Showing 6001 words to 9000 words out of 100116 words

Chapter 3 - UMMIE Complete Hausa Novels By Autar mama.txt

09 Nov 2025

2168



Da sauri ta juya masa baya tana kara goge idanunta.

"Uncle Zayd Ummana sai kuka take yi nima shiyasa nayi kuka, Dan Allah ka bawa Ummana hakuri ni bana so inganta tana kuka"

Rage tsaho yayi ya dawo yana riƙo UMMIE ya ce " Nima haka UMMIE, kukan Ummanki yana sa ni naji zafi a zuciyaata yana sani na kasance cikin damuwa, amma insha Allah watarana sai labari"

Tashi tsaye yayi ya kalli Zarah ya ce " Muje na kaiki gida"

Bata ce komai ba, shi yafara yin gaba hannunsa riƙe dana UMMIE har suka iso inda motarsa ta ke.

Wayarsa ce ta fara ruri. Dubawa yayi yaga Yusuf ne. Karamin tsaki yayi kafin ya daga yana faɗin " Hello"

Tana ji Yusuf ya ce " Zayd ka dauko files a mota kazo ina jiranka"

Kallon Zarah yayi kafin ya ce " S..sir zan kai Zarah gida ne bata jin dadi"

"Ayyah kace ina gaisheta ya UMMIE? "Ok sir"

"Yawwa, kafin ka tafi ka kawo min files ɗin"

Be jira cewarsa ba ya katse wayar. "Ina zuwa" Zayd ya fada barin wajen.

Jingina tayi jikin motar tana riƙe da hannun UMMIE.

"Hawaye basuyi deserving zuba a fuskarki ba Zarah"

Da sauri ta kalleshi. Sosai ya kara manyanta rabon data ganshi 2yrs kenan.

"Sir" Ta fada tana kalllonsa.

Hankici ya bata yana fadin " Wipe those tears Zarah. Hannunta na rawa ta karba tana goge fuskarta.

"Ummana mu tafi yunwa nake ji"

Buɗe motar Zayd yayi yana fadin " UMMIE shiga"

Ba musu ta shiga seat din gaba.

"Insha Allah komai zaizo karshe kinji? Dama shi gidan aure gidan hakuri ne, ki dage da addu'a" "INSHA ALLAH, kayi hakuri da abinda ya faru banyi tunanin Shehu zeyi wannan banzan tunanin ba"

"Bakomai Zarah, Allah ya kara sauki"

Daga haka ko minti ɗaya be kara baya bar wajen.

Gidan gaba ta shiga sannan Zayd ya tada motar suka bar wajen.

Maimakon taga ya dauki hanyar gidanta sai ya dauki hanyar zuwa gidansu..

*Hmm Zayd sannu da kokari😒*

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!

Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 5" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1170077868?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=3R%2FLSi5vzgol6do%2B6oYxpiyTKptpWkP75lsBTMcmvRmXkZmbklBlk2PLM%2F5k%2FEclnLMVHKOu%2B87X8T%2B%2F7F%2FFKuQMLMOJ0HmZecuCWx%2BstZICbCVSKE%2FGMNIYkAfeSNhE

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Shafi na biyar*

"Zayd ina zamuje? Ta fada tana kalllonsa cike da mamaki.

Ko kulata beyi ba ya kara speed. "Ka tsayar da motar nan Zayd, ina kake tunanin kai ni?

Nan ma banza yayi ma ta yana tukinsa. "Idan baka tsaya ba zan fita duk da kaa gudu"

Sai a lokacin ya rage gudun ya ɗan kalleta ya ce " Zarah gida zan kaiki"

"Na ce maka ina bukata ne? Dan Allah ka mayar dani gidan mijina yafi min"

"Miji? Har wannan ya kai matsayin ki kirashi da mijinki Zarah?

Kau da kai tayi daga kalllonsa ta ce " Eh, ko ba komai shine uban ƴata kuma bazan taba canza hakan ba"

"Good yayi kyau, amma duk abinda zaki faɗa ki fada amma gida zaki dawo"

"Wai Zayd meyasa baka fahimta ne Dan Allah ka kaini gida idan bazakaje ba ka saukeni"
Birki yaja ganin yadda take magana a zafafe.

Kallonsa tayi da sauri dan ta ji tsoron birkin daya taka. Horn aka farayi masa ba kakkautawa, gefen titi ya gangara yana dai² ta parking ɗinsa yayi yana faɗin "Fita"

Da mamaki ta ce " In fita kuma?

Banza yayi ma ta dan baya so ya yi ma ta magana cikin tsawa.

Shuru motar tayi dan UMMIE tuni tayi bacci.

Fitowa yayi daga motar ganin bata da niyyar fita zagayo ya bude bangaren da take ciki ya ce " Fito"

Kalllonsa ta tsayayi cike da mamaki dan batayi tunanin dagaske yake ba amma yanayin fuskarsa ya tabbatar ma ta dagaske yake.

A sanyaye ta fito daga motar tana rike da UMMIE.

Rufe murfin motarsa yayi ya zagaya ya shiga ya bata wuta ya bar wajen.

A baya ta goya UMMIE tana kallon titi, ita bata da ko sisi gashi yayi nisa da ita ballantana ta ce zata tafi a kafa.

Ta dade a tsaye a bakin titin kafin ta fara tafiya UMMIE goya a bayanta.

Sam Zayd be yi ma ta adalci bada zai sauketa a titi a daren nan.

Kusan minti talatin ta dauka tana tafiya amma ko rabin hanyar gida batayi ba.

Tasan yau kashinta ya bushe a wajen Shehu. Tana cikin wannan tunanin taji horn a bayanta.

Da sauri ta juya tana kallon motar. Zayd ne, bata san lokacin da ta saki murmushi ba.

Fitowa yayi ya kalleta ya ce " Am so sorry Zarah, gaba daya na kasa controlling kaina, shigo na kaiku gida"

Murmushi tayi sosai hakan ba karamin dad'i yayi masa ba. Ƙarasowa yayi inda take tsaye ya karbi UMMIE ya saɓa a kafadarsa ya ce " Kiyi hakuri"

"Bakomai Zayd muje"

Ta fada tana yin gaba. Bayanta yabi da kallo cike da tausayinta yasan da beyi nauyin baki da zurfin ciki ba da yanzu ita ɗin mallakinsa ce, da yanzu yana nan yana cikata da roman soyayya yana kuma bata farincikin da tayi deserving, amma ƙaddara ta riga fata.

"Zayd! Yaji ta kira sunansa. Da sauri ya taho yana kara faɗin kalmar sorry.

Motar ya shiga sannan itama ta shiga ta karbi UMMIE.

Har suka iso gidanta babu wanda yake ƙala a cikinsu.

A bakin gate ɗin gidan yayi parking, tana kokarin fito da UMMIE taga Shehu ya fito daga gidan. Da sauri ta kalli Zayd ta ce " Sai da safe"

Sam bega Shehu ba hakan yasa yaja motarsa ya bar wajen.

Wani banzan kallo Shehu yake watsawa Zarah kafin ya koma cikin gida. Bayansa ta bi riƙe da hannun UMMIE wadda ta farka daga bacci.

A falo ta tarar dashi yana jeka ka dawo. Tana shigowa ya tsaya yana kallonta, ransa a matuƙar ɓace ya ce " Uban waye ya saukeku a mota?

"Uncle Zayd" UMMIE ta faɗa tana kalllonsa.

Kamo UMMIE yayi ya riƙe ma ta haɓarta ya matse sosai ya ce "Ni zakiyi wa karya?

"Ka saketa dan Allah"
Zarah ta faɗa tana kokarin kwace UMMIE dake hawaye.

Sakin UMMIE yayi ya riƙo Zarah ya ce " Wato yawon iskancin da kika saba kika je ko? Kin samu sake shine kika bi wani kato yaje ya kwanta dake ya biyaki kudi ko?

Cikin bacin rai ta tureshi tana fadin " Idan zargina kake ka sakeni Dan Allah! A musulunci ma auren mu be halasta ba tunda kana zargina"

Riƙo hannunta yayi ya matse yana fadin " Bazan sakeki ba"

Shuru tayi tana jin zafi sosai.
"Fada min waye wanda ya saukeku?

Kasa magana Zarah tayi saboda zafin da ke ziyarta har brain dinta.

"Bazaki fada ba kenan?

UMMIE kuwa riƙe kafar Shehu tayi tana roƙansa ya sakar ma ta Ummanta amma daga karshe na kafar yasa yayi ball da ita ta fadi ƙasa tana tsadantara kuka.

Belt din dake jikin wandosa ya ciro yana rike Zarah sosai ya fara dukanta kamar wanda aka aiko.

Sosai ya zane ta tas jikinta duk yayi ja dan har abayar jikinta ya cire daga ita sai skirt da vest gaba ɗaya ya yi ma ta rudu² da jiki.

Cike da rashin tausayi ya ce " Ki sameni a ɗaki"

Kasa magana tayi dan hukunta duk yayi ma ta nauyi ga gefen fuskarta duk ya kumbura. Da kyar ta iya isa inda UMMIE ke zaune tana taɓa goshinta inda ya kumburo saboda bigewar da tayi.

Rungumeta tayi sosai tana fashewa da kukan daya ki zuwa tun dazu.

Bata son wani dukan, da kyar ta tashi ta kai UMMIE daki ta bata paracetamol sannan ta sakata tayi bacci ita kuma ta nufi wajen Shehu tana me jera masa Allah ya isa.

★★★★★★★

*Two days later*

"Maaama, duk _wannan abincin na mutun daya ne? Yaron ma da ba wani cin abinci yake ba? Kin hanani fita office, kin hana Ra'uf zuwa_ makaranta, duk saboda dawowar Farooq, uhmmmm it seems like shine na gaban goshinki kuma kin fi sonshi and ina kishi"

"Auta ne fa! Yaron da nayi kusan shekara biyu ban gani ba dole kuwa bayi dokin ganinsa, kuma kai dashi baku da wani banbanci a wajena, kayi sauri ka shirya kaje daukoshi dan kasan baya son jira"

Murmushi Yusuf yayi yana faɗin " Yes ma'am"

Dariya tayi har ya bayyanar da hakori gwal din dake manne a hakorinta yayi das.

Tashi tsaye yayi yana gyara hular kansa ya ce " Ya maganar da kukayi Aunty ƙarama?

"Komai zai tafi dai-dai insha Allah, nasan bazai ƙi zabi na ba"

Gyaɗa kai yayi yana ficewa ita kuma ta rakashi da addu'a.


******

"Zarah! Wai ba magana nake miki ba? A gidan uwarki kika samo wannan cikin har na tsawon wata uku?

Hawaye na zuba a idanunta ta ce " Wallahi cikin ka ... Bata karasa ba sakamakon mari daya dauke ta dashi me rikita ganin mutun.

"Karya kike wallahi! Ni nasan wannan ba ciki na bane saboda ina da matakin da nake bi saboda kar ma ki sake haifar min da a gidan nan kuma kinji na rantse Wallahi wannan cikin sai kin zubar dashi ni ba bawanki bane"

Babu ko sallama ta faɗo cikin falon tana kallonsu.

Da sauri Zarah ta fara goge hawayenta tana kallon Sa'adah ta ce " Shigo"

Wani kallo Sa'adah tayi ma ta kafin ta dauke kai ta kalli Shehu tana sakin wani shegen Murmushi ta ce " Ashe kana gida"

"Eh wani abu ne?
"A'a dama a kan event din da zamu kama ne 600k ne kuɗin"

Tsaki yayi kadan ya ce " Shikenan zan miki transfer"

Daga haka ya wuce ya bar wajen.
Da sauri Zarah ta kalli Sa'adah ta ce " Event din menene?

"Karassss Sa'adah tayi da chewgum kafin ta ce " Aurena da mijinki"

Ko minti ɗaya bata kara ba ta bar falon.
"Aure? Zarah ta faɗa cike da mamaki.

'Yanzu kenan amanarta Sa'adah za ta ci?

Shuru tayi tana tunano lokacin da take amarya a gidan Shehu.

*******

"Gaskiya ƙawata kin mo re, sai ka ce a novel wannan gida haka! Ga miji san kowace mace ƙin wadda ta rasa? Wai ni kuwa ya ake ciki ne wata biyu har yanzu ba labari ko dai ba'ayi abun bane?

Wani kallo Zarah tayi wa Sa'adah kafin ta ce " Jefa ƴar iska ce!

"Ahtoh zancen gaskiya ne ai, wai yaushe yake dawowa ne?

Sa'adah ta kuma tambaya tana kallon agogo.

"Six" Zarah ta ba ta amsa. Ganin just 2pm ya saka Sa'adah yi mata sallama ta tafi.

Washe gari by 6pm sai ga Sa'adah, lokacin dawowar Shehu kenan ana ta rungume² irin dai na dokin amarci wanda ba kowanne ne ya cika zarce wa ba.

"Oh, kuyi hakuri" Sa'adah ta fada tana komawa, duk da kiran da Zarah ta dinga yi ma ta bata dawo ba sam ta tafi.

Daga baya ma Sa'adah zata zo tun rana bata tafiya sai isha'i kuma shi ne yake kaita gida, a da chan babu abinda Sa'adah bata sani ba a kanta daga baya Zainab tayi ma ta magana ta daina fada ma ta komai, ashe abinda Zainab ta faɗa ma ta zai kasane, duk yadda suke da Sa'adatu? Tun yarinta sun taso tare makotan juna kuma kawayen juna shine zata saka ma ta da auran mijinta?

Hawayen da suka zubo ma ta ta share tana a fili ta ce " Menene ma amfanin kukan? Su suka sani"

*Hmm wallahi hattara dai amare masu giggiwa! Ko wani sirri ki dauka ki fadawa kawarki ke bari kiji baki da kawar da ta wuce mahaifiyarki karki yarda da fadawa kawarki matsalarki idan baki da uwa ki riƙe sirrinki daga ke sai Allah daya halliceki, wata ma kawar washegarin da aka kaiki zata wani dinburo miki waya ta ce " Shegiyas ya kike ya anyi abun? Wani abun dan uban ki? Nace wani abun? Saboda baki da kai notikan kanki sun kwance sai ki ce " Eh anyi mudai mun wuce wajen saura ku, wannan wani irin abune dan Allah? Duk wannan kananun abubuwan da kuke gani duk yana cikin sirrin aure! Meyasa baxaki iya boyewa ba? And maganar zuwan kawa gidanki yau tazo gobe yazo jibi ma haka har ta samu courage din tambayar karfe nawa mijinki yake dawowa? Wlhy wannan ba sabon abu bane! Abune da yawanci yake faruwa akwai wadda ma saboda rashin kamun kai Ni da kunne na naji lokacin ina school ita amarya ce satinta uku ta dawo makaranta munje wajen alwala naji tana fadawa kawayenta wai abun mijinta tafi tsahon hannunta daga gwiwar hannu zuwa yatsu! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Wannan wace iriyar rayuwa ce da zakizo cikin kawayenki kina tona ashirin mijinki? Nasan za'a samu masu tsinin bakin da zasu ce bani da aure nake wannan maganar! Amma gaskiya ce dole na fada wallahi, a karshe dai zan bada shawara a kiyaye fadawa kawa sirrin aure! Wallahi a kiyaya musanman masu sabon aure, da kuma ki bari Budurwar makota ta dinga shigo miki gida ko da yaushe har ku saba tasan sirrinki wallahi makashin na tare da kai gwanda ya zamana baki santa ba mijinki ya aureta akan tasan sirrinki mijinki ya aurota me kenan? Hmm Allah yasa mu dace amma akwai kuraren da amare sukeyi sosai, wallahi wata ba iya auren mijinki zatayi ba har da mallakeshi idan kinci Sa'a ki tsira da auran idan kuwa akasin hakan ta faru sai dai ki zama labari. Ni kham na fadi iya wanda na sani Allah yasa mu gyara duk da kowa da tashi ƙaddara*


Autar mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨

_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_

*FREE BOOK*

*MALLAKAR*
*Autar Mama*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)

*Follow me on Wattpad @Autarmama56*

I just published "Chapter 7" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1171688369?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=oKbkoJ9AirGafTVTOyqtFOArGAs9lq7moWkO%2FmyMsCC21QB0R3PMRu3OqG%2BUjGHFKl5iQMkfRnuffo4jA7yF7rAFOdmqnohLK69uZScNlbPYjj19mxWwmjGKHRI6k6aP

*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*

*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*

*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*

https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg

✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽‍♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽‍♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽‍♀️

#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500

Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!


*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only*

*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*

*Shafi na bakwai*

A tare su ka kalli bakin ƙofar falon. Shine a tsaye cikin suit hannunsa riƙe da briefcase top din suit din riƙe a dayan hannun nasa tare da makullin mota.

Da sauri Zarah ta miƙe tsaye tana kalllonsa. Ƙarasa shigowa yayi yana kallon kayan dake hannunsu kafin ya maida dubansa ga Zarah ya ce "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login