Showing 15001 words to 18000 words out of 54616 words
Chapter 6 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt
saboda wani irin abu da yaji da tayi magana duk da muryanta ya canza,
A sanyaye yace. "Meke damunki naji muryanki wani iri....? "
"Am not well...."
Ta bashi amsa, se yaji duk ba dad'i yace. "Meke damunki....? "
"Zazza'bi...."
Jinjina kai yayi. "Okey kinsha magani.....? "
Girgiza kai tayi kaman yana ganinta. "Aa...."
"Saboda me....? "
"Abinci nake jira inci tukun....."
Ta bashi amsa, lumshe ido yayi yanaji kaman karya denajin muryanta. "Okey kici abincin kisha magani I will call later...."
"Okey."
Ta furta a sanyaye ya cire wayan a kunninshi yanajin wani iri......
Ji yayi ya kasa natsuwa unin ranan seda ya kirata sau uku dan yaji lafiyanta.....
*****
Yau bayan ta tashi good morning message ta mishi lokacin yana asibiti yana duba patient, bayan ya koma office yaga message dinta, zama yayi akan kujeran yana nazarin kar yarinyar ta rainashi.....
Message ya rubuta mata.....
```"Am fyn tanks I lyk ur sweet voice my friend....```
Lokacin suna zaune a falon mommy suna kallon waqan Enrique lylesias na bailando itada Farhan,
Ta'be baki tayi a ranta tace. "Annamimi....."
Reply tai mishi.
```"Lyk urs ai naka yafi nawa dad'i sosai```
Murmushi yayi.
```"Did yhu want to know ur name a guna? ....```
Da sauri ta rubuta.
"```Yes.....```
```"JEWEL.....```
Tura mata yayi kafin ya sake rubuta.
```"Did yhu lyk d name....? ```
Murmushi tayi tarubuta.
"```Y not, did yhu want to know ur own? ....```
```"If yhu wish..... ```
Shine abinda ya rubuta mata,
Tsaki taja wanda yasa Farhan saurin dagowa. "Ke kuma dawa....? "
......"bakowa...."
Ta fad'a tana rubuta...
"```TWINKLE....```
Ta tura mishi.
Kwafa yayi.
```"Y meyasa se twinkle? ......```
Tsaki tayi a fili tace. "Dan rainin wayau ni bance meyasa se jewel ba sekai...."
Dubanta Farhan yayi yana jinjina kai. "Mansu da alama kin fara Facebook a karamar waya ko....? "
Tsaki taja tana hararanshi. "Allah kyauta min...."
Tashi tayi tana fadin. "Ni karka takuramin bari inyi daki...."
Binta yayi da ido yana murmushi kodai soyayya Mansu ta fara,
Seda ta kwanta kan seatern dake d'akin aunty Angle sannan ta rubuta.
```"Saboda I know U're shinning lyk twinkle....```
Kwafa yayi. ```"Don't forget we are friends....```
```"I know....```"
Ta bashi amsa.
Kafin ya turo mata.
"```Wani school kike zuwa? ....```
```"Nayi candy dis year....```
Da sauri yace. ```"Wani school kikayi....? ```
```Turkish international school.....```
Shiru yayi yana nazari ya kasa yarda yasanta dan besan wata wacce tayi candy dis year ba,
```"How my siblings...? ```
Ta tura mishi.
```"I don't have....```
Ya bata amsa, murmushi tayi ta rubuta. ```"Haba dai baka yarda nasan kaba ko to bari in lissafo maka....```
Kwafa yayi ya rubuta. "```Ehemmm inaji...```
Reply ta mishi. ```"Kaga Farhan shike binka se Angle wacce itace autanku....```
Cikin mamaki yace. ```"Who told yhu?...```
Cikin zolaya ta rubuta. ```Google....```
Murmushi yayi danya fahimci yarinyar akwai barkwamci, basar da maganan yayi ta hanyan rubuta.
```"hummm am very suprice bansan kiba but yhu know somethins about me dat really amazing....```
Murmushi tayi. "```Oh ba abin mamaki bane kasani ko a family dinku nake ta 'bangaren mommy...```
Ta'be baki yayi, may be dan yasan mommy nada dangi a kaduna kuma baya magana da matan family dinsu sedai gaisuwa hakan yarubuta.
```"Okey yanzu me kikeyi...? ```
```Am just relaxing in my momma falo...```
Kwafa yayi.
```"Am in hospital I want to go home, we talk letter...```
Bayan ta karanta bata mishi reply ba ta barshi.
Tun daga wannan rana shaquwa me karfi ta shiga tsakanin Jewel da Twinkle ko suyi waya ko suyi chat.
Result din su Mansu na waec ya fito jarabawa yayi kyau dan gaba d'aya Mansu ta cinye se farin ciki takeyi yanzu jamb kawai ake jira ta zana tafara karatu dan ita tace bataso tayi karatu a wata qasa a Nigeria takeso tayi.
******
Yau tun safe tacewa Ayya anjima zataje tayi shopping su cornflakes dinta dasu goldenmone dansun qare,
Bayan tayi wanka ta shirya cikin atampa riga da skert tayi kyau sosai ta dauki hijabi tasaka har qasa ta saka eye glass dinta kudi ta amsa a hannun Ayya dazatai siyayyan ta saka cikin LV bag dinta tayi kyau matuka fitowa tayi ta taras Bala driver bayanan hakan yasa ta fita gate din gidan,
Seda tayi tafiya sosai sannan ta samu napep ta shiga tace ya kaita "Down Town Mall...."
Sunyi tafiya sosai kansu kai, a kofar mall din ya ijiyeta ta fito tazage jaka tabashi kud'in ta shiga,
Siyayya tayi na duk abinda ya kawota suka zuba mata a babban Leda amsa tayi ta fito...
Da yike yamma ta farayi bata samu abun hawaba hakan yasa tafara tafiya akan titin ko zata samu a gaba.....
Tazo wucewa ta wani layin da yake shiru shiru ta hango wasu mashaya, kauda kai tayi tazo wucewa wani ya taso yasha gabanta....
A mugun rude tajuya tayi baya zata koma dan layin shiru yake babu kowa
cin karo tai dawani abayanta idanunshi jajir da alamun yasha yai tatil yace ". Ke ina zakije?"
Kwalama sauran dabama su lura da ita ba kira yayi yace ".. Babbaa jimana munyi sabon kamu yau..."
Da sauri a mugun rude tai gefenshi zata wuce yatareta yace. "Ki tsaya mana baby nakira su suzo...." arude tana dan waigen bayanta jin sahun mutane suna zuwa ta kwalama tsohon data hango yana gadin wani babban gida kira. "Baba...Baba..." daidai lokacin sauran sun iso wajen fashewa sukai da dariya dayan yace ". Baba wai me gadi kike kira? Ke yarshi ce...?"
daya daga cikin su yace ". kaima jibeka dawata magana ina Baba mai gadi yakeda kyan haifan irin wanan lu'u lu'un?...." daya daga cikinsu yace "....kodai me zuwa bashi kayane?...."
kulle bakinsu sukayi suna zaro ido irin na isgilanci, fashewa tai da kuka ta duka a tsakiyan su tana kwalama Baba kira. "Babaa..." daya daga cikinsu yace " Baba baze iya temakon kiba en mata dan yata'ba kokarin temakon wata yasha wuqa, dan haka ki tsaya mu huta kawai kingan mu mushida kici har ki koshi ko yan mata....." yay maganan zai kama mata hannu boye hanunta tayi ajikinta tafashe da kuka.
Hijabinta ya fizgo ya mikar da ita tsaye fasa wani irin ihu tayi a mugun tsorace ta bugamai kafarta hakan yasa yay baya yasaketa yana tsaki dan yaji zafi da sauri sauran sukayo kanta tawani irin kwasa da gudu tana kuka wanda ta zubar da gaba daya kayan dake hannunta jaka kadai ya rage mata.
Daya daga cikinsu ya wani hambareta yawani irin tadiyota tafadi akasa hancinta ya shiga cikin yashin dake wurin.
Kafafunta yajawo tafasa ihu sosai tana kuka ta dibi kasan wajen da hannuwanta biyu ta juyo da kanta cikin kuka, watsa musu kasan tayi a idanu hakan yasa ya saketa da sauri yay ihu shida sauran suna sosa ido suna kokarin budewa sun kasa, dawani irin sauri ta tashi tadau jakanta taruga aguje suka biyota, gudu take sosai tana kuka, black hijabin ta gabaki daya ya baci da kasa tana gudu suna binta....
wayan tane dake cikin jaka yafara ringing da sauri ta zube kasa tana kokarin zuge jakan sunkuma sun kusa cin mata, cikin ikon Allah ta zage jakan taciro wayan ta miqe taci gaba da gudu tabar jakan a gurin batareda tama lura da wanda ya kirataba tayi picking takai wayan kunninta cikin kuka take fadin.
"Zasu kamani ka temakini zasu kama......"
Kuka ta fashe dashi dan bama ta gani sosai dan glass dinta ya fita a idanunta ya fashe, Aryan dake zaune a office a rud'e ya miqe tsaye. "Hello jewel su waye zasu kamaki.....fadamin am with yhu.."
Kuka taci gaba dayi..."Zasu kamani katemakamin....."
A rude yake fadin. "Su waye fadamin...."
"Bansan suba....."
"Okey a'ina kike yanzu ina zuwa maza fadamin........."
Bama tareda ta banbance wayeba tace. "Ina cikin street din unguwan rimi amma dai ban san sunan street dinba...."
Tsayawa yayi chak...."duba ko zakiga wani sign board ko wani alama ki fadamin...."
Juye juye tafarayi tana gudu, daidai lokacin idanta ya sauka akan sign board din dake manne "Gomari street..." ta bashi amsa da sauri ya zari key din mota....."kisamu wani guri ki 'buya ina zuwa..."
Ficewa yayi a guje, da gudu tanufi wani gate da take ganinshi a bud'e tana shiga ta datse gate din.....
Tsaye sukayi suna buga gate din, a rud'e Mansu tayi cikin gurin da gudu wanda daga ganima ba'a tareba....
Tana jin yanda suke dukan gate din, lafewa tayi a jikin bango tana kuka sosai,
Mugun gudu Aryan yakeyi hankalinshi a tashe burinshi be wuce yaje ya temaki Jewel din shiba.......
Mimi queen ✍️.
2022-09-26, 6:29 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*
_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)
Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*
_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa
_____________________________________
Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.
Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.
Bismillahir rahmanir raheem.
23&24.
Sosai suke dukan gate din. "Bazaki bud'e ba karki bari mu 'balla gate din mu shigo......"
Tana lafe jikin bango se kuka takeyi sosai,
Daidai lokacin motocin police ya shawo kwanan, jin jiniya yasa daya cewa. "Kai en sanda mugudu......."
A sukwane suka fara gudu, En Sandan da sauri sukayi parking suka fito suka bisu cikin yardar Allah suka kama hudu, biyu suka tsere....
Mansu jin shiru sun dena dukan gate din se jiniya dake tashi sama sama yasata karisa a hankali ta kanga kunninta jikin gate din....
Lokacin wani police ke waya yana fadin. "Yes sir yanzu zamu kariso mun kama wasu smokers ne a kan hanya......"
Wani irin dad'i taji jin an kamasu, da sauri ta bud'e gate din ta fito.
Daidai lokacin yan sandan suka nufi mota dasu daya na fadin. "Zakuci uban kune....."
gudu ta farayi dan tabar layin,
Aryan kam nacan yakusa shiga street din gosulu ya tsareshi se faman tsaki yakeyi yana dukan sitiyari, da kyar yasamu ya wuce.
Yana shiga street din wajen sign board din yayi parking, yayi dialing numbanta...
Lokacin tana tafiya a hanya, jin ringing din ya firgitata har seda tayi yar quwa, ido ta zubawa screen din wayan dashi kadai ya rage a tare da ita,
Se lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta tuna wayan da tayi d'azu da tana buqatan temako, har wayan ya katse batai picking ba se lokacin ta duba taga ashe Aryan ne, godiya ta farayiwa ubangiji daya turo polisawan nan da wuri da yanzu shikenan asirinta ya tonu.
Daidai lokacin ya qara mata kira na biyu still bata d'auka ba at list seda ya mata kira kusan sau goma batai picking ba....
Aryan duk ya rud'e ya dauka ko sun kama tane a rud'e ya bud'e motan ya fito, wage murya yayi yana kiranta.
.... "Hey jewel is me....jewel..."
Dan besan sunan taba.
Kiran magrib da Mansu tajine yasata fashewa da kuka dan duhu yafarayi kuma gashi bata gani a duhu sosai ba tareda glass ba, da sauri ta lalubi numban Farhan yana dauka ta feshe mishi da kuka....
A rud'e ya miqe tsaye. "Baby gurl wot happen meya faru.....? "
Kuka taci gaba dayi ta kasa bashi amsa, a rud'e mommy tace. "Meya faru Farhan...? "
". Wallahi mommy bansaniba ta kirani kuma tana kuka ta kasa magana...."
Da sauri mommy ta fizge wayan. "Baby mommyn kine fad'amin meya faru.....? "
Jin mommyne yasata qarasa kuka, sosai mommy ke lalla'banta tafada musu duk hankalinsu ya tashi harda Angle....
Cikin kuka tace. "Mommy wasune suka biyo ni.......
Nan ta fad'a musu komai , hankali tashe Farhan yace. "Kina ina yanzu...? "
"Bansaniba Ya Farhan duhu nake gani bana gani sosai....?"
A rud'e yace. "To ki jirani ganinan zuwa. "
Da sauri mommy tace. "Kar kije ko ina ki samu guri ki zauna ga Yayan kinan zuwa, kinji Mansu na? ....."
Gyada kai tayi tana kuka sosai, da gudu Farhan ya zuri key yai waje,
Aryan kam jin an kira magrib yasashi shiga mota cikin damuwa ya kirata sosai batai picking ba, a wani masallaci ya tsaya yai sallah yai mata addu'a Allah sa tana lafiya.
Farhan kam tracking number dinta yayi inda ya nuna mishi location din da take, aiko yana zuwa ya hangota ruku'be se kuka take da sauri ya fice yana isa ya ta'bata, seda ta firgita.
"Ke nine..."
Ya fad'a, jin muryan Ya Farhan yasa ta fad'a jikinshi tana kuka sosai, shafa kanta ya hau yi. "Is Ok....."
Hannunta yaja har mota ya bud'e yasata ya zagaya ya zauna, daura kanta tayi kan kujeran ta lumshe ido hawaye nabin idanun nata,
A Nani fresh yayi parking ya fice batareda ya mata maganaba, cold stone icecream ya siya mata dan yasan tanasan shi kuma dan yanaso yaga tadena kuka,
Miqa mata yayi. "Ga favorite dinki my baby gurl...." amsa tayi kawai ta ijiye a gefe, nan yashiga yaja zuwa gida.
Tana shiga falo ta fad'a jikin mommy tana kuka sosai da gudu Angle tazo itama tana kuka ta rungumeta,
Kuka Mansu take sosai, d'ago kanta mommy tayi tana share mata hawaye. "Banaso kina kuka kinga idanunki basuda kwari sosai Mansu na......"
Cikin kuka tace. "Yanzu mommy dasun kamani da shiken......."
Mommyne tayi saurin katseta da fadin. "La..la...la.....baby jikin kine ya 'baci haka ga hannunki duk rauni Angle maza kaita ciki ta canza kaya kafinnan Farhan maza kira Dikko yazo ya mata dressing inda taji ciwo......"
Da sauri Farhan yace. "Zan kira doctor Ridwan kawai kinsan Ya Dikko baze ta'ba yiwa Mansu dressing ba....."
Jinjina kai mommy tayi, Angle ta riqe Mansu sukayi ciki.
Matsa mata Aunty Angle tayi seda tayi wanka duk ta qurqurje,
Alwala ta d'auro bayan tafito ta gabatar da Magrib sannan suka fita lokacin doctor na jiranta, dressing guraren da taji ciwo ya mata ya rubuta magunguna, Farhan ne ya tafi pharmacy siyowa mommy kuma ta tasa Mansu a gaba tana bata abinci,
Mansu na ganin Farhan ya dawo ta fara kuka dan batasan magani da kyar suka lalla'bata tasha, d'aga waya mommy tayi ta kira Ayya danta fad'a mata Mansu a nan zata kwana amma wayanta a kashe,
Hakan yasa ta kira Dikko, lokacin shiganshi gidan kenan duk ya damu, d'aga wayan yayi a sanyaye ya gaidata cikin kulawa tace. "Dikko wani abu na damun kane....? "
Daidaita muryanshi yayi. "A'a mommy me kikaji..? "
". Naji muryanka wani irine...."
Girgiza kai yayi. "A'a bakomai mommy..."
Kwafa tayi dan mommy irin Iyayen nanne masu kula da yaransu da bibiyan halin da suke ciki shiyasa koya taji canji se taji a jikinta.
Allah sarki uwa.
". Kana kusa da Ayya ne.? "
Girgiza kai yayi. "A'a mommy.."
"Okey inka shiga ka fad'a mata cewa Mansu na nan anan zata kwana kace mata lafiyan ta klau.."
Ji yayi kaman mommy ta bashi saqon mutuwa nan take ranshi ya 'baci tunawa da wata Mansu kawai da yayi.
Cikin wani murya yace. "Mommy am sorry bazan iya isar da saqon kiba, sedai zan shiga in kiraki ki fad'a mata....."
Shiru mommy tayi ta rasa abun cewa, katse wayan yayi yanzu dama saboda wannan Jakar mommy ta kirashi "mtsssswwww. "
Tsaki yaja wallahi bacin mommyne da ko sunan Mansu baze yarda a fad'a ta cikin wayan shiba, tashi yayi yaje yasamu Ayya zaune tana kallon tashar Al-jazeera zuciyanta jagule da tunanin Mansu bata dawoba.
Dialing numban mommy yayi ya miqama Ayya, amsa tayi a ranta tana fadin. "Ja'iri miskilin banza baze iyawa mutum magana sedai ya miqo ma mutum waya. "
Cikin girmamawa mommy ta gaida Ayya ta amsa, nan mommy tafad'a mata a gidansu Mansu zata kwana, jim tayi kafin tace. "Lafiyan Mansu klau ko Maryam....? "
. "Eh. " mommy tace tareda fadin. "Gamata kiji da bakinta. "
Amsan wayan Mansu tayi. "Hello Ayya...."
"Yar Amana inji kina lafiya dai ko....? "
"Lafiyana klau Ayya...."
Taba Ayya amsa,
Ayya tace. "To kidai dawo da wuri kinji....."
"Toh...." tace.
Runtse ido Aryan yayi yau ta wayanshi ake waya da wacce yafi tsana duk duniya bacin mommy da seya amshe wayanshi.
Amsan wayan mommy tayi. "Ayya kiyi hakuri ki bamu aronta na sati daya zan turo miki Angle gobe...."
Jim kadan Ayya tayi. "Kuma kukace lafiya...? "
"Eh dama akwai abubuwan da akeso a kammala matane akan jarabawan jamb da zatayi kuma dole se tana kusa dan akwai su tom print kuma dole seda hannunta...."
"Toh shikenen se takwaran tazo...."
Katse wayan mommy tayi domin ta roqi sati d'ayan ne dan tanaso duk raunin da Mansu taji su warke kafin takoma,
Miqa mishi wayan tayi tana fadin. "Dan albarka gobe seka fito ka had'amin breakfast da safe kaga memin batanan...."
Hararanta yayi ya amshi wayanshi yayi hanyan fita yana fadin. "Tunda ita take miki kijira ta mana nine kukun ki..."
Dariya tayi tace. "Allah shirya minkai Dikko duk gidanku nafi sanka bayan Mansu kuma duk kafi kowa ja'iranci...."
Seda tayi Isha'i sannan mommy ta qara hada mata coffee me zafi ta bata, bayan tasha ta kaita dakinta dan daddy bayanan yana Russia.
Lumshe ido tayi se lokacin ta janyo wayanta kiran Aryan ta gani bila adadin ganin ya damu sosai yasa tayi mishi message kaman haka.
```"Am safe am in house now, am sleepless we chat tomorrow....```
Yana gani ya saki ijiyar zuciya shidai yasan basanta yake yiba amma yana jinta a ranshi, ganin tace tanajin bacci yasa ya barta sema yakama wasu ayyukan wanda da besamu daman yiba........
Washe gari.
Da yike yanada baqi da wuri ya fito ya had'a breakfast dinshi yaso ya share Yar tsohuwan se kuma ta bashi tausayi hakan yasa ya had'a mata tea ya soya mata plantain, arish da kwai ya kai mata dinning batareda ya mata maganaba ya fice,
Karfe 2 yasamu kanshi bayan yayi relaxing a resting room dake cikin office dinshi wayanshi kirar Iphone 14 X ya janyo.
Numbanta yai dialing, lokacin tana kwance kan kujeran dakin mommy picking tayi a sanyaye ta kai kunni....
. "Jewelllllll....."
Ya kira sunan kaman maraya,
"Uhmmm...."
Ta amsa ta maqoshi.
"Shine jiya kika tafi ko did yhu know yanda hankalina ya tashi na dauka sun kamamin jewel ne..."
Shiru tayi a sanyaye yace. "Sun miki wani abune....? "
Girgiza kai tayi. "A'a..."
". Hummm are yhu sure. " ya tambaya.
"Eh...." tace
Kafin ya kuma cewa
. "kinji ciwone.? "
A sanyaye tace. "Eh... "
Zazzafan huci ya saki. "Okey lemme come and drees the injury..."
Cikin shagwaba tace. "It's a minor injury am Ok now...."
"Hummm."
Ya saki
"Menene kuma Twinkle? ..."
"Tunani nake da sun miki wani abu to da duniyan nan ta mana kadan amma duk da haka basu shaba senasa anyi arresting dinsu...."
Huci ta saki. "Base