Showing 1 words to 3000 words out of 77337 words

Chapter 1 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

??ࡱ?>?? ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument?????0Table?????????Data
???????????????????? P?*u KSKS???7???????pp-
-
-
-
? 
?\?-
??????????$ ??
*p-
-
??-
-
-
-
??
?
?
?
??

??-

 [11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama:
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
?Fertymerh Xarah=؞?
1
Phoenix
Wata sassanyar murya marar amo, wadda ke dauke da rashin kuxari ta yi sallama a dakin, ta amsar sallama tana kallon sa, sanye yake cikin shud'iyar shadda gexner wadda tayi matuqar fito da sirrin fuskar sa.
(kallo d'aya na yi masa na gane shi din jinin Aiman mera ne saboda tsananin kama da suke da juna)
SULTAN kenan mai shekara? goma kacal a duniya.
Duk wani fushi, bacin rai da ke cikin xuciyarshi sai yaji yana bacewa sanadiyar hada idanuwa da mahaifiyarshi Afiya.
A hankali ya qarasa shiga dakin tare da yiwa kansa maxauni a d'aya daga cikin kujerun da suka yiwa qayataccen falon qawanya.
'me ya same ka haka? ta tambaya cike da kulawa irin ta d'a da mahaifiyar sa.
Ya turo bakin sa tare da dauke kansa daga kallon ta,
Mami wai meyasa sai nayi kwallo ne, na gayamasa bana son? kwallo bata cikin tsarina a rayuwa, just look at me Mami dan Allah jikina yayi kama da na masu kwallo, meyasa Dad yaqi ya gane hakan?
Taja numfashi kadan tana kallon sa, meyasa kai kuma baka jin magana ne, sau nawa kake so nayi ma mgn akan wannan, miye aciki dan ka faranta ran mahaifin ka, kayi masa abinda yake so?
Ya qara tsuke qaramin bakin sa hade da yatsina fuskarsa, yana qoqarin tashi ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu.
Look sultan dole ne xakayi abinda mahaifin ka ya umurce ka dashi matuqar baka son raina ya baci akan ka, mahaifinka bai kasance mai bijirewa umarni iyayen sa ba, tun yana yaron sa ya taso da son kasancewa d'an kwallo amma mai martaba ya hana sa yana so ya xama cikakken likita domin yana sha'awar ace yau jinin sa mai ceton al'umma ne, sai ya xamana bashi da aiki ko lokacin wani abu idan ba kallon ball ba sai karatun sa, ya baiwa kallon ball muhimmanci fiye da tunanin ka wanda alokacin ko mace bata gabansa, ya kasa cika burin sa na xama d'an kwallo amma ya cika burin iyayen sa wanda albarkar hakan ke tare dashi har kake ganin sa a matsayin da yake yanxu, meyasa kai baxaka cika masa burin na sa ba.
Sultan ya dubi cikin dake jikin ta kafin ya motsa bakin sa da kyar yace, Mami ba gashi kina dauke da wani baby ba, ya bari idan kin haihu yaron ya cika masa burin sa amma ni ball baya cikin future plan d'ina, we have horses a gidan nan ni shine burina na xama d'an tseren doki.
Allah ya kyauta sultan amma baa nan gidan ba, footballer xaka xama ko kana so ko baka so final decision din mu kenan, ta gefen karatun ka xaka iya xabar fannin da kake so ka xama in your future.
Bai qara magana ba ya tashi xai fice ko me ya tuna ya juya yana kallonta kamar xai yi kuka.
Mami ban daina wannan mafarkin ba, yau ma nayi and again naga taurarin biyu suna kusanto junan su.
Ka cigaba da addua, nima Ina kan yi. Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya bacewa ganin ta, ta rasa ma'anar wannan mafarkin da sultan keyi, wata takwas kenan da ya soma irin wannan mafarkin na taurari biyu, Allah kad'ai ya san me yake nufi da hakan.
NIGERIA
Fitowar ta da kwarya a hannu yayi dai dai da shigowar dabbobin gidan, da sauri ta ajiye kwaryar wanda madarar shanu ce aciki ta qarasa garken nasu tana d'aure su d'aya bayan d'aya.
Tana cikin d'aurewa ya shigo gidan bakin sa dauke da sallama, yana riqe da wata qatuwar sanda a hannunsa tare da wata baqar Leda dake dauke da lemu da ayaba aciki.
Ta amsa sallamar tana kallon sa da murmushi,
Sannu da xuwa maigida. Murmushi yayi yana ajiye kayan hannunsa ya qarasa inda take yana kama mata d'aure shanu dan baxata iya ita kad'ai ba suna da yawa.
Sun dauki tsawon mintuna kafin su gama d'aure su, suka dawo tsakar gidan suka xauna.
Bari na kawo maka ruwa mai gida, tayi qoqarin tashi ya dakatar da ita, kiyi xaman ki anjima xan sha (suna mgnr cikin rashin kwarewa a hausa kasancewar su Fulani asali )
Murmushi tayi ta gyara xamanta, ya janyo ledar gabanta ya Ciro ayaba da lemu d'aya d'aya ya dauka ya bata sauran yana fadin kici sosai Halimatu saboda cikin dake jikinki likita yace a riqa baki wannan.
Murmushi tayi batare da tayi magana ba ta janyo ayaba ta bare tana ci a hankali, ya tsura mata ido yana kallonta cikin tsananin so da birgewa, yana matuqar son matar sa kamar yanda take son sa take kula dashi, kawaici da kunyar ta suna birgeshi, yana tausaya mata musamman yanayin cikin nata dake matuqar bata wahala tunda ta same sa bata qara lfy ba, kullum da xaxxabi take kwana wataran ma duk abinda taci sai ta amayar dashi har xuwa lokacin nan da cikin yake cikin watan haihuwar sa.
Bayan ta gama cin ayabar ta dubesa da murmushi cikin harshen fulla tace kasan addu'ar me nayi mana yau dana yi sallah.
Ya girgixa kansa yana kallon ta da murmushi, ta shafa cikin kafin ta sunkuyar da kanta qasa cikin jin kunya tace nayi addua abinda ke cikin ciki ya kasance namiji ne saboda ya taimakeka xuwa daji da dabbobin nan.
Yayi murmushin da haqoran sa suka bayyana, yace nagode da wannan addua halimatu amma tunani na da naki ba d'aya ba ni Ina son mace kuma kullum ita nake addu'ar Allah ya bani mai kyau da kawaici kamar ki, mai haquri da sanyin hali irin naki.
Ta sa tafukkan hannunta biyu ta rufe fuskarta cikin matsinanci farin ciki, shima yana murmushi ya tashi yayi hanyar dakin sa.?
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama
*SULTAN MERA*
Haske writers Association
?Fertymerh Xarah=؞?
2
Bayan wasu kwanaki.....
Safiyar yau ta tashi bata jin dad'in jikinta, komai ta na yin sa cikin dakewa da dauriya kada mai gidan ya lura tasan ba qaramin aikin sa bane ya fasa fita kiwo yau.
Ta xauna da kyar bayan ta ajiye masa kofin madara a gabansa, ya dube ta yana kallon yanda take yatsina fuska,
Lafia halimatu ko jikin ne? Ta girgixa kanta da sauri tana kallonsa,
Ba jikin bane tashin xuciya nake ji kamar ko yaushe, baxan iya cin komai ba a yanxu sai xuwa anjima idan ta lafa.
Ya sauke numfashi cikin gamsuwa da bayanin ta, ya dauki kofin ya kai bakin sa had'e da lumshe idanuwansa.
Sai da yasha sosai kafin ya ajiye kofin, ni xan tafi halimatu, idan kinji jikin ya tsananta kije maqota kisa yaro yaje ya Kira ni, baxan je da nisa ba yau saboda yanayin jikin naki, dan Allah karki sa wasa ko kunya ki cutar da kanki kinji.
Ta gyad'a kai tana murmushin qarfin hali, tana qoqarin tashi ta raka sa taji ya riqo ta,
Yace na yafe yau ki kwanta ki huta, xan biya ma na turo maki yakumbo ta xauna dake.
Nagode sosai Allah ya dawo da kai lafia.
Amin... Ya shafi kanta yana fadin Allah ya miki albarka, ya barmin ke har qarshen rayuwata ina son kasancewa dake cikin farin ciki, ina matuqar son ki halimatu, ya sumbaci goshinta cikin wani yanayi.
Ta lumshe idanunta tana murmushin da ya bayyana fararen haqoran ta, suna had'a ido tayi saurin sanya tafin hannuwanta ta rufe fuskar ta cikin jin kunya, murmushi kawai yayi sanin halin ta ya tashi ya fice.
Ta bisa da kallo cikin so da qaunar kasancewa da shi a koda yaushe, kafin ta fara tuno bayan ta.
Asalin su...? A gurguje pls
Malam Ard'o shine sunan mahaifin halimatu yaya ne a gurin mahaifin Ma'awiya (mijin halimatu).
Akwai shaquwa da yarda sosai tsakanin iyayen nasu, lokacin da Halima ta isa aure aka so aurar da ita ga wani Habibu yaron hakimin garin ne, kasancewar mutanen garin sun San ba yaron kirki bane sai mahaifin ma'awiya da halimatu suka bijirewa auren wanda ba qaramin matsala yaso ya janyo masu a garin ba.
Akwai shaquwa mai tsanani tsakanin ma'awiya da Halima irin na yaya da qanwar sa wanda iyayen suka yi tunanin soyayya? ce tsakanin su wannan dalilin ya saka iyayen qudirin had'a su aure.
Tun daga lokacin da suka ji wannan labari shaquwar su ta qara tsananta, halimatu yarinyace kyakkyawa mai matuqar kunya sosai, tana da son wasa da raha, tana da haquri ba kasafai kake ganin bacin ran ta ba, tana da kau da kai akan abinda bai shafe ta ba ko acikin abokanta yam'mata sabanin ma'awiya da idan kaga dariyar sa tabbas yana tare da halimatu ne, ba wani babba bane sosai shekarunsa 25 kacal a duniya halimatu na da 17.
Bayan saka bikin su ne mahaifin halimatu ya soma rashin lafiya wanda bai jima ba Allah yayi masa cikawa dama mahafiyar ta, ta jima da rasuwa. Kafin mutuwarsa ya dauki duka dukiyarsa ya damqawa ma'awiya da cewa ya kula masa da halimatu batare da cin amanar ta ba.
Ma'awiya ya karbi amanar da hannu biyu, duka shanu da sauran dabbobin dake gidan mafi akasarin su duk na halimatu ne, yana kula da su sosai kamar yanda ya daukarwa mahaifin ta da mahaifin sa alqawarin haka.
Tun bayan auren su musu bai taba had'a su ba, suna xaune cike da so da qaunar juna, har Allah ya kawo wannan cikin da take dauke dashi tana watan haihuwar ta.
Jin ciwon ya lafa mata ta tashi da kyar ta fito tsakar gida dai dai da shigowar ma'awiya, tayi masa kallon mamaki tana fadin
Lafia maigida ka dawo yanxu,
Naje ban sami yakumbo ba, taje birni wurin sana'ar ta shine hankalina ya kasa kwanciya da yanayin ki na dawo na qara duba ki.
Murmushi tayi tana kallonsa, tace ai na gayama ba abinda ke damuna kuma yanxu kaga shaidar hakan, dan Allah ka kwantar da hankalin ka.
Taya hankalina xai iya kwanciya bayan nasan yanayin da kike ciki.
Ta matsa a hankali kusa dashi ta riqo hannun sa ta sumbata, abinda bata taba masa ba a tsayin lokacin da suka dauka tare hakan ya saukar masa da kasala lokaci d'aya ya tsuramata idanu yana kallon ta cikin mamaki, ta d'ora hannun sa akan tsinin cikin ta, kaji yaron mu yana cikin qoshin lfy kuma ya hana mahaifinsa shiga damuwa, yana son mahaifin sa yana son kasancewa da mahaifin sa kamar yanda mahaifiyar sa take buri da fata a koda yaushe, ta d'ago da kyar tana kallonsa ido cikin ido tare da sakar masa murmushin da har abada baxai taba gushewa a xuciyar sa ba, tsananin dad'i ya saka shi rungumota sosai cikin kirjinsa ya saka hannun shi yana shafa gadon bayan ta a hankali cikin wani yanayi marar misaltuwa, da kyar yace ina son ki halimatu har qarshen rayuwata, ya kai bakin sa ya sumbaci goshinta kana ya juya ya fice da sauri tunawa da dabbobin kawai ya bari a daji.
Kamar kar ya juya ya tafi ciwo ya sake dawowa, da kyar ta d'aga qafafuwanta ta koma cikin daki ta xauna.
Sai dai me duk yanda tayi ta kasa xama ciwon sai tsanantawa yake, sai faman cije yatsa take tana yarfar da hannu yayin da hawaye suka soma kwaranya a kyawawan idanuwan ta.
Phoenix
A hankali take saukowa daga saman benen kamar wacce bata son taka qasa cikin tsananin ciwon Mara da ya dame ta tuntuni.
Sultan dake xaune a falon yana buga game da sauri ya taso yana kallon yanayin ta,
Mami meke damun ki, baki da lafiya ne.
Ta gyad'a kai da kyar tana cije lips din ta,
Na Kira mahaifinka bata shiga, meyiwuwa ya shiga tiyata ne ya kashe wayar, dauko min key din motata muje asibitin.

Da sauri ya haura sama, ta soma tafiya da kyar xuwa farfajiyar gidan, bata jima ba sai gashi ya fito yaje ya bude mata motar ta shiga da kyar.

Mami xaki iya driving kuwa, kingani da an koyamin mota da yanxu ba shikenan ba.

Ta murmusa da kyar tace at your age shekara goma ina kai ina iya mota musamman a wannan qasar, yi sauri shiga mu je.

Ya xagaya ya shiga motar.

Da kyar suka iso asibitin sai dai qarfin hali kawai take yi saboda yanda take fitar da numfashi kawai xai nuna Ma tana cikin mawuyacin hali, duk yanda taso ta fito motar ta kasa ko d'aga qafafun ta sai nishi take sama sama.

Ganin haka sultan yayi cikin asibitin da gudu kai tsaye office din Dr mera ya nufa, baya ciki, fitowar sa tayi dai dai da qarasowar mera tare da wata nurse a bayan sa da ganin yanda take binsa da sauri tana rubutu a file xaka gane akwai bayanin da yake mata.

Cak ya tsaya yana kallon sultan cikin ware idanu batare da yayi magana ba.

Sultan ya nuna masa hanyar da ya fito yana fadin Mami xata mutu dad.... ai bai jira ya qarasa ba ya nufi hanyar waje da gudu.

Inda ya tsinkayo motar can ya nufa yanda ya same ta kad'ai xai nuna masa babu numfashi a tare da ita, cikin rud'ewa ya dauke ta yayi cikin asibitin da ita.
[11/20, 10:25 AM]Ummi Tandama:
*SULTAN MERA*
Haske writers Association

? ?Fertymerh Xarah=؞?
3
D'aukar ta yayi ya nufi cikin asibiti da ita, kai tsaye Labour room ya nufa da ita, da sauri nurses suka Mara masa baya.

Sultan na qoqarin shiga Labour room din, mera ya juyo yana kallon sa.

Wait outside son,
Meyasa daddy? Ina so naga yanda Mami xata bamu baby.

Mera ya bata fuska had'e da nuna masa hanyar fita, kaje ka jirani office yanxu xamu xo ma da babyn.

Sultan ya make kafada cikin bata fuska kamar xaiyi kuka,
Ni baxan je ba, I will stay with my mother, ai ni na kawo ta asibiti ba kaine ka kawo ta ba, so allow me to be with her,? she need me not you, yayi cikin labour room din yana share hawayen sa.

Tsananin mamaki ya hana mera motsawa daga inda yake yabi yaron da kallo har ya isa gadon da Afiya take kwance, cikin xafin nama mera yaje ya dauko shi ya fita dashi kai tsaye office din sa ya nufa dashi,

Kana son ka nuna min taurin kai cikin mutane ko, xaka min bayani idan mun je gida, ya juya ya fice.

Lumshe idanunsa kawai yayi kafin kace me, barci mai nauyi yayi gaba dashi.

Bata yi wata doguwar naquda sosai ba ta haifi yar'ta mace, sosai xaka ga tsananin farin ciki shimfide a fuskar mera,

Alhamdulillah ya fad'a yana sumbatar baby bayan an gyara ta, yanxu yaran sa uku kenan, akwai wadda take biwa sultan Amira tana gida Nigeria tare da iyayen su, ya dubi Afiya da barci take sosai yana jin wani nishad'i a tare dashi.

Kai tsaye aka nufi aminity da ita, nan ya soma Kira gida yana sanar dasu haihuwar Afiya sai murna ake taya sa.

Yana xaune bakin gadon da Afiya take kwance riqe da jaririyar sultan ya shigo kai tsaye inda take ya nufa ya riqo hannunta idanun sa akan ta,

Mami yanxu nayi irin wannan mafarkin, tauraruwar taxo daf daf dani ta qara haske sosai, me hakan yake nufi?

Nima ban sani ba sultan, ta fad'a tana kallonsa.

Mera yace hey baka ga qanwar ka bane, baka murna da xuwan baby ne.

Sultan ya girgixa kansa batare da ya kalle sa ba,

I don't want to see her again saboda ita ka hana ni na xauna da Mami dax'u.

Aiman bai qara magana ba, yayi shiru kawai yana tunanin hali irin na sultan wannan dalilin ya saka baya son ya xauna Nigeria saboda baya son ya taso cikin sarauta ko kad'an.

Sultan wani irin mutum ne mai naci da kafiya akan abu, yana da iko da izza da nuna shi wani abu ne akan kowa tun yana qaramin sa dalilin hakan ne yake nisanta shi da sarauta saboda idan ya xauna acikin ta tabbas komai xai qaru akan halayen sa, yaron bai jin magana ko kad'an.

Nigeria.....

Sai faman juyi take a qasan dakin? tana karanta duk wata addua da taxo bakin ta, qarfin ta ya qare bata da wani kuxari nishi ma da kyar take yin sa, a yau tana mai dana sanin barin mijinta ya fita ya barta da tuni ya jima da kai ta asibiti ko nemo mata mai karban haihuwa da xata taimaka mata.

Naquda ta taso gadan gadan tana ji tana gani kai ya bullo, tsananin rud'ewa ta rud'e sosai, ga ciwo ya tsananta.

Wani qarfi ya xo mata tayi wani nishi mai tattare da gajiya cikin ikon Allah sai ga santaleliyar mace ta biyo, ta tsurawa yarinyar ido bata da wani qarfi ko kuxari da xata iya d'aukar yarinyar tana cikin wannan yanayin taji kukan shanu suna shigowa wanda alama ce ta mai gidan ya dawo.

Jikinsa ke bashi ba lfy ba, ya kasa xama a dajin dalilin da yasa ya tattaro su kenan suka dawo gida, har ya gama d'aure dabbobin bai ji motsin ta ba, hankalinsa duk yana kan qofar d'akin ko xai ga fitowar ta.

Da sauri yayi hanyar d'akin, kicibis yayi karo da ita kwance cikin jini kamar wacce babu alamar rai a tare da ita, batare da kyankyami ba ya tsugunna gabanta tare da rungumota xuwa jikinsa, ta bud'e idanunta da kyar tana kallonsa cikin wani yanayi na ciwo.

Ma'awiya ta Kira sunan sa karo na farko a rayuwar ta, ya dube ta yana fadin,

Meyasa kika min gardama halimatu, ni nasan baki da lfy kika musanta min, muje asibiti ne, ta girgixa kanta da kyar hawaye na xubowa a idanuwanta.

Kayi haquri ka yafe min, kuma ka kula min da jaririyata da amana kada ka bari tayi maraicin UWA ka xame mata UWA da UBA? a rayuwar ta.

Ya juya da sauri yana dube dube sai a lokacin idanunsa ya kai ga jaririyar dake kwance a qasa cikin jini sai motsi take da qafafuwanta, yayi saurin maida duban sa ga halimatu,

Kika haihu da kanki, meyasa kika min haka, meyasa baki gayamin haihuwa taxo maki ba, karki tafi ki barni halimatu, baxan iya wata rayuwa da kowa ba bayan ke, kar kije ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login