Showing 42001 words to 45000 words out of 100116 words
hau ban damu ko nawa zasu ce tunda urgent flight ne"
"OK sir" Zayd ya fad'a yana fitowa, shima fitowa sukayi sannan suka bar kanfanin.
Kasancewar sa sannane the owner of Two brothers yasa basu wani sha wahala ba akayi ready din komai. Within one hour suka bar Kano.
Bayan sun sauka ya rasa ina zai dosa, gaba daya hankalinsa baya jikinsa.
Zaunar dashi Zayd yayi yana ciro wayarsa dan su duba inda location na coffee shop din yake.
Wani kiran ne ya sake shigowa wayar Yusuf, again unknown number ce. D'auka yayi yana karawa akunne ba tare da yayi magana ba.
"Zama samu gawar d'an uwanka a Coffee shop din da muka d'aukeshi"
Wani dum zuciyar Yusuf ta buga da sauri yabtashi ya ce " Ku fad'a min nawa kuke so Dan Allah karku kasheshi"
Dariya yaji an fashe da ita kafin kuma yaji ance " D'an uwanka taurin kai ne dashi mun ja masa kunne ya k'i ji! Bama buk'atar kudi ransa kawai muke bukata"
Sai kuma yaji shuru, kusan second biyar kafin yaji sound na muryar Farooq yana sonyi magana. "Zaku iya zuwa yanzu saboda ya samu wanka da sallar gawa kafin ruwa ya tafi dashi"
Kafin Yusuf ya ce wani abu yaji karar harbi. Wayar hannunsa ce ta fadi yayi suman tsaye idanuwansa suka firfito zuciyarsa tayi wani irin bugawa.
Rik'eshi Zayd yayi yana zaunar dashi sannan ya d'auko wayar da ta fad'i.
Kusan minti biyu sannan hankalinsa ya dawo jikinsa da sauri ya tashi jikinsa na rawa ya ce " Coffee shop Zayd muje"
Kafin Zayd ya ce wani abu wayar Yusuf ta fara ruri. Da sauri ya dauka.
Muryar Farooq yaji yana fadin " Brother karkazo, kar kazo is a trap please kat Mama ta rasa Two sons din... Be karashe maganar ba Yusuf yaji kamar an bugawa Farooq abu. Runtsa idanunsa yayi ya bude su zuciyarsa na tafasa.
"Karfe 1 na dare"
Daga haka yaji an jatse wayar. Kallon Zayd yayi ya ce " Sunce 1 na dare kafin nan zamu iya saka police cikin lamarin saboda a kamasu"
"Hakane, muje police station by now ma nasan suna investigation a kan case din"
Cewar Zayd yana kallonsa.
Police station beyi musu wahalar nemowa ba, already case din yana hannunsu kuma sun kara samun wani clue a kan lamarin bayan zuwansu Zayd.
SS a ka kira saboda badda kama tun karfe biyu na rana aka tura jami'ai guda biyar wadannan suka badda kama, wani yana siyar da abu wani yana zaune kamar pagal wani kuma yana gefen titi da kayan sana'ar gyaran takalmi wani kuma yana siyar da rake.
Ko wanne yana da distance da d'an uwansa kuma ko wanne yana gabatar da aikinsa yadda ya kamata.
Gaba d'aya Yusuf ya rasa nutsuwa.
Sun a zaune a police station kiran Mama ya shigo wayarsa.
Katsewa yayi ya kirata, cikin muryar kuka ta ce " Farooq!
Runtsa idanunsa yayi yasan by now tasan komai maybe Ramlah ce zata fada ma ta dan babu inda bata kurdawa a Internet zata iya ganin news din, Mama ba news take kalla ba, Mama... Sai kuma yayi shuru ya kasa cigaba da magana.
Zayd ne ya karbi wayar yana fadin " Insha Allah Farooq zai dawo gida cikin koshin lafiya Hajiya ki kwantar da hankalinki"
In charge a man case dinne ya karbi wayar yana fad'in " Mahaifiyarsa ce?
Kai kawai Zayd ya daga alamar eh.
Kafin d'an sandan yayi magana Mama ta katse wayat sakamakon faduwa da tayi a hannunta.
*KANO*
Bayan sallar la'asar Zarah ta maida Ummie gida bata shiga ba a kofar gidan ta tsaya sai data ga shigar Ummie sannan tasa me napep ya dawo da ita gida tana jin duk ba dadi jikinta.
Bayan ta isa gida ta danna kiran number Zayd.
Bugu d'aya ya dauka, "Ya ake ciki?
"Sai zuwa anjima, gobe insha Allah zamu dawo"
"Shikenan Allah ya kubutar dashi"
"Amin" ya amsa yana sauke ajiye zuciya.
Sallama sukayi . ta ajiye wayar tana lumshe idanunta.
Mama kuwa Asibiti suka nufa da ita banda juka babu abinda Ummie da Sabir sukeyi, tun Ramlah na tausayinsu har ta fara yi musu masifa.
Tashin hankali ne ya sakacta faduwa har ta suma, dakin hutu aka kaita ta huta kafin ta farka a sallamesu.
★
Kamar yadda suka fada 1am dai-dai suka cillo Farooq jamar tsumma ta cikin mota aikuwa ya gangaro ya dawo gefen titi kafin su rufe kofa aka sakar musu wuta amma ina babu wanda ya raunata a cikinsu sakamakon sun rufe motar da wuri kuma bullet proof ce.
Wani irin dukan kasa ACP yayi yana jin wani takaici, jiniyar yan sanda aka saka yana juyawa yaga jamiam fararen jaya sun saka motar a tsakiya sun firfito hannunsu d'auke sa bindigu.
Yusuf da Zayd me sika fito cikin d'aya daga cikin motocin da gudu suja nufi inda suka ga an saka gawar Farooq jini duk jikin farar t shirt din dake jikinsa ko kotsi bayayi.
"Go down! Go down! A in da Acp din ya fada da karfi kasantuwar daya daga cikin 'yan ta'adar ya fito da wata mahaujaciyar bindiga wadda ko ma'aikatan tsaro basu da irinta.
Harbi ya saki fatatata ta ko ina.
Sam beji zafin shigar bullent din ba sai abu me d'umi daya ji yana shiga jikinsa har cikin pant din dake jikinsa. A hankali ya sunkuyo yana kallon gefen cikinsa.
"Zayd! Yusuf ya kira sunansa da karfi ganin halin da yake ciki....
Musayar wuta aka dinga yi tsakanin police da yan ta'addar amma ina bindigun yan ta'addan yafi na yan sandan, tuni suka wuce mutun daya ne kawai ya raunata. Police wajen uku aka harba.
Cikin tashin hankali Yusuf ya tallafo Zayd ganin yana shirin fad'uwa, idanunsa sunyi ja.
Wani irin azaba ne ya ziyarci kwanyar Zayd lokaci daya .
Motar asibiti ce ta zo aka saka Farroq, Zayd sa kuma sauran mutun uku da suka samu harbi"
A motor ACP Yusuf ya bisu yana ji kamar ya fashe da kuka.....
*Sorry for the typing errors*
Autar Mama ce.
✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma ƙalubalan rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
*Autar Mama*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow me on Wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 16" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1181220702?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=PLkLDk%2B4yH5fThRZchqXmVWogU%2BhnmNeYT5kf0941uz7byIYbcT1yMYZ6T%2FT%2FLHBcGtPGWjEAJECDsEN5%2F1delU41KIk5u6716t3MrHfXdwik3o6xd%2FX%2FWzsdDWZTMWE
*Idan zaki fara bi ki fara tun yanzu ba sai nayi nisa a dinga cewa daga page one ba, dan na wahala turawa lokacin da nake rubuta Ƙawaye*
*Comment da voting shi zai sa a dinga samun update da wuri*
*Whatsapp group pls banda maza, and idan kina group one kar ki shiga wannan duk abu daya ne*
https://chat.whatsapp.com/I1e40OT9rRwBgFU3xD0aYg
*Aslm inayiwa masoyana fatan alkairi, inamasu bibiyan littafin Momin haneef,tazomuku dasabon littafinta maisuna RA YUWAR SAFEENAT Labari maijike dad'umbun darasi yaudara cin'amana da kuma soyayya zai ilimantar daku kubiyoni acikin Labarin shi wannan littafin dakud'ine kiyi kokari kimallakeshi karkibari astaya baki labari bayida stada akan kud'i kalilan zakusamu 200 naira only kiyi magana tawannan number 07026368879*
*Ina kuma sanar daku zagwaguri zazzafan littafin mu maisuna kamar su d'aya kuyi kokari kunema akan kud'i kalilan 300 naira only👌*
*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.
*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)
𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.
*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*
Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...
*K'ANWATA*
*Dandano!Dandano!!*
Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..
Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573
Nomal. guda d'aya N 300 ne
guda biyu N 500 ne
Special guda d'aya N 500 ne
guda biyu N 1000 ne
Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank
✌🏼Fitattu biyu masu ban mamaki🫀Hakika babban goro sai magogin ƙarfe 😍, Hakk'un wani kaya sai amale ke d'auka🐫, Fitattu biyu👯🏽♀sun shiirya tsaf domin nishad'antar daku 🤓 sun shirya tsaf domin fadakar daku🧠 sun shirya tsaf domin dilmiya zuciyoyin ku cikin bege da shauk'in so💋💞, wohoho tabbas ️sahun giwa👣 mai ɓadda na raƙumi 🐪,Fitattu biyu😍✌🏼 masu tafiyar k'asaita, sheƙi, da walwali hak'ik'a koda kud'in ka saida rabon ka😘🏃🏽♀️ Fitattun Ƙarshen shekara😍 salon su daban ne dana sauran domin natsuwa da tunani sunyi aiki pure love and romance abun dai sai wanda yakaranta😍 maza ku hanzarta neman naku karku bari abaku labari🏃🏽♀️
#Oum Sumayya:- *GAMIN GAMBIZA*✍🏽 Nrml 300 Vip 500
#Oum Ikram:- *SOYAYYA CE SILAH* ✍🏽 Nrml 300 Vip 500
Duka biyu 400👌🏼
Vip 700👌🏼
Via 4210014214
Eco bank and send the evidence of payment via 08139624956
Or mtn/airtel credit via 07017296839 banda vtu hoton kati kawai!
*Shafi na Sha shida*
Bayan sallar magariba Zayd ya shigo gidan. Be tarar da kowa a falo ba, ya kusa shiga dakinsa Zarah ta fito hannunta rike da plate tana cin goat meat wanda tayi wa hadadden hadi.
Kallon plate din yayi kafin ya kalleta ya ce " Wannan fa? Sai a lokacin ta san dashi, murmushi tayi kadan ta ce " Dazu naje kasuwar layi na siyo ko zaka ci?
"Eh bari nayi wanka sai ki zubo min" Ya fada yana kokarin shiga dakinsa.
"Uhm toh babu! Iya cikina na siyo dan Aunty ta ce bazata ci ba kuma kaima ba iya ci zakayi ba dan da yaji"
"Zan iya ci indai kika bani! Ya fada cikin sanyin murya dan ransa ya biya sosai.
Bata ce dashi komai ba ta nufi kujera ta zauna tana cin abinta hankali kwance.
Dawowa yayi kusa da ita kamar zece da ita wani abu bata ankara ba taji ya wafce plate din yayi dakinsa da dan sauri.
"Zayd!" Ta kira sunansa da karfi. Amma yana shiga daki ya kulle kofar. Cikin takaici ta nufi dakin Aunty. Aunty na Athkar taga Zarah fuska babu fara'a.
Sai da ta karasa sannan ta kalleta ta ce " Menene?
"Zayd ne fa! Ki ce masa ya bani Nama na kinsan banyi abincin dare da ni ba kuma ya karbe min nama ya shiga daki"
"Bana son shashanci kuma! Shine zakiyi min kuka da godai² dake? Aunty ta fada ganin yadda Zarah ta yi da fuska.
Shush Zarah tati dan idan tayi magana tana iya ganin kuka zatayi ita kadai tasan irin son da take yi wa goat meat.
Ta shi Aunty tati ta fice daga dakin, bayanta Zarah ta bi.
Kofar dakin Zayd suka nufa, bugawa Aunty tayi tana fadin " Fito ka bata namanka! Kuna abu kamar kananan yara"
Shuru bai amsa ba, kallon Zarah tayi ta ce " Ba mamaki ya shiga wanka jira zai bude ya baki abunki"
Daga haka Aunty ta bar waken cike da takaicinsu.
Be dad'e ba ya bude kofar yana fadin " Shigo"
Bata ce dashi komai ba ta shiga dakin. A kan centre table taga namanta ko tabawa beyi ba. Kallonsa tayi sannan ta kalli naman ta ce " Bari na zuba maka"
"A'a barshi nayi zuciya, amma gama ci zamuyi magana"
Data kafada tayi alamar bata damu ba ta dauki namanta ta fito daga dakin.
Sai kusan 10 sannan ya fito daga daki tana ta danna wayarta. Zama yayi a kujerar da ke kusa da ita ya ce " Zaki aureni?
A wanna bazata taji maganar tashi. Tashi tayi daga kishingid'an da ta ke ta na kallonsa.
Gamin fuskarsa baby alamar wasa ya saka ta hadiyi wani yawu kafin ta ce " Ni karatu nake so"
Numfashi ya ja da karfi kafin ya sauke a hankali ya ce " Ai aure baya hana karatu ko?
"Nasani amma nasan bazaka barni ba idan ka aureni"
Marairaice fuska yayi yana kallonta ya ce " Zarah kina so na mutu banyi aure bane? Bakya so Aunty taga jikokinta? Please Zarah ki amince bansani ba ko rayuwata tana gaf da karewa ban sani ba ko ina da tsahon kwanan da zan iya jiranki har ki kammala karatunki"
Jikinta ne yayi sanyi, a hankali ta sauke idanunta tana kallon yatsunta.
"Zarah! Ya kira sunanta. Bata daga ba sai amsawa Kawai da tayi. "Kinfi kowa sanin yadda yanayi na yake ina da kishin da bazan iya barki kina fita kullum zuwa makaranta ba"
Ta shi tayi tsaye tana kallonsa ta ce " Shikenan ka nemi wata matar" Daga haka ta wuce ta barshi a wajen da kallon bayanta.
Ya dade zaune a falo yana tunani, tasan bazai iya hakura da ita ba shiyasa ta ce masa haka, amma idan tazan wata ai bata san wata ba"
Sai kusn 12 sannan ya kwanta.
Washe_gari, basu ma hadu da dan da sassafe ya shirya ya fice kasantuwar ankawo musu wata kwangila na gina wani asibiti a chan Abuja gashi ko kammala construction din ba'ayi ba.
Daf da sallar La'asar ya kirata ya shaida ma ta da ya yadda data cigaba da karatun amma ta bari bayan aure ayi duk abinda za'ayi na makarantar ta aminta kuma taji dadi.
Bata ya dawo da daddare ya shaida wa Aunty yadda sukayi kuma zaije kauye dan yi wa yan uwansu magana.
Ko mai na tafiya dai² dan har anyi maganar aure ansa 4weeks. A chan kauyen za'ayi komai, biki saura kwana biyu sannan zasu koma idan an dauro aure sai su dawo"
Zainab taji dadin faruwar wannan lamarin kuma da ita za'a tafi kauyen baysn daurin aure sai su dawo ta re.
Har anci sati daya cikin kwanakin da aka saka na bikin.
Kudi Zayd ya turawa Zainan ya ce ta hado abinda baifi samunsa ba amma kaya masu kyau dan tafishi sanin zabin Zarah din.
Gidansa ya fara ginawa yasa himma kasancewar s kamfanin da yake aiki ake yi masa ginin cikin kankanin lokaci aka gama, duk da cewa ba wani kato bane gidan amma ba karya ya hadu dan kamfanin Two brothers sun kware a harjar zanen gida, makaranta d.s har ma da ginawa"
Ba'a wani charjeshi fees ba dan Yusuf yayi masa discount sosai cikin 100% na kudin daya kamata ya biya 30% kawai ya biya. Har furniture komai Two brothers ta saka masa. Sosai kuma yayi wa Yusuf godiya dan yasan yayi masa sosai.
In 3weeks gidan ya kammala komai ya zuba a cikin gidan.
Tum bikini saura sati biyu Zarah take avoiding dinsa kuma sharadin me gyaran jiki ne.
Sosai Zarah tayi kyau ta hadu kamar ba ita ba farar fatarta ta fito sosai gashi ta hadu da gyara abun sai wanda ya gani lol...
Tana cikin cin naman da me gyaran jiki ta bata ya fado falon kamar an jefoshi. Kallo daya yayi ma ta ya dauke kansa dan ya nuna ma ta fushi yake da ita.
Ko a jikinta ts cigaba da cin abinta hankali kwance. Ganin bata ce dashi komai ba ya sashi nufo inda take ya ce " Baki ganni bane?
"Na ganja mana, anjima jirgin Zainab zai iso ta ce tana kiranka baya shiga kaje ka dauko ta"
"Uhm naji" Ya fada yana kare ma ta kallo dan ta sauya ta kara kyau ga wani khanshi me sanyi da yake tashi a jikinta.
Numfashi ya ja da karfi yana saukewa a hankali ya ce "kinyi kyau 'yan ma ta na"
Shush tayi masa. Kusa da ita ya zauna yana fadin" Nima zanci"
Ajiye plate din tayi, tsoka daya ya dauka ya saka a baki ya fara taunawa kafin ya kalleta ya ce " Ya naji d'and'anon so weird"
Banza tayi masa ta cigaba da cin kayanta.
Ta shi yayi yana gyara zaman rigarsa ya ce " Beyi dadi ba"
"OK" Ta fad'a tana dan murmushi.
Karfe 8 saura Zainab ta iso gidan, tare da lefen Zarah akwati biyar, sosai Zarah tayi mamaki dan tayi zaton bazai yi ma ta lefe ba amma gashi har akwati biyar.
Sai da suka gama duba lefen har Aunty sannan aka rufe Zayd ya kai dakin Aunty ya ajiye.
Zarah ce ta kaiwa Zainab kayanta dakinta ta kawo ma ta abinci tana yabon yadda ta zama ta kara kiba da kyau.
Sakon godiya Zarah ta turawa Zayd me dadi kafin ta kashe wayarta dan tasan zai kiranta ita kuma bata shirya yi masa magana ba.
"Wai ni kuwa bazaki dauko Ummie ayi bikin nan tare da ita ba?
Cewar Zainab tana kallonta. "Sai muje gobe" Zarah ta bata amsa.
"Da dai yafi dan duk dinkuna na ba wanda banyi ma ta ba"
"Kice kun shirya fin amarya kyau"
Dariya Zainab tayi tana kwanciya.
Washe_gari Zayd beje aiki ba dan Yusuf ya bashi hutun 3weeks.
K'arfe goma suka shirya ita da Zainab ko wacce tasha hijabi da nikaf da,safa. Zayd na karyawa ya gansu sun fito sakale da jaka a hammata.
"Ina kuma zuwa? Ya fada yana kallonsu. "Gidan Shehu zamu dauko Ummie"
"Oho ku bari anjima zanje na dauko ta"
"Kasan dai yana zuwa aiki kuma wannan banzar matar tashi bazata baka ba ko?
Cewar Zainab tana kallonsa.
"OK jira na gama sai mu tafi"
Zayd ne ya kaisu har kofar gidan Shehu.
Invitation ya bawa Zarah ya ce " Ki bawa Shehu" Karba tayi tana fadin " Toh"
Daga haka suka fita.
A falo suka tarar da Ummie, Sa'adah da kuma Shehu suna cin abinci.
Ummie na ganin su ta gane Ummanta da gudu ta tashi ta nufeta tana rungumeta dage nikaf din Zarah tayi tana tsugunnawa dai² tsohon Ummie ta ce " Ummie! Sai