Showing 57001 words to 60000 words out of 257774 words

Chapter 20 - MUHIBBA Book Complete by Sameena Aliyou.txt

lugar es aburrido..Por eso le pedí a la tia que viniera... Espero que no te importe Paa (Wajen nan babu dad’i Paa, is kind of boring.. Shisa nace Tia tazo... I hope you don’t mind Paa)

K’asaitaccen murmushi ya sakar mata kana shima ya amsa cikin harshen spanish “Cualquier cosa por mi princesa..” (Duk abinda Gimbiyata take so)

Itadai Raheema sai dubansu take tana faman ci gaba da murmushin yak’e dan bama tasan mai suke fad’i ba....

Lokaci guda ta d’an gyara zamanta cikeda k’issa kana Ta dubi Zahra tace “Daughter nima dai za’a koya min Spanish d’in nan yanda nan gaba za’ake tattaunawar dani...!”

Murmushin da yafi kama da yak’e Zahra tai kana tace “Sí Señora, I don’t have problem with that..!”

Raheema ta kuma sakin murmushin yak’e kana tace “Toh yanzu dai a fassara min mai Daughter da Paa suka tattauna..”

Murmusawan Zahra Ta kumayi dan already Mahmood ya tashi daga parlorn ya shige wani k’ofan yana amsa kiran Turaki

Zahra Ta d’an gyara zamanta kana tace “Pronto lo verás con tus ojos”

Raheema Ta kuma yin yak’e kana tace “Ai kin kuma shigar dani duhu daughter...!”

Murmusawa Zahra tai kad’an kana tace “Cewa nai da sannu idanunki zasu gane miki...!”

Raheema Ta kuma sakin murmushi kana tace “Oh I guess babban surprise za’a min...!”

Zahra Ta murmusa da gefen baki kana tace “Créeme uno muy grande” (Ki yarda dani, Babba ma kuwa)...

Raheema Ta kuma sakin murmushi cikeda jin dad’in babban surprise d’in da Zahra zatai mata, watak’ila Zahra ta fara sonta da mahaifinta ne... Ta kuma sakin murmushi tana mai gyara zamanta, lokaci guda tana mai kuma initiating fira tsakaninsu da Zahra...
**

Muhibbah ta dubi Umaima tana mai girgiza kai “What..! No gaskiya ni bazanje sashen Yarima Mahmood ba, mai kike tinanin za’a d’auken a Masarautar nan... Zahra yarinya ce bazata fahimci komai ba... Ki k’yale zancenta kawai...” Ta k’arashe tana mai tufke sumarta data ida tajewa cikin ribbon...

Umaima ta zauna saman stool kana tace “Babu wanda zai kawo komai, besides Raheema na cen... Kika sani ko da amincewarsu gaba d’aya suke so kije cen... It is not as if kin aikata wani abu maras kyau ne, ga Zahra ga kuma Raheema duka suna cen ba Ke kad’ai bace...”

Muhibbah ta kaikaito tana dubanta kana tace “Raheema na cen..?”

Jinjina mata kai Umaima tai kana tace “K’warai kuwa...!”

Lokaci guda Muhibbah ta juyo tana kuma duban kanta a madubi, ta saki murmushi mai k’unshe da ma’anoni kana ta juyo taceda Umaima “Alright fine... Kunci gari Keda Zahra...!”

Umaima ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa ko ke fah, maza tashi tashi ki shirya.. I’ll help you get ready....”

Take Umaima ta tayata shiryawa cikin kaya na alfarma, dikda babu wani kwalliya saman fuskrta tayi kyau har ta gaji...
Umaima tai mata K’uri kana tace “Inama ku had’uda Prince F a hanya sai ya kusan sumewa ina fad’i maki....

Hararan wasa Muhibbah Ta aika mata kana tace “Kedai kinji dashi.. Must I have to wear all this...? Ni fah ba d’iyar Saraki bace....”

Umaima na kuma sakin murmushi take fad’in “Soon zaki zama matar Saraki, so better get used to it...”

Muhibbah ta girgiza kai a hankali kana tace “Au har kin yanke...?”

Umaima Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa d’an sarki ma Sarki ne...!”

D’an murmusawa sukai gaba d’aya a tare kana suka nufo k’ofa....

Suna isowa k’ofar Yarima Mahmood Umaima ta juya tana fad’in “Ai Ke kad’ai zaki shige dan ni ba’a bani izinin shigowa ba...!”

Muhibbah ta dubeta baki sake kana tace “Wai da gaske kike..?”

Umaima ta d’aga mata gira tana fad’in “Sosai kuwa... A fito lafiya Rankishi dad’e..!” Tana ida fad’in haka ta juya tana murmushi

Sauk’e fuci Muhibbah tai a hankali tana duban k’ofar sashen.....




SameenaAleeyou 📚
[6/29, 4:49 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*



*025*




*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Daga yanda yake tsaye ya baiwa k’ofa baya yana fuskantar tanfatsetsen window dake gabansa tai tsaye tana dubansa... Wani irin muguwar fad’uwan gaba taji sanda ta hangi gadon bayan Mahmood, yanda kasan mai laifi yaga wanda yaima laifi hakan nan ta tsinci zuciyarta cikin wannan yanayi... Maiyasa dik sanda ta kasance taredashi takeji wane irin al’amari na daban, maiyasa dik irin tsanar da tai masa yafi k’ullatanta a bayan idanunsa, maiyasa da zaran tai arangama dashi sai ta nemi wannan tsanar ta rasa, sai ta rasa control ta kuma rasa wane irin yanayi ne take tsintar zuciyarta ciki.... Wayar da yakeyi ne ya tafi da hankalinta... Ta d’an lab’ab’e kad’an jikin k’ofar tana sauraron abinda yake fad’i cikin wayar “I can’t be mistaken Turaki, na tabbata naga wannan mutumin, kuma ka sanni I won’t rest har sai na isa k’arshen al’amarin nan.. Dole za’a k’ara tsaro cikin gidan sannan za’ai installing CCTV cameras all over the Palace koda hakan na nufin karya k’a’idan Masarautar ne, hakan ne kawai zai bamu daman warware wasu al’amara dake faruwa cikin gidan cikin sauk’i....

Gabanta ya yanke ya fad’i, cikin zuciyarta take kuma nanatawa CCTV cameras, hakan na nufin za’a ganta kenan... Kai no no way bata fara komai ba, maiyasa Mahmood ke shirin ruguza mata shirinta... Idan tai sake tabbas Mahmood zai lalata mata dik wasu shirinta tun kafinma Ta fara... Fuzar da fuci tai a hankali sanda muryarsa ya kuma dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi...

Da mamaki saman fusakarsa yake dubanta...

Tai k’ok’arin dawowa cikin hayyacinta, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta...
“Your Highness, barka da dare...!” Ta fad’i murmushin saman fuskarta...

Har lokacin dubanta yake fuskarsa babu alamun walwala, baice da ita komai ba saima had’e hannayensa da yai waje guda yana dubanta, wane irin duba yake mata tamkar duba na tuhuma ko na mai laifi, take taji jikinta yayi sanyi sosai, domin kaw sosai ya tsareta da wannan idanun nasa masu firgitar da dik wani mai laifi... Ta had’iyi miyau da k’yar tana kuma satan kallonsa... Tamkar ta juya ta koma a guje haka taji...

Neman kalamai ta soma saman harshenta dake faman sark’ewa tana furta “Am...Am... I’m sorry your Highness, I... I was told that..!”

Muryar Zahra ta sinkayo kaman daga sama ne ya katse mata bayanin da take da k’yar da baki da hannaye
“Tia Hibbah...! I thought you wouldn’t come... Sannu da shigowa... k’araso, shigo...!” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Muhibbar suka shige cikin parlorn... Ita dai Muhibbah gaba d’aya jikinta ba’a sake yake ba, sai faman waigowa take tana kuma duban Mahmood da yai tamkar baisan suna wajen ba.... Ga mamakinta sai kuma taga bai nan da alama k’ila saman bene ya haye ko ficewa yai gaba d’aya.... What if ya ganeta ne... What if ya fara saka shakku da kokonto akanta... Tabbas gaining trust d’in Zahra kawai yayi kad’an dole ta sami yardar Mahmood... Bazata bari ya saka shakku akanta ba, sannan wannan cameras da yake maganan installing ko ina cikin gidan babban barazana ne ga shririnta....

Raheema dake faman zuba had’edd’en soup cikin bowl tana fad’in “Ehen Daughter you need to taste this soup kafin Paa ya tasting, I cooked it myself... I really want to hear your opinion....!!” Burki taiwa kalaman nata sanda ta juyo rik’eda bowl d’in tana duban abin mamaki... Wai dama wannan shegiyar uwar shishigince surprise d’in da Zahra Ke fad’i... Baki sake take dubansu... Bata ankara ba saiji tai bowl d’in ya fad’i tauu saman k’afarta, soup mai zafi dake ciki ya k’ona mata k’afa ga tangaran d’in ya yanka mata fata... Ta saki k’aran azaba daidai lokacinda Muhibbah ta isa da sauri tana k’ok’arin taimaka mata...

Raheema ta finciki k’afarta tana fad’in “Don’t you dare.... How dare you..!! Mai ya kawoki nan... You’ll pay for this munafuka algunguma mayya...!!”

Daga Zahra har Muhibbah tsaye sukai suna mata duban mamaki... Zahra da tsoro ya nuna saman fuskarta tace “Aunty Raheema meke faruwa, Mai Tia taimaki... Taimakonki fah take son yi... Look you’re wounded, Deja que ella te trate la herida ... es su profesión” (Ki k’yaleta ta duba ciwonki fanninda ta k’ware ne...)

A zuciye Raheema dake tsananin fuci ta juyo tana duban Zahra kana Ta soma fad’in “Shut your mouth you little brat, this is all your fault...How could you... Ta yaya zaki katse min hira da mijina ki kirawo mana wannan shu’umar wajen nan... Just who do you think you are..!? Na jima da sanin baki so na auri mahaifinki, but ban zaci munafuncinki yakai har haka ba, tell me so kike Ki lik’awa babanki ita ko mai da zaki gayyato mana ita...? Toh bari kiji na fad’a miki, Yarima Mahmood is mine, he’s mine... I don’t care if you’re his daughter... The next time da kika sake yunk’urin aikata wani abu mai kama da haka ni da kaina zan hukuntaki, maras kunya kawai...!”

Zahra da tuni ta soma huci da hawaye, lokaci guda take furta “You’ve no right to talk to me that way..! You are not my mother, you can’t punish me... You’ve no right over me...I hate you, I hate you.... And yes I never liked you, I don’t want you for my father... To hell with you..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na sauk’o mata....

A zuciye Raheem Ta mik’e zatakaiwa yarinyar mari Muhibbah tai saurin rik’e hannun Raheema tana mai sakin huci itama...
“Don’t you dare lay a finger on her...!!”

A guje Zahra ta nufi upstairs tana kuka sosai take kiran mahaifinta....

Raheema ta dube Muhibbah shaye da mamaki kana tace “Excuse me...! Wacece Ke... How dare you interfere..! Sakar min hannuna kafin na sakaki kiyi nadaman da baki tab’a irinsa ba tsawon rayuwarki.... Munafuka mai bin mazan mutane..!!”

Wannan karon murmushi Muhibbah tai kana tace “Why...? Tsoro kikeji...? Baki yarda da kanki bane...? How many times do I have to tell you babu abinda zanyi da Yarimanki... Ni inada Sarki already... Bana buk’atan Yarima, amma ga shawari guda d’aya... If you’re scared of losing your prince... Then ki sami igiya mai k’arfi ki d’aure zuciyarki dana d’iyarsa waje guda... Aikin banza kike idan har yarinyar nan bata k’aunarki... Shawari ce..!!” Ta k’arashe tana mai sakin murmushi saitin fuskar Raheema... Tana ida fad’in haka tasa kai tai ficewarta daga sashen gaba d’aya, tana tinanin mai zatai gameda batun dasa cameras a cikin gidan da Mahmood Ke k’ok’arin yi, she really needs to come up with something, dole tasan yanda zatai tasa a datse batun saka cameras cikin gidan....

Haka Raheema tabi bayan Muhibbah da kallo har ta b’acewa ganinta, kumafa abinda Muhibbah ta fad’i mata gaskiya ne... Idan har tana son samun kan Mahmood da gaske toh fah dole tai hak’uri da wannan sangartacciyar yarinyar har ta samu ta mallakesa, idan yaso daga baya sai tasan yanda zatai da yarinyar.... Tana ida tinanin ta d’aga idanu tana duban benen, lokaci guda ta kuma sauk’e huci a hankali kana ta soma jan k’afarta mai ciwo ta nufi benen da d’ingishi...

Tana haurawa ta hango Zahra zaune parlorn saman ta tak’ure waje guda ta kifa kanta cikin gwiwarta tana kuka mai tsuma zuciya....

Ta gallawa yarinyar harara tana mai yatsina fuska, lokaci guda tai k’ok’arin saita kanta kana ta nufi cikin parlorn cikeda k’issa, gefe da Zahra ta isa ta zauna had’ida kwantar da murya “Daughter I’m sorry... Believe me I didn’t mean to... Kiyi hak’uri dan Allah... Please don’t tell your Paa about this... Kiyi hak’uri rainane ya b’aci amma bana nufin dik abinda na fad’i kinji koh....!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin rungumo Zahra...

Idanunta masu zuban hawaye ta d’ago tana duban Raheema dashi kana tace “Don’t touch me... Karkizo kusa dani... Bana sonki da Paa d’ina... Bana so ya aureki... Ke muguwa ce... Ni Ki k’yaleni... Just go away..!!” Ta k’arashe tana mai kuma kifa kanta cikin k’afafunta...

Takaici ya kuma turnuk’e Raheema a mak’oshi, batasan Mahmood da matarsa wane irin goyo sukaiwa d’iyarsu ba, shakka babu goyon turai Mahmood yai mata shisa bata ganin mutane da gashin ido, an gama sakalta yarinyar sai abinda take so... Ji take kaman ta d’add’auketa da mari amma sai tai k’ok’arin saita kanta sanda ta tuna kalaman Muhibbah... A hankali ta mik’e tana kuma duban Zahran kana ta fice daga parlorn ta nufo k’asa...

Gimbiya Zeenatu na kwance saman kujera mai lilo na sarauta, gefe da ita kuyangace ke rik’eda parantin kayan marmari tana d’auka d’aya bayan d’aya tana ci cikeda kmasaita da mulki... Tamkar wacce aka jefota haka suka hango Raheema na shigowa na sakin huci... Kuyangin suka shiga sadda kawunansu suna gaidata, sai faman sakin huci take tana jan k’afarta dake ciwo...

Gimbiya Zeenat ta tashi daga kishingid’en da take ta zauna sosai tana duban Raheema...

“Ke kuma fah... Miye haka...?”

Raheema taja Ta zauna kujera mai duban ‘yar uwarta kana tai alamawa bayin kan cewa su fice... Babu musu suka risina suka fice gaba d’aya....

Gimbiya Zeenat tace “Ke nake saurare Raheemah, mai kuma ya faru... Ya na ganki kin dawo cikin fushi keda kika tafi zance da masoyinki.... Sannan mai ya sami k’afarki na ganki haka nan...?”

Huci kawai Raheema ke sakewa tamkar tafashesshen kunu....

Gimbiya Zeenat tace “Ke Raheema ki bud’e baki kimin magana Bana san shashashancin banza...!!” Tai maganar cikin hasala....

Raheemar ma a hasale take fad’in “Aunty ni fah na gaji, na gaji da wannan shed’aniyar d’iyar Mahmood d’in... Wannan yarinyar da kike gani sam babu alkhairi a tattare da ita....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin huci...

Mik’ewa tsaye wannan karon Gimbiya Zeenat tai kana tace “Bani labari mai ya faru...?!”

Tas Raheema ta kwashe dik abinda ya faru ta sanar da ‘yar uwarta... Da mugun mamaki Gimbiya Zeenat ke dubanta kana ta d’an girgiza kai alamun rashin yarda tace “You mean to say Mahmood baisha miyar nan da muka gama masa had’i ba..?!!”

Sai sannan Raheema ta tina ashe fah miyar da aka shirya musamman dan Mahmood an gama masa had’i da komai shine ta tuntsirar dalilin ganin Muhibbah... Ta dafe kanta cikin sauri tana mai furta “Na shiga uku Aunty wllhi baici ba...!”

Saukan wane irin jahilin mari taji a k’uncinta, ta d’ago tana duban Auntyn tata dake sakin hucin b’acin rai... “Ashe ke shashasha ce ta bugawa a jarida ban sani ba... Ashe Ke doluwace Ta k’arshe.. Kinsan da yaya aka had’a maganin nan... Kinsan kwanakin maganin nan nawa a tsibirin iskokai... Shine dan dak’ik’anci da shashashanci zaki zubar kuma dik zaman nan baki San yanda duk kikai kika basa yaci ba..?? Dak’ik’iyar inace Ke Raheemah..!!?” Ta k’arashe tana mai jijjiga Raheema dake kuka dafe da k’uncinta....

Raheema na kuka take fad’in “Aunty wllhi ba laifina bane laifin shegiyar Muhibbar nan ne.... Aunty makirar nan ta shige dik tinaninki...!”

Hankad’ata gefe Gimbiya Zeenat tai tana mai ci gaba da sakin tururi “Bazamu tab’a rasa Mahmood ba, dole ya zamto yana k’ark’ashin ikonmu.... Amma kafin nan sai mun b’atar da wannan yarinya Muhibbah dake k’ok’arin kutso Kai cikin rayuwarsa data d’iyarsa..!!”

Raheema ta dubeta da mamaki kana tace “Aunty ya za’ai mu b’atar da ita, bayan ko idanunta tsoro suke bani...!”

K’asaitaccen murmushi Gimbiya Zeenat tai kana tace “Na b’atadda wad’anda suka fita balle ita... Akan mulkin nan babu abinda bazanyi ba... Juwariyya..!!!”

Raheema ta kuma dubanta da mamaki kana tace “Mai ya kawo Juwariyya cikin batun nan Aunty..?!”

Murmusawa Gimbiya Zeenatu Ta kumayi kana tace “Itace solution d’inmu... Itace zamu umarta ta bincika mana komai gameda Muhibbah... Idan muka San ko wacece ita kaita k’asa bazai mana wuya ba, dan ni ban yarda da wannan Muhibbar ba...!”

Raheema ta saki murmushi cikeda jin dad’i “Gaskiya Aunty Ke d’in ta dabance, badon Giwa ta rigaki shigowa gidan nan ba da anyi shu’umar Sarauniya.! Toh amma do you think we can trust Juwariyya..?!”

Murmusawa Gimbiya Zeenat ta kumayi tana mai zama cikin kujerar lilonta, tana juyi bisa take fad’in “Ai a halin yanzu babu wacce zamu yarda da ita samada Juwariyya tinda har ta juyawa ahalinta baya dan cikar burinmu... Karki mance duk wani information kan Yayanta ita ke kawo mana, so na tabbata bazamu samu matsala da ita ba....!”

Murmusawa Raheema tai kana tace “K’warai kuwa Aunty shawarinki yayi..!”

Suka kuma duban juna a tare suna masu sakin murmushin cin nasara....

***

Zagaye d’akin take faman ci gaba da yi waya manne kunnenta tana mai ci gaba da fad’in “Ansar please pick up... Pick up please... Ina tsananin buk’atar shawarinka...!!”

Har saida wayar ta kusan katsewa Ansar ya d’aga yana mai furta “I can see someone’s already missing me, Sorry wanka na shige ban jima da isa masauk’i ba na tsaya restaurant nayi takeaway... Do you want some... Na kawo miki...?!” Yai maganan teasingly...

Katse wasan nasa tai da fad’in “Ansar akwai matsala....!”




SameenaAleeyou 📚
[7/1, 10:39 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*



*026*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*




Gathering natsiwarsa yai waje guda yana mai furta “Ina saurarenki... Meke faruwa...?”

Fuzar da fuci tai a hankali tana mai zama cikin gado “Ansar Mahmood yana so ya dasa cameras in every angle cikin Masarautar... I mean he can’t do that... Zai b’ata min shirina, bayan babu abinda na fara...” Ta k’arashe cikeda damuwa...

Lokaci guda ya isa ya zauna bakin gado yana mai furta “What..! Hibbah you need to leave that place right away, muddin aka saka cameras you’d definitely get caught..!”

Jinjina masa kai tai kaman yana kallonta kana tace “What do I do now Ansar... Mai zanyi na hana yuwar hakan...?!”

Fuci ya fuzar a hankali kana tace “Muhibbah ki bar maganan mission d’in nan naki... Abubuwan da suke faruwa sign suke nuna miki cewa akwai matsala gaba... Before everything gets out of hands let’s leave, tun ban bar cikin garin nan ba... Zanzo ni na d’auki, mu koma gida...!”

Katsesa tai da fad’in “Haba Ansar, kai saikace ba namiji ba, sai gashi kaman ka cire tsoro da shakku cikin sai kuma ka sake komawa ruwa..!”

Shima ya katseta da fad’in “Dik abinda ya shafeki Muhibbah bazan masa tinani d’aya ba.. I’ll think through and think through and think it through... Karkiga laifina sabida banso ki shiga matsala ne....!”

“Are you saying na ajiye makamaina na bika mu koma gida, what about the justice that I deserve..? So kake na tafi na mance komai..!?”

Cikin kwantar da murya yake fad’in “Ba nufina ba kenan Muhibbah... Nafi kowa so Ki samu adalcin da kika cancanta duk duniyar nan...!”

“Idan gaskiya kake fad’in then ka dena sare min gwiwa with your negative thoughts...!”

Ansar ya fuzar da huci, cikin b’acin rai yake furta “Ni ban hanaki aiwatar da komai ba... From the very start, I’ve done nothing but supporting you, amma abinda nakeso ki gane a nan shine dik abinda zakiyi do it the right way...think it through first Muhibbah.. Idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login