Showing 21001 words to 24000 words out of 100116 words
ma cikinsa bane dan lokacin tana zuwa aiki, data gaji da maganganunsa shine tayi quiting job din amma duk da haka bata tsira ba.
Ta haifi UMMIE da kwana uku ya ce ta tafi gida, a gida akayi suna UMMIE taci sunan Ummanta wato Fatima shine ta sa ma ta UMMIE.
Watan UMMIE uku ya dawo da ita tana son mijinta amma ta rasa me ya hau kansa yake ba ta wannan wahalar tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu, tana zaune ne kawai dan Ummanta ta ce tayi hakuri da abinda yake ma ta amma da tuni ta bar auren.
(Ni kuwa nace sannu Damo... Itama Ummantaki da tace kiyi hakuri abun beyi tsamari haka b a lokacin, ki zauna yayi ta gallaza miki😂)
Lumshe idanunta tayi tana jin hawaye masu zafi na gangarowa bisa kuncin nata.
Bata san lokacin da Shehu ya dawo ba dan sai tashi tayi lokacin kiran sallar asuba. Ta daɗe batayi bacci ba irin na yau.
(Ni kuma nace gwanda kiyi baccin akwai lokacin da zaizo ko rintsawa bazakiyi b😂😜)
★
"Zayd me ya faru ne? Tunda kazo office baka hayyacinka na dauka 3days off din dana baka zaisa k dawo normal but it seems like kana da bukatar ƙarin tima ko?
"No sir thanks! Ya faɗa yana kokarin kawar da damuwarsa, a kwanakin nan soyayyar Zarah kara ruruwa take a zuciyarsa ji yake kamar yaje ya sace ta ya aureta! Amma ya zaiyi? Matar aurece yasan tunanin ta da yake yawan yi ma is unfair amma ya zaiyi? Yana kokarin danne soyayyarta, yana kokarin ganin ya kawar da komai ya saka shi Kasan ransa amma a yan kwanakin nan ya rasa gane kasan he can't Hide his feeling anymore gaba ɗaya yabi ya zama wani iri? What's happening to me?
Ya faɗa a fili ba tare da ya sani ba.
Murmushi Yusuf yayi yana kallon dan ya gama karantarsa tsaf.
"Addu'a ita ce mafita Zayd! Da nayi niyyar zuwa Canada saboda gudanar wani aiki akan zanen University din da aka bamu kwangila, but yanzu inaso kuje kai da Kabir it will make you feel better, kuma ka nutsu ka duba yadda wajen yake domin makaranta akeso a zana a gina shi kuma kamar yadda yake a zane ka gane ko? Ni mistakes Please, zamuje a shirya komai saboda by next week nakeso ku tafi"
"Ok sir" Ya faɗa yana shafa kansa. Fita yayi ya barshi a office ɗin shi kuma ya life kansa a desk din dake gabansa yana ji kamar zuciyarsa zata fashe saboda yadda yake ji....
★★
Half trouser jeans ne a jikinsa sai shirt mara nauyi hannunsa na dama riƙe da wayarsa na hagu kuma cup ne yana shan coffee a hankali yana kuma danna wayarsa.
Mama ce ta sakko daga stairs tasha kyau cikin atamfa ta yada gyale kato ya rufe ma ta jiki sosai sannan ta sakala jakarta a kafada tana riƙe da makullin mota.
Sai data karasa sakkowa ta kalleshi ta ce " Dole dai ka fara zuwa aiki bazai yu wannan zaman ba! Ni zan fita"
Ajiye cup din hannunsa yayi ya kalleta ya ce " Ina zakije?
"Gidan Aunty ku mana! Magana zamuyi a kan aurenka da yarinyar nan UMMIE dan bana so ya wuce wata uku"
Bata jira cewarsa ba ta fice. Ransa duk ba dadi yayi relaxing a kujera yana imagine yadda zai zauna da wadda baya so ko na digo hawaye, baya so ya bawa yar mutane wahala, da an barshi yasan dole² watarana yaga macen da tayi masa ko da bai dora yadda yake son Zarah ba amma za'a wani kakaba masa yarinya karama! Ko wata biyu barayi da yin graduation na O level ba. Tsaki yana me tsaho yana dafa goshinsa,ana yin auren tafiya zaiyi ya barta.
Da wannan tunanin ya dauko cup din coffee dinsa ya cigaba da sha.
*****
Biki saura kwana ɗaya, Zarah tayi matukar mamakin ganin Shehu ya shigo da akwati babba ya ajiye a gabanta wai na ta ne.
Har yanzu ji take kamar mafarki yake especially ma ganin yadda akwatin ya cika da kaya makil.
Shigowa dakinta yayi yana gyara lens din hannun rigarsa ya ce " Idan zaki alkinta ki alkinta dan karki sake sa ran zan miki wani kayan, taso ki zuba min abinci"
Daga haka ya fice ya barta a dakin tana binsa da kallon mamaki.
Bai daɗe da fita ba ta biyo bayansa gudun kar ya balbaleta da masifa.
Abinci ta zuba masa ta kawo gabansa sannan ta dauko ruwa ta kawo masa.
Kamar zata tafi sai kuma ta tsaya muryarta na ɗan rawa ta ce "N..Nagode"
"Uhm" Kawai ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Ita kuma bata kara ko minti ɗaya ba ta bar wajen ta koma ɗaki.
Har bacci ya fara daukarta taki an cillo ma ta abu a fuska. A ɗan tsorace ta tashi tana ambaton Allah.
Ganin rafar yan dari biyar 5 guda uku tayi, daukar kudin tayi tana kalllonsa ta ce " Wannan fa?
"Kiyi siyayyar kayan wannan cikin da ke jikinki sannan kiyi kunshi da kitso na biki dan su Hajiyata zasu dawo gobe saura kuma ki fada musu wata magana kiga yadda zanyi dake"
Bata ce komai ba shi kuma ya fice ya barta. Sai yanzu ta gane inda ya dosa, ashe duk yana yi ne dan idan Hajiya ta dawo ta dauka ya canza.
Ajiyar zuciya tayi ta cire takardar dake jikin kuɗaɗen ta fara kirgawa.
250k ne kuɗin, murmushi tayi kadan tana yi wa kudin ma'adana sannan ta koma ta kwanta tasan Zainab zata zo soon ita zata bawa kudin ta hado ma ta abubuwan da aka fi buƙata.
Washe_gari.
Tana zaune a falo misalin 9am Shehu ya fito daga daki sai khamshi yake yasha wani kyau na musanman. Dauke idanunta tayi daga kansa tana cigaba da danna charbinta.
"Na tafi" Ya faɗa yana kallonta. Harara ta doka masa tana faɗin " Ai ina da ido"
Rage fara'arsa yayi ya ce " ke! Ubanwa kike harara?
Tashi tsaye tayi ta ce " Ubanka!
Daskarewa yayi a wajen dan tun da yake da ita bata taɓa mayar masa da magana ba.
Yana ji yana gani ta wuce ta gefensa mamaki duk ya hanasa yin motsi.
Kiran da ake masa ne ya dawo dashi daga shocked din daya tafi, daukar wayar yayi yana fitowa daga falon.
Zarah kuwa zuciyarta bugu ta dinga yi dan tasan idan Shehu ya shigo kashinta ya bushe, bata san ma lokacin data yaba masa magana ba.
Ƙarfe 12 saura aka daura aurensa sa Sa'adah.
Zarah na dakinta ta jiyo Muryar Hajiya(yayar ummansa) sai Aunty Rabi (kanwar Ummansa).
Tashi tayi da sauri tana fitowa, Aikuwa dai su dinne har da kanwar mijinta Juwairah.
Bakinta a washe ta karaso inda suke tana fadin " Ashe har kun iso"
"A'a jiranki muke yi! Aunty Rabi ta fada tana ma ta wani kallo.
"Rabi! Dattijuwar da ta zauna a kujera ta fada ranta a haɗe.
Shuru Aunty Rabi tayi tana neman kujera ta zauna sai karewa falon kallo take yi.
Hannun Zarah Juwairah ta riƙe tana dan matsawa kaɗan.
Murmushi Zarah tayi tana kwace hannunta ta ce " Yarinya an girma"
Fari Juwairah tayi da idanuwanta sannan ta ce " Bikina ma saura wata biyu"
Zaro ido Zarah tayi bata ce komai ba ta nufi inda su Hajiya suke. Har ƙasa ta gaidasu. Hajiya de kawai ta amsa a sake amma Aunty Rabi a ciki² ta amsa.
Zarah bata damu ba dan inda sabo yaci ace ta saba da halinta.
"Ke ya naga bakiyi taro ba Zarah? Hajiya ta fada tana kallonta.
"Yaushe zatayi? Tana fama da bakinciki" Cewar Aunty Rabi.
Banza Hajiya tayi ma ta tana kallon Zarah ta ce " Meya dameki ne Zarah? Naga kinyi duhu kin rame! Jikinki duk tabo"
Shuru Zarah tayi dan bata jin zata iya yin wata magana kuka be kufce ma ta ba.
" Hajiya kin dameta da tambayoyi fa" Juwairah ta fada tana ƙarasowa ta riƙe Zarah tana karawa da fadin " Aunty zarah muje mu gyara dakin da zasu zauna nasan baki gyara ba saboda baki san zamu zo ba ko?
Tashi Zarah tayi hukunta a sanyaye ta ce " Na gyara ya faɗa min zakuzo ai muje ku kai luggage dinku"
Da toh Juwairah ta amsa tana dauko luggage dinsu su tabi bayan Zarah.
Aunty Rabi ce ta kalli Hajiya ta ce " Kinga tsabar wulakanci ko ruwa bata bamu ba ko?
Ran Hajiya a ɓace ta kalli Rabi ta ce " Wallahi idan baki fita a idona ba sai na saba miki"
Shuru Rabi tayi dan dama a ce babbar ya is a second mother.
Basu daɗe ba suka fito, Kallon Hajiya tayi ta ce " Hajiya me za'a dafa muku?
"Dafa koma menene kinji?
"Toh" zarah ta amsa tana nufar hanyar kitchen. Bin bayanta Juwairah tayi.
Fatira da miyar green beans da hanta tayi musu sannan Juwairah tayi zobo.
Zuba musu tayi Juwairah ta kai musu. Ita kuma ta zuba musu tare ita da Juwairah.
Yaji dadi zuwansu sosai dan ba karamin ɗebe ma ta kewa Juwairah take ba.
By 6pm suka fara jiyo hayaniya alamar yan kawo amarya sun fara hallara.
Kan wani lokaci fakon ya cika da bakin jawo amarya. Kusan 7pm sannan motar amarya tazo, hayaniya kamar zasu fasa gini an kade dakin amarya an ma ta shinfida amsa turaren wuta tun kafin amarya tazo.
Sosai kham amarya ta amsa sunanta dan tayi kyau sosai kamar ba ita ba.
Hajiya ce ta kira Zarah da Juwairah da suke daki suka fito. Kanwar mahaifiyar amarya ce tayi musu nasiha sannan aka damka amarya a hannun Uwargida a matsayin amana. Komai anyishi ba tashin hankali har aka kai amarya dakinta jama'a suka fara watsewa saura ƙawaye masu jiran su siyi baki.
Sai wajen 9 gidan ya dawo dai² baki sun tafi. Suna zaune suna kallo a wayar Juwairah ya shigo dakin baku a washe.
Ajiye ledar dake hannunsa yayi ya ce " Gashi, ke kuma Juwairah ungo wannan ki kaiwa su Hajiya"
Karɓar dayar ledar Juwairah tayi tana fadin " Bazaka shiga ku gaisa ba?
"Eh, sai gobe" Daga haka ya fice ko sallama beyi wa Zarah ba. Taɓa baki Zarah tayi tana binsa da harara.......
*Storm is coming* 😭😭😭
Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
*Autar Mama*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow me on Wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 12" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1177420761?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=jv%2F9p9xdIomZx8tEUvxrvg%2B0UxpLomuqSQFXpv3VKIVT3Ml4Xq4KXtLLNXkQ5PIfonZN7Z81BJ2ExTU%2BrwYQctYwrvD7XpqOxfxYmGWy72nJeRmInC%2BrjIXogaPoXEPG
*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*
*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*
*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*
https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg
*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*
*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*
*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.
*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)
𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.
*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*
Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...
*K'ANWATA*
*Dandano!Dandano!!*
Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..
Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573
Nomal. guda d'aya N 300 ne
guda biyu N 500 ne
Special guda d'aya N 500 ne
guda biyu N 1000 ne
Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽♀️
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!
*Shafi na sha biyu*
Ƙarar slippers dinsa dake sauka bisa tiles din dake jere a stairs ya sanar ma ta da isowarsa.
Ransa a ɓace yake sosai, ƙarasowa yayi kusa da su yana karewa kayan lefen kallo zuciyarsa na tafasa sosai.
" Yawwa Umarun Mama zo kaga kayan 500k kawai zaka ciko saboda za'a karasa siyayya sannan za'a bawa amarya kudin gyaran jiki da sauran abubuwa"
Mama ta faɗa tana kalllonsa fuskarta cike da annuri.
"Ok" Kawai ya faɗa yana neman waje ya zauna.
"Bro! Wannan hade ranfa?
Cewar Yusuf yana kallonsa. Dama jira yake, kallon Yusuf yayi ya ce " Nifa bana son yarinyar nan wallahi!
"Farooq kenan! Aikuwa tunda kaƙi bi ta lallams zaka bi ta dole! Umarni kuma nake baka ka aureta!
Daga haka ta tashi ta basu waje. Kusa dashi Yusuf ya dawo yana taɓa kafadarsa ya ɗan duka alamar rarrashi sannan ya ce " Hakuri zakayi, tun farko laifin ka ne da ace ka fito da mace kayi aurenka da yanzu ba wannan zancen akeyi b...
"Enough please! Farooq ya faɗa da ƙarfi yana tashi tsaye. Da kallo kawai Yusuf ya bishi, tsabar takaici tsaki Farooq yaja yana barin falon!
★
Da kyar aka iya ceto rayuwar Zarah! Ba karamin jini ta zubar ba wanda shima da kyar ya tsaya kuma dole ayi ma ta karin jini.
Leda biyu na jini ya siyo aka ajiye dan ya huce kafin a saka ma ta, nurse ɗin dake kula da ita ne ta kalleshi kafin ta maida dubanta kan drip din dake shiga jikin Zarah ta ce " cikin jiki ta ya zube! Kuma akwai ragowar pieces zakuyi flushing dinsu idan magungunan da muka rubuta beyi flushing dinsu ba, and tana bukatar kulawa sosai"
"Insha Allah" Ya faɗa yana jinjina kai kamar na kirki.
Duk abinda aka bukata a asibitin ya siyo ya ajiye.
**
Ɓangaren Sa'adah kuwa su na tafiya ta koma daki tayi kwanciyarta. Tana ta jiran dawowarsu amma har dare shuru.
Wayarta ta dauka ta kira shi har sau biyu amma bai dauka ba. Gaba daya haushi ya isheta, ƙaramin tsaki tayi tana kwanciya tare da lumshe idanunta.
A asibitin Shehu ya kwana har wayewar gari Zarah ba ta tashi ba.
Sai da Nurse tazo ta duba ta sannan ya taho gida dan yayi wanka ya tafi aiki Sa'adah kuma ta zauna da ita kafin ya dawo.
Jinin zarah ya fara cin karo dashi duk ya bushe, cike da mamaki yake kallon duk inda jinin ya zuba, direct dakin Sa'adah ya nufa, a kwance ya ganta tana latsa wayarta. Tana ganinsa ta mike da sauri tana fadin "Baby ya jikin Zarah? Da kyar jiya na iya yin bacci, ga wayarka a gida shiyasa ban kiraka ba ya take yanzu?
Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan shafa kansa ya ce " Cikin dake jikinta ya zube"
Wani murmushi Sa'adah tayi kafin ta tsuke fuska kadan ta ce " Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, ya zube?
"Hakane, amma meyasa baki gyara wajen dana ce ba?
"Wani waje kuma? Ta faɗa cike da bariki.
"Da zamu fita jiya ban faɗa miki ki gyara wajen ba?
Bata amsa masa ba ta wani riƙe cikinta tana yin ƙara. Da sauri ya riketa yana fadin " Lafiya?
"Tun jiya cikina ke ciwo kaɗan²" Ta fada tana wani shuumun murmushi.
"Sannu, kwanta bari na kawo miki magani"
"Uhm" Ta fada tana zama. Fita yayi ya shiga dakinsa be daɗe ba ya dawo riƙe da maganin ya ballo ma ta sannan ya bata ruwa tasha tana bata rai tare da jero masa Allah ya isa ranta dan shi ya sa ta shan magana ba tare da ciwo ba.
Kwanciya tayi tana wani bata fuska, rufeta yayi yana faɗin " Ki kwanta bari na gyara wajen nazo nayi Shirin aiki"
"Ok" ta fada tana bin bayansa da harara.
Shi ya gyara wajen da jini ya bata har dakin Zarah da toilet komai ya gyara.
Sai wajen 12 yayi shirin aiki, bacci ya tarar da Sa'adah tana yi, hakan yasa ya barta ya fita.
Yana shiga mota yayi dialing number Zayd, har ta gama ringing be dauka ba, text message ya tura masa sannan ya dauki hanyar zuwa asibiti.
Yana office yana duba yadda building dinsu na Canada yake tafiya yaga wayarsa tayi haske. Dubawa yayi yaga missed call daga Shehu sannan kuma ga message daya shigo just now.
Ganin sunan Zarah a message din yasa shi