Showing 30001 words to 33000 words out of 54616 words
Chapter 11 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt
fice, sunkuyar da kai Mansu tayi qasa ganin irin wani kallo yau da Dikko yake mata kuma gashi sun fita sun barta.
Bud'e baki yayi cikin murya me breaking yace. "Je..wel....."
Banza ta mishi ta qara sunkuyar da kai, tana wasa da kyawawan yatsun hannunta,
A hankali yakai left hand dinshi ya zare drip din dake jikinshi, a hankali ya tashi.
A sanyaye ya sauka a hankali ya qarisa kujeran da take zaune, duqunnawa yayi ya daura hannayenshi a cinyarta yasa hannun ya d'ago kanta,
Seda gabanta ya fad'i ganin yanda idanunshi sukayi jajawur,
Kawar da kai tayi da sauri.
Cikin muryan kuka yace. "Please look in to my eyes Jewel ko zaki iya fahimtar irin san da nake miki, I love you more Mansu.....tabbas kinmin hukunci mafi tsauri a rayuwa but I will not judge you on it cos I love you fiyeda tunaninki.....kuma kema nasan kina sona ko My Jewel.? I vow to be royal to be honest and truthful with you at good and bad times bazan kuma barinki ki zubda hawaye ba please marry me Jewel......."
Wani irin murmushin izgilanci tayi ta d'ago ta sauke gaba d'aya idanuwanta cikin nashi.
Cikin nuna rashin tsoro tace.
. "Hummm I regret every bit of our relationship, I mean it I regret every single bit of it, you know what I hate you either is over between us...."
Tureshi tayi ta miqe zata fice, da sauri ya riqo hannunta......
. "I love you to the extend that I can't effort loosing u I love u then now an forever, am sorry please don't judge me for duk abubuwan da suka faru a baya I regret it, I repeat I regret it please forgive me..... "
Kuka ya fashe dashi dan ji yake kaman ana hura mishi wutan santa a cikin zuciyanshi.
Murmushi ta kumayi. "Am so done with you like hummm you are to smart actually I thought something was wrong with you cos u seems off...."
Cikin kuka yace. "I love you please marry me I promise to make you the happiest women on earth, I promise to be your friend, your brother and I promise to love you forever and am gonna be the best husband ever.
Am sorry for every hurt, I will tell the hole world that I love u inasanki sosai...."
. "bazan ta'ba sanka ba Dikko na fad'ama komai ya qare tsakaninmu the game is over and I......."
Bata qarisaba ya sulale a qasa yana juyi tuni bakinshi ya fara fidda kumfa,
K'ara tasa nan take hawaye suka fara fita a idanunta ta rasa me zatayi, daddy ne da mommy suka shigo dakin ganin halin da yake ciki yasa mommy tafita da sauri kiran Doctor....
Tambayanta daddy yake meya faru, amma ta kasa magana se kuka takeyi duk tabi ta firgita....
Tana tsaye Dr Ridwan ya shigo suka maida Aryan kan bed, sannan doctor ya mishi wani allura nan da nan kumfan ya dena fitowa ya koma kaman gawa illa numfashi da yakeyi sama da sama shize tabbatar maka yanada rai.
Juyowa doctor yayi yana tambayansu meya faru,
Dukkansu Mansu suka kalla,
Da gudu Mansu dake kuka sosai ta bud'e kofan ta fice da gudu, tana kuka fita tayi daga asibitin tana fita ta tari napep ta shiga.
Har suka kai , barnawa complex bata dena kuka ba ta bashi kudin shi ta shige gidan da gudu, Ayya na d'akinta hakan yasa ta shige d'akinta da gudu tana wani irin kuka me fitan rai.
Lubna ne da Nadiya sukazo gidan dan duk sun kirata be shigaba kuma sunje asibiti batanan,
Bayan sun gaisa Ayya tace musu. "Inaga ta dawo domin naji shigowanta d'azu ku shiga tana ciki....."
D'akin Mansu suka nufa, tana raku'be gefen gado se kuka takeyi tana ganinsu ta tashi da gudu taruga ta fad'a jikin Nadiya.
...."Na shiga uku Nadeeya Dikko na sona sosai bashida lafiya saboda ni wallahi nima inasanshi amma bazan iya rayuwa dashi ba, I want him to regret before I want him to know you can't disrespect women and go free,
Amma inasanshi sosai Nadiya please ku temakeni banasan ganinshi cikin damuwa pleasssss..... "
Ta fashe da kuka ta sulale a qasa dukkansu suka tarbota cikin tausayawa, da kyar suka samu Mansu tayi shiru daganan a hankali bacci ya d'auketa,
Gaba d'ayansu suka bita da kallon tausayi, Nadiya najin dana sani domin gani take itace ta jefa duka zuciyoyi biyun a halin da suke ciki yanzu, domin ita taba Mansu wannan shawaran.
Tun daga ranan Mansu bata sake zuwa asibiti ko gidansu Mommyba kullum tana gida.
Shikam Aryan kwananshi uku besan inda kanshi yakeba.....
A rana na hudu ya farka yana kiran sunan Mansu,
Lokacin kowa yana d'akin, daddy, mommy, Farhan, Lubna, Atif, Nadeeya harda doctor Ridwan.
Kowa ya cika da mamakin jin ya farka da sunan Mansu amma badda Farhan, Nadeeya da Lubna,
_To meke tsakaninsu kenan?.
Kowa ke tambaya a ranshi.
Doctor Ridwan ne ya dubi su daddy. "Dama nafi tunanin da abinda DrDikko yake buqata, to yanzu na tabbatar da bincikena dan haka wannan Mansun da yake kira ita yake buqata dan haka kuyi gaggawan mai abinda yakeso domin yanasanta sosai, dama sau tari wa'inda basu ta'ba soyayya ba in suka fara gushewa hankalinsu yakeyi se kuga ba abinda bazasu iyaba wadu har mutuwa sukeyi akan abinda sukeso dan basu iya so kadan ba, dan haka dan Allah ku ceci rayuwar tsayayyan namiji irin Doctor, yanzu dai ku bashi guri ya huta..."
Yana fadin haka ya fice.
Gaba d'ayansu sun cika da mamaki a sanyaye dukkansu suka fice.
Washe gari.
Mommy da Daddy da Farhan suna d'akin ya bud'e ido, kallo daya ya musu ganin ba Mansu a d'akin yasa ya maida idanshi ya lumshe lokaci d'aya hawaye suka fara zuba a idanunshi tuna abinda Mansu tace na bata sanshi.
Matsawa mommy tayi kusa dashi. cikin tausayawa tace. "Son.....meke damunka.."?
Daura kanshi yayi kan cinyarta hawaye na dad'a zuba a idanunshi, itama nan take taji hawayen sun wanke mata fuska cikin muryan kuka tace.
. "I know u're My strong brave boy,
My Son feel free fad'amin meke damunka....."
... "Mommyyyyy....."
Ya fad'a tareda d'ago kai, sumarshi ta shafa. "Na'am yarona...."
Daddy da Farhan ya kalla suma da suke tausaya mishi ganin halin da yake ciki a kan mace,
Kafin ya kuma kallon mommy yace. "Mom.....Mansu..Mansuuuuu...inasanta sosai she's my jewel mommy....amma ita ta tsaneni tace bata sona tanaso tarama duk abinda na mata, kuma ai I regret ko mommy.....? "
Cikin kuka ta d'aga kai, kaman karamin yaro yaci gaba. "Mommy na bata haquri nace ta aureni amma tace bazata aure niba, mommy nikuma idan bata aure niba mutuwa zany....... "
Rungume shi mommy tayi ta fashe da kuka, tanajin qaunar d'an nata ako ina,
Karisawa daddy yayi ya shafa kanshi yace. "Dikko na indai ka aureta zaka rayu zaka tsaya tareda da daddynka bazakayi nisa da niba...? "
Da sauri ya d'ago yana d'aga kai. "Eh daddy..."
Murmushi daddy yayi. "Na maka alqawari indai na isa da Mansu sena mallaka maka ita na har abada...."
Kuka ya fashe dashi na murna ya rungume daddy, da sauri shima Farhan ya rungume shi shima yana kuka.
Jin za'a bashi Mansu yasa ya saki jiki yaci abinci da magunguna sosai,
Duban daddy yayi. "Daddy na warke mu koma gida inga My Jewel..."
Shafa kanshi yayi. "Ka bari ka qara samun sauqi..."
. "daddy you know am a doctor zan iya kula da kaina please inaso in ganta...."
Daddy ne ya riqeshi suka fice, mommy da Farhan kuma suka tsaya d'ebo kaya.
A mota daddy yayi dialing numban Mansu, lokacin tana zaune tanacin abincin da take jinshi kaman magani.
Dauka tayi ta gaidashi, bayan ya amsa yace. "Kizo gida yanzu ina nemanki ki taho tareda da Ayya...."
Gaban tane ya fad'i amma ta daure tace. "Toh...."
Katse wayan tayi ta fad'awa Ayya saqo, basu jimaba suka shirya.
Bala driver ya d'aukeshi zuwa millinoin city.
Allah ubangiji ya jiqanki Ammyn mu Allah kai haske kabarinki Allah raya zuri'a.
Please kuyi mata addu'a matsayin uwa take a guna.
Matar Abdul ce ✍️.
2022-10-11, 10:31 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)
Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa
_____________________________________
Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.
Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.
Bismillahir rahmanir raheem.
39&40.
Kan Mansu na qasa tunda ta zauna a kan carpet din bata d'ago kaiba gaban tane keta fad'i, Aryan na zaune a gefenta ya kafeta da idanuwa jiyakeyi kaman ya cinyeta ya huta se faman murmushi yakeyi.
Daddyne ya kira sunanta. "MANSURAT....."
D'ago kai tayi. "Na'am daddy....."
Maida kai tayi qasa tana sauraran abunda daddy zece.
. "MANSURAT kiyafe mana munsan mun miki ba daidaiba amma ganin mun isa dakene yasa muka aikata hakan...."
Qara sinnar da kai tayi tana girgiza kai tuni hawaye yafara bin kuncinta, cikin dakewa tace. "A'a daddy niba abinda zakumin na kuskure akoda yaushe ku masu iko ne dani kuma nime biyayya ce a gunku...."
. "Alhamdulillahi....."
Daddy ya furta, kafin ya dubi Ayya yace. "Ayya yau zamu fad'a musu komai yau zamu fayyace musu abinda muka b'oye musu muna jiran lokaci, to yau lokaci yayi..... "
Murmushi Ayya tayi. "Allah nagode maka daka nunamin wannan rana da raina ban mutuba za'a fad'i wannan sirrin da muke b'oyewa shekaru da dama...."
Cikin rashin fahimta Aryan yace. "Daddy wani sirrine wannan....? "
Mommy ce ta harareshi. "Yi ma mutane shiru..... "
Maida baki yayi ya tsuke, Mansu kam idanta na runtse in banda hawaye ba abinda ke sintiri bisa kuncinta, a cikin zuciyanta kam
" Innalillah wa'innan ilaihir raji'un. " kawai take maimaitawa.
Daddy ne ya nisa. "Uhmmmm. "
Kana yace. "Shekaru tara da suka wuce lokacin Mansu nada shekaru goma sha uku a duniya, muka zauna nida Ayya muka yanke hukunci dukkanmu bamuda buri daya wuce muga mun had'a Mansu da Aryan aure, sedai su sun tsani junansu hakan yasa muka yanke shawara a wannan lokacin muka nemi dangin mahaifin Mansu muka d'aura musu aure batareda sanin suba dan lokacin Mansu ko hankalin kanta bata saniba, hakan yasa muka maida Mansu gaban Ayya inda Aryan yakeyi da niyyar in suka taso tare qila su fara san junansu duk randa suka bud'e baki sukace sunasan juna semu bayyana musu wannan sirrin da babu wanda yasani daga ni se aminina Alh. Abubukar da wakilan Mansu se mommynku da Ayya,
Amma se gani mukayi tsanan kullum qaruwa yakeyi hakan yasa muka jinkirta ba tareda mun sanar dasu wannan sirrin ba mun qudurta ko za'ayi shekaru dubu d'ayanku be bud'e baki yace yanasan d'ayaba bazamu fada mukuba,
Shiyasa na haramtawa Mansu kula kowa kuma nima bana amsan duk wanda yazomin da maganan neman aurenta.
Munyi matuqar farin ciki da Dikko da kanshi ya bud'e baki yace mana yanasan Mansu kuma yayi nadaman duk abinda yayi a baya,
Princess ki gafarcemu munsan bamu kyauta mikiba amma ki fad'a mana idan bakisan Dikko se a raba auren dake da Dikko duk yaran mune bazamu tauye miki haqqinki ba a matsayin ki na yarinyar mu......"
Mansu kuka takeyi na fitan hankali dan gaba d'aya ba wanda bejin kukanta, tarasa ina zatasa kanta
. "Allahumma ajirni fi musibatin wakhlifni khairan minha, innalillah wa'innan ilaihir raji'un....."
Shine abinda take fad'a cikin ranta tana kuka, cikin kuka muryanta na cracking tace. ".... Da...ddy.....har abaaa...da....ni me biyayya ce....a gareku......bazan ta'ba bijirewa umarnin kuba akoda yaushe za'bin ku shine nawa..... "
Ba wanda beji dadin abinda ta fad'a ba, Dikko kam ya rasa ina zesa kanshi saboda murna baki har kunni, Farhan kam cike yake da tausayin Mansu haka Lubna.
Cikin jin dad'in magananta daddy yace. "Mungode sosai Mansu Allah muku albarka gaba d'ayansu yabaku zaman lafiya, zanyi magana da mommynku se asa ranan tarewan naki kinji ko.....? "
Batace komai ba taci gaba da kuka, nan daddy yayi addu'a ya rufe taro da addu'a ya tashi.
Da gudu Mansu tayi d'aki tana kuka, kowa ya bita da kallon tausayi Aryan ya bita da wani irin murmushi dake qunshe daso ji yakeyi yau yafi kowa murna ya mallaki Jewel dinshi, da sauri ya tashi yafice cikin murna yana dialing numban Atif,
Shima da kallo suka bishi Farhan ne ya tashi jiki a sanyaye ya rasa murna zeyi ko baqin cikin an quntatawa Mansu dan yana matuqar tausayin ta,
Farhan na ficewa itama Lubna tayi d'akin aunty Angle inda Mansu ta shige, suka bar mommy da Ayya kawai.
Tana kwance kan gado tana kuka sosai, d'agota Lubna tayi. "Ki dena kuka Mansu..."
Fad'awa tayi jikin Lubna. "Lubna na shiga uku dama ni matar aurece dama Dikko shine mijina, wata zuciyan mara adalci na rad'amin su daddy basu yimin adalciba da suka min aure tun ban mallaki hankalin kainaba batareda sani naba dan sunga ni marainiya ce amana ce a gunsu shiyasa sukamin haka ga Aunty Angle nan meyasa basuyi mata hakaba ko dan ni basu suka haifeni ba..... Amma zuciya me adalci na fad'amin cewa aisu ma matsayin iyayene a guna kuma suna ganin sun isa danine shiyasa kuma ai inasan Aryan kawai inaso in koyamai hankaline..... "
Tayi murmushi. "Huuummm Lubna zuciya ta biyu tayi gaskiya tabbas su daddy sunfi qarfin haka a guna danko yanka namana sukayi suka bani inci banda bakin magana, kuma inasan Dikko sosai kawai dai ban shirya rayuwa dashi yanzu bane seya gane kurenshi amma yanzu banda freedom komai nayi da nufin d'aukan fansa ni zunubi zan samu a gurin ubangiji na, Lubna banida hujja Dikko yayi nasara a kainaaaaa.......... "
Ta fashe da kuka.....
Itama kuka Lubna takeyi sosai ta kasa lallashin Mansu,
Mommy ce ta turo kofa hakan yasa Lubna sauke Mansu kan bed ta fice, karisawa mommy tayi wacce da alama itama taci kuka, ta d'ago Mansu dake kuka dan bata sanma mommyce ta shigoba,
Kan jikin mommy ta fad'a ta qara sakin kuka, shafa yalayalan gashinta mommy tayi. "Baby gurl.... "
Kuka taci gaba dashi,
. "Mansu na kiyi shiru kinji am a woman i can feel what u're feeling nasan bamu kyauta miki ba amma kiyi hakuri kinji baby na....."
D'ago kan Mansu tayi da idanunta ke rufe tana kuka sosai, share mata hawaye mommy ta soma tana zubda hawaye a sanyaye tace. "Mansu u're my daughter inasanki sosai fiyeda tunaninki kuma nasan na isa dake, amma zan roqeki wani alfarma badan ban isaba,
Mansuna ki temaka kiso Dikko ki rayu dashi ki temaki rayuwarshi ki manta da duk abubuwan da suka faru tsakaninku a baya ku shinfid'a sabuwar duniya Dikko na buqatarki Mansu, nasha wahala a haihuwanshi sosai yafi wata shida baya motsi seda yafi shekara d'aya a cikina sannan na haifeshi kuma dazan haifeshi aiki akamin bansha zan rayuba shima yasha wahala bamu d'auka ze rayuba inasanshi sosai Mansu inajin tsoron in rasashi nafi qaunarshi fiye da Farhan da Angle amma nafi sanki dashi domin qaddaranku d'ayane Mansu, ina matuqar tausaya miki tun kina ciki Allah ya d'auramin sanki, tun kina ciki nake roqon mahaifiyarki ta bani ke bamu ta'ba sanin cewa ashe a hannuna zaki tasoba nizan raine kiba.
Please ko badan niba ko dan soyayyan da Dikko yake miki ki temaka ki rayu dashi ki bashi farin ciki inaso yanda kuka taso tare kuqare tare pleaseeeeee......... "
Rungume mommy tayi sosai dukkansu suna kuka......
*********
Da kyar Mansu ta dawo yanda take amma sam taqi yarda ta koma gidan Ayya dan bataso ta had'u da Aryan tana ganinshi.
Yau daddy ya kira Dikko, bayan yazo yake ce mishi. "Munyi magana da mommynku tace tanaga se nanda wata d'aya Mansu zata tare, domin itama tanaso ayi babban biki a tarewan 'yarta kuma akwai abubuwan da takeso tayi, kaima inda abinda kakeso kayi kaje kagama kafin lokacin sannan ka za'bi gidan daya maka inda zaku zauna a cikin gidajena...... "
. "Toh.... " kawai yace.
Ya tashi ya fice jiki a sanyaye rai duk a 'bace, main falo yaje ya zauna ko ze ga fitowanta domin yanzu koya kira wayanta baya zuwa duk ya shiga damuwa, amma yanajin matuqar dadi idan ya tuna itad'in matar shice.
Sedai harya qaraci zamanshi ya tafi bata fitoba.
Yau Nadiya ta kawo mata ziyara.
Suna zaune kan gado a d'aki,
Duban Mansu tayi ganin tana walwala a fuska kaman bakomai a ranta yasata cewa.
. "Matar Aryan yanzu kin sadaqar kenan kin miqa wuya.... "
Murmushi me ciwo tayi "Nadee mommy ce da kanta ta roqeki inso Aryan in rayu dashi wallahi ko bana sanshi zan fara koyawa kaina sanshi balle kuma inasanshi kawai dai zanja mishi aji ne baze gane da wuriba.... "
Dariya Nadiya tayi. "Lallai wallahi nayi mamaki dajin cewa dama can Aryan mijin kine duk zagin da kika mishi yanzu kin samu zunubi.... "
Dafe kai tayi. "Itama dai Aunty Angle taci dariya haka ta kirani tana tamin iskanci yanzu wai ashe matarshi ya dinga cewa mahaukaciya kinga aunty Angle akwai mugunta,
Amma kinsan meye Nadee ai ubangiji baze kamani da laifin da nayi cikin rashin saniba.... "
Murmushi Nadiya tayi kafin tace. "Kinsan d'azu muka gama maganan da Sweet Atif kinsan meyace wai dama tun tuni an fad'a muku ku mata da mijine kuna cikin tsanan nan se muga yanda zakuyi.... "
Da sauri Mansu tace. "Ai wallahi dase an raba auren kinsan ko meye ake kira da tsana.... "
. "Hummm tsana kam soyayyace me karfi domin kam inya juye ya koma soyayya se yaba kowa mamaki,
Domin kam dama duk inda kukaga tsana me tsanani tayi yawa to qasanshi qunshe yake da soyayya me qarfi dan ga babban alama nan mun gani..... "
Nadiya ta fad'a cikin zolaya.
Duka Mansu ta d'aka mata.
Please manage, kunsan an mana rasuwa daurewa nakeyi ina muku typing.
Taku koda yaushe. Halima Isah (Mimeey).
Matar Abdul ce ✍️.
2022-10-12, 9:00 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)
Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar