Showing 93001 words to 96000 words out of 100116 words
anjima! Ki gaida Zarah!
Da toh ta amsa sannan ta shiga cikin gida.
A falo taga Aunty tana cin abinci. Da sauri ta wurgar da jakarta tana karasawa inda take ta zauna.
Zarah data fito daga dakin dake kasa ta kalleta ta ce "Yanzu bakonki yazo bakya nan!
"Mun hadu a waje har Leda mamansa ta aiko min dashi kin ganta kusa da jakata" Cewar Ummie tana nuna jakar.
" Ashe dai Farooq mijin Ummie me shiyasa be aureki ba! Cewar Aunty tana kallon Zarah.
Basar da maganar Zarah tayi tana kallon Aunty ta ce " Kafin ki tafi dai zaki sha ciwan kai na surutun UMMIE"
"Eh fa! Ai ke ta gado!
Dariya Ummie tayi tana tashi ta nufi daki, Zaki yayi bacci shi kuma Khaleel yana islamiyya.
8pm
Ummie da Aunty ne kawai a daki, Aunty na kallo Ummie kuma nayin karatu.
Kusan minti 20 suna a haka kafin Ummie ta kalli Aunty ta ce " Aunty in tambayeki?
"Inajinki" cewar Aunty ba tare da ta kalleta ba.
" Dazu naji kince Allah yayi Farooq miji nane shiyasa be auri Ummana ba?
Sai a lokacin Aunty ta kalleta ta ce " Eh fa! Yaso auren Zarah ai tun lokacin kafin ta auri mahaifinki! Lokacin tana aiki a karkashin yayansa a matsayin sakatariya, sai Kuma Zayd shi kuma ya sota tun kafin ta hadu ba babanki Amma Allah yayi babanki zata fara aura sai Kuma daga baya ta auri Zayd gashinan har yanzu suna tare"
Shuru Ummie tayi na kusan minti daya kafin ta kalli Aunty ta Kuma fad'in " Be taba aure ba ko?
"Ya taba! Amma ranar daurin auren ya gudu ya bar matar daga nan Kuma ya hadu da tsautsayi akayi kidnapping dinsa aka harbeshi a kirji da kyar ya tashi kusan shekara yayi a coma, be Dade da tashi ba ya saki matar Kuma yanzu yayansa ne yake aurenta har sun haihu da yarsu Nawal"
Jinjina kai Ummie tayi tana tunano maganar Taj! Ko dai akan Ummanta Hakan ya faru da Farooq? Toh fansa yazo dauka kenan? Fansa kuma? Ai ba laifi Ummanta tayi masa ba?
Da ire² wannan tunanin bacci ya dauketa.
Washe_gari
Tun daren jiya Zarah ta hana Zayd baccin kirki dan bata so yarta tayi aure inda zata sha wahala! Tana ganin kamar idan Mama tasan Ummie Farooq zai aura zata tsaneta ne saboda tun farko Maman ta nuna bata son ta toh meyasa yanzu zata so yarinyarta.
Tsaf ya gama shirinsa yana fesa turare ta shigo dakin tana fad'in " Tun jiya nake magana mmma kaki cewa komai?
Murmushi yayi kadan Yana kallonta ya ce " Yau duk fad'an ne ya saka ko wankan safe ba'ayi ba?
Hade rai ta kuma yi tana kallonsa ta ce " ni fa tsoro nake ji!
Hannayenta ya kamo yana shafawa a hankali ya ce "Khairan insha Allah! Ki daina damuwa insha Allah zakiyi alfahari da auren nan! Indai Ummie tana sonsa! Kedai kawai kiyi addua"
Numfashi ta sauke kadan tana zare hannunta daga nashi sannan ta fita daga dakin.
Ummie na kurbar ruwan tea Zarah ta fito.
"Ummana yau 11am zamu gama, zanje gidan Rahama kafin la'asar zan dawo tun da akayi biki ba....
Zarah bata bari ta karasa ba ta ce " Ba sai kinyi dogon sharhi ba, kije amma idan kika zauna kinsan sauran!
Cike da murna Ummie ta amsa da toh.
12 Saura ta baro mkrntr. Yau Taj ko zuwa beyi ba.
Gidansu Taj ta fara zuwa, Aunty ta gani a falo hannunta rike da tray Wanda aka jera abinci a kai.
Murmushi tayi tana karasawa ta ce "Ina kwana?
"Lafiya Lau UMMIE! An biyo sahu anji shuru ko?
"Eh wallahi kuma wayar sa bata shiga!
"Baya jin dadi! Bari nake na kai masa abinci"
Karbar tray din hannunta Ummie tayi tana fad'in " muje"
"Toh yi gaba bari na kawo ruwa da magungunan da aka siyo dazu"
Da toh Ummie ta amsa tana nufar dakinsa.
A zaune ta ganshi ya jingina da jikin gado idanunsa a lumshe. Ajiye tray din tayi a kasa tana fad'in " Wai meyasameka?
Bude idanunsa yayi da sauri yana kallonta, itama kallonsa takeyi.
Aunty ce ta shigo ta ajiye magungunan da ruwa tana kallonsa ta ce " Ga abinci nan kaci kasha magani!
Da toh ya amsa, kallonsa Ummie tayi ta ce " Allah y baka lafiya! Ni zanje gidan Rahama ne"
Kai kawai ya gyada ma ta sannan ta fita.
Tafiyace me tsayi tsakani...
Bata dade tana buga kofa ba aka bude. Mijin Rahama ne? Gaidashi tayi tana fad'in "Rahama fa?
"Tana ciki! Ya bata amsa yana nuna hanyar shiga cikin gidan.
Cikin gidan ta nufa tana Yan kalle². A kwance taga Rahama tana kallo falon sai khamshi yake.
Sallama tayi, da sauri Rahama ta tashi zaune jin muryar Ummie.
Dariya tayi tana amsa sallamar ta ce " Shine ko sanarwa babu?
"Uhm! Kedai barni! Me kika dafa? Yunwa nake ji!
Cewar UMMIE tana zama kan kujera.
"Sannu gara! Ni har yanzu ban fara girki ba! Amma bari na dumama miki Wanda na saka a fridge dazu ba dadewa"
Da toh Ummie ta amsa tana kara relaxing.
Sai bayan sallah la'asar sannan Ummie ta fito, har bakin gate Rahama ta rakota suna ta hira.
"Wallahi Ummie karkiyi wasa! A yadda nasan Barr. Farooq wallahi mutumin kirki ne!
"Au Barr. Ne? Cewar Ummie cike da mamaki.
"Eh a da ba! Yanzu kham judge ne! Kawai dai mun saba da Sir ko Barrister ne!
"Ohk, shikenan zance masa na amince yace min zaizo anjima da daddare"
"Yawwa gwanda karkiyi wasa da danarki Kuma ki dage da addua sosai"
"Insha Allah, Wai nikuwa Rahama kinsan me?
Kai Rahama ta girgiza alamar A'a.
Sai da Ummie ta sauke numfashi sannan ta ce " Akwai wata yar kawar yar class din mu kin gane? Toh a baya an taba raping dinta tana da kananan shekaru a lokacin, so sai yanzu data girma wanda ya aikata abun ya dawo wai Yana so ya gyara kuskurensa ya aurenta! Me kike gani?
"K***t, tun lokacin ba'a dau mataki akan Dan k***t Uba ba?
Cewar Rahama a kufule.
"Eh! Saboda gudum yaduwar abun! Cox yarinyar babanta na da kudi sosai Abu kadan press suke jira su samu abun yad'awa"
"Eh toh da wannan da wannan! Amma wallahi yanzu dama ce ta samu! Ta yarda da soyaytar shege ta jikashi da madarar kauna ta bar Dan iska a gefe!
"Allah ko? Cewar Ummie tana nazarin abun.
"Eh! Ke! So fa babban cuta ne wallahi!
"Amma kina ganin babu wata matsala a hakan? Kar naje na bada shawara a samu matsala zzo ana dambe dani"
UMMIE ta karashe maganar cikin raha.
"Seriously hakan yayi ai shi ya fara cutarta insha Allah wata mtsalar bazata biyo baya ba"
Godiya Ummie tayi ma ta.
"Ungo nan dubu biyar ce ya ce a baki ki hau mota! Ni dake kar tasan kar ce! Naira 500 sai ta kaiki gida sauran Kuma a lalitarki zaki saka! Allah ne kadai yasan damfarar da kikayi wa Uncle Zayd da Abba lokacin bikina"
Waftar kudin Ummie tayi tana fad'in "Nasan halinki sai ki iya cire 4k ki ban 1k"
Dariya Rahama tayi tana daga ma ta hannu ita kuma ta fita tana murmushi.
9pm
Abinci da ta shiryawa Farooq ta fito dasu daga kitchen tana jerawa a kan katuwar sallayar da ta shinfida kan rug.
"Ummie 'yan mata an iya tarbon saurayi! Naso Aunty bata tafi ba! Cewar Zarah tana dariya.
"Eh so nake ya kara Sona ai! Na san dai na fiki kyau!
Ummie ta karashe maganar tana dariya.
"Wato tasan gaskiya? Zarah ta tambayi kanta.
"Toh ai haka nake so! Nafison kyakkyawata tazo a farko a komai! Allah yayi Miki albarka UMMIE"
Da amin Ummie ta amsa tana sakarwa Ummanta murmushi me kyau....
*Autar Mama ce*
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨
_Labari daya danganci soyayya da kuma k'alubalen rayuwa_
*FREE BOOK*
*MALLAKAR*
Autar Mama
*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
(E.W.F)
*Follow mr on wattpad @Autarmama56*
I just published "Chapter 39" of my story "UMMIE". https://www.wattpad.com/1202237908?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=WkMp%2BCIZUlLq%2FmxQDNyfZvCUoNZDYvrcAI4y1TS3QEbT7ZGpaeaQ9yqDm9JA5zPhMoEk9K1NuquIRHY4nbPkm0tmG%2FtjkJsIHsrLAsogRhELecqKdX%2FDdk7Pwu8FGLii
*Whatsapp number, free to contact me 08142904255*
*BAK'AR SAKAYYA*
*Bak'ar sakayya, labarine a kan tsantsar soyyar gaskiya wadda ta fara tun daga yarinta, ya sota tamkar ransa! Yayi fada da kowa a kanta! Yayi kokarin sadaukar da rayuwarsa saboda soyayyarta! A nata b'angaren itama ta soshi soyayya me zafi hade kuma da yarinta... Shin kunsan me yake faruwa?.... Ko yaya Yidi da Bardo zasu kasance? Ya labarin soyyarsu zai kasance? Me kuke tunani a kansu?... Hmm a wajena kawai zaku samu wannan amsoshin akan nera 300 ga masu turuwa ta banki, masu turo kati kuma 400 ne masu idan kuma Vip group ne zaki biya 500 posting sau biyu a rana*
*Hmm, ga Yazeed fa! Yaro dan gata! Amma kash! Ya kasance dolo! Sanadiyyar hakan ya,rasa me zama dashi! Baya iya yin komai da kansa! Ya tashi ba tare da uwa ba! Yayansa kadai ne sanyin idaniyansa! Hmm Yidi ta shigo rayuwar Yazeed but how? Hmm wanna amsar zaku sameta ne a,wajena kuma duk cikin littafina me taken _BAK'AR SAKAYYA_*
*Soyayya ta wahalar da Bardo! Yasha gubar so! Yasha azabar so! Yasha masifar so! Soyayyar Yidi taso hallaka rayuwarsa!*
*Kukan jaririn da ya cika wajen ne ya tsorata ta! Ajiye tulunta tayi ta karasa gefen rafin gabanta na faduwa..... Hmmm Tsintuwa! Tsintuwar yaro! A gefen rafi... Hmm zaku samu cikakken labari a wajena ni Autar Mama akan farashi me sauki kamar yadda na fada normal group 300ne posting sau daya a rana! Idan kuma katin waya zaki turo zaki bada 400, sai vip group 500 posting sau biyu a rana*
*Shafi na talatin da Tara*
*2 weeks later*
Ummie na kwance a kan babbar kujera tana ta wasa da kalbarta dayan hannun kuma handout ne tana karatu, Zarah ce ta fito daga kitchen tana fad'in " Ta shi ki wanke min nama! Kin karanta handout dinnan ya kai sau biyu saboda bakya son aiki ko?
Kafin Ummie tayi magana suka jiyo sallamar me gadi. Zarah ce ta amsa tana fad'in "Baba shigo"
Shigowa yayi cikin ladabi ya gaida ita ta amsa sannan ya ce " Hajiya dama wanine ya ke neman karamar Madam kuma kwana uku baya ma wani dai haka babba shima yazo yayi tambaya a kanta mancewa nayi ban fad'a, na yanzun dai yaro ne"
"Toh Baba gatanan zuwa"
Cewar Zarah tana kallonsa.
Da sauri Ummie ta ta shi tana fad'in " Yau dai wankin nama ya kamaki!
Ta karashe maganar tana dariya. Girgiza kai Zarah tayi tana murmushi. Ummie bata dad'e ba ta fito sanye da hijabi har kasa, Allah ya bada sa'a Zarah tayi ma ta sannan ta fita.
A zaune ta ganshi a kan wani a chaba kusa da gate kansa a kasa.
Karasawa tayi tana yin sallama. A hankali ya dago kansa, kuri sukayi wa juna, sosai kyawunta ya rudashi! Tabbas idan da be santa ba zai ce balarabiya ce duk da kasancewarta bakar fata.
Ummie kuwa kasa motsi tayi gaba daya! Ko a cikin duhu ta shafa fuskar Saleh sai ta ganeta ballanta da rana tsaka!
Abinda ya faru 6yrs back ne ya dawo ma ta sabo dal a zuciyarta. Kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai take maimaitawa.
Sai da taji nutsuwa tazo ma ta sannan ta juya a hankali ta fara tafiya. Da sauri ya diro daga kan mashin din yana shan gabanta ya ce " Dan Allah Ummie kiyi hakuri! Nazo na gyara abinda na bata! Ummie wallahi nayi nadama! Bayan ke babu wadda na taba aikatawa haka wallahi! Kema so nake na gyara abinda na bata! Tun bayan aikata hakan a gareki na yi bankwana da farinciki! Ummie Dan Allah karki bari na karashe rayuwata cikin dana sani! Na miki alkhawarin farin ciki har karshen rayuwata!
Ko tausayi be bata ba! Tsaki tayi ta wuce cikin gida ta barshi a wajen.
Tana shiga falo ta cire hijabinta ta wurgar tana fad'in " Shege!
"Shege? Zarah ta fada tana kallonta. Tashi tsaye tayi tana cewa " Gidan Aunty zanje"
"Aikuwa baki isa ba! Ha Ilham ga khaleel a chan sai kije ki kara ma ta wani ciwan kan ko?
Turo baki kadan Ummie tayi tana daukar hijabinta ta handout dinta ta tafi daki.
★
Nihal ce zaune a cinyarsa yana tayata aikin makaranta. Ummie ce ta fito daga kitchen rike da tray, tsohon ciki ne ma a jikinta.
A kusa dashi ta ajiye tray din tana fa din " Yaya Farook gashi!
"Yawwa! Sannunki! Ya fad'a yana kallon tray din.
Zama tayi a kujera tana kallonsa ta ce " Yaya har yanzu dai shuru!
Dagowa yayi ya kalleta kafin ya ce " Na me fa?
"Maganar aure mana! Dariya yayi sosai har Nawal na zamewa daga jikinsa.
"Shikenan ai tunda dariya na baka"
Cewar Ummie tana kiran Nawal dan su karasa aikin.
"Soon insha Allah dan ina tunanin kafin Azumi za'ayi auren!
Cike da mamaki Ummie ta kalleshi ta ce " What?! Are you serious?
"Yeah! Ya bata amsa.
"Tabdijan! Cewar Ummie dan abin ya bata mamaki.
"Ba wani abun mamaki bane! Nima ji nayi hakan ya kwanta min! Anjima zanje na samu babanta nasan bazai hanani ba"
"Allah ya tabbatar da alkhairy! Dole mu fara shiri nan da wata biyu fa?
Gyada kai yayi alamar hakane. Yusuf ne ya shigo cikin suit. Sassauta tie din yayi yana ajiye jakarsa ya ce " Ya naga anata washe hakora?
Nawal ce ta zo da gudunta tana yi masa oyoyo.
Daukarta yayi yana dariya sannan ya sauketa.
" Yaya Farooq ne zaiyi aure! Ummie ta fad'a tana kallon Yusuf.
"Aure Farooq? When? Kuma wacece? Yusuf ya fad'a cike da mamakin lamarin.
"Anjima zaka rakani wajen babanta bayan sallar Ishai"
Gyada kai kawai Yusuf yayi dan har yanzu mamakin abun be barshi ba.
A nan gidan Yusuf ya yini sai bayan sallar magariba sannan shi da Yusuf din suka nufi gida wajen Mama.
A falo suka tarar dasu, Mama, Ramlah da kula Sabir.
Upstairs Farooq ya tafi danyin wanka. Yusuf kuma zama yayi kusa da Sabir yana fad'in " Gashinan yayi yawa ayi aski!
"Yanzu na gama magana! Ya ce wai gayu! Cewar Mama tana kallonsu. "Almakashi zansa na yayyanke"
Ramlah ta fada tana murmushi.
"Yau fa dan naki yayo miki sirika! "Sirika? Farooq ko kai?
"Ni kuma? A'a A'a biyu na sun isheni! Farooq dai! Yanzu ma wajen mahaifinta zamuje!
Cikin tsananin farinciki Mama ta ce " Bana son wasa fa!
"Wasa kuma? Dagaske nake fa!
"Ikon Allah! Amma gaskiya lamarin nan yayi min dadi, Allah yasa rabonsa ce! Kuma yasa jinkirin alkhairy ne"
"Amin! Suka amsa gaba daya.
Ya dade kafin ya sakko. Yasha manyan kaya yayi kyau sosai.
Murmushi dauke a kan fuskar Mama ta kalleshi ta ce " Allah ya bada sa'a"
Da Amin ya amsa yana murmushi dan yasan Faisal ya fesa musu.
Sallama sukayi wa Mama sannan suka tafi.
A kofar gidan Zayd yayi parking yana kallon Yusuf daya kashe da mamaki.
"Yes! Ummie nake so! Tun kafin ta zabi wanna Dan naka taga sabon jini gwanda na zo na fara kafa tawa gwamnatin.
Dariya Yusuf ya fashe da ita yana dukan Farooq kadai ya ce " Baka da dama wallahi! Ai baka fad'a min! Allah yasa ban fad'awa Sabir ba da anyin abun kunya!
"Da sai dai ya hakura wallahi! Cewar Farooq yana fitowa daya motor. Shi ma Yusuf fitowa yayi yana gyara rigarsa ya ce " Da anyi Baba kwabo!
Dariya Farooq yayi ba tare da yace ko mai ba ya nufi gate din gidan ya fara knocking.
Bugu biyu aka bude. Zayd ne sanye da jallabiya hannunsa rike da Hydar dake kafada dayan hannun kuma Khaleel ne.
"Wa nake gani haka? Ya fada yana kallonsu.
"Mu ne dai! Wani important abune ya taso kuma we have to be in the office right now! Cewar Yusuf yana kallonsa.
"Toh, bari muyi sallah sai muje"
Dariya Yusuf yayi ya yana daukar Khaleel ya ce " Kafi babanka kyau!
Dariya Khaleel yayi cike da jin dadi. Saukeshi yayi yana kallon Zayd ya ce " Nagodewa Allah daya bani manager kmr kai! Babu wani aiki mun dai zo wajenka be but muje muyi sallar gaba daya!
Masallacin dake dan nesa dasu suka nufa.
Sai kusan 9 suka dawo gida dan Zayd ya biya wajen me suya saboda Ummie.
Shi ya fara shiga falon yana kallon Zarah ya ce " Bakin dare mukayi samo musu abin tabawa! Ke kuma Ummie tafi da yaran nan daki"
Da toh ta amsa tana tashi tsaye ta ce " Naman fa?
"Au! Ya fada yana mika ma ta ledar hannunsa. Murmushi tayi ta karba sannan ta wuce sama tare da yaran.
Iso yayi wa su Yusuf din suka shi go, Zama sukayi a akan rug. Da sauri Zayd ya ce " Ku zauna a kujera mana!
"Nan ma is ok! Farooq ya fad'a yana dan murmushi. Shi ma Zayd murmushi yayi dan ya fara harbo jirgin.
Zarah ce ta fito hannunta rike da tray wanda ke dauke da abin tabawa.
A gabansu ta ajiye tana fa din "Ina yininku?
Yusuf ne kawai ya amsa banda Farooq. Dagowa tayi ta kallesu. Murmushi ta sakar musu sannan ta wuce sama.
Ajiyar zuciya Farooq ya sauke, shekaru 6 kenan rabon daya ganta! Tabbas idan so cuta n hakuri ma magani ne! Kuma yana fatan tarin soyayyar da yayi wa Zarah a baya ta dawo kan yarta!
"Shine abinda ya kawo mu! Kasan bazamu tsaya boye² ba.
Abinda yaji Yusuf ya fada kenan.
"Alhamdulillah! Ta bangarena babu matsala! Sai dai wajen Ummie ko mahaifinta! Amma badamuwa ka fara zuwa dan ku fahimci juna idan yaso daga baya sai kaje ka samu shi Baban nata"
"Shikenan! Bari mu tafi! Yusuf ya fada yana tashi.
"Zan iya ganinta yanzu? Cewar Farooq yana kallon Zayd.
"Badamuwa" Zayd ya amsa yana hawa stairs.
Da sauri Yusuf ya kalleshi ya ce " Me haka?
Banza Farooq yayi masa.
"Idan ka gama ka sameni a mota! Idan kuma da rabon zakayi tafiyar kafa shikenan"
Be jira cewarsa ba ya fita