Showing 45001 words to 48000 words out of 100116 words
kuma ta rungumeta zuciyarta na karaya.
"Ummana kinga Aunty Sa'adah tasa Abba ya kaini an aske min gashi ko? Ta karashe maganar tana cire hular kanta. Ai kuwa ga kanta tas dashi ba gashi ko kadan.
Da sauri Zainab ta cire nikaf dinta tana taba kan Ummie ta ce " Kan ubanchan"
Sai kuma ta kalli Sa'adah ta ce " Uwar waye yace kiyi ma ta aski?
"Ummie ce bata son kitso shiyasa nasa aka yi ma ta" Cewar shehu yana kallon Zainab.
"OK" Zainab ta fad'a tana jinjina kai amma ita kadan tasan me zatayi wa Sa'adah.
Its dai Zarah bata ce komai ba ta sai hawaye dake zubo ma ta na takaici.
"Zuwa mukayi mu tafi da Ummie sabida ta hallarci bikin ummanta" Cewar Zainab tana karbar jakar Zarah ta ciro IVC din da Zayd ya ba ta ta mikawa Shehu ta ce " Ana gayyatar ka"
Data haka ta nemi kujera zauna tana fadin " Sa'adah ko ruwa babu?
Banza Sa'adah tayi ma ta zuciyarta cike sa haushi.
Zarah ce ta mayar wa Ummie da hular ta tana fadin " Jeki saka takalmi"
"Ina kuke tunanin zuwa?
Cewar Sa'adah.
"Baki isa kin hanani daukar yarinyata ba" Zarah ta bata amsa.
Shi sai Shehu kasa cewa komai yayi.
Zarah ce ta kalli Zainab ta ce " Muje"
"A'a mu dan taya Sa'adah hira tunda naga Shehun aiki zai tafi"
Tunda Zarah taji haka tasan akwai abinda Zainab din ta shirya.
Girgiza kai tayi tana Kallonta. Da kyar Shehu ya iya tashi yana fadin " Allah ya sanya alkhairy"
Da Amin Zainab ta amsa. Jakarsa ya dauka ta aiki ya fice ba tare da yace da kowa uffan ba.
Yana fita Zainab ta cire hijabinta ta je ta kulle kofa tana kallon Ummie ta ce " Dauko min almakashi wallahi Sa'adah sai na miki aski yau"
Aikuwa Ummie da gudu ta nufi kitchen bata dade ba ta dawo da scissors.
"Zainab me haka,wai mu tafi dan Allah"
Cewar Zarah tana kallonta.
"Ke Ummie dauko min clipper din babanki yi sauri"
Zainab ta kara fada tana kallon Ummie.
"Bansan in da yake ba" Ummie ta fada tana kallonta.
Sa'adah kuwa kokarin tashi take amma ta kasa dan tayi nauyi.
Zarah rike min hannunta.
Duk da Zarah bata so Zainab tayi hakan ma amma gwanda itama taji idan da dadi.
Rike Sa'adah tayi Zainab kuma ta bude kanta, kitsone guda shida. Haka Zainab tabi kitson nan ta ciresu tas a kan Sa'adah sai hawaye ta keyi. A gabanta Zainab ta ajieye kitson tana fadin " Ummie bazata dawo gidan nan sai gashinta ya dawo kjma wallahi kika kara aske ma ta a kotu zaki ji ki sakarya kawai" ko jikaf din basu mayar ba suka baro gidan.
Zayd har ya gaji da jiransu.
Ummie na shigowa motar ya kalleta ya ce " Ya naga goshinki ba gashi?
Ko gyara zama Zainab batayi ba ta ce " Wannan yar iskar ce ta saka sakaran ubanta yayi ma ta aski nima kuwa sai da nayi wa Shegia kafin mu fito"
"Good! Cewar Zayd yana tada motar subar kofar gidan......
*4 days to the wedding*
Sorry for the typing errors.
Autar Mama ce
✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
*Autar Mama*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow me on Wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 18" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1183371201?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=CnjS3OYFsfcLcTAtV8W8%2BJROWL0VtgNtV4DFF6uz2fudt5IOmnUwnFFfJMJjIy449LeTSEg4QzB7dapjiMxEStpJo4NSazFB%2BPg28%2B8oS75wFY1%2FzVDOGHCh1VYCeyJN
*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*
*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*
*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*
https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg
*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*
*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*
*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.
*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)
𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.
*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*
Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...
*K'ANWATA*
*Dandano!Dandano!!*
Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..
Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573
Nomal. guda d'aya N 300 ne
guda biyu N 500 ne
Special guda d'aya N 500 ne
guda biyu N 1000 ne
Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽♀️
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!
*Shafi na Sha takwas*
*Washe gari*
Tun da tayi sallar asuba bata koma bacci ba, gari na waye wa ta fara gyara dakinta duk da cewa beyi wani datti ba amma ta kara kintsa shi, burner ta nema amma bata gani ba fitowa tayi daga d'aki tana k'arewa falon kallo, lallai Zayd ya kashe 'ya'yan banki dan ba k'aramin tsaruwa falon yayi ba.
K'ofar kitchen a bude take hakan yasa bata sha wahalar ganewa ba. Breakfast me sauki ta hada musu shayi bread da kuma kwai.
A dining ta jera komai tan sauke nunfashi a hankali. Dakinta ta koma danyi wanka. Har tayi wankan ta fito cikin atamfa riga da zani amma Zayd be fito ba.
Zama tati taco abincinta hankali kwance tana ta baza idanu amma har ta gama Zayd be fito ba. Dakin da take tunanin shine nasa ta nufa ta fara knocking. Jin be amsa ba ya saka ta tura kofar dakin a hankali, sanyi sosai falon ya dauka dan ya ware AC. Karewa falon kallo tayi komai yayj ba karya, hanyar bedroom ta nufa shima sai data gama kare masa kallo sannan ta kalki kan gado.
A cikin bargo ta hangoshi ya rufa har kansa. Kamar wadda ke tsoran a kamata haka ta nufi inda yake a hankali. "Goma fa ta wuce"
Gyara kwanciyarsa yayi yana kuma jan bargo.
"Kasan su Inna zasu zo ko? Ya kamata ace ka tashi kayo cefene da za'ayi musu abinci dan banga kayan masarufi ba"
"Zaraaaah" Ya kira sunanata yana jan karshen muryarsa cike da bacci. Yaye bargon tayi tana kallonsa.
A hankali ya bude idanunsa yana kallonta daga sama har kasa, sai kuma ya tashi zaune yana fadin " Ina gaisuwar? Yanzu dai ni mijinki ne ba Zayd din gida ba wanda said kinga dama kika gaishesa.
Murmushi tayi kadan tana durkusa ta ce " Ina kwana?
"Haka ake gaisuwa? Haka ya kamata? Ya fada yana wani hade rai. Cike da mamaki ta ce " Ya ake yi to?
Tasowa yayi daga kan gadon yana riko hannunta ya tasar da ita tsaye, ita dai sai kallonsa take yi. Side hug ya bata yana wani matseta kafin ya hura ma ta iska a kunne ya sumbacin kumatunta ya ce " Good morning my darling Z"
Murmushi tayi kadan tana dan tureshi ta ce " Ni bazan iya wannan ba"
"OK shikenan, ni zan dinga miki ai, yawwa shine jiya kika kulle kofa ko?
Ji tayi kamar ta nitse dan kunya amma sai ta maze ta ce " Na gama abinci har naci nawa, in kawo maka nan ko zaka fito kaci?
"Eh zan fito but first muje kiyi min wanka"
Zaro ido tayi ta juya da sauri zata tafi, riko hannunta yayi yana dawo da ita kusa dashi idanuwansa cikin na ta ya ce " Bana son kunyar nan kinji ko?
"Uhm" Ta fad'a tana son kwace hannunta.
Sakinta yayi yana shigewarsa toilet. Tafi minti uku a tsaye a wajen sannan ta fita daga dakin.
Bata koma daki ba kitchen ta nufa ta kimtsa shi ta bude fridge, komai da take bukata akwai har yayi kankara ma. Murmushi tayi tasan wannan aikin zainab ne.
Fito da abubuwan da zatayi amfani tayi ta ajiye su dan su huce kafin ta fara girki.
Sauke ajiyar zuciya tayi fuskarta dauke da murmushin jin dad'i. Bazata cika baki ba amma tasan Zayd bazaiyi treating dinta kamar yadda shehu yayi ba.
Breakfast dinsa ta hada a tray ta nufi dakinsa.
Har yanzu yana toilet, ajiyewa tayi ta fice da sauri dan bata so ya fito tana nan haka kawai ta rasa dalili kunyar Zayd ta shigeta tun lokacin da aka daura aure.
Tana zaune a falo taji ya dafata ta baya. Bata juyo ba said zuciyarta data buga. Yana lura da yanayinta ya rasa gane me ya shigeta meyasa ta ke tsoransa dan shi yanayinta ya nuna masa tsoransa take ji.
Ajiyar zuciya ya sauke yana zagayowa ya zauna kusa da ita ya ce " Sai yaushe zasu zo?
"Nafi tunanin da yamma, tunda ba nisa zuwa dare sai su tafi"
"OK" Ya fada yana kallonta.
Ta shi tayi tana fadin " Bari na kunna kallo"
Hannunta ya jawo ya dawo da ita kan kujera yana bin ta da kallo.
"Zan kunna kallo" Ta fada zuciyarta na bugawa ganin yadda yake kallonta. Murmushi yayi kadan ya ce " Ok" Sakinta yayi ta tashi da sauri ta nufi wajen TV.
Kasa jonawa tayi dan ji tayi jikinta na rawa. Gaba daya haushi da takaicin kanta duk ya isheta ko aurenta na fari batayi wannan abun ba sai kuma wannan? Shi kanshi Zayd tasan baya jin dadi kawai bazaiyi magana bane.
"Barshi zan jona" Ta ya fada daga bayanta. Matsawa tayi tana binsa da kallo har ya jona. Be ce da ita komai ba ya koma mazauninsa yana canza channel.
Hanayar daki ta nufa cike da haushin kanta. Bin bayanta yayi da kallo zuciyarsa cike da mamaki.
Ajiye remote din yayi yabi bayanta. A gaban mudubi ya ganta ta tsirawa kanta idanu. Inda take ya karaso yana saka hannayensa ya zagaye kugunta fuskarsa akan kafadarta suns kallon juna ta mudubi.
Numfashi ta sauke a hankali tana sauke idanunta kasa. "Zaraaah! Please ki saki jikinki" Ya fada yana kallonta ta mirror.
Shuru tayi dan bata san me zata ce masa ba. Juyo da ita yayi yana kallon fuskarta ya ce " Karki sa na fara kokwanton soyayyar da kika ce kina min ko kuma nayi tunanin kin amince da aurena ne saboda Aunty da Zainab, Zarah inason muyi rayuwar aure me cike ds farinciki da kuma soyayya, meyasa zaki fara da wannan yanayin? Ko nayi miki wani abu ne?
Ya karashe maganar yana dago da habarta. Kin kallonsa tayi dan tana daga idanunta hawaye ne zasu zubo wanda ita kanta bata san na menene ba.
Numfashi ya sauke yana sakinta dan gaba daya ta sagar masa da gwiwa ba haka yayi zato daga gareta ba.
A sanyaye ya fice daga d'akin. Zama tayi a gefen gado tana dafe kanta cike da takaicin abinda takeyi. Amma ya zatayi ba laifinta bane itama ba'a son ranta take haka ba, ta rasa gane me yake damunta amma tun wuri ya kamata ta gyara bata so ta zama solar kawo wani misunderstanding tsakaninta da mijinta.
Da sauri ta sha re hawayenda suka zubo ma ta, tashi tayi tana fitowa daga dakin. Bata ganshi a falo ba, dakinsa ta nufa nan ma baya nan. Wajen gidan ta fito ta duba ko ina bata ganshi ba. "Ba dai ya fita ba? Ta fada a fili.
Cikin gidan ta dawo ta dauko wayarta tayi dialing number dinsa. Bugu biyu ya dauka yana fadin " Ina jinki"
"Kana ina? Ta fada a hankali"
"Na kusa karasawa gida zan gaidasu Inna ne"
"Shikenan" Ta fad'a a sanyaye. "Wani abu ne? Ya saka fada dan jin kamar bata so fitar tashi ba.
"A'a" Ta bashi amsa tana kashe wayar.
Kwanciya tayi a kujera tana lumshe idanunta, yana dawowa zata bashi hakuri daga aure jiya har ta fara b'ata masa rai? Da auren fari ne tasan zai mata uzuri ta rufe masa kofa sannan tana wani treating dinsa kamar stranger.
Tana cikin wanna tunanin wayarta ta fara ruri. Tana ganin sunan Zainab ta dauka da sauri tana fadin " Na dauka zaki ko da safe ai dan duk wasu kayan basan i da kikai musu matsugnni ba"
"Ba wannan ba Zarah, naga Yaya yazo ba wani fara'a ko washe bakin nan da sabon ango yake yi banga yana yi ba"
Shuru Zarah tayi na 'yan seconni kafin ta ce " Zarah dama ilimin karantar yanayin mutun kikayi ba harkar lafiya ba! Daga ganin sa sai ki fara wani banzan tunani"
"Hmm ke abunne yaban mammaki gasu Inna chan ma said tsiya suke masa wai baya dariya, toh nidai zan baki shawara a matsayinki na kanwata kardai ki bada damar da abu mara dadi zai fara faruwa tsakanunku kinji ko?
"Insha Allah, yaushe zaku zo?
"Zuwa gone sunce yau hutawa zasuyi ni da yau nake son tafiya na barwa kishiyata miji gwanda na koma"
Dariya Zarah tayi tana fadin " Dad'inta dai dashi kika ganta"
"Eh amma yanzu dai mijin mu ne! Ban ma fada masa ina ciki ba sai jiya na aka turo min da result na BT aka tabbatar min wata biyu"
"Masha Allah, ya kamata dai ya sani da wuri Allah ya saukeki lafiya"
Zarah ta fada cike da farinciki. "Amin, kuma karki fadawa kowa dan ko Aunty bata sani ba"
Murmushi Zarah tayi ta ce " Baki da matsala, yaushe din zaki tafi?
Daga d'ayan b'angaren Zainab ta ce " Gobe insha Allah, by 10 zamu zo gidan ki zuwa azahar sai na kirashi kinga kafin la'asar yazo sai mu tafi dan jibi Abuja zamu koma daga chan ma ya ce zasu wuce Lagos shida uwargida idan kwanata ya zagayo"
"OK Allah ya kara had'a kanku" Da Amin Zainab ta amsa sannan sukayi sallama.
White rice da stew tayi wanda yaji naman kaza taso yanka ganye a kai amma babu wanda zata aika.
Bata ci abincin ba ta zauna zaman jiranshi har yamma be dawo ba kuma ta kira wayarsa a kashe. Gaba daya bata jin dadin gidan.
Bayan tayi salkar magariba ta sake wanka ta saka doguwar riga me kyau amma mara nauyi.
Gamin yunwa na nema halakata yasa ta zuba abincin taci. Sai da akayi salkar ishai ya dawo.
Tana zaune a falo tana kallo taji sallmarsa. Kallonsa tayi sannna ta amsa tana fadin " Sannu da zuwa"
Murmushi yayi ma tabyana fadin " Ayi hakuri yau nayi laifi, Sule ne ya takura sai na zaga gari dashi shiyasa"
Ya karashe maganar yana zama kusa da ita. "Kinyi kyau" Ya fada yana kallonta.
K'asa tayi da kanta tana murmushi. "Sarkin kunya! Banci komai ba kawo min abinci"
Ya fada yana kallon TV.
Sai da ta kara warming din abincin sannan ta kawo masa.
"Amarya da heavy food haka? Ya fada yana fara cin abincin.
Bata ce komai ba sai murmushi kawai ds tayi.
"Kazar amarcin ki ma baki ci ba tana fridge" Ya fada yana nuna fridge din dake falo.
Bata ce dashi komai ba shima bai kara magana ba har ya gama cin abincin.
Sun dade a falo suna kallo har kusan 12am sannan ya kalleta ya ce " Bakya jin bacci?
Sai a lokacin ta samu courage din cewa " Kayi hakuri"
"Hakuri kuma Zarah? Me kikayi?
Shuru tayi dan itama bazata ce masa ga abinda tayi ba tasan dai bata kyauta ba.
"Amarya ai bata laifi ko ta kashe dan masu gida, tashi kije ki kwanta"
A sukwane ta tashi ta nufi dakinta, bayanta yabi da kallo yana murmushi.
Har bacci ya dauketa bata daina tunaninsa ba.
Washe_gari.
Karfe 11 saura su Inna suka zo har da Ummie da Zainab.
Tasha nasihohi sosai dan shima anyi masa nasa jiya. Sun kara zaga gidan sosai sai yamma sai Zainab ta tafi Ummie kuwa cewa tayi taga gidan zama babu inda zata tafi.
Sai bayan magariba Zayd ya mayar dasu Inna gida suna ta saka musu albarka.
Zarah na yi wa Ummie yankan farce Zayd ya shigo gidan yana kallonsu ya ce " Yanakan farce da daddaren nan salan ki yanke ta?
"Yayi tsaho dayawa dazu ta jimin ciwo" Zarah ta fada tana kallonsa.
Zama yay yana kallon Ummie ya ce " Kwakwis!
Turb'une fuska Ummie tayi tana kallon Zarah ta ce " Umma kinga