Showing 54001 words to 57000 words out of 77337 words

Chapter 19 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

qaseem ba, gaba d'aya sun rikid'e sun juye kamar bana yayan ta ba mai tsananin nan.

Ji tayi tsigar jikin ta yana tashi sannan bugun qirjinta ya tsananta tun da take bata taba jin irin wad'annan abubuwan da take ji ba game da yaya sultan wasu sabbin feelings ne, xata iya fassara su da qauna wadda jigon ta soyayya ce.

Ta janye idanun ta da kyar daga kallon sa had'e da sunkuyar da kanta bugun xuciyar ta na qara tsanantawa idan haka ne xuciyarta bata mata adalci ba, ta kai kanta inda Allah bai kai ta ba, ta soma addu'ar Allah ya cire mata wannan sabon al'amari da ta tsinci kanta a ciki, cikin daqiqa da basu wuce goma ba.

Sultan wani irin mutum ne mai kid'ima xuciya da gigitata, bata da ja itama ta afka tun daga first sight, me xatayi me xata ce banda ta bada kai bori ya hau, idan bata amsa ba ai yaxama butulci ga ubangiji daya dube ta ya turo mata shi dan ta rufawa rayuwar ta da qurciyar ta asiri ta xamo cikakkar mutum mai daraja kamar kowa, murmushi tayi har qasan xuciyar ta tare da saka tafukkan hannuwanta ta rufe fuskarta kafin ta tashi da sauri ta shige cikin toilet had'e da rufo qofar, shima murmushin yayi yana bin kayan da ta xubar gurin da kallo kafin ya tashi ya fice.

Yinin ranar wasan buya suka yi dashi duk yanda yaso ya ganta taqi yarda gashi ba waya ne da ita ba, ya fita daga gidan ma xuwa inda ammi ya jima sosai bai je ba daga can ya nufi inda mommy, bai dawo gidan ba sai past 10 na dare, wanka yayi ya shirya cikin kayan sa na barci kafin ya janyo wayar sa yana dialing number yasmeen.

Tuni ta dad'e da yin barci, jin qarar wayar ta ya saka ta yin firgigit daga barcin da take, hidaya ta bud'e idanun ta tana jan dogon tsaki kafin ta juya mata baya, tayi mamakin ganin kiran sultan tayi saurin Kara wayar a kunnen ta tana fad'in yaya.

Yace ba hidaya wayar, ta d'auke wayar daga kunnen ta cikin mamaki kafin ta dubi hidaya tana fad'in malama kina ji ki tashi yaya na magana, hidaya ta juyo tana kallon ta kafin tace ni barci nake ji baxan iya waya yanxu ba, kafin yasmeen tayi magana ya tsinke wayar saboda yana jiyo abinda hidaya d'in ke fad'a, fitowa yayi ya nufi d'akin nasu lokacin yasmeen na qoqarin kwanciya tana ganin sa tace yaya..

Hidaya na jin yasmeen ta fad'i sunan sa ta qara lafewa had'e da rumtse idanun ta sosai cikin fad'uwar gaba, kamar daga sama taji yana fad'in xaki tashi ne ko sai na hau gadon na janye abinda kika lulluba da shi.

Ba shiri ta tashi xaune tana murza idanunta tare da fad'in Mi magete(xan yi maganin ka)

Me kike cewa ya tambaya yana kallon ta, ta turo baki tana fad'in ba komai, yasmeen ta gimtse dariyar da taxo mata, yace ki karbi wayar hannun yasmeen I will call back, ta karbi wayar tana kallon sa cikin langabewa tare da fad'in? shikenan, murmushi kawai yayi ya fice.

Yasmeen sai mamaki take tace meke faruwa, hidaya ta turo baki tana fad'in min mi somi(ni na gaji)

Yasmeen tace dame, tace yana takura ni da yawa, yasmeen xata yi magana sai ga kiran nasa ya shigo wayar kamar baxata d'auka ba sai da ta kusa tsinkewa kafin ta d'auka tana turo baki.

Muryar sa da ta jiyo ta saukar mata da wata irin kasala, _just to say good night_

Ta lumshe idanunta ta bud'e a hankali tana kallon yasmeen da ta kafe ta da idanuwa cikin mamakin ta da tuhuma tayi murmushi tana d'auke kanta gefe kafin tace have a sound sleep and sweet dreams, yace with you in mind? tayi murmushi kamar yana ganin ta tace in both the soul and mind... tana jin sautin murmushin sa cike yake da mamakin hidaya bama shi kad'ai ba kusan haka ne a gurin yasmeen da tayi mutuwar xaune dan bata taba tunanin hidaya ta kai haka ba.

Zan so na nad'o maku muhimmiyar hirar da ta gudana a tsakanin wad'annan masoya a yau, to amma tafi qarfin hannun Pherty ya rubuta banda ta xuba masu ido tana kallon su cikin birgewa da sha'awa.

Hira ce ta masu ilimi wad'anda suka san abin da suke yi, ba yan I luv u, I kiss u, I will die for you, without u am hopeless ba, wannan hira ce mai ratsa xukata love at first sight sun yarda sun amince da xama a qarqashin inuwar aure ta har abada su rayu tare.

_welcome to the new and wonderful life full of love and happiness HIDAYA & SULTAN_

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*


*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nnan number 08169334980*

36

Yau kam gidan d'auke yake da manya baqi, su ameera sun dawo hutu, sai hidimar dawowar su ake tayi.

Amira tuni ta daina jin haushin hidaya suna shiri sama sama ba laifi, sai dai salwa ce har yanxu bata sauko daga xafin da ta d'auka akan hidaya ba, a yanxu ta rasa wace irin shaquwa ce tsakanin sultan da hidaya wanda kusan kullum sai ta gansu tare, xaune suke su biyu ta tsura masa idanu,

Tace yaya sultan kullum ina so mu xauna muyi hira tun da na dawo amma kaqi bani fuskar yin haka meyasa?

Yace kin xo ki saka ni gaba ki tambaye ni ne saboda kin ajiye ni.

Ta girgixa kanta a hankali xuciyar ta na xafi, ya dube ta yana fad'in,

Ya karatun naku hope kuna maida hankali ba wasa kuke da neman soyayya a gurin maza ba, salwa tayi murmushi tana fad'in aa yaya ai Abba ma shaida ne akan muna karatu sosai sanda yaje kai mana xiyara ya gani.

Sultan ya jinjina kansa yana fad'in fine and good, ya tashi yana fad'in xan shiga daga ciki bai jira cewar ta ba yayi shigewar sa, xaman sa kan sofa bada dadewa ba yaji an kai masa peck gefen kumatu ta bayansa, ji yai tsikar jikinsa ta tashi ya juya da sauri yaga mai masa wannan aikin, idanunsa acikin na hidaya tana tsaye tana murmushi, ya tashi da sauri ya ja hannun ta ya nufi d'akin sa da ita.

Ni sa'an kine, kin raina ni ko,
Tace aa yasmeen ce fa tace yau ranar kiss world Day ne na qasar da kake xama, wai haka kana can xaune lonely babu mai yi Ma shine ta tursasani naxo nayi ma.

Ya jinjina kansa yasmeen ba qaramin raina shi tayi ba, hidaya xatayi magana ya saka qaramin yatsansa akan qaramin bakin ta yana kallon ta cikin ido, yace ke kuma baki da wayo shine kika xo kiyi, kin taba jin ranar kiss world day a rayuwar ki, wait ma a ina kika koyi peck haka, wa kika taba yi mawa?

Yaya ba kowa fa, nima ban san yanda akayi nayi ba amma ai ka gayamin duk yana cikin soyayya ko, ya dube ta yana fad'in idan mun yi aure nace, don't try it again bana so.

Tace kayi haquri baxan qara ba.
Yace kima qara ki gani, xan baki mamaki.

tayi murmushi batare da tayi magana ba.

*

Sultan da hidaya suna son junan su, merah ya fad'a yana kallon ta da manyan idanuwan su.

Ko yaushe suka yi haka da kai, ta fad'a tana tsare sa da idanu, yaushe kake tunanin sultan xai so hidaya akan me.

Hannun ta ya riqa suka nufi window, ya d'aga labulen yana nuna mata yasmeen, hidaya, amira da kuma sultan d'in dake wasa cikin garden.

A tunanin ki yaushe sultan xai xauna yayi magana tare da qanina sa, kin taba gani balle har yayi wasa dasu, hidaya ta canxa maki yaro Afiya, daga xafi da tsananin fushi, rashin sakin fuska xuwa mai sanyi babu komai a xuciyar sa yanxu banda kasancewa da wad'annan mutanen ko da yaushe, babu tsawa da hantara da yake masu, sune friends d'in sa kuma sune yake jin dad'in xama dasu duk ta dalilin hidaya, are you not happy, shin hidaya bata cancanci ta xauna da sultan xama na har abada ba, hidaya bata cancanci ta xamo suruka a gurin ki ba idan har kin kasa bata matsayi irin na yasmeen a xuciyar ki, me hidaya tayi a rayuwa haka da baki son ta.

Yaushe nayi da kai cewa bana son ta, kada ka min sharri aiman.

Idan kina son ta meyasa bakya son ta da sultan? ta yatsina fuska tana fad'in hidaya bata da asali fa and again she is not a Virgin ka sani.

Bar mgnr asali domin nasan mahaifin ta kuma ina da yaqinin cewa hidaya ta taso tare da yan uwanta ba wai tana rayuwa da mahaifin ta ne kawai ba, menene acikin budurci da kike ta magana a kansa, tana qarama akayi raping d'in ta akwai alamar girma a tare da ita lokacin da har kike tunanin ta rasa budurcin ta, yasmeen ta fara period when she is 13 and hidaya ta fara when is 14....

Ni ba wannan nake magana ba, sultan baxai kasance da hidaya ba...

He will be ya katse ta, sultan xai xauna da hidaya a matsayin sa na miji a gare ta, babu wanda ya isa ya raba wannan auren a yanxu.

Nayi dana sanin amince ma a wancan karon na cewa xaka raba auren, You deceive me Aiman... tayi shiru tana qoqarin maida hawayen da suka xo mata tare da d'auke kanta gefe, janyota yayi ya had'a ta da jikinsa ya rungume ta had'e da saka hannun sa d'aya yana yawo da shi a gadon bayan ta cikin shigar rarrashi.

Yace believe me xakiyi farin ciki da kasancewar hidaya in law a gurin ki, duk da hidaya tana da kafuwa nasan she is good, na roqe ki kiyi haquri ki barsu idan akwai wadda kike son had'a sultan da ita I promise xan cika maki wannan burin.

Tayi shiru batare da tayi magana ba, idanun ta na kan window tana kallon su har lokacin sultan da hidaya sun taru akan yasmeen da amira suna jiqa su da ruwa, wannan farin ciki da take gani a fuskar sa tana son ya dauwama acikin sa na har abada, idan hidaya ce farin cikin sultan meyasa baxata taya sa son abinda yake so ba a matsayin ta na mahaifiya.

Da kyar tace yaushe bikin nasu, yaushe xasu san cewa su mata da miji ne.

Aiman ya d'ago ta yana kallon ta cikin mamaki, yace kin amince su xauna tare, ta gyad'a kanta cikin tabbatarwa, yayi murmushi yana fad'in nan da sati biyu tuni na gama gyara gidan da xasu xauna.

Tace meyasa baxasu xauna anan tare damu ba, su duka yara ne fa.

Yace xanyi tunani dai.....

*

After a week

Sai faman shirye shiryen bikin su ake tayi, yau saura sati d'aya a fara gudanar da bikin auren, farin ciki a gurin sultan baxai misaltu ba, hidaya kuwa ko a jikinta sai sabgogin gaban ta take it duk da tana cike da fargaban auren.

Aiman, Afiya, Amira, Yasmeen, Sultan, Hidaya ne xaune a falon suna qara tattauna abubuwan da suke so ayi a bikin banda hidaya wacce ta maida hankali sosai a kallon TV da take yi kamar babu ta a falon.

Sarkin gida yayi sallama ya shigo falon yana fad'in ranka shi dad'e kana da baqo a waje, wani dattijo ne ke son magana da kai.

Aiman yayi Jim kafin yace, amma meyasa bai jira na fita office BA xai same ni anan gida.

Da nayi mashi wannan tambayar yace shi ba marar lafiya bane lallai kai yake son gani kuma yake son yayi magana da kai acikin gida.

Shikenan ba damuwa shigo da shi, sarkin gida ya juya da sauri ya fice.

Kusan minti biyar da fitar sa suka jiyo sallama, aiman yayi masa ixini da ya shigo yana miqawa Afiya mayafi ta lulluba ajikinta,

Kinji ance baqo xai shigo amma kin xauna bayan kinsan abinda ke jikin ki, tuba nake ranka shi dad'e ta karbi hijab d'in ta saka tana fad'in tuba nake ranka shi dad'e.

Tun da dattijon yaxo aiman ya kafe shi da idanun sa yana son tuna inda ya san fuskar, da hannu yayi masa alama da ya xauna.

Dattijon ya girgixa kansa yana fad'in ba sai na xauna ba, wad'annan kujeru masu tsada basu cancanci irina ba, duka yaran suka juya suna kallon sa, sultan ya san fuskar ya manta inda ya Santa haka hidaya ma ta soma tunanin ina ta taba ganin fuskar, tana tunawa ta tashi tana fad'in,

Baba kaine a gidan mu, me kake so ne ko kayi mantuwa a mota ta ne?

Aiman ya dube ta yana fad'in kin san shi ne,

Eh daddy na taba taimakon sa na rage masa hanya na kaishi gida amma nayi mamakin dana ji yana magana saboda ranar komai bai ce min ba.

Aiman ya dubi dattijon yana fad'in to ko tayi ma wani laifine ka biyo ta har gida haka da sassafe?

Yace aa ko d'aya ya dubi hidaya yana fad'in min on baffa mada(ni ne baffan ki hidaya) ta bud'e idanu sosai tana kallon sa, yasmeen ta tashi tana fad'in kaine baffan hidaya, a take sauran suka miqe cike da mamaki.

Hidaya ta matsa kusa dashi da sauri tana fad'in ni, ni d'in hidaya, you mean kaine baffana, how, ta yaya, baffana ya dad'e da mutuwar ko daddy ta fad'a tana kallon aiman.

Merah ya gyad'a kansa yana qarewa dattijon kallo, iya rud'ewa hidaya ta rud'e ta juya tana dafe kanta kafin ta qara juyowa tana kallon sa tabbas muryar sa sak baffanta ko cikin dubban mutane xata shaida hakan sai ta rumtse idanun ta gam ta d'ora hannun ta akan fuskarsa tana lalabawa, gabanta yayi mummunan fad'uwa ta ja da baya a hankali tana qara kallon sa, tabbas shine, shine baffana ta fad'a da qarfi tana fad'awa jikin sa ta qanqame shi sosai tana kuka.

Me kike yi haka, how dare you xaki had'a jiki da wannan, how sure are you shine baffan ki.

Ta goge hawayen ta tana kallon sultan dake maganar cikin bacin rai, xata yi magana baffa ya hana ta, ya dubi sultan yana fad'in na san waye kai a yau, nayi mamakin yanda akayi ka kasance jinin Doctor, kana tambaya ta ko nasan waye kai, kasan iya lokacin dana d'auka ina binciken ko kai waye, kaine yaron aiman kwaya d'aya namiji, kaine yaron nan d'an kwallo wanda tauraruwar sa ke haskawa a yanxu, wannan da bai d'auki talaka da mutum da daraja ba,wannan wanda yake d'aukar kowa wulaqantacce ne a gurin sa, na gama sanin ka da rayuwar ka amma ni ka sanni, kasan waye ni, nine wannan talakan da ka raina, ni ne wannan talakan da ya taba motar ka da kankana ka mare shi, nine wannan talakan da ka tashi bigewa a hanya saboda hanya ba tamu bace ta manyan mutane irin ka, kuma nine talakan nan mahaifin hidaya..

Sultan ya katse sa a fusace xai yi magana hidaya ta d'auke shi da mari, cikin mamaki kafin ya qara yunqurin magana ta qara d'auke shi da mari tana ja da baya, ta ja hannun baffa tana fad'in baffa xo mu tafi na rama ma alqawarin dana d'aukar ma kuma baxan aure sa ba tunda ya wulaqanta min kai.

Baffa yace wai da auren sa xakiyi kenan, da kuwa an cutar da rayuwar ki.

Cikin fusata Afiya tayi kan hidaya xata dake ta aiman yayi saurin riqe ta yana fad'in, noo barta ta nuna halaccinta ta hanyar sakamin da wannan rashin kunya kai tsaye na dukan sultan a gabana batare da Kara ba,

Afiya tace dama tsintacciyar mage bata mage, banda jaraba irin ta sultan dama me xaiyi dake, sauran wani inaji nan aka kawo ki an maki fyade ko qarya ne.

Fyade sultan ya maimaita yana kallon hidaya cike da mamaki, bama shi ba duk yaran dake falon sun tsorata barin ma hidaya tace fyade kuma ni, yaushe?

Aiman ya dubi baffa yana fad'in alheri ya had'a ni da kai ba sharri ba kuma babu ta inda na cutar da kai ko kuma cutar da abinda ka bani amana, kana raye kaqi neman yar'ka kaqi xuwa gare ta, ka barta cikin qunci da tunani na rashin ka, yanxu ta xama mutum ka kwaso qafafu kana kiran kai mahaifin ta ne, ka d'auki hidaya ka tafi da ita duk inda xaka je amma ka sani akwai auren sultan d'ana akan ta ashe baka gama sanin ko waye sultan ba har yanxu, baka san labarin sultan ba tun da har ka kasa gano wannan yaron da ya raina ka yake kyamatar talakawa yana auren yar'ka.

Gaba ki d'aya yaran suka xubawa merah kallo cike da tashin hankali, hidaya tana da auren sultan yaushe hakan ta faru kuma yaushe akayi.

Baffa ya soma matsar kwallah yana fad'in ka cutar da rayuwata da ka had'a ya'ta da wannan marar kirkin yaro.

Aiman yace ko kuma ka cutar da rayuwar ka na guduwa ka bar yar ka batare da ka waiwaye ta ba alhali kasan yanda ka barta.

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*

_On this special day, I wish you all the very best, all the joy you can ever have and may you be blessed abundantly today, tomorrow and the days to come! May you have a fantastic birthday and many more to come& HAPPY BIRTHDAY XARAH DANGE<؂?_

37

Ta ya kake tunanin xan gudu naje nayi rayuwa babu hidaya ba, ita kad'ai nake so, ita kad'ai nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login