Showing 48001 words to 51000 words out of 77337 words

Chapter 17 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

baxata jima sosai ba, bata jin dad'in jikinta shine bata son hayaniya.

Yace kira fu'ad maza ya maidota gida, ta shirya kafin mu dawo.

Ta gyad'a kai tana dialing number fu'ad.

Yana xaune da hidaya kiran nata ya shigo, hidaya na gani ta soma roqon sa akan yace baya gida, haka kuwa ya gayawa Afiya.

Tace kana komawa gida maza maza ka maidota gida.

Tau shikenan mamee, nima yanxu ina hanya xanxo airport d'in.

Ta tsinke kiran, hidaya ta dube sa tana fad'in da gaske yaya xaka je.

Yace yes mana ai dole ne, d'an uwa rabin rai and again best friend, I miss him a lot, ki jira idan na dawo sai mu fita tare daga can na maida ki gida, ta gyad'a kai jiki a sanyaye.

*

2hours da dawowar sa, tun bayan fitowar sa sashen sarki yake raba idanu yaga ta inda xai ganta amma shiru babu ko alamar hakan.

Wa xai tambaya ina hidaya bai sani ba, kowa yaxo ya gaida sa yana masa barka da dawo wa banda hidaya, yana so ya ganta yaga yanda ta koma a yanxu domin girman yasmeen ma ya bashi mamaki duk da yana ganin ta a video call ashe bai ga komai ba sai bayan sun had'u airport ballantana hidaya, ina ta shiga haka?



*idan baka biya ba kada ka karanta, xaka biya haqqi inda baka da iko, ga mai buqata ya tuntubi wannan number 08169334980
*[11/20, 10:25 AM] Ummi Tangama:

*SULTAN MERAH*

*33*

Hidaya tashi na kai ki gida tun d'axu mamee take kira sai fad'a take min.

ta tunxuro baki, yaya ka bari xuwa da dare sai muje ni wallahi nafi jin dad'in xama anan akan can saboda hayaniya tayi yawa.

Yace aa maza d'auko key na motar ki kixo mu tafi, ina jiran ki a waje, ya fice ta bisa da kallo kafin ta tashi tana fad'in ko ba komai ai nayi yawo yau.

Tun da suka shigo farfajiyar gidan ta sami kanta cikin fargaba, Dr aiman ne ya fito daga gidan yana kallon fu'ad kafin ya maida kallon sa kanta.

Daddy I... ya katseta ta hanyar d'aga mata hannunsa
Yace kin ga dama kin dawo kenan, I was not happy with you hidaya.

Tace daddy dan Allah kayi haquri wallahi bana jin dad'in jikina ne shiyasa na bar gidan saboda hayaniya anan, and again daddy maganin dana sha ne ya saka ni barci amma kayi haquri baxan qara ba, ta fad'a had'e da qarasawa wurin shi tana riqe kunnuwan ta duka biyu alamar neman afuwa.

Yace is ok ki shiga ciki and make sure kin je kin gaida yayan ki.

Insha Allah ta fad'a cikin murmushi kafin ta nufi cikin gidan, kicibis suka yi Karo da yasmeen dake tafe tana cin inibi at same time tana latsa wayar ta, kallon ta tayi qasa da sama tana yatsina fuska kafin ta tabe baki ta juya batare da tayi mata magana ba ta fice.

Me kuma kika tsaya yi anan? Fu'ad dake shigowa ya tambaya yana kallon hidaya, kafin tayi magana yasmeen ta juyo tana kallon sa da murmushi tana fad'in,

Yaya har ka dawo again.
Ya gyad'a kai yana kallon ta shima cikin murmushin sa mai qayatar wa dai dai lokacin wayar sa ta d'auki qara, yana dubawa yaga amira ce sai yayi dialing call d'in had'e da barin falon gaba ki d'aya, itama yasmeen tayi shigewar ta.

Ajiyar xuciya hidaya ta Saki kafin ta juya xata nufi d'akin su idanun su suka sarqe dana juna, lokaci d'aya suka bud'e idanuwan su cike da mamakin ganin juna haka ba xato.

Dogon matashin nan ma'abocin ilhama, kwarjini da cikar xati wanda a cikin barci ko a f???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?arke, dare ko rana, tsufa ko kuruciya fuskar sa baxata taba bace mata ba, ga wannan qamshin da bata jin sa a jikin kowa in ba shi ba wanda ke qara dagula mata lissafi akan sa, ta d'auke kanta da sauri tana fad'in

Sannu da dawo wa.... Kamar ba da shi tayi magana ba, yayi shiru tamkar bai ji ba, yana nan tsaye ya xuba mata oily eyes d'in sa, tana qara d'agowa suka had'a ido, ta sauke idanun ta da sauri tana fad'in lafiyar sa qalau kuwa? tunanin ta a xuciya tayi maganar sai taji muryar sa kamar daga sama yana fad'in loosing of memory for the second time shi kike so? tayi murmushin yaqe batare da tayi magana ba ta juya da sauri ta bar gurin, kallo ya bita da shi har ta shige part d'in su,

Hidayar daya tafi ya bari ta qara girma ta xama budurwa mai xati yar shekara goma sha biyar, ko a ina a jikinta hutu ke magana, qugunta ya fito qirjinta ya ciko, fatar jikinta sai sheqi take, ji yake kamar ya je ya rungume ta ko ya sami sauqi a cikin xuciya da gangar jikinsa,?

Mami hidaya nono in sha, yaji sautin tamkar saukar aradu a kunnuwansa, wata irin kunya da nauyi suka saukar masa lokaci d'aya, Allah yasa yarinyar ta manta bata wannan tunani, ko wane irin kallo take masa, ya fice ya nufi bangaren sarki batare da ya qara bi ta kan ta ba.

Yana fitowa sai ga fu'ad, yayi dariya had'e da kaiwa sultan duka a qirji yana fad'in

Our footballer wai kaga yanda ka dawo yanxu tamkar ba kai ba, ni fa wannan Karon baxan yi yawo da kai ba ina jin haushi saboda yam'mata na.

Qaramin tsaki sultan yayi yana kallon sa, yace har yanxu baka daina ba kana nan da wannan halin naka,

Fu'ad yace kaima baka canxa ba kenan, wait ma wai har yanxu baka da yarinya?

Sultan ya gyad'a masa kai cikin tabbatar wa, kallon sa fu'ad yake cikin mamaki kafin yace

You don't have feelings ne ko me, ko dai baka da lafiya ne?

Banda lafiya as how, an gayama kowa ne irin ka da bashi da aiki sai akan mata.

Aa karka min sharri yaran nan su ji, nifa na rasa gane kaina wlhy ina cikin damuwa, duka ina son su.

Wane yaran? Sultan ya tambaya yana kallon sa.

Amira, yasmeen and hidaya.

Mtsew duka ka had'a ka aure su tunda ka xama mahaukaci, kai d'an iska ne ma wlhy na bugawa a jarida dating two sisters at the same time.

Ka kirani koma miye naji, amira ita tace tana sona ai, yasmeen da hidaya kuma ni nace ina so and xan baka mamaki dan xan iya had'asu su biyu na aura xan sami sarki da maganar.

Nuna sa sultan yayi da yatsa yana fad'in are you serious kana son hidaya da gaske.

Yes mana, fu'ad ya tambaya cikin son gwada sa ya ga ko ya damu da hidaya.

Tabe bakin sa yayi yana fad'in ka gama siya mana raini a gurin su ynxu d.... Ya katse sa da sauri yana fad'in akwai wani sauran raini ne a yanxu bayan kai da kayi wasa a cikin su kuma kayi wanka a cikin su.

Sultan ya rumtse idanun sa kafin ya bud'e yana kallon sa, ok go ahead Allah ya baka sa'a ya juya ya fice, shima fu'ad barin gidan yayi.

*

Sis wad'annan kayan haka masu kyau fa ina kika samu,

Yasmeen ta kauda kanta gefe tana fad'in yaya sultan ya bani tsaraba,

Hidaya tayi murmushi tana d'aga kayan masu kyau gaske, taji yasmeen tana fad'in yace kije ki karbi naki.

Hidaya tace meyasa sai naje, ki karbo min mana.

Yasmeen ta tashi tana fad'in idan na karbo maki kada ki saka, kinsan dodo ne da in kinje xai cinye ki.

Wai meke damun ki kwanan nan masifa kike ji yasmeen ko miye abin fad'a anan.

Yasmeen tace ina kika je da yaya fu'ad d'axu, hidaya ta bud'e idanuwan ta sosai tana kallon ta cikin mamaki.

Tace tambaya ta kike ko tuhuma ta kike yi akansa, laifine dan na fita da yaya fu'ad a yanxu.

Yasmeen tayi shiru kamar baxata yi magana ba sai kuma tace before bana damuwa ko na ganku tare kamar yanxu, saboda yanxu ina son sa.

A hankali ta xare glass d'in dake idon ta tana kallon ta sosai, tace kina son sa kenan muna son abu d'aya ni da ke, sai kuma tayi murmushi tana qara kallon ta xamu auri miji d'aya ni da ke kenan shikenan muna tare har abada baxa mu rabu ba kenan.

Yasmeen ta girgixa kanta tana fad'in aa ke xaki auri yaya sultan please hidaya kada kice you can't.

Na auri yaya sultan ta ya, son sa aka gayamiki ina yi ne ko kuma shi ya fad'a miki yana sona.

Ko bai fad'a ba nasan yana son ki and with time kema xaki fara son sa wallahi yaya sultan ba irin matan dake gujewa auren su bane.

Hidaya ta juya ta fita tana fad'in ni yaya fu'ad nake so kuma shi xan aura b.... maganar ta sarqe mata lokacin da suka had'a ido dashi, ta had'iye wasu yawu da kyar kafin ta raba ta gefen sa ta bar gurin da sauri.

Yasmeen ta juyo tana kallon sa tana fad'in, yaya...

Yace meke tsakanin ki da fu'ad, ta sunkuyar da kanta cikin fad'uwar gaba tana fad'in ba komai.

Then meke tsakanin hidaya da fu'ad, ta soma inda inda tana fad'in yaya ita ma ba komai fa.

Abinda naji tana fad'a shima ba komai? Yasmeen ta dube sa tana fad'in, Yaya kaima kana son hidaya ne? ya d'aure fuska yana fad'in yaushe nayi haka dake, ta shagwabe fuska tana fad'in please yaya ka so ta dan Allah ka aure ta wallahi kun dace.

Sultan ya qara d'aure fuska yana kallon ta, waye xai aure ta ni sa'an ki ne ko kuma kece xaki xaba min macen da xan aura, yara da ku har kun san miye aure ma?

Tayi shiru tana tunxuro baki, ya cigaba da fad'in idan kuna shirmen ku, ku daina saka ni a ciki, ya juya ya fice.

Yasmeen tayi shiru tana fad'in tace bata da lokacin shirme, shima yanxu yana fad'in bashi da lokacin shirme, confused, menene shirme anan soyayya kome?

*

Da dare bayan sun gama cin abinci suna qoqarin barin dinning sultan ya shigo falon,

Fuska a d'aure yake kallon hidaya yana fad'in

Ke kawo min abinci na a d'aki ina jira, yasa kai ya fice, hidaya da Afiya suka bisa da kallon mamaki, Aiman kuwa ko a jikinsa sai abincinsa yake ci, ganin hidaya bata da alamar tashi ya dube ta yana fad'in,

Me kike jira, ko kurma ce ke, hidaya ta tashi da sauri ba dan ta so ba ta janyo plate ta soma xuba masa, yasmeen kuwa taji dad'in haka ta tashi ta nufi d'akin ta, Afiya kuwa ta tsare Dr merah da kallon mamaki, hidaya na barin gurin tace

Ban fahimce ka ba dama ka gayawa sultan da auren sa akan hidaya ne,

Ya girgixa kansa yana fad'in meyasa kike wannan tambayar,

Tace saboda me xai ce ta kai masa abinci a d'aki bayan anan ya saba ci beside ma ga yasmeen ita meyasa bai ce ta kaima sa ba.

Kai tsaye aiman yace saboda ya isa da ita, bar mgnr auren su sultan bai da iko akan hidaya ne tana qanwar sa? Tayi shiru tana kallon sa, ki sa masu idanu ba ruwan ki.

Tace aa ba haka muka yi ba, yanxu yarinya tana da wanda take so shima sultan xai nemi dai dai shi.

Waye take so, aiman ya tambaya bayan ya ajiye spoon dake hannun sa.

Qaseem abokin sultan yana ta xarya a gidan nan saboda ita.

Ashe baki da tunani ban sani ba, taya yarinya tana d'auke da igiyar auren d'anki akan ta har kike barin ta saurari wani daban, idan ita bata da masaniya akai ke kuma fa, ashe abinda ake aikatawa a gidannan kenan.

Ban fahimce ka ba mataccen aure kishin me xaa yi akan sa, idan bata saurari wani a yanxu sai yaushe xata yi idan sun dai dai ta kansu yana sakin ta ba sai auren ba sai a had'a dana ameera da fu'ad, salwa da sultan idan ma baya son salwa sai a had'a shi da wata daban.

Yace gaskiya ne, anyi girman banxa, to bari kiji babu wanda ya isa ya raba wannan auren a yanxu koda yaran basa son juna kuwa ki daina wani tunani raba auren a yanxu, idan akwai wacce sultan d'in ke so ya kawo xaa aura masa ko nawa ne amma auren sa da hidaya har abada.

Wannan xance ne kawai kake yi aiman, duka duka sultan d'in shekarar sa nawa da har kake tunanin xaiyi mace biyu a yanxu, haka muka yi da kai, wai meyasa maza baku da alqawari ne.

Ya tashi yana fad'in koma menene kice, banda alqawari saura gobe ki kira ni macuci again, ya ture abincin gabansa ya fice ransa ba dad'i.

Sallama tayi can ciki kamar bata so ta shiga d'akin, kamar baxai amsa ba shima sai can ya amsa yana kallon ta cikin d'aure fuska, aje akan stool kije ki kawo min ruwa, ta ajiye ta juya ta fice ya cigaba da chatting d'in sa.

Bata jima ba ta dawo da gorar Swan a hannun ta, ta ajiye har xata juya taji yana fad'in da baki xan sha ruwan kenan ko kuma ni xanje na d'auko Cup, ta juyo ta d'an dube sa sai kuma ta fice tana bata rai, haka ta dawo ya soma fad'in kin kawo ruwa xallah? ba wani juice haka kika ga ina cin abinci? Ta girgixa kanta kamar xata yi kuka, yayi qaramin tsaki yana maida idanun sa kan wayar sa, nan ma bata jima ba ta dawo tana ajiyewa xata fita ya dawo da ita, da hannu yayi mata alama akan ta xauna qasa ta jira sa har ya gama cin abinci, cikin sanyi jiki ta xauna a takure.

Ya soma cin abincin yana kallon ta, a hakan kike maganar xaki auri fu'ad kula da miji Ma baki iya ba baki san yanda xaki yi ba komai sai an nuna maki,

Kamar baxatayi magana ba kuma sai ta bud'e baki da kyar tace ai kai ba mijina bane shi da yake mijina xan yi masa,

Ya gyad'a kai yana fad'in haka ne, amma ai ni yayan ki ne kuma na isa dake.

Tayi shiru tana tunxuro baki, kallon qaramin bakin nata yake ba qaramin birgeshi take ba idan ta tunxuro shi, he feels like tasting the lips amma ta yaya, ya lumshe idanuwan sa yana cigaba da cin abinci tare da bin ta da idanu yana qare mata kallo.

Shiru shiru ba hidaya ba alamar fitowar ta, Afiya ta kasa nutsuwa ta nufi d'akin merah tana gayamasa hidaya bata fito ba har yanxu tana d'akin.

Tun da kina son kiji dalilin rashin fitowar ta sai kije d'akin kiga menene suke da ya hana fitowar ta tun d'axu, yana gama maganar ya shigewar sa toilet dan gabatar da arwallah.



*littafina na kud'i ne mai so ya tuntubi wannan number 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama:

34

Shiru tayi xuciyar ta ba dad'i amma tabbas xata yi magani wannan abin baxata bari hakan ta faru ba, tayi kwafa tana barin d'akin.

Kusan sau biyu yasmeen tana leqawa falo bata ji motsin fitowar hidaya ba, tace chab yarinyar nan ta raina min wayo tana son yayana take nuna halin ko in kula akan sa, ta soma murmushi.

Ta soma gajiya da xaman da take tace yaya dan Allah ka barni na tafi.

Yayi shiru kafin ya nuna mata wata qatuwar Leda a bedside yana fad'in kije dashi, ta tashi da sauri taje tana duba cikin ledar kafin ta d'ago tana kallon sa.

Tace yaya wannan na waye kuma,
Yace ki bawa hidaya nata tsaraba ne, tayi murmushi tana kallon sa Karo na farko kafin tace nagode ta juya da sauri ta bar d'akin domin taje ta nuna wa yasmeen.

*

Two days....

Tun da ya shigo falon idanun sa ke kanta, Yayi nisa a cikin kallon ta, yana hasashe masu yawa akan ta, yana kallon dogon hancin ta, manyan idanuwanta masu maiko, da d'an qaramin bakin ta tamkar cokali ba ya shiga duka.

Ba wannan ne kad'ai abinda ke d'aukar hankali a halitta hidaya ba, gashin idon ta mai tsayi da gashin girar ta mai taushi baqi kuma siriri, gefen kunnuwanta kuwa duk saje ne mai fallasa cewa akwai yalwantaccen gashi a kanta.

Bai san ya akayi yarinyar ta shiga xuciyar sa haka sosai ba, bai taba soyayya ba bai san menene son ba sai akan ta, a ganin sa tayi qanqanta sosai da ya tsaya yana bayyana mata dimbin soyayyar dake danqare a xuciyarshi yanxu, wannan yar mitsilar yarinya duka tashin yaushe ce, yarinyar da ya tafi ya barta qirji a shafe tayi matuqar bashi mamaki, yanda yake hasashen xai ganta ta xarce fiye da tunanin sa, yaushe xai iya tunkarar ta da soyayya, wane kallo xata yi masa idan taqi amincewa da soyayyar sa shikenan wani raini xai shiga girmansa xai qara xubewa a gurin ta bayan katobarar da yayi a baya.

Haka jikinta ya bata kamar ana kallon ta, d'agowar da xatayi suka had'a ido dashi wanda ya sakata jin kunya, ta kai tafukanta ta rufe fuskarta cikin dariya da jin nauyi yanda take ta xuba loma a gabansa.

Sannan ne yasan cewa 'he is lost ya tafi cikin tunani sosai, yayi saurin d'auke idanun shi akan ta yace kawo min chips da Scottish salad da juice yanxu ya fad'a cikin basarwa kin wani xauna sai jibgar abinci kike,

Ta tashi kamar bata so dan ya takura ta da yawa ita dake cin abinci xai wani saka ta aiki, kitchen ta nufa tana tunxuro baki, idanun sa akan qaramin bakin nata.

Tana dawowa ta ajiye masa komai a gabansa, kamar xai tsaida ta sai ga Afiya ta fito daga d'aki tana kallon su, hidaya ta bar falon da sauri.

Mamee ashe kina ciki ya fad'a yana kallon ta, bata amsa ba ta xauna kusa da shi tana fad'in ina kaje tun d'axu ina neman ka.

Ya shafa sumar kansa yana fad'in, ina tare da friends d'ina.

Tace kana son yin aure yanxu sultan? Kallon ta yayi cikin mamaki da fad'uwar gaba wannan magana tayi masa nauyi da kyar yace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login