’a masa hannu ya d’agosa tsaye, su biyu d’in hannayensu rik’e cikin na juna.... Yak’i sosai suke da abokan gaban nan har saida Suka kashe abokan gaban gaba d’aya hardai sukai nasaran kama shugaban abokan gaban nasu wanda ya jagoranci yak’in ...Babban abinda ya firgita Yarima Mahmood shine wannan shugaban abokan gaban da sukai nasaran capkewa k’afafunsa kawai Mahmood ya kalla ya gane d’aya ne daga cikin ‘yan uwansa.... Cikin tsananin tashin hankali yake bin k’afafun da kallo hardai ya kusan k’arasowa zuwa fuska... Saidai kash kafin ya k’araso zuwa fuskar ya farka daga baccin bai hangi ko wanene cikin k’annen nasa ya kawo masu wannan hari ba....

Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali yana mai shafe sumar kansa... Wannan mafarki da d’aure Kai yake... Waye cikin ‘yanuwansa yayi mafarki dashi...? Tambayar da ya tsaya masa a mak’oshi... Sannan mai yasa Ja’afar ya saka kaya na alfarma ba kayan bayi ba...? Sannan Maiyasa D’an uwansa ke k’ok’arin kashesa Ja’afar ya tare masa...? Shin ina Ja’afar...? Mai yasa zai tafi yabar Masarautar nan...? Sannan idan har Jafar ya cika bawa ai bazai tab’a barin Masarautar nan ba..? Toh ya akai ya sami k’arfin gwiwan barin Masarautar yana a matsayin bawa..? Wad’annan tunani sun kasa barin kwanyar Yarima Mahmood... Baccin da bai iya komawa ba, ya mik’e ya zira jallabiyarsa fara k’al kana ya fito waje....

A b’angaren Muhibbah kaw ma iya cewa da alama baccin ya k’aurace mata itama... Mafarkin mahaifanta taitayi, musamman mahaifinta da takeji can k’asar zuciyarta tamkar Yana nan a cikin Masarautar nan...
Mayafi ta d’auka ta rufa akanta kana ta fito haraban masauk’in nata... Tai jigum tana duban sararin samaniya tana hango taurari jefi jefi... Lokaci guda tunanin rayuwarta na baya na zuwa mata... Maiyasa takejin rauni cen k’asar zuciyarta...? Maiyasa takejin d’aukan fansa bai kamaceta ba...? Shin anya abu mai kyau takeyi...? Shin hak’uri da yawan afuwa baifi d’aukan fansa ba....? Toh amma ta yaya zata iya yafe masu Ta mance komai...? Wasu hawayen suka kuma gangaro mata wani b’angare na zuciyarta naci gaba da raya mata
“You’re not a bad person Saudatu... Ke ba muguwa bace, burinki na d’aukan fansa na nufin kema kin zamto daidai dasu... Ask yourself, Ki tambayi kanki Maiyasa cen k’asar zuciyarki kikejin rauni da fad’uwan gaba..?
A fili ta baiwa zuciyar tata amsa “Sabida ni mace ce wacce a halittana tun fil azal akwai rauni....!”
Take taji zuciyar nata na kuma bata amsa da fad’in “Ba haka bane... Sabida Ke ba muguwa bace, bazaki iya cutar da d’an adam kaman yanda su suka cutar dake... Saudatu Ki aje makamanki Ki bi shawarin Ansar ki komaga sabon ahalinki wanda Allah ya maye maki gurbinsu da iyayenki da ya d’auka daga gareki...!

Cikin kuka take girgiza kai tana mai furta “Toh mahaifina fah da nakeji a ajikina Yana nan raye cikin Masarautar nan... Bazan iya tafiya ba tareda na tabbatar da zargina ba...!”

Zuciyar tata taci gaba da fad’i mata “Mahaifinki baya raye Saudatu... Kawai kinsa ma ranki haka d’in ne shiyasa kike zaton hakan ne....!”

Kame kanta tai sosai had’ida tak’urewa jikin garu tana kuka sosai take furta “No no no... Ya isa....ya isa haka...!!” Kuka sosai ya kufce mata... Tana mai k’unshe bakinta da duka tafukan hannayenta biyu...

Kaman sautin kukan mutum yake saurarowa daga nesa, ya d’an dakata da tafiyar nasa had’ida kasa kunnuwansa sosai, kasancewar dare ne komin k’ank’antan k’ara sai kaji dab kunnuwanka... A hankali yake bin hanyar da yake sauraron sautin kukan na fitowa daga nan....

Cen ya hangota tak’ure ta kifa kanta da gwiwa tana cazgan kuka....
Tsaye yai yana dubanta cikeda tausayawa.... A duniyarsa baison yaga mace na kuka irin haka koda kuwa baiwace ba d’iya ba, harga Allah yakanji babu dad’i cikin zuciyarsa... A hankali yaci gaba da takowa zuwa gareta, saida ya k’araso har yanda take kana yai sallama cikin muryarsa mai cikeda aminci....

D’if kukan nata ya d’auke tamkar anyi ruwa an d’auke, dikda k’irjinta dake bugawa a hankali hakan bai hanata k’ok’arin saita kanta ba.... Tai saurin gogewa hawayen fuskarta had’ida d’agowa... A karo na farko da sukai eye contact tin bayan dawowarta Masarautar....

Yau Yarima Mahmood ne tsaye a gabanta, tabbas abubuwan da suka faru wancan lokacin sun shiga dawo mata daki daki, saidai ya zama dole tai k’ok’arin saita kanta ta tattaro duka jarumtarta ta had’e waje guda...
Ta k’ak’aro murmushi a hankali kana ta mik’e tsaye tana mai gyara mayafinta..
“Barka da dare Rankashi dad’e..!” Tai maganar tana mai duban k’Asa...

Yarima Mahmood da har lokacin hannayensa Ke hard’e ta baya jinjina mata kai yai a hankali kana yace “Barkanki...! Ke kuwa mai kikeyi a nan cikin daren nan.....?”

Ta d’an saci dubansa jin tambayar da ya jefo mata kana Ta kuma k’ak’aro murmushi tace “Babu komai rankashi dad’e ni bak’uwa ce a Masarautar... I guess rashin sabo da wajene yasa bacci ya k’aurace min shisa na fito nan na zauna....!” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yatsun hannunta....

Jinjina kansa yai a hankali kana yace “Shiyasa kike kuka...? Ko kinsan sautin kukanki ka iya hana wasu halittu samun nitsatsen bacci cikin Masarautar nan...?”

Wannan karon d’agowa tai tana dubansa sosai kana ta d’an kauda fuskarta gefe....

Ganin tayi shiru babu amsa yasa Yarima Mahmood gyara tsayuwarsa had’ida d’aga kansa sama kad’an....

“Bakiyi kamanni da bayi ba... Shin wacece Ke...?!” Ya k’arashe yana mai sauk’e idanunsa akanta da alamun tuhuma...

Ji tai wani abu ya tokare mata mak’oshi, tai k’ok’arin daidaita natsuwarta
“Bak’uwar Umaima ce ni Rankashi dad’e....!” Tai maganar tana mai sadda kanta k’asa...

Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta tamkar wanda ya tina wani abu kana yace “Muhibbah..?!”

Ta d’ago itama tana dubansa, lokaci guda ta sami kanta tana mai jinjina masa kai alamun eh....

Yarima Mahmood ya gyara tsayuwarsa kana yace “It was you then...Kece wacce kika taimaki d’iyata Zahra...”

Taji murmushi na zuwa saman fuskarta kana tace “Nayi abinda ya kamata ne your highness...!”

Tinda suka soma magana sai yanzu ya sinkayo wani zak’i cikin muryar nata bayan ya ambaci


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login