Showing 63001 words to 66000 words out of 77337 words

Chapter 22 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

xama da d'an iska ba kuma.

Yace nine d'an iska? tayi shiru tana d'auke kanta gefe cikin bacin rai bata ankara ba taji ya fisgota, hannun sa na dama yasa yayi baya da hannuwan ta guda biyu, yasa d'ayan ya matse ta sosai a jikinsa, yace nine d'an iska right?ta girgixa kanta da sauri cikin tsoro tace kayi haquri ba da kai nake ba, a hankali ya soma kissing d'inta tun daga bakin ta wuyan ta xuwa qirjinta, ta bud'e baki xata yi ihu saboda dimaucewa yayi saurin toshe bakin ta da nasa yana girgixa mata kansa, idanun sa sun rikid'e jajir kuma sun juye da tsimin soyayyar ta dake taso masa a yanxu, duk wasu qofofin sadar da jini cikin gangar jikinta sun daina aiki suna karban saqon sultan, gaba d'aya tsigogin jikin ta sun gama tashi da sabon al'amarin da bata taba ji cikin gangar jiki da xuciyar ta ba ganin ta kasa ko motsi sai ya cigaba da sumbatar ta yanda yake so, tsoro ya shige ta bata manta wancan lokacin da xafin ba nan take wani qarfi ya xo mata ganin yanda jikin sa ke rawa ta fisge hannun wa tare da turasa baya, abin ka da marar qarfi tuni jiki yayi lagwas yayi baya cikin rashin kuxari, ya xuba mata lumsassun idanuwansa dai dai lokacin suka jiyo muryar baffa yana fad'in,

Ina hidaya gani na dawo xo kiga kayan.

Gaban ta yayi mummunan fad'uwa hankalin ta ya tashi jikin ta ya d'auki rawa tana fad'in shikenan baffa kashe ka xai yi.

Sultan ya d'aga kafadar sa yana fad'in and so, sai me idan ya kashe ni gwanda ya kashe ni dana xauna duniyar ina cigaba da kallon tsanar da kike min.

Xa tayi magana taji baffa yana fad'in ko barci kike hidaya, bari na shiga bayi na fito, da kyar ta amsa masa da cewa tana xuwa ta dubi sultan tana fad'in xaka bar d'akin nan ko me, yace ba inda xanje sai yaxo ya same ni anan idan ya so ya qara buga min sanda aka na mutu yanxu ya soma ne ya fad'a yana kallon ta cikin xare ido, hannunta tasa ta fisgosa suka fito d'akin suna fitowa ta Saki hannun ta nufi tulin kayan da baffa ya ajiye a gurin dai dai lokacin ya fito daga toilet.

Ganin sultan ya saka shi sakin butar dake hannun sa yana kallon qofar shigowa kafin yace ta ina ka shigo gidannan.

Sultan ya nuna masa qofar shigowa, baffa ya dubi qofar tana rufe yanda ya barta kafin ya juya cikin mamaki yana kallon hidaya yace ina wannan yaron ya bi ya shigo.

Cikin rud'ewa da tashin hankali hidaya ta soma ina ina tace ni.. ni.. uhm.. uhm nima ban sani ba baffa ganin sa kawai nayi yanxu.

Cikin fusata baffa yayo kansa ko kad'an sultan bai tsorata ba yana tsaye yana kallon baffa har yaxo gurin sa, riqa hannun sa yayi Karo na biyu ya qara fitar da shi gidan tare da rufe qofar.

Sultan yayi shiru yana qara bin gidan da kallo, wannan gida ake masa wulaqanci akan sa, wannan gida ake masa korar kare haka, damn it ya shuri motar sa, ya bud'e motar sa ya ciro wata kwalbar guys da tun jiya yake tunani yasha ko kar ya sha, wannan baqin ciki da kalaman hidaya suka qara tunxura sa ga balle murfinta ya soma xubawa ruwan cikinsa, da qarfi ya kaiwa qofar shuri wanda nan take ta balle ta fad'i dama ba wani qarfine da ita ba, hidaya da baffa suka juyo lokaci d'aya suna kallon qofar yana tsaye da kwalbar a hannun sa idanun sa sunyi jajur kansa sai wani juya masa yake saboda rashin sabo.

Hankalin hidaya ya tashi sosai ganin wannan kwalbar a hannun sa, yaushe ya fara sha, dama yana sha duk bata sani ba, ta tashi da sauri tayi cikin d'aki tare da rufe qofar, cikin fusata baffa ya qara tura sa waje tare da tsayuwa bakin qofar yana fad'in,

Marar tarbiya sai kaxo ka shiga gidan na gani, kana wannan shaye shaye kake tunanin xan baka ya'ta, hankalin sultan ma baya gunsa yana ganin hidaya ta shige shima ya shiga tasa motar da qarfi ya ja ya bar qauyen.

Taimakon Allah ne kawai ya kawo shi gidan yanayin parking d'in shi ma xaka gane babu lafiya, yana tafe yana tangad'i da kwalbar a hannun sa, amira ta fara ganin sa cikin wannan yanayin cike da tashin hankali ta koma kitchen tana sanar da Afiya, tana ganin sa ta soma salati tana fad'in giya kuma sultan.

Aiman dake aiki akan system ya d'ago da sauri yana kallon sa suna had'a ido sultan ya soma fad'in I rape her daddy.. Sai ya jefar da kwalbar dake hannun sa nan take ta tarwatse gurin, ya cigaba da sanin ni ban sani ba sun bani wani abu na sha, sanda na ganta I can't control myself, na basu haquri but why are they punishing me?

Nan take sultan ya fara kwarara amai a gurin...

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980 or?08030811300*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980 or? 08030811300*

40

Aiman girgixa kanshi kawai yayi ya tashi ya bar falon gaba ki d'aya, Afiya da kanta ta riqa sa ta kaishi har d'akin sa ta kwantar dashi.

Mai aiki ta gyara falon gabaki d'aya, amira hankalin ta ya tashi tayi matuqar tausayawa sultan tana son taje ta gayawa sarki ko xai saka hannu a al'amarin tana tuna gargadin aiman gare su muddin yaji mgnr ta fita sai ya bata masu sosai.

Afiya na fitowa amira ta nufe ta tana fad'in yanxu mami ya xamu yi yaya sultan giya fa yaje ya sha.

Tace barshi xan ci ubansa ne idan ya tashi, so hauka ne akan wata banxa da bata damu dashi ba xai xo ya bata rayuwar sa a banxa xai gane kuren sa.

*

Guy amma meyasa tuntuni baka gayamin ba may be a time d'in idan aka yi bincike xaa gane ko waye amma gaskiya am not happy da abinda ya faru kuma akan hidaya, to wai yanxu shi dattijon yace baxai bada ita bane.

Ni fa abinda ke bani tsoro da mamaki fu'ad ni ke shiga gida ana fiddo ni kamar wani almajiri, kaga gidan da ake min wulaqanci a kansa, ranar ban san me ya hau kaina ba harda kashin dabbobi na shafa a jikina a rud'e nake bansan me nake yi ba abinda nake so kawai ya bani hidaya amma bashi da tausayi he send me out yana jifa na da kalamai marar dad'i meyasa baxai yafe min ba tunda na roqe sa.

Fu'ad yace gaskiya wannan dattijon bai kyauta ba ko dan saboda karamcin da daddy yayi masa bai kamata yayi wa nasa d'a haka ba, mutane yanxu basa rama alheri da alheri sai dai su bika da tsiya amma guy da gaske mami take yi fa yanda ranta ya baci haka tsab xata iya gayawa sarki ka soma sha banda hauka me ya kaika ka xauna qasashe baka bata rayuwar ka ba sai yanxu kuma akan wata da bata damu da kai ba.

Sultan yace ai na bari wancan karon ma tsautsayi ne da bacin rai kuma koma me nayi ai ba laifi bane soyayya tana da dad'i a yanxu na yarda da abinda kake cewa, akwai dad'i fu'ad I kiss her, abinda nayi a baya baxan gane dad'in sa ko akasin sa ba saboda baa hayyacina nake ba wannan dana sani wannan da nasani yanxu I enjoy it, na kuma yarda kud'i ba komai suke baka ba a rayuwa yau gashi ina da kud'in amma na rasa farin cikina, ya xanyi da rayuwa ta.?

Komai xai dai dai ta insha Allah amma hidaya kanta ta bani mamaki nayi xaton xata nemi ta dawo ko dan saboda daddy da yasmeen, ina soyayyar da take nuna Ma yanxu tana nufin duk babu?

Sultan ya tabe bakin sa yana tashi tare da d'aukar key d'in motar sa yana fad'in xo muje ka gani da idon ka kuma kaji da kunnuwan ka babu ranar da baxan je wannan qauyen ba haka kuma babu ranar da baxata dubi tsabar idanuna bata furta min Kalmar tsana ba.

*

Tun da suka xo gidan fu'ad ke kallon yanayin sa dama qauyen gaba ki d'aya banda so so ne me xai kawo sultan wannan qauyen ko a mafarki shi kansa bai yi tunanin akwai abinda xai nema a cikin wannan qauyen ba, ya tabe bakin sa yana saman motar xaune sultan ya dawo yana kallon sa yana fad'in ina ji kamar bata cikin gidan, shi dattijon ma ko gaisuwata yaqi ya amsa ni fa na soma gajiya da wannan wulaqanci I can't take it any more.

Fu'ad ya tsurawa wata kyakkyawar bafillatana dake doso su idanu, tana sanye cikin kayan su na Fulani da kwarya akan ta, tafiya take cikin nutsuwa kanta a qasa, sultan ga wata baby ba.

Sultan ya juya yana kallon inda fu'ad ke nuna masa, kurr yayi mata da idanu kafin ya gane ta cikin fad'uwar gaba ya diro daga saman motar yana fad'in hidaya ce.

Fu'ad ma ya sauko yana fad'in tabbas hidaya ce amma bata da hankali ne dai dai lokacin da hidaya ta qaraso gurin hannu sultan yasa ya finciko ta tare da kifar da kwarya dake kanta nonon ya xube gabaki d'aya, a fusace ta d'ago tana kallon sa cikin masifa ganin yanayin tasa fuskar yasa ta had'iye na ta fushin ba shiri.

Da aure na a kanki kike fita haka ba mayafi, al'ada ko hauka sai kace baki da ilimi just look at you har gashin kanki ma a waje.

Ta fisge hannun ta da qarfi tana kallon sa an fita d'in ina ruwan ka mecece matsalar ka dani, ni bani da wani auren ka akaina tuni na watsar dashi, baxan xauna da d'an iska marar mutunci ba, baxan cigaba da son ka ba nace bana son ka ko dole ne, ina da wanda nake so a yanxu mai tarbiya kuma shi xan au... tayi shiru sakamakon mari da sultan ya d'auke ta dashi sai da tayi kamar xata fad'i, shima fu'ad ransa a bace yake da hidaya yau.

Yace hidaya kin bani mamaki, sultan d'in kike gayawa haka, cikin xafin marin ga kwallah ta taru a idon ta take kallon sa an masa d'in shi waye, kada ka qara min magana ba ruwan ka dani ta juya tana kallon sultan tana fad'in ka mare ni.

Yace an mare ki d'in ko xaki rama ne ya fad'a yana matsowa cikin ta, ta soma matsawa daga baya tana fad'in nace bana son ka nace bana son ka kill me.. dai dai lokacin baffa ya fito jin kamar muryar hidaya ganin yanda sultan d'in ke tunkaro hidaya ya saka baffa shan gaban sa yana fad'in anan d'in ma fyade xaka mata kenan, ya juya yana kallon hidaya me yayi maki haka kike kuka.

Cikin kuka tace ya kifar da nonon baffa shine kuma ya mare ni, batare da tunanin komai ba baffa ya d'auke sultan d'in da mari yana fad'in bar qofar gidannan tun ban nakasa ma rayuwa ba banxa marar tarbiya wallahi ka qara sa mata hannu da sunan duka sai ka gamu da fushi na.

Cikin fusata sultan yace well ka rama marin da nayi ma a yanxu, xaka qara kuskure ne idan ka sake d'ora hannun ka a fuska ta da sunan duka saboda na daki matata, kuma wallahi hidaya ta sake fita haka sai nayi qarar ka kotu ita d'in matar aure ce kuma ka sani, ya dubi hidaya cikin bacin rai yana fad'in qofar gidan nan kika qara fitowa batare da ixini na ba Allah ya isa.

Baffa yace idan qofar gidannan ta kace sai ka hana mata fitowa, ko kuma idan kai d'an iska ne ka sake takowa qofar gidannan in gani.

Sultan yace sai naxo kuma gobe xan xo idan naxo ka kashe ni ko kuma ka nakasa rayuwata kamar yanda kace ai ba yanxu ne Karo na farko ba.

Baffa yace shikenan ga fili ga mai doki shege ka fasa, sultan xai yi magana fu'ad ya jasa a fusace ya saka shi a motar suka bar gurin, cike da bacin rai baffa yaja hannun hidaya suka shiga cikin gida.

Guy gsky wannan tsohon bashi da mutunci, fu'ad ya fad'a bayan ya hau babban titi, amma duk laifin na hidaya ne har ni take cewa na kyale ta, wannan small rat d'in duka tashin yaushe ce har ta isa ta min rashin kunya ma oh lallai.

Sultan kamar baxai yi magana ba sai kuma yace wai taya hidaya tana da ilimi ta sani sannan kuma tasan da aure akan ta xata fita ba mayafi ba kallabi akan ta sai wannan duwatsu nasu na iskanci, ta Saki gashi tana tafiya a hanya wannan wace rayuwa ce.

Fu'ad yace ni wlhy bangane ta da farko ba naga ko a gida mami bata bari su xauna gida ba hula akan su ballantana har su fita harabar gida da kai a sake, hidaya ta bani mamaki sai kace ba mai ilimi ba al'ada ai bai fi addini ba.

Shiru sultan yayi yana kallon waje xuciyar sa na masa quna.

*

2 days....

Da sallama ya isa falon mahaifin nasa jiki a sanyaye, aiman na xaune a qasan carpet yana cin farfesun naman d'awisu da yasa aka kawo masa daga sashen sarki.

Nesa kad'an dashi sultan ya xauna yana kallon sa fuska ba walwala yace daddy kayi haquri tuntuni na gane kuskure na baxan qara ba amma dan Allah kasa baki a dawo min da hidaya please.

Aiman ya dube sa kafin ya maida hankali ga cin naman da yake batare da yayi magana ba, ganin bai yi magana ba sultan ya cigaba da fad'in amana ta akaci a ranar daddy wani abu aka bani nasha, sai naji jikina yana canxawa to avoid doing something bad na tashi nace xan xo gida a wannan lokacin wallahi daddy ni ban san ya akayi ba ni dai na ganta kamar babba, ban san menayi ba a lokacin, daddy ka tambayi fu'ad? ko girlfriend bani da, bani da wadda nake so, am not into that, please daddy kayi haquri.

Merah ya qara kallon sa kamar baxai yi magana ba sai kuma ya tura masa plate d'in naman yana fad'in idan ci xaka yi gashi ka ci.

Sultan ya dube sa ya dubi naman, cikin bacin rai ya kau da shi gefe yana fad'in baxan ci ba, hidaya nake so kaje ka karbo min.

Aiman ya lumshe idanun sa yana fad'in baxan iya ba gaskiya bani na bata ba balle naje neman gyara kai da ka bata sai kaje da kanka, sultan xai yi magana aiman yayi saurin cewa get out please bana son damuwa.

Sultan ya tashi ya fice a fusace kamar ya saka ihu, aiman ya bishi da kallo sosai yana bashi tausayi yanda ya dawo cikin qanqanin lokaci kamar ba sultan ba, har wata rama yayi sosai ya lumshe idanun sa cike da tunani iri iri.

Yana fitowa ya sami yasmeen a falo tana xaman jiran sa, fitowar sa yasa ta tashi tana fad'in yaya tun d'axu na shirya dan Allah kaje dani naga hidaya.

Duk da yana cikin halin bacin rai bai hanashi yi mata alama da ta biyo shi ba, da sauri kuwa ta bi bayan sa cike da murna.

Yasmeen sai kallon qaramin qauyen take, ko a mafarki bata taba tunanin xata xo irin wannan qauyen ba, lallai hidaya kamar baa nan ta fito ba.

Tare suka nufi cikin gidan baffa na shirin fita hidaya na tsaye tana bashi saqon abinda take so ya siyo mata daga birni, tana ganin yasmeen ta buga uban tsalle taje da gudu ta rungume ta.

Oh sis I miss you so much, hidaya ta fad'a tare da kaiwa yasmeen peck a kumatu, sultan dake tsaye yaji kamar shine tayi wa haka, yasmeen sai murmushi take ta dubi baffa ta gaidashi, fuska ba walwala yake amsa mata hidaya Ma bata ji dad'in yanda yayi ba, taja hannun yasmeen suka nufi cikin d'akin.

Sultan na qoqarin bin su baffa ya tsaida shi yana fad'in.

Kai malam miye haka, rashin kunya da tarbiya xaka nuna min na shiga d'aki batare da ixini ba.

Sultan yace kayi haquri baffa nayi tunanin komai ya wuce a yanxu.

Tunanin ka kenan ba abinda ya canxa, tukunna ma banyi ma kashedi da karka qara xuwa qofar gidan nan ba, uban me ya dawo da kai.

Sultan ya dube sa yana fad'in baffa ka saba xagin mahaifina nayi haquri bana tanka ma amma yau tare nake da qanwata idan taji kana xagin mahaifin ta tunanin ka ya xata ji bayan nata mahaifin ko da wasa bai taba xagin mahaifin hidaya ba.

Dallah malam rufa min baki, fitar min daga gida kada nayi ma rashin mutunci.

Sultan ya d'aga kai yana kallon gidan kafin ya girgixa kansa batare da yayi magana ba ya juya ya fice.

Yasmeen ta dubi hidaya da ta ajiye mata ruwa da madara tana fad'in, sis rayuwa tafe take da destiny Kala Kala kin manta da yaya sultan kin bude sabuwar rayuwar da ta bani mamaki ko ni bakya tunawa da ni ko?ta fad'a tana qarewa d'akin kallo.

Hidaya tace haka dai kike gani ni na isa na manta dake kice Allah kin tuba

Ni ba wannan ba maganar yaya sultan nake maki nasan kina sonsa yana son ki amma meyasa kin kasa duba masa, meyasa baxa Ku tallafi juna, ku baiwa xuciyoyin ku abinda suke so ba, yaya sultan yayi kuskure ya Kuma gane kuskuren sa yayi Nadama mai suna Nadama amma har yau hidaya kin kasa karban tuban sa meyasa?

Murmushi hidaya tayi tana Kallonta Wanda iyakacinsa fatar bakin ta saboda nauyin ta da take ji a yanxu,

'tace na karbi tuban sa yasmeen, wata qila dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login