Showing 78001 words to 81000 words out of 100116 words

Chapter 27 - UMMIE Complete Hausa Novels By Autar mama.txt

09 Nov 2025

2195

Shiyasa naked kokarin komawa" Cewar saleh yana murmushi. "Amma ka cuceta wallahi!

Abokinsa ya kara fada yana kallonsa. "Hakane nasani amma indai ubanta ze bani aurenta inasonta!

"What! Aure? Wai baka da hankali ne? Banza Saleh yayi masa dan haryanzu shaukin abun be barshi ba.

Ni kuwa nace zakaci ubanka...




Yammacin ranar.

"Zarah! Kya kama kuka haka kawai? Kodai akwai abinda nake miki wanda bakyaso? Ko kuma Zaydu?

"Aunty babu komai! Tabbas babu abinda zance daku said godiya saboda kunyi min abubuwan da ba kowani relatives ne suke iya you wa relatives dinsu ba! Tun safe nake ji na ba dadi yanzu ba zazzabi amma na tsinci kaina cikin yanayi mara dadi, ban kuma san dalilin kuka na ba"

Ajiyar zuciya Aunty ta sauke tana kallonta ta ce " Kiyi ta nanata innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Kai kawai Zarah ta gyada zuciyarta ba dadi.

Misalin karfe 9na dare tana kwance a dakinta Zayd ya shigo, tashi zaune tayi tana kallonsa ta ce " yau baka dawo da wuri ba"

"Eh na je asbiti ne, ya jikin naki?

"Da sauki yanzu! "Allah ya kara sauki, Zarah inaso lahadi me zuwa amayar da aurenmu idan kin yarda! Na gaji da zama haka"

"Karatu zan koma" Ta fada tana juya masa baya. Murmushi yayi ya tashi bisa kafafunsa dake dan rawa kad'an, kafin ya ce " Zarah!

Kin juyowa tayi, zama yayi ya ce " Da kin juyo da kinga abinda yasa na kiraki amma tunda baki juyo ba shikenan.

Sai a lokacin ta juyo ta kalleshi ta ce " Menene?

Murmushi yayi yana rungume hanayyensa a kirjinsa ya ce " Zan barki kiyi karatu amma bayan aure"

Sake juya masa baya tayi dan tasan fada kawai yakeyi ba barinta zeyi ba.

Saukar numfashinsa tayi a gefen wuyanta, kafin ta ankara taji hannayensa rike da kugunta. Zaro ido tayi tana kokarin juyowa amma ya hana hakan faruwa dan ya riketa sosai.

Kwantar da kansa yayi bisa kafadarta yana sauke numfashi a hankali ya ce " Please Zarah! Kiyi hakuri nasan nayi kuskure but yanzu zan gyara kinji?

Kasa magana tayi dan ya kashe ma ta jikinta sosai, juyo da ita yayi suna kallon junansu, a hankali ya fara kokarin hade bakinsu...
"Zayd! Yaji Aunty ta kira sunansa. Zaro ido yayi waje haka ma Zarah..........

*Kar ku mayar da Auren ku kwasowa Amina abin kunya😂 ku kwasu musu abun kunya ita da Khadija, only k'awaye fans can relate*

*Yawwa ina sanar dake zan fara sabon labari me taken _BAK'AR SAKAYYA_ Littafin na kudi ne! Just 300 idan ta account zaki tura idan kuma kati ne 400 sannan akwai VIP group wanda zan ke yin posting a rana sau biyu a rana insha Allah 500 ne, zan fara posting Bayan sallah karama insha Allah, labarin ya fita daban da sauran labaran kuma insha Allah bazan baku kunya ba*

Autar Mama ce
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

https://www.wattpad.com/1197828456?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=ueAlDbrs6Yf%2FP%2FLws18VsVhO0mqo1SJapmFf5tQ1%2FQGNUIbRfhguTWuUADLEpzYX%2FT%2FUYM7hTcYZv%2F3%2FyvrfVZIHkZxK68VRxskfs9qQqJK%2F2frtAq4cgrup8ZdzZMK7

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da uku*

Window dake jikin d'akin Ummie ya zuge yana lekawa a hankali, ganin ba kowa sai Ummie dake kwance drip a hannunta ya sashi sauke ajiyar zuciya. Amma me yasa aka saka ma ta drip? Ya tambayi kansa.

"Kai tunanin me kake yi? Idan ba kowa ka ga wannan ka cire karafunan ka shiga"

Juyowa yayi yana kallon abokinsa dake kasa kafin ya ce " Yarinyar kamar bata da lafiya drip ne ma a hannunta. " Kaima kasan dole tayi rashin lafiya ai! Yarinya karama ka haike ma ta ni wallahi ta bani ma tausayi"

Shuru Saleh yayi dan shima tabbas Ummie ta bashi tausayi musanman ma tunowa da irin kokawar da suka dinga yi jiya da ita. Runtsa idanunsa yayi kadan kafin ya budesu yana maidasu kan Ummie.

Sam bega fitowar Sa'adah daga bayi ba dan ya tafi duniyar tunani. "Saleh? Yaji ta kira sunansa da karfi. Da sauri ya kalleta sai kuma ya saki tagar ya dira kafin ta isa bakin tagar sun gudu.

Cike da mamaki ta dawo kusa da Ummie tana kallonta zuciyarta fal tunanin me Saleh yake yi a wajen kuma meyasa ya gudu data ganshi? Sosai alamun rashin gaskiya suka bayyana a fuskarsa. K'ara sosai Ummie ta saki lokacin data farka wani azababben zafi da tajina kasanta kuma kamar an daure wajen.

Da sauri Sa'adah ta kalleta tana fad'in " Sannu Ummie"

" Saleh ne! Wallahi Saleh ne yaji min ciwo! Shine! Saleeeeh ne" Cewar Ummie tana fashewa da kuka.

Kalmar Innalillahi wa inna ilahi rajiun kawai Sa'adah ke maimaitawa bugun zuciyarta na karuwa.....



Cikin nutsuwa Mama ke kallon Yusuf da ya gama zubo ma ta bayani kusan na minti biyar. Murmushi tayi kadan ta ce " Shikenan Yusuf Allah yayi maka albarka kuma ya sa hakan zaisa Auntyn ku ta sakko daga fushin da take da no da kuma Farooq"

Murmushi shima yayi yana tashi tsaye ya gyara rigarsa ya ce " Bayan magariba zanje insha Allah"

"Allah ya kaimu" Mama ta amsa tana komawa ta kwanta. Shi kuma ya fita. A daki ya tarar da Ramlah tana danna wayarta. Toilet ya shiga ba tare da yace da ita komai ba. Be dade ba fito yana goge jikinsa.

"Madam! Wani kallon kashi tayi masa ba tare da ta amsa ba. Murmushi yayi a fili ya ce " Komai ya kusa zuwa karshe Ramlah!
"Karshenta kace aure zaka kara ko? Toh kayi mu gani"

"Shikenan ko fara shirin zama da kishiya dan nan da wata biyu zuwa uku zanyi aure insha Allah"

Da sauri ta kalleshi, sai kuma ta fashe da dariya ta ce " Yusuf kenan! Ni dinnan! Ni kadai ce matarka wallahi! Baka isa ba! Idan kaga kayi aure toh sai dai mutuwa nayi"

Daga haka ta fice ta barshi a dakin yana murmushi.

A unguwarsu Ummie yayi sallar magariba. Yana idarwa ya nufi gidansu. A kofar gidan ya tsaya ya fara knocking.

"Waye? Yaji muryar Ummie. "Yusuf! Ya fada atakaice. Kusan 10s sannan ta bude tana kallonsa. Shigowa yayi yana fad'in " Aunty fa?

"Ta je gidan barka dazu har yanzu dai bata dawo ba amma anjima kadan zaka ganta nasan ta tsaya a yi magariba ne sannan ta taho"

"OK" Ya fada yana yin gaba. A kujera ya zauna sannan Ummie ta shigo tana fad'in "Bari nayi sallah"

Daki ta shiga ta dan jima sannan ta fito ta nufi kitchen ta kawo masa ruwa da lemo ta na zama dan nesa dashi ta ce " Ina yini?

"Lafiya lau Ummie ya makaranta?

"Alhmdll munyi ma hutun 2nd semester"

"OK Allah ya bada sa'a" Da amin ta masa tana dauke ka ta daga kallonsa.

"Yanzu an girma an dena jin tsoro a tafi an barki ke kadai" Ya sake fada hankalinsa a kan wayarsa.

Murmushi kawai Ummie tayi tana kallon TV.

"Zaki iya auren me mata da d'a?

Taji ya jefo ma ta tambayar bazata. Zuciyarta tace ta buga kadan bakinta na dan rawa ta ce " N..n..nidai kawai ina addua Allah ya bani na gari wanda zai soni tsakani da Allah kuma ya kula da ni"

"Masha Allah hakan abune me kyau! Ummie! Ya karashe maganar yana kiran sunanta. Kallonsa tayi ba tare da amsa ba. Ajiye wayarsa yayi yana maida hankalinsa gareta ya ce " Zaki iya aurena?

"Kai kuma? Ta fada cike da mamaki. "Eh Ummie! Ni, ko na miki tsufa?

Kai ta girgiza alamar a'a kafin ta dora da cewa " Nasan zaka aureni ne dan ka gyara kuskuren da Yaya Farooq yayi zaka aureni ni dan ka gyara duk abinda ya bata! Ni kuma bana son irin wannan auren! Nafiso na auri wanda yake sona"

" Ni nace miki bana sonki ne?

Ya fad'a yana kallonta.

"A'a amma nasan dalilin da yasa kake son aurena kuma ni bazan iya kishi da Aunty Ramlah ba!

Kafin ya kara wata maganar Aunty karama ta shigo bakinta dauke da sallama.

"Wai Allah ne ya taimakeni hadari ya hado lokaci daya nasha wuya kafin na samu napep! Ummie bani ruwa"

Ta karashe maganar tama cire hijabin jikinta.

Sai a lokacin ta kira da Yusuf sake zaune. "Au! Ashe kana nan! Toh Adda ta turo ka ne ko yaya?

Murmushi yayi yana fadin " Sannu da zuwa, ina yini?

Zama tayi tana amsawa, ruwan da aka kawo masa ta dauka ta tsiyaya ta sha tana fad'in " Ya addah?

"Tana nan cikin damuwa wallahi" "Ai shikenan ni ai na dena fushin da ita amma banda Farooq tunda bai da mutunci!

"Hakane kiyi hakuri Aunty karama insha Allah zai gane kuskuransa" "Ai dole ma wallahi! Ummie ko ba kanwarsa bace ai be kamata yayi ma ta haka ba ballanata sun hada jini! Ni har kunyar mutane nake wallahi! Bana so asan sako min ya yayi wallahi!

Aunty ta karashe maganar cikin takaici. Murmushi Yusuf yayi yana dan kallon Ummie kafin ya ce " Bamu waje" Tashi tayi ta koma daki jikinta duk a sanyaye.



"Wai yau babu aiki ne Zaydu? Aunty ta fada tana kallonsa. Gyara wuyan rigarsa yayi yana kallon TV ya ce " Akwai bazan je ba ne Aunty Yusf yace na huta na kwana biyu"

"Toh, sai ka raka Zarah ta ce zata ce gyaran gashi kuma zata biya gidan Zainab"

"A'a! Ni na gama shiryawa tafiya zanyi" Ceqar Zarah tana fitowa daga daki hannunta rike da mayafi.

Ajiye jakarta tayi sannan ta yafa mayafin tana dora jakar a kafadarta bayan ta kara gyara goyanta.

"Wai mayafi zaki saka? Zayd ya fada yana kallonta. "Gashi ka gani" Ta fada tana dauke kanta faga gareshi. "Ai mayafin babbane!

Cewar Aunty tana kallon Zarah. "Ni ba ina damuwa bane da ita ta fita babu mayafin ma amma ta ajiye min yarona kar rana ta dafar dashi"

Zaro ido Zarah tayi tana kallonsa cike da mamaki. "Eh ki fita ba mayafi amma Indai da khaleel zaki fita sai kin saka hijabi.

Kwafa Zarah tayi tana cire mayafin da jakar ta kwanto khaleel dake bacci ta ajiyeshi a cinyar Zayd ya gyara rigarta sannan ya yafa mayafin ta rataye jakar ta ce " Aunty na tafi"

Daga haka ta nufi hanyar fita.

"Zarah! Zarah! Zarah! Ya kira sunata da karfi amma ko juyowa batayi ba. Murmushi Aunty tayi dan tasan ba tafiya zatayi ba tunda har zataje gidan Zainab to ba yanzu zata dawo ba kuma bazata bar Khaleel a gida ba"

Mik'awa Aunty Khaleel yayi yana tashi tsaye, sosai kafafunsa suka fara rawar kerawa, baki bude Aunty take kallonsa kafin ta kira Zarah da karfi. Jin yadda Aunty ta kirata ya saka ta dawo da sauri.

Zayd ta gani a tsaye amma kafafun na rawa sosai. Kasa motsi tayi ta kame tana kallonsa tana ji kamar mafarkin data saba yi ne.

Da kyar ya koma ya zauna kafafunsa na yi masa wani iri. Hawayene suka fara biyo kuncin Zarah hawayen da ake kira da tears of joy. Karasowa tayi tana kallonsa.

"Yaushe ka fara tashi? Ta fada tana rike damtsen hannunsa. Idanu ya tsira ma ta yana kallon cikin idanuwanta wad'anda ke cike da farinciki.

"Kusan sati biyu kenan da idan na tashi faduwa nake but yanzu akwai improvement sosai, doctor yace tu da kafafun basu sirance ba zan dawo dai dai insha Allah"

Zayd ya fada yana kallonsu. Rungumeshi Zarah tayi tana fashewa da kuka dan tana yawan mafarkin wannan ranar.

Lumshe idanunsa yayi yana dan shafa bayanta a hankali. Kusan 1min tana rungume dashi kafin hankalinta ya dawo jikinta. Da sauri ta matsa tana goge hawayen idanunta.

"Ni rashin kunyar nan ta isheni! Kafin ku janyo min abin magana gwanda amaida auren nan, zan kira kan in mahaifan ku jibi lahadi azo a mayar da auren nan gaba bansan me zan gani ba"

Aunty ta fada tana tashi ta saka khaleel a kafada ta nufi daki.

Riko hannun Zarah yayi ganin tana son tashi. "Kin yarda? Kai ta gyada alamar eh. Murmushi yayi ya ce " Allah ya tabbatar mana da alkhairy!

Amin ta fada tana kwace hannunta ta gyara mayafinta ta jakarta ta nufi daki.

Bata dade ba ta fito sanye da hijabi da bayanta goye da khaleel.

"Sai dai ki tuka kanki dan nace driver yaje gida hutun 2days"

"Ba marsala zan hau napep kawai"

"OK toh sai kin dawo ki kula" "Insha Allah ta fada tana fita.

Bata dade a saloon ba saboda ba layi, karfe 3 saura ta je gidan Zainba. Sosai suka sha hira nan take shida ma ta ramar lahadi zaa mayar da auren, dan dole Zainab ta tilasta ma ta suka je gidan kunshi iya ja akayi ma ta me kyau. Dan abun gyara Zainab ta ba ta sannan ta bata wasu kaya data di ka musu ita da Ummie ta ce ta ajiye idan Ummie tazo ta bata.

Sosai kayan sukayi kyau tunda yanzu magariba tayi kuma basu da wani nisa sosai zata biya ta kaiwa Ummie kawai idan Shehu ya yarda ma zata taho da ita dan ta dade bata ganta ba.

Sai da tayi sallar magariba sannan ta bar gidan Zainab. Said data biya super market ta siyowa Ummie da Ihsan abubuwan kwadayi sannan ta nufi gidan Shehu.

Tasan Ummie zata ji dadi idan taga kayan dan yarinyar tana son ado sosai.....

Knockin din gate din gidan tayi, me gadi ne ya leko yana fadin " Waye? Ganin Zarah ya sashi fadada murmushinsa. Hade fuska tayi dan ba wani zaman dadi sukayi da me gadin ba, gaida ita yayi ta amsa tana wucewa cikin gidan....

*magane pls kiyi hkr dani two days dinnan insha Allah kafin ramadan zan gama insha Allah*

Autar Mama ce
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
Autar Mama

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow mr on wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 34" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1199411815?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=BNv4QvqeVlFq%2BXa1cLZ3%2FgtWAXlIf5yUSz05bDANUxAj%2FkcpCkmhKbmxGp92O4dBr1Bh%2FIqzS2qj9vwzmub9cxFTSH9vR2RVjjFYmBWl446Rkj5Mju7jfE2SzWxOp6vv

*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*

*BAK'AR SAKAYYA*

*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*

*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*

*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*

*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*

*Shafi na talatin da hudu*

A kofar falon ta tsaya tana gyara Khaleel dake mutsu² zai fara rigima.

Tana shirin kwankwasa kofar Shehu ya bude yana shafa fuskarsa dake cike da damiwa.

Mutuwar tsaye yayi yana kallonta, sosai kirjinsa yayi wani mummunan bugu. Bake-bake yayi a jikin kofar yana fad'in " K..Ke ce da daddaren nan?

Kallonsa take yi ganin sa duk a birkice. "Zan wuce nazo ganin Ummie" Ta fada tana kallonsa.

"Ummie tayi bacci zaki iya tafiya"

Sosai take ganin wani bakon lamari a tattare da Shehu ya wani susuce duk ya birkice kamar mara gaskiya.

"OK ga wannan ka bata" Ta fada tana mika masa kayan hannunta. Karba yayi ita kuma ta juya ta tafi zuciyarta cike da tunani kala².

Tana fitowa bakin gate din ta fara tafiya zuciyarta na darsa ma ta wani abu! Tun da take da Shehu be taba hanata shiga gidansa ba ko bayan rabuwarsu amma yanzu ta karanci wani yanayi daban a gareshi ko dai Ummie bata da lafiya? Ta fada a fili. Tsayawa tayi da tafiyar tana tunani.

Ko minti

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login