Showing 54001 words to 54616 words out of 54616 words

Chapter 19 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt

Ya tsinewa Mai Aikatasu. Wajibi Ne Ga Dukkan Musulmi Idan Yaga Makaho Ya 6ata Hanya Ya Dawo dashi. Ko Idan Yaga Zai tsallaka Hanya Mai Haɗari Wajibi Ne Ya Kama Hannunsa ya tsallakar dashi Matukar Yanason Ya Ku6uta daga La'antar Ubangiji. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:


عن ابن عباس رضي الله عنه: أن رسول الله صلي الله عليه وسلم قال: ”لعن الله من كمه الأعمى عن السبيل، لعن الله من عمل عمل قوم لوط“
{أحمد: ١٧٧٩}


An Kar6o Daga Ibn Abbas (ra), Lallai Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Kautar da Makaho Daga Kan Hanya (6oyewa Makaho Hanya), Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Aikata Aikin Mutanen Lud”.
{Ahmad: 1779


5. ZAGIN MAHAIFA:


عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: ”لَعَنَ اللهُ مَنْ لَعَنَ وَالِدَهُ ، وَلَعَنَ اللهُ مَنْ ذَبَحَ لِغَيْرِ اللهِ ، وَلَعَنَ اللهُ مَنْ آوَى مُحْدِثًا ، وَلَعَنَ اللهُ مَنْ غَيَّرَ مَنَارَ الْأَرْضِ“
{مسلم: ١٩٧٨}


An Kar6o Daga Aliyu bn Abi-Dalib (ra), Daga Annabi (ﷺ) Yace: “Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Zagi Iyayensa. Allah Ya Tsinewa Wanda Yayi Yanka Don Wanin Allah. Kuma Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Taimakawa Ma6arnaci. Sannan Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Sauya Alamar Kasa (Floti, Gona)”.
{Muslim: 1978}


Kila Wani Yayi Mamakin Ya Za'ayi Mutum Ya Zagi Mahaifansa, ba Lallai Sai Mutum Ya Buɗe Baki Yace Dubesu Ya Qunduma Masu Zagi ba, Hadisin da Zaizo Zaiyi Bayanin Wata Hanya da Akebi ta Zagin Iyaye ba Tare da an Farga ba.


A Wani Hadisin Kuma da Abdullahi bn Amru Ya Ruwaito, Manzon Allah (ﷺ) Cewa Yayi:


عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: ”إِنَّ مِنْ أَكْبَرِ الْكَبَائِرِ أَنْ يَلْعَنَ الرَّجُلُ وَالِدَيْهِ“. قِيلَ يَا رَسُولَ اللَّهِ وَكَيْفَ يَلْعَنُ الرَّجُلُ وَالِدَيْهِ قَالَ: ”يَسُبُّ الرَّجُلُ أَبَا الرَّجُلِ، فَيَسُبُّ أَبَاهُ، وَيَسُبُّ أَمَّهُ“
{رواه البخاري}


An Kar6o Daga Abdullahi bn Amru (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Lallai Yana Daga Cikin Mafi Girman Zunubi Mutum Ya Zagi Mahaifansa”. Sai Akace: Yaya Za'ayi Mutum Ya Zagi Mahaifansa? Sai Yace: “Mutum Ya Zagi Mahaifin Wani, Shi Kuma Wani Shima Sai Ya Rama Ya Zagi Mahaifin Wanda Ya Zagi Mahaifinsa”.
{Bukhari Ya Ruwaitoshi}


6. ZAGIN SAHABBAN ANNABI (ﷺ): Haka Kuma Yana Daga Cikin Nau'in Mutanen da Ubangiji Ya Tsine Masu Mai Zagin Sahabban Annabi (ﷺ).


Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:


عن ابن عباس رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: ”من سب أصحابي، فعليه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين“
{الطبراني: ١/١٤٧/٣}


An Kar6o Daga Ibn Abbas (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Duk Wanda Ya Zagi Sahabbai Na, La'anar Allah, da ta Mala'iku da ta Mutane Gaba Ɗaya Ya Tabbata Akansa”.


Har Wayau Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:_


عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخدري قَالَ: قَالَ رَسُولُ الله ـ صلَّى الله عليه وسلَّم: ”لاَ تَسُبُّوا أَصْحَابِي؛ فَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَوْ أَنْفَقَ مِثْلَ أُحُدٍ ذَهَبًا مَا أَدْرَكَ مُدَّ أَحَدِهِمْ وَلاَ نَصِيفَهُ“
{البخاري: ٣٣٩٧ ومسلم: ٤٦١١}


An Kar6o Daga Abi-Sa'idil Khudry (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Kada Ku Zagi Sahabbaina, Domin da 'Dayanku Zai Ciyar da Kwatankwacin Dutsen Uhud Na Zinari, Bazai Riski Mudun Ɗayansu ba Ko Rabinshi”.
{Bukhari: 3397, Muslim: 4611}


7. MAI BAYAR DA CIN HANCI DA ME KARƁA: Mai Bayar da Cin Hanci Yana Mai Jin Daɗi ba Tare da Tilastashi Akayi ba da Wanda Ya Karɓa Cin Hancin Suna Dãgã Cikin Jinsin Mutanen da Ubangiji Ya Tsine Masu.


Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa a Cikin Ingantaccen Hadisinsa:


عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: ”لعن رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم الراشي والمرتشي“
{الترمذي: ١٣٣٧}


An Kar6o Daga Abdullahi bn Amru (ra) Yace: “Manzon Allah (ﷺ) Ya Tsinewa Mai Bayar da Rashawa da Wanda Ya Kar6eta”
{Tirmizi: 1337}.


Allah ubangiji ya bamu ikon Amfana dashi.


Amin.




Halima Isah Idris ce (Mimi), Matar Abdul.


Se kun jini a sabon book dina insha Allah.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login