Showing 30001 words to 33000 words out of 100116 words
masa ba kenan? Ta tambayi kanta.
"Kinyi shuru? Ya sake faɗa yana kallonta.
" Bakomai kawai ina addu'a ne zan kwanta"
Bai ce komai ba sai kallonta da yake yi, itama bata karanta tanka masa ba ta kwanta tana lumshe idanunta.
Fita yayi daga ɗakin.
Abincin da Aunty ta ajiye masa ya ɗauka yana fadin " Aunty me yake damun yarinyar nan?
" Shehu ne ya saketa shine fa take wannan abu wallahi kamar na rufeta da duka"
Cewar Zainab tana kallonsa.
"Saki? Ya faɗa yan kallon Zainab. "Eh dazu yazo ya bata takardar"
Ta kuma bashi bayani.
Zama yayi a kujera yana ajiye abincin ya ce " Allah yasa hakanne yafi alkhairy"
Da Amin suka amsa gaba ɗaya.
Kasa cin abincin yayi haka kawai yake jii ba dadi a jikinsa.
*A Month after the divorce*
Farfajiyar gidan ta cika da manyan mata da kuma yan mata har da kananan yara.
Kowa na shagali gabansa haka ma makeken falon dake gidan.
Gaba ɗaya ko ina ba matsala tsinke.
Ta ƙofar baya dake wajejen BQ Farooq da Yusuf suka fito zuwa wajen gidan. Sunsha kyau cikin shadda ɗinki babban riga yar yayi.
"Wajen hour kenan da kiran press amma naga wayam!
Yusuf ya faɗa yana kara kallon inda suke.
Ran Farooq ba dadi ya ce " Auren wa zaka sa a Press? Ni nace karsu zo saboda baza'a je ana circling face dina ana yada ni kowa na fadar albarkacin bakinsa ba! Ka fi kowa sani! Ka sani i despise that girl and even the marriage!
Riƙeshi Yusuf yayi yana faɗin " Calm down kasan yanzu su Baffah zasu zo ko?
"Seriously Yusuf na tsani yarinyar nan! Tana tunanin zata samu peace of mind ne idan ta aureni! Never! Ganganar jikina kawai zata aura amma zuciyata bazata taɓa kasancewa tare da ita ba"
"Nasani Farooq, amma kayi hakuri kaji? UMARNIN UWA zaka cika"
Zai yi magana wasu dattijai uku suka fito daga main gate na gidan.
Kana ganinsu kaga usulin Fulani. Daya daga cikinsu ne yada kafadar Farooq ya ce " Ai na dauka har kun tafi"
"A'a Baffah ku muke jira"
Cewar Yusuf yana ɗan matsa hannun Farooq a kan ya saki fuskarsa.
Kwace hannunsa yayi yana nufar motarsa. Su Baffah ne suka bi bayansu ko wanne fuska a sake.
A kofar gidansu UMMIE yayi parking yana fitowa. Yusuf ne ya karaso inda yake yana fadin " Ango da jan mota"
"Pls ka ajiye joke a gefe am not in d mood"
"Ok" Cewar Yusuf yana gyara wuyan rigarsa.
Motoci ne sosai a kofar gidan, kasancewar ango da mukarrabansa sun hallara yasa aka fara shiga mota dan zuwa masallacin dake nan gaba dasu dan anan za'a daura auren.
A masallacin suka tarar da wasu bakin har sun hallara ciki harda Zayd da Kabir.
Ƙarfe sha daya na safe aka daura auren Farooq da UMMIE a kan sadaki Naira dubu hamsin.
An sha hotuna sosai, Zayd yayi masa Allah ya sanya alkhairy sannan ya kalli Yusuf ya ce " Sai yaushe zaka dawo aiki?
Murmushi Yusuf yayi yana faɗin " Sai kace nine angon? Ai insha Allah gobe zaka ganni a office, wani abu ne?
"Eh zamuyi magana ne"
"Ok toh shikenan" Yusuf ya faɗa yana murmushi.
Farooq kuwa yana samun sarari ya fece ba tare da kowa ya lura ba. Sosai Yusuf ya kulu dan mutane sai tambayar ango suke sai bada excuses din karya ya fi ga yi.
Karfe 7 na dare aka tafi dinner, Kowa yaga ango yasan yana da damuwa haka dai akayi abinda za'ayi aka kai amarya gidanta.
A dakin Mama ra kwana dan tun da aka dawo daga dinner aka nemi ango aka rasa.
Washe gari...
Har karfe tara na safe ba'aga Farooq ba wayarsa kuma a kashe, ran Mama ya ɓaci sosai dan ya kunyata ta a gaban jama'a.
UMMIE kham taci kuka dan tun daren jiya maganganun Yayarta suke dawo ma ta, bata fatan ace zatayi dana sanin auren nan.
Wanka tayi ta shirya cikin atamfa riga da zani sannan ta sakko ƙasa.
★
Zarah, Aunty da kuma Ummie ne a falo suna cin abincin tare. Cikin nutsuwa Aunty ta kalli Zarah ta ce " Dama inaso muyi magana a kan UMMIE"
Da sauri Zarah ta kalli Aunty ta ce " Menene?
Sai da Aunty taja numfashi sannan ta ce " Shehu yaje makarantarsu UMMIE kwanaki, bansan me yake nema ba amma tabbas idan kikaga kare na shinshina takalmi to dauka zeyi"
"Shehu kuma? Zarah ta faɗa cike da mamaki.
"Shi fa" Aunty ta bata amsa. Shuru Zarah tayi na yan wasu dakiku kafin ta ce " Ai kuwa be isa na bashi UMMIE ba ko duk garin nan za'a taru bazan bayar da ƴata ba gashi wancan bigaggen ya dawo gidan da zama wallahi bazai yu ba sai inda karfina ya ƙare"
"Gaskiya ne Zarah Nima ban goyi bayan ki bashi ummie ba dan tarbiyyar ta ake gudu"
"Hakane Aunty shi da ya ce ma ba yar bace har yana da bakin ce min na bashi ita?
"Shine ai" Cewar Aunty tana shan ruwa.
Bangaren Sa'adah kuwa ita ta zuga Shehu ya dawo da ummie dan ta dinga tayata aiki ba sai ya samo yar aiki yana biyanta ba, dakin Zarah na da tasa Shehu ya gyarawa Kaninta Saleh yanzu ya dawo gidan da zama har Shehu na shirin kai shi Nijar dan yin karatu duk da cewa wani abun ba'a san ransa yake ba amma baya son bacin ran Sa'adah.
Kwanaki na ta tafiya watanni na shudewa kwanaki nata karewa, Zarah har ta gama iddah da kusan wata biyu kenan, cikin watan da ta fita daga iddah akayi bikin Zainab kuma basu da nisa sosai sai dai ace Masha Allah dan itama Zainab mijinta balaifi yana da rufi asiri kuma ya yarda zata cigaba da zuwa aikinta.
Bangaren Farooq kuwa tun lokacin daya bar wajen daurin aure ba'a sake ganinsa ba yasan su Mama zasuyi tunanin ya tafi kasar waje kuma za'a iya nemansa hakan yasa yayi tafiyarsa Abuja yake zama a chan dan shi kham bazai dawo ba sai an san yadda za'ayi da ɗiyar mutane saboda baya sonta baya jin kuma zai iya zaman aure da ita, dole ya fara neman aiki a nan Abuja kuma cikin ikon Allah ya samu har ya fara zuwa, ya canza layi be yarda ko Yusuf ya kira ba dan yasan kadan daga aikinsa ya tona masa asiri.
★
Tayi kyau abinta cikin abaya ja da adon baƙi amma kana kallon fuskarta zaka ƙarancin tsantsar damuwa, tana kokarin saka dan kunne Mama ta shigo ɗakin.
Murmushi Mama tayi tana kallonta ta ce " UMMIE Allah yayi miki albarka! Dan Allah UMMIE ki cigaba da hakuri kinji? Bana so mahaifiyarki ta san da wannan zancen kinji?
Murmushin ƙarfin hali UMMIE tayi kafin ta ce " bakomai mama, kuma na miki Alkhawarin babu wanda zaiji wannan maganar daga wajena"
Shafa kumatunta Mama tayi tana fadin " Nagode UMMIE, kuma nasan Farooq zai dawo dan bazai dawwama zama a inda yake ba"
"Hakane" UMMIE ta fada tana kokarin saita kanta.
Murmushi Mama tayi sannan ta fita.
Zama UMMIE tayi tana haɗe kanta da gwiwarta ta fashe da kuka zuciyarta nayi ma ta zafi sosai, ita ya dawo kawai ya saketa! Wannan wani irin lamarine haka ya gudu ya barta da aurensa? Tabbas ga zancen Aunty Hadiza ya fito auren namijin da baya sonka abune mara dadi gashi wajen 5months bata ga mijin da ta aura ba.....
★★
Kayan UMMIE take wankewa dan su taru dayawa sauri take kasancewar Yamma tayi.
Aunty ce ta fito daga ɗaki tana kallonta ta ce " Har yanzu wankin ne baki gama ba Zarah?
"Kedai bari Aunty kayanta akwai dauda"
Cewar Zarah tana dan bata rai. "Toh bari na tayaki" Aunty ta fada tana tsoma hannu cikin ruwan daurayar. Cikin kankanin lokaci suka gama wanki.
Ana kiran sallar Magariba UMMIE ta shigo tana faɗin " Ummana! Ummana! Ni dai wajen Abba zan koma ya ce min zai daina dukanki idan na koma kuma zai dinga kaini makaranta yana dauko ni kuzo ki hada min kayana"
Ta karashe maganar tana wucewa cikin daki da gudu.
Kallon Zarah Aunty tana dauraye hannunta a famfo ta ce " Wato bin yarinyar nan ya dinga yi yana kanainayeta da maganganun karyarsa ko?
Zarah bata jira cewar Aunty ba tabi bayan UMMIE da sauri.
Har ta canza kayanta zuwa na gida. Tana ganin Zarah ta nufota tana fadin " Ummana muje ki kaini"
Kamo hannunta Zarah tayi tana ciro USB na cazar wayarta ta nade skirt din jikinta ta rike hannunta da kyau ta ce " Me kika ce?
Narai² UMMIE tayi da idanu kafin ta ce " Wajen Abba zanje"
Zula ma ta tayi a kafa tana fadin " Maimaita"
"Nidai wajen Abba zanje" UMMIE ta sake faɗa tana hawaye. Zarah zata kara dukanta Aunty ta kwace USB din ta ce " Ya isa haka, UMMIE zo nan"
Da sauri UMMIE ta nufi wajen Aunty tana matsar hawaye.
"Da nace zamuje na kaiki gidan Aunty Zainab ta dinga kaiki wajen wasa amma tunda bakya so shikenan"
"Ni dai wajen Abba zanje" UMMIE ta sake faɗa tana kallon Aunty.
"Toh shikenan jeki dauki abinci kici yana kitchen"
Da toh UMMIE ta amsa ta nufi kitchen din. Ran Zarah a ɓace ta ce " Bansan me Shehu ya fadawa yarinyar nan haka ba"
Dogon numfashi Aunty ta sauke ta ce " Gaskiya kham ya dau lokaci kafin ya shawo kanta amma bai isa ba wallahi"
Har UMMIE tayi bacci bata daina maganar a kaita wajen Abba ba.
Sai wajen 10na dare Zayd ya dawo a matuƙar gajiye.
Zarah ce kawai a falo tana Kallo, sannu da zuwa tayi masa ya amsa yana wucewa dakinsa.
Ya dade a ciki kafin ya fita har yayi wanka ya sauya kaya zuwa marasa nauyi dan ana dan zafi.
"Bani abinci na yau tun rana banci komai ba"
Ya karashe maganar yana zama a kujera. Tashi ta ta nufi kitchen, sai da ta dumamar abincin sannan ta zubo masa ta kawo ruwa ta ajiye sannan ta koma mazaunin ta ta cigaba da kallo.
"Zainab ta ce kince zaki koma aiki?
Taji ya fada, kalllonsa tayi kafin ta ce " Eh, inaso kayi wa Sir Yusuf magana ko ba secretary ba inaso dai na cigaba da yin aikina dan bana jin dadin zaman"
Wani kallo yayi ma ta ya cigaba da cin abincinsa sai daya kammala sannan ya ce " Kinaso ya baki matsayin PA ne?
Harararsa tayi kadan kafin ta ce " Bangane ba"
"Ok nasan dama zai miki wahalar fahimta amma yanzu zan ganar dake"
Ya karashe maganar yana dawowa kusa da ita. Matsawa tayi kadan ta ce " Ko matsayin messenger ne ma inaso kawai bana son wannan zaman"
"Ok zan nema miki wani aikin but banaso ki cigaba a wajen Yusuf"
"But why? Ta fada tana tsareshi da idanunta. Shina idanu ya zuba ma ta yana kallonta. A hankali ta kuma fadin " Meyasa?
"S..saboda ina sonki Zarah" Sai kuma ya tashi tsaye yana ɗan runtsa idanunsa ya dade goshinsa ya ce " Yusuf ma haka and Farooq tayata kike tunani zan bari ki koma aiki nan wajen?
Gabansa ta dawo tana kalllonsa ta ce " Eye contact please" ........
Autar mama ce
✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
*Autar Mama*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow me on Wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 15" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1180379278?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=llp5VPrVm4qKJ4cQgE4%2Bt1xgd8%2Bn2KlZBvXpd9UtRmaufkf6nQrpfoTlLVE6ZjtP2Kj5dWDN78ceIVW92Pd8jj5TVI4GHUAlsJzVjNAuigMCNBP%2FeLDVYNREyBBvmIDk
*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*
*masu tambaya kuyi hakuri tun farko nayi jawabi bazan tura ta Private ba!*
*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*
*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*
https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg
*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*
*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*
*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.
*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)
𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.
*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*
Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...
*K'ANWATA*
*Dandano!Dandano!!*
Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..
Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573
Nomal. guda d'aya N 300 ne
guda biyu N 500 ne
Special guda d'aya N 500 ne
guda biyu N 1000 ne
Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽♀️
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!
*Shafi na sha biyar*
★
Ummie na zaune a falo tana kallo duk ta watsar da al'amuran Farooq dan yanzu ma karatu take shirin komawa, sakkowar Mama yasaka ta juyo da dubanta gareta tana d'an sakin murmushi ta ce " Har kin tashi?
"Eh, inaso zanje gidansu Ramlatu ne zan karbo Sabir daga wajenta tunda bata da hankali"
Shuru Ummie tayi tana mamakin mace irin Ramlah ko ita da ta ke da kananan shekaru bazata yi wautar da Ummie tayi ba, tabbas ta samu miji mai hakuri da wani ne da tuni ya aika ma ta da takardar saki amma Yaya Yusuf jiran ma dawowarta yake.
"Ummie tunanin me kike yi haka? Mama ta fada tana zama kusa da ita.
"Bakomai bari na kawo miki abinci" Ta karashe maganar ta na ta shi ta nufi kitchen. Da kallo Mama ta bita tana me jin tausayinta, ita kadai tasan yadda zatayi dealing da Farooq idan ya dawo.
Bangaren su Shehu kuwa, yanzu bashi da wani kwanciyar hankali kasantuwar Sa'adah bata sarara masa shi kuwa ko kadan baya iya tanka ma ta ga mugun tatsarsa da take yi kuma kudi bana wasa take karba ba karatun ma da yayi niyyar tura Sale tace ya fasa kawai ya sashi a wata makarantar anan bayan kuma ta karbi kudin da niyyar ita zatayi komai.
Tin da ya shi go gidan ya fara cin karo da tsimma. Sale ya gani zaune a kan kujera yana busa sigari. Kallonsa yayi sannan ya kalli falon ko ina kacha².
"Kai ina Sa'adah?
Sai daya zuk'i sigarinsa sannan ya ce "Tana bacci a daki"
Cikin takaici ya nufi dakinta yau dai kham ya gaji da bakin kazantar ta tana fakewa da ciki ne ya sakata.
A kwance y ganta tayi dai² a kan gado tana sharbar bacci daga ita sai daurin kirji. Karamin tsaki yayi yana kallonta ya ce "Ke Sa'adah? Shuru ko motsi batayi ba. Jikin gadon ya daka da karfi, aikuwa a frigice ta tashi tana gyara daurin zaninta.
"Sa'adah ya gidan kacha² haka? Kuma sau nawa zan fada miki ki fadawa kaninki ya daina min shaye² a cikin gida?
Hamma ta saki tana gyara zamanta da kyar dan tayi nauyi sosai kafin ta kalleshi ta ce " Haba Baby daga zuwa zaka tasheni haka?
"Wai Sa'adah me yake damunki ne? Duk zamana da Zarah ban taba gani tayi irin wannan kazantar taki ba"
Tsaki tayi dogo kafin ta yi masa wani kallo ta ce " Kaga bana son cin fuska! Toh uban waye yayi min cikin daya sani yin kazantar? Tun yaushe nake ce maka ka dawo da Ummie ta dinga tayani aiki amma kak'i? Shekarunta 8-9 babu abinda bazata iya ba dayake tsoranta kake ji ka kasa zuwa ka karb'o 'yar ka"
Zama yayi a gefen gado yana shafa Kansa ya ce " Zanje anjima da magariba yanzu dai kawo min abinci na ci"
Hammata ta sosa tana fadin " Ni banyi girki ba tun fitarka danka yake ta min gula a ciki ka fita ka siyo mana abinda zamuci"
Baice komai ba ya tashi ya fita, yana fita ta fada bandaki dan yau kwananta biyu batayi wanka ba.
Kamar yadda Shehu ya fada bayan sallar magariba ya nufi gidansu Zarah. Ya dan dade a kofar gidan