Showing 90001 words to 93000 words out of 257774 words
Chapter 31 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt
baka yawan rai k’aramin had’ari na samu amma da sauk’i...!”
Yai shiru tamkar mai nazari sai kuma yace “Likita ya dubaki....?”
Wannan karon Giwa ce ta basa amsa da fad’in “Karka damu Sadauki lafiya lou take wannan raunin ba komai bane, na riga masa likita ya dubata...”
Jakadiya ta had’iyi k’uncinta jin abinda Giwa ta gama fad’iwa Mahmood, lallai ta yarda Giwa tayi nisa a makirci tinda har ita da take ta hannun damarta bata k’yale ba...
Jinjina kansa kad’an Mahmood yai had’ida mata fatan samun sauk’i Giwa na fad’i masa zasu wuce gidan Wambai gaisuwa...
Jinjina kai yai cikeda girmamawa yace a sauk’a lafiya... Tawagar Giwa suka sa kai ana ci gaba da wasa Giwa duk wani taka k’afarta da zatai a k’asa..
**
Video call yau d’in yaji ya kirata sabida kewarta da yai sosai, yana zaune Office d’insa saman kujerarsa na duba marassa lafiya yai mata K’uri ta fuskar wayar nasa yanda take ci gaba da goge gwiwar hannunta data karje with cotton wool... Lokaci guda take ci gaba da fad’in “I couldn’t believe what I saw either, I mean... Mai ya kawo sunana rubuce jikin k’yalle, and what worries me the most shine k’yallen da sunana Ke rubuce bisa anyi crossing... Mai ahalin AbdulJabbar suka aiwatar da sunana...”
Katseta Ansar yai da fad’in “Wait what’s that... Are you injured...?”
D’an fuzar da fuci tai a hankali tana mai gyara zamanta take kuma duban hannun nata kana tace “Oh! Just a small scratch but I’m okay... Kar ka damu likita...”
Fuzar da huci yai a hankali yana mai kauda kai gefe cikeda damuwa “Hibbah bamu yi haka ba... You promised me you won’t put yourself in harm ways.. You promised me you’d take good care of yourself... Toh mai nake gani yanzu...!” Ya k’arashe cikin d’an tsawatarwa...
Fuzar da huci tai a hankali kana tace “I’m sorry..Okay, it won’t happen again...I’d be more careful next time...Yayi maka..!” Ta k’arashe cikin raunin murya...
Shafa fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kana yace “Do I have a choice..!”
Dariya yaso bata ta d’anyi kad’an yayinda Ansar ke fad’in “Aw Wato ma dariya na baki...!”
Muhibbah tace “Gani nayi Likitana ya fini damuwa da lafiyata...!”
“Of course you’re right... Na fiki damuwa da lafiyarki... My next patient zai shigo Hibbah.. Do you want me to attend to them...?!” Yai tambayar cikin kashe murya...
Murmusawa tai kad’an tace “Likita bakada dama... We talk later.. Take care.. Bye..!”
Katseta yai da fad’in “I love you...!”
Murmushi kurum tai cikin tsananin sanyin jiki wanda ita kanta bata San dalilin jin hakan ba kana Ta katse kiran ta koma cikin kujera ta zauna sosai tana mai lumshe idnunta.. Abubuwa ne da dama cunk’ushe cikin zuciyarta...
**
A can gidan Wambai kuwa yanda aketa karb’an gaisuwa Gimbiya Zeenatu ma da tata tawagar Sun halarta... Raheema sai faman aikawa Juwariyya muguwar kallo take, dik itace ta janyo Mahmood yanzu bai kulata, gashi ta kula sam maganinsu baiyi tasiri akan Mahmood d’in ba tinda gashi shiru shiru har yanzu babu wani canji tun ranan data barbad’a maganin a sashensa... Tai k’wafa tana mai kuma hararan Juwariyya...
Ga mamakin Raheema Murmushi Juwariyya Ta sakar mata kana ta tura mata sak’o ta waya
_Haba mutumiyar ko gaisuwa babu, ai ya kamata Kimin ta’aziya for old time sakes... How about idan muka keb’e Ta baya, I’ve something special for you..!_
Raheema ta karance sak’on ta kuma d’agowa tana duban Juwariyya dake ci gaba da sakar mata murmushi tana mai mik’ewa tsaye kana ta shige wata k’ofar.. Tana shigewa Raheema ma ta mik’e tana mai gyara mayafinta had’ida satan idanun mutane musamman Su Zuhra da Zahra da Umaima dake zaune daga can gefe... Ta d’an rank’wafo taceda Zuhra “Best bara na d’an amsa waya...”
Zuhra ta jinjina mata kai tana mai ci gaba da jan cazbaha dake hannunta Raheema tasa kai tabi k’ofar da taga Juwariyya tabi...
Raheema na shigewa Juwariyya ta maida k’ofar ta rufe... Raheema ta finciko wuyan Juwariyya tana fad’in “How dare you... Laifinki ne Mahmood bai kulani yanzu, you messed everything up...!”
Fincikewa Juwariyya tai tana fad’in “Ki saurareni Raheema shisa na kiraki wajen nan to make it up to you.. Amma idan bazaki saurareni ba fine kina iya tafiya...!” Ta k’arashe cikin huci...
Gyara tsayuwarta Raheema tai tana fad’in “Fine, tell me mai kike son sanar dani... Wani amfani abinda zaki sanar dani zai min...?!”
Juwariyya ta murmusa kad’an kana tace “Zai muku amfani both you and Mahmood, it might help you win him back.... Shi kuma Ya Mahmood zai masa amfani yasan yanda zai ya kare kansa da mulkinsa...!”
Raheema ta d’an gyara tsayuwarta tana fad’in “Mai kike nufi...?”
Juwariyya ta fuzar da iska kad’an kana tace “You know nafi kowa san Ya Mahmood ya d’ale Karagar nan... Banson Yaya na ya d’ale...”
Raheema ta katseta da fad’in “Ke naji naji... Just go straight to point da Allah bansan iyayi...!”
Juwariyya tace “I saw my brother and Ya Yazeed together at the hospital before my father passed away...!”
“So, sai mai dan kin gansu tare..Ta yaya hakan zai taimaka min win Mahmood back...?”
Juwariyya ta fuzar da fuci a hankali... “Dad’ina dake baki cin Riban zance Anty Raheema.. Ahalin gidan nan da ahalin Sarki AbdulJabbar basa jituwa anyi masu wannan shaidan, so zai matuk’ar wahala for those two to get along, naji sun ambaci sunan Ya Mahmood, and one thing to be certain of shine ba abin arziki suke k’ullawa ba..They might be planning something against him... Ya kamata ki sanar da ya Mahmood yasan yanda zai fuskanci wad’annan biyun kin fahimta...”
Shiru Raheema tai tamkar mai nazari sai kuma ta jinjina kanta tana mai sakin murmushi a hankali...
Juwariyya Ta murmusa tace “Na gyara abinda na b’ata I guess...”
Kafad’anta kad’an Raheema ta dafa kana tace “Baki tab’a birgeni irin na yau ba... I must say thank you...” Ta k’arashe tana mai nufan k’ofa... Saida ta fice da wasu dak’ik’ai kana Juwariyya ta fice....
Ko ba komai yau ta sami abinda zatai amfani dashi ta karkato hankalin Mahmood zuwa gareta, amma kafin nan ya kamata ta soma shan cikin Yazeed taji mai yake shiryawa kan Yarimanta... Tai k’wafa tana jinjina bak’in zuciya irinta Yazeed wanda har zai kaisa ga halak’a d’an uwansa...
**
Yazeed ya kuma gyara zamansa yana duban Ubandoma daketa faman had’iyan abincin da Yazeed d’in ya kawo masa hannu baka hannu k’warya... Ya ida ci yana mai tand’e yatsu yake fad’in “Godiya nake rankashi dad’e shakka babu yau d’in Sun mance dani... Yunwa kaman zai karni sai gashi Allah ya kawoka, Ubangiji ya saka da Alkhairi Rankshidade...!”
Yazeed ya katsesa da fad’in “Daina godiya tun yanzu kasan ance komai yanada lada...!” Yai maganar shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa...
Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana k’walalo idanu yake duban Yazeed... Yazeed ya kuma gyara rigar kufta dake sanye jikinsa cikin yanayin salonsa da yafeyi idan yana shirya wani mugun abin... “Ubandoma na tabbata ka yarda dani tinda har na baka abinci ka ci without thinking twice... Ba tareda kayi wani tunani ba sabida yunwa dake azalzalanka ka amsa kaci...!” Ya d’anyi fasali yana mai rage girman idanunsa yake furta “Baka tunanin zan iya sanadin rayuwarka yanzu a wajen nan...?!”
Gumi ne ya shiga karyowa Ubandoma, ya shiga zaro idanu waje jikinsa na rawa yake furta “Kamin rai Allah shi baka yawan rai... Wayyo na shiga uku ni jikan Tandu inada yara kada ka maidasu marayu Allah shi baka yawan rai...!” Ya k’arashe yana hawaye had’ida had’e hannayensu biyu waje guda alamun rok’o...
Murmusawa kad’an Yazeed yai da gefen bakinsa kana yace “Kar ka damu ni ba mugu har haka bane... Abu guda yanzu nakeso kamin shine ka biya ladan abinda na maka yau...!”
Ubandoma ya zaro idanu yana fad’in “Mai kenan Rankaidad’e...?”
Yazeed ya kuma murmusawa kad’an yace “Da kyau Ubandoma, kai d’in kanada saurin fahimta... Nasan ba Yayana Mahmood bane ya baka umarnin shiga gidan Wambai... Kuma ban damu nasan ko wanene ya kake ma aiki ba, iyakacin abinda na sani shine kaid’in munafukin Mahmood ne... Toh inaso kai amfani da wannan shara taka ta iya makirci da munafunci ka d’aura alhakin dik abinda kai akan Mahmood... Ka sanar da Masarautar nan cewa Mahmood shine bak’on Buzu kuma ya turaka ne domin ka kashe Wambai... Ka fahimta...?”
Da tsananin mamaki Ubandoma ke dubansa. Lokaci guda ya shiga girgiza kai yana duban Yazeed d’in yake fad’in “Ta yaya zan soma k’age irin wannan Rankaidad’e... Da dai ka nemi wani abin amma banda wannan...!”
Huci kurum Yazeed yake yana dubansa rai b’ace... Lokaci guda ya shak’o wuyan Ubandoma yana fad’in “Kai k’ask’antaccen Bawa, kai kayi kad’an Yarima Yazeed ya nemi wata alfarma wajenka... Umarni kawai zan baka kabi .... Ka fahimta...?!!!” Ya k’arashe yana mai jifada Ubandoma gefe wanda tuni ya zube yana haki had’ida sosa wuyarsa dake masa zogi, sai tarin azaba yake...
Yazeed ya d’an yarfe hannunsa kad’an had’ida gyara zaman zobensa da ya kusa ficewa kana ya kuma duban Ubandoma, murmushi ya sakar masa wannan karon kana yace “Idan ma baka goyi bayana kayi abinda na umarceka sanin kanka ne bazasu barka da rai ba... You know perfectly well how they do things here... Bazasu barka ka fita da rai dubu ya faru da haka... Kuma kar ka mance Wambai ya riga ya rasu fitarka a nan a halin yanzu zai matuk’ar wahala...!”
Ubandoma ya kuma zaro idanu yana maimaita “Wambai ya rasu...?!”
Yazeed ya murmusa yace “Karka damu idan ka bani had’in Kai zan fitar dakai muddin na zama Sarki... Sannan zan baka matsayi mai girma, zan fifitaka fiyeda yanda ba’a tab’a fifitaka cikin Masarautar nan ba... Kawai Kayi abinda na umarceka shikenan ka tsira...!” Ya k’arashe cruel smile d’in nan nasa saman fuskarsa...
Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana duban Yazeed da tuni yakai k’ofa.... Ya kuma juyowa kaman zai magana wayarsa Ta d’auki ruri Raheema ce mai kiran nasa...
Yana d’agawa daga d’aya b’angaren tace “You and I need to talk... Let’s meet up...!” Bata jira amsarsa ba Ta katse kiran....
**
Zama Muhibbah tai tana kuma warware zanen nan had’ida nazarinsa, nan Ta d’auko wayarta Ta kunna ta had’e zanen tana k’are masu kallo... Babban abinda ya bata mamaki shine duk yanda tai zaton zanen nan abu guda ne ashe ba abu guda bane, sunada salo da tsari iri guda amma Sun banbanta kad’an... Ita kanta bazatace ga difference d’in tai figuring out a halin yanzu ba hasalima sosai kanta ya kuma shiga duhu... Ga dai hikima iri guda anyi amfanida wajen tsara Taswiran amma sun banbanta da juna... Ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya a hankali, ya zatai yanzu... Lumshe idanunta tai a hankali ta tafi duniyar tunanin abinyi... Idan har tana so ta fahimci zanen nan Ta iya warwareta ya kamata ta zaga cikin gidan nan ta k’arewa ginin kallo tunda gida ne na sarauta sannan ta shiga museum na cikin Masarautar nan taga Taswirori na tarihi wala’alla Ta sami wani clue gameda wannan Taswira mai wahalan fasaltuwa da fahimta... Watak’ila Ta iya samun wani HASKE a can Zauren Ajiya na kayan tarihi dake cikin Masarautar...
Sauri sauri ta mik’e ta shirya tsaf, tai shiga irinta masu mulki harda Alkyabba, sosai shigar ya amsheta, nan ta fito tana taku cikeda k’asaita irinta masu mulki...
Tana tafe take tinanin toh wa zata soma tunk’ara tunda hankalin mutanen gidan gaba d’aya bai jikinsu sabida rashi da aka masu, Toh kodai ta kirawo Fu’ad ne.... Toh amma bataso ake ganinsu tare balle wani yai suspecting wani abu... Kawai ta yanke shawarin tambayan Sarkin Fada...
A haraban Masarautar ta tadda wasu bayi ‘yanmata guda biyu yanda ta tanbayesu suyi mata jagoranci zuwaga Sarkin Fada, babu musu bayin sukace Ta biyosu... Muhibbah tasa kai tana tafe biyedasu
Can Rumfar Sarkin Fada suka taddashi tareda wasu Fadawan, suna ganinta suka isa sukai mata gaisuwa...
Muhibbah ta dubi Sarkin fada tace “Da Allah wani tambaya nake...!”
Sarkin Fada yace “Rankidad’e kyakkyawa fad’i tambayarki..!”
Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Shin yaushe ne ake bud’e d’akin ajiya na cikin Masarautar nan... So nake nasan wasu al’adu na cikin gidan nan kafin na tafi...!”
Sarkin Fada da sauran Fadawan suka dubi juna jin tambayar da tai... Muhibbah ta bisu da kallo gaba d’ayansu yanda suke kallon kallo ma juna...
Murmushin yak’e tai wannan karon kana tace “Ah shikenan, Ina tunanin ba ko yaushe ake bud’ewa ba kenan...!”
Sarkin Fada yace “Ba haka bane Rankaidad’e Mai kyau, ai Wato idan ba ahalin gidan nan ba Sarkin Fada baida hurumin bud’e miki Ma’ajiyin Gidan nan... Yin hakan zaisa na shiga matsala...!”
Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tace “Toh shikenan babu matsala, na gode sosai...!”
Har tasa kai ta juya saiga wani bawa guda ya k’araso yayiwa Sarkin Fada magana a kunne...
Tana tafe ta sinkayo muryar Sarkin Fada na fad’in “Rankidad’e Mai kyau... Dawo da baya... An umarce Sarkin Fada ya bud’e miki duk wata zaure da kika buk’ata cikin Masarautar nan.... Sarkin Fada yana neman afuwanki...!” Ya k’arashe yana mai baza babbar riga had’ida mik’ewa...
Ita dai sai ‘yan waige waige take tana mamakin waye yai umarni da a bud’e mata Zauren Ajiya....
Tafiya mai d’an tazara kad’an sukai kana suka iso Zauren ajiyan kayan tarihi na Masarautar.... Sarkin Fada yasa mabud’i ya bud’e... Ta ware idanunta tana duban dogon ginin mai tsawon gaske da dadd’en tarihi... A hankali tasa k’afarta tana takawa cikin ginin tana duban manyan zanen hotunan bayi da masu sarauta da irin yak’i da akai a shekarun baya shekaru masu yawan gaske na wasu k’arnin....
Ji tai k’ofar mai nauyin gaske ya rufe da ita a ciki, dan bata ankara ba sai jin sautin rufuwarsa tai gashi abinka da tsohon gini mai girman gaske ko ina saida ya amsa... Ta waigo cikin sauri tana duban bayanta, gabanta ya yanke ya fad’i ganinsa da tai tsaye bayanta hannayensa a hard’e Ta baya shid’inma ita yake duba...
Yana sanye cikin bak’ar rigar Kufta wanda ya fito da asalin Farin fatarsa, shigar kufta yai gaba d’aya dan harta takalman k’afafunsa bak’ak’en Kuftane da akai masu kwalliya da farin zare mai d’aukan idanu k’warjininsa sai ya cika wajen gaba d’aya....Tai saurin janye idanunta daga barin dubansa k’irjinta naci gaba da bugawa...
**
Gimbiya Zeenatu na kishingid’e a parlornta na alfarma bayan sun dawo daga ta’aziyan gidan Wambai Hadimarta ta shigo ta sanar da ita shigowar Yarima Yazeed...
Sosai tai mamakin jin Yazeed yazo gaisheta har sahsenta, kodashike ba abin mamaki bane tunda rashi akai gaisuwan ta’aziya ya shigo mata... Tuni Ta basa izinin ya shigo... Ya kuwa shigo cikeda k’asaita, sukai gaisuwa irinta masu mulki kana yai mata ta’aziya... Gimbiya Zeenat taji dad’in shigowarsa tuni aka cika gaban Yazeed da kayan mak’ulashe da tand’e tand’e, ya kuwa zauna sosai kaman wani mutmin arziki, Gimbiya Zeenat ta mik’e ta basa waje dan ya saki jikinsa yaci kayan motsa baki da aka kawo masa.... Haurawarta sama da kad’an Raheema ta fito cikin gayu da kwalliya... Yazeed dake kishingid’e irin zaman masu mulki murza zobban hannunsa kurum yake yana k’arema Raheema dake sauk’owa kallo from head to toe....
*Sak’on gaisuwa mai tarin yawa tareda fatan Alheri gareku msoyana... Sameena na kaunarku a dik yanda kuke..!*
SameenaAleeyou📚
[8/1, 8:41 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*39*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Tai k’ok’arin tarttaro natsuwarta gaba d’aya, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskrta “Your Highness... Barka da yammaci.!” Tai maganar tana mai daidaita tsayuwarta...
Kaman bazaice komai ba har wannan lokacin, sai dubanta da yake daga nan yanda yake tsaye hannayensa hard’e Ta baya... Gaba d’aya sai tajita ba daidai ba, zuciyarta yaci gaba da bugawa da sauri sauri... Maiyasa yake dubanta haka..? Kodai ya karanceta ne ya soma zarginta... Kai inaa hakan bamai yuwa bane, musamman yanzu data soma samun hanyar da matsalanta zai warware.. She can’t allow someone to get suspicious of her...Tai saurin d’ago idanunta aiki nan idanunsu ya sark’e waje guda.. Fuskar nan nasa tamau... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi ya kasa shigewa....
Gyaran murya Tai kad’an tana k’ok’arin had’o kalamai saman bakinta “Tuba nake your Highness... Na zaci kowa zai iya ziyartan Zauren ajiya na.....” Burki tai ma kalaman nata ganin ya soma d’ago k’afafunsa yana takowa cikeda k’asaita... Zuciyarta taci gaba da bugawa ganin ita yake nufowa... Tai saurin lumshe idanunta tana k’ok’arin karanto duk addu’an da yazo bakinta...
Dai dai gabanta Mahmood yaja ya tsaya har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya yai k’uri ma labb’anta yanda take motsasu a hankali alamun tana karanto addu’a, a hankali yake k’arewa fuskar nata kallo tin daga labb’anta zuwa karan hancinta har zuwa idanunta da suke a lumshe masu cikeda tsoro... Wani irin yarr yaji gaba d’aya illahirin jikinsa... Yanayin da ya jima baiji hakan ba a tsakanin lokacin... A hankali ya janye idanunsa daga barin duban nata, cikin takunsa mai cikeda k’asaita ya soma takawa har ya isa gaban wani k’aton hoto mai k’unshe da zanen mutane cikin shiga irinta mulki da sarauta... Ya kafe hoton da idanu hannayensa hard’e ta baya...
“Halittanmu baisha bambam da mutanen da sukazo kafin mu ba, saidai halayya da d’abi’unmu sun banbanta...Wani zamani muke ciki wanda cin amana da yaudara, zalunci da k’eta su sukafi jagoranci sama da kyawawan d’abi’u masu nagarta...!” Ya k’arashe yana mai juyowa...
Tinda ya soma magana take k’ok’arin bud’e idanunta a hankali har Ta ida waresu...
Daga nan yanda yake tsaye yai gyaran murya kad’an yace “Having curiosity aroused..?!”
K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e tai ta d’ora saman labb’anta “K’warai your Highness... Masarauta mai cikeda d’inbin tarihi da kyawawan d’abi’u had’ida al’adu irin haka... Babu wanda zaiso ya shigo cikinta ya tafi ba tareda ya yi dubi da wad’ann kyawawan hikayoyi da suka aje Martaban Masarautar har Ta kawo tsawon wannan lokaci...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta..
Baisan dalili ba amma tunda ta soma magana yakejin kumatunsa na motsawa kad’an sihirtaccen murmushi da ba lallai ka fahimci hakan ba shine sama fuskarsa tasa...
Ya d’an gyara tsayuwarsa yana dubanta sosai, saida yai taku kaman guda uku, sai kuma yaja ya tsaya “You seemed so sure...?!” Ya fad’i yana dubanta....
Ta kuma murmusawa kad’an tana mai k’arasawa jikin wani k’atoton zane mai d’aukeda hoton wani basarake sanye da rawani da alkyabba wanda ko ba’a ce ba kasan dadd’en zane ne... Tasa hannu tana shafa wasu rubutun da akai k’asan zanen da haruffan ajami na Arabic... Lokaci guda taci gaba da furta “An samu Masarautar ne ta hanyar nagartattun mutane wanda jajircewarsu da k’wazonsu had’ida gaskiyarsu da son gaskiyarsu sune suka had’u suka kafa Daular... Kuma