Showing 39001 words to 42000 words out of 77337 words

Chapter 14 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

mafarki yanxu, I feel bad, kamar yanda na taso da ita tun ina qarami haka nake son kasancewa da ita har mutuwa ta.

Tace to ni me kake so nayi ma yanxu, ko xanje nema ma tauraruwar ne? Yayi shiru bai san me xai ce ba, dame kuwa xata taimaka masa tunda ba neman tauraruwar xata je yi ba, ba kuma siyo masa ita xata yi ba, maganar fu'ad ta fad'o masa a xuciya (guy ba kome kake so kake nema xaka bada kud'i a baka ba, akwai abubuwa da yawa da kud'in ko isar ka baxai iya siya ma ba) kenan gsky ne da kud'in sa baxai samu tauraruwar sa ta dawo gare sa ba, bayan wannan menene kud'i baxai siya ba?

Ganin yayi shiru ya xurma acikin tunani sai ta shafi gefen kumatunsa, tace wannan ba abin damuwa bane, mafarkin ta da kake da rashin yin sa a yanxu duk daga Allah ne shi kuma kad'ai yasan me yake nufi da hakan.

Yayi murmushi iya labban sa batare da yayi magana ba ya juya ya fice.

*

Da gudu suka shigo cikin falon kamar ko yaushe, suna dariya suna fad'in ni na riga nice first, suka soma jifa da kayan su nan tsakiyar falon, amira da salwa suka nufi d'akin su.

Uniform d'in jikin su suka cire ya rage daga su sai pant, yasmeen ta riqe qugunta tana fad'in yau baxaa min wanka ba bana so.

Hidaya tace idan munje islamiya sai na fad'a bakiyi wanka ba.

Yasmeen tace ai anyi min da safe yanxu kuma bana so.

Ni kuma yau baxan ci abinci ba cewar hidaya tana qoqarin tashi.

Meyasa bakya jin yunwa ne.

Hidaya ta gyad'a kanta batare da tayi magana ba.

Yana shigowa gidan idanun sa a tsakiyar falon, ko ina kaca kaca da kaya, can schoolbag can socks can takalmi duk wani tarkacen su sun xube sa a gurin.

Idan na rumtse idona na bud'e baku kwashe kayan nan kuka dawo yanxu ba duk sai na ji maku, suka juyo suna kallon sa yana tsaye idanunsa a lumshe, ko yaushe ya shigo basu da labari, jiki na rawa suka soma kwashe kayan, kai tsaye d'akin Mariya suka je suka xube kayan suka dawo.

Yaya sultan mun gama, yasmeen ta fad'a tana kallon sa.

Yace daga yau idan na qara ganin kun dawo skul kun shigo mana gida da gudu sai kunyi tsallen kwado na 3hours a gidannan kum... Yayi shiru sakamakon bud'e idanun sa da yayi sai akan qirjin hidaya da babu riga a jikinta, gabansa ya fad'i ya dauke idanunsa da sauri yayi hanyar d'akin sa batare da ya dube su ba.

Fisabilillah yarinya da qirji kamar na maxa a shafe har yayi wannan katobarar, innalillahi ko wane kallo yarinyar take masa a yanxu, ya daki kansa me ya hau kansa haka meyasa bai dawo cikin hayyacin sa ba a lokacin.

Mami hidaya nono insha, ya tuna wannan kalma tabbas ya jita kuma ya gani da wani ne ya gayamasa hakan baxai taba yarda ba, ya ilahi dad'in abin gobe xan bar qasar amma na cuci kaina a wurin wannan yarinya, banda hauka me xan sha anan gurin abinda ko tasowa bai soma yi ba, kenan har su Mami kallon sa suke da wannan abin=?D?

Ya soma tattara duk abinda yasan xai buqata yana had'awa, kome ya tuna sai gabansa ya fad'i ya tashi da sauri yana dubawa babu sa babu alamar sa, tabbas tunda ya sami sauqi bai ga abin ba, ya fita d'akin da sauri kai tsaye d'akin aiman ya nufa, yana ganin sa ya kauda kansa gefe yana fad'in wannan yaron ya sake dawowa again ko dame yaxo yanxu.

Daddy xobe na, bangan shi ba, Aiman ya tsura masa ido kafin yace nima ban ganshi ba ban taba lura baya hannun ka ba.

Ya ilahi kamar ya rusa kuka saboda baqin ciki, but why daddy wai taya xaa kawo ni baku binciki komai akai na ba.

Aiman yace ta lafiyar ka xamu bi ko xamu tsaya neman dukiya ne, an xo da kai baka numfashi taya kake tunanin wani xobe ko waya xai xo mana a lokacin.

Sultan yayi shiru duk wani farinciki daya ke ji yau ya neme sa ya rasa dalilin wannan xoben, meyasa komai ke subulce masa a yanxu, meyasa damuwa da baqin ciki suke son xama abokan sa a yanxu, damn nigeria, ya tsani wannan qasar fiye da xaton mai karatu, qasar da tunda ya sako qafa a cikinta qaddarori da bala'i ke samun sa, dalilin wannan qasar ya soma rashin tauraruwar sa, yayi abinda baxai taba yafewa kansa ba, laifin da har yau baisan hanyar da xai bi ya gyara kuskuren sa ba, ina ma xai ganta, dalilin wannan qasar ya shiga halin da baya farin ciki da kasancewa acikin sa xama da qananan yara har su san girman sa, yau gashi ya rasa wannan abu mai matuqar muhimmanci a rayuwar sa duk acikin wannan qasar, ya juya ya fice kamar ya tashi sama saboda baqin ciki babu abinda xai saka shi qara dawowa qasar a yanxu.

Aiman ya bisa da kallo sanin babban rashin da sultan d'in yayi na wannan xoben, xobe da aka jima ana had'a miliyoyin kud'i kafin ayi masa shi, yau babu shi, waye ya d'auki wannan xoben a ina xasu same sa duk bai sani ba a yanxu amma tabbas yana da yaqinin sultan kawai keda irin xoben a yanxu kasancewar sunan sa da nasa aka rubuta acikin xoben (SAM).

*

Gobe sultan xai tafi amma ban qara jin ka tada wannan maganar ta raba auren sa da hidaya ba.

Auren da aka riga aka qullashi akan gsky baxaa raba shi ba, idan biki ne kike mawa xan ware kud'i masu yawa kuyi shagalin da duk kuke so.

Wani kallo tayi masa tana tashi daga jikinsa, me kake nufi ban fahimce ka ba.

Yace abinda kunnuwan gimbiya suka jiyo mata, ni na rasa har yau dalilin daya sa kike son raba auren.

Saboda basu dace ba, rayuwar su ba d'aya ba hidaya tana da kirki, yarinyace da tasan kanta tasan rayuwa, tana d'auka da ganin kowa a matsayin nata, bata da rayuwa mai mugunta, tana da haquri da kau da kai akan komai sabanin sultan kafi kowa sanin waye shi.

Yace yauwa kika sani ko sanadiyar ta, ta canxa maki yaro idan bai xauna da irin hidaya ba so kike ya xauna da mai hali irin nasa.

Tace sultan baxai xauna da macen da bata da BUDURCI ba, baxaa ma yarona auren dole ba, mace shi xai xabawa kansa ya aura ko yar gidan waye a qasar nan amma baxan had'a xuria da wacce har yau bamu san asalin ta ba.

Aiman yace wlhy kaf halin ki sultan ya d'auka, wannan aqidar ta sultan naqin kasar sa da kyamatar talakawa a gurin ki ya same ta, wannan itace tarbiyar da kike ikirarin kin bashi, menene budurci, menene acikin budurci samun mace kamila natsatsiya mai hankali shi yafi soyuwa akan auren ballagaxar mace mai budurci, baki buri yaron ki yayi aure a gidan mutunci sai gidan masu kud'i, akawo yarinyar da baxata girmama ki ba ballantana d'anki da take aure tana ganin itama ai yar mai kud'in ce tana da ikon yin komai ba wanda ya isa ya hana ta, inace hidaya ba maxa take bi ba fyade aka mata, ko tana da laifi acikin wannan abun ki gayamin yanxu.

Wannan hasashen ka ne yarima, ya'yan masu kud'i nawa aka aura aka xauna dasu lafiya, tell me ni gidan talakawa ka d'auko ni ko kuma yaya Aliyu dake auren qanwar ka gidan talakawa ya d'auko rumaisa, baka da wata sauran kalma da xaka kare kanka da ita a yanxu, inaji yarjejeniya muka yi da kai kuma ka amince meyasa kake son maida kanka cikin sahun masu alqawari suna karyawa.

Ya sauko daga saman gadon cikin fuskar rarrashi sanin halin kayan sa idan ta birkice ba wanda ya isa ya sauko da ita, oh Afiya.

Yace ki yarda dani xan raba wannan auren amma ba yanxu ba sai sultan ya dawo dalili mutanen da suka san an d'aura auren wane kallo kike so suyi ma sultan, yaro d'an shekara ashirin kacal a duniya yasan ya auri mace ya sake ta, sultan xai rabu da hidaya I promise you ko yana so ko baya so balle nasan baxai taba son ta ba shima yar gidan mai kud'i xai aura akashe masa naira da daloli a shagalin bikin jikan sarki da tsohon shugaban qasa.

Batare da ya bari tayi magana ba yaja hannunta yana fad'in xo muje muyi wanka jikina ba dad'i uwar gida sarautar mata, gimbiya shalelen Aiman Mera.

Washe garin ranar kaf mutanen gidan sun fito harabar gidan yin sallama da sultan sai shagwaba yake ta xubawa kakannin nasa kamar kar yaje.

Masu xuwa raka shi airport duk sun shiga motar amma banda hidaya tana tsaye abunta tana kallon wani gu daban.

Hidaya kixo ki shiga mota xamu tafi, yasmeen ta fad'a da qarfi.

Sauran basu lura bata cikin motar ba sai yanxu, sultan yayi mamaki me yarinyar take nufi.

Hidaya ta girgixa kanta batare da tayi magana ba ta juya cikin gida.

Bai san dalili ba amma baiji dad'in haka ba, yana ji mera na fad'in a kyale ta tun da babu dole ga xuwa rakiyar wanda bai san muhimmanci ta ba, ya san magana ya gaya masa sai bai damu ba ya cigaba da abinda yake yi batare da ya qara bi ta kanta ba.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=؞?

29

Aiman ya tsura mata idanu, yana observing yanayin ta, kwata kwata ta canxa a yanxu ba kamar da ba, meke damun yarinyar?

Yace xo nan hidaya, xo naji waye ya tabamin ke a gidannan, waye ke saka ki kuka haka, ko waye shi tabbas xan bata masa rai.

Kamar baxata je ba amma daga yanayin kalamansa taji sanyi a ranta ta yarda baxai dake ta ba tunda tayi ta talatin, ta fito tana tafiya a hankali cikin tsoro kamar wadda kwai ya fashewa a jiki.

Aiman ya riqo ta ya xaunar da ita kusa dashi yana kallon ta,

Yace ki share hawayen bana son kukan, da sauri ta saka bayan hannun ta tana sharewa bayan ta cire glass na idon ta.

Wancan karon ta nawa kika d'auka? Ya tambayeta yana tsare ta da idanuwan sa masu rikita d'an adam.

Muryar ta na rawa tace na goma sha shidda.

Yace hakan na nufin kina da damuwa a yanxu wadda ban sani ba, naga canji sosai a tare dake hidaya, tell me menene matsalar ya fad'a yana riqo duka hannayen ta cikin kulawa.

Tace babu komai.
Yace akwai tell me, ko su amira su fita xaki fad'a min, ta gyad'a kai da sauri, ya dube su tare da masu alamar su fice, ba dan sun so ba suka fita dai dai lokacin Afiya ta shigo falon ta xauna tana kallon su.

Yace gayamin meyasa result naki yake haka, meyasa bakya karatu, bakya maida hankalin ki kamar farkon wancan xangon, ko kin fiso nayi ta kashe maqudan kud'i na akan school fees suna tafiya a banxa.

Ta girgixa kanta tana goge hawaye sosai.

Yace to gayamin naji damuwar ki, cikin rawar murya tace ya.. ya sultan sai kuma ta fashe da kuka.

Sultan ne damuwar ki hidaya, ta gyad'a kai tana share hawayen ta.

Yace to ai kinga sultan ya tafi baxai qara takura ki ko ya dake ki ba, ga yasmeen kiyi wasa da ita ba shikenan ba.

Ta girgixa kanta tana fad'in ni kace ya dawo muyi wasa baxan qara ture sa ba.

Aiman yaja numfashi yanxu ya fahimci inda ta dosa, ba tana kuka saboda sultan yana hantarar ta bane ya gane damuwar ta saboda rashin sultan d'in ne, sosai ta bashi tausayi ba qaramin sabo tayi dashi ba dole ta damu.

Yace sultan ya tafi karatu hidaya, baxai dawo yanxu ba, amma idan kina so na kaiki gurin sa ku cigaba da wasa tabbas sai kin dage kina karatu sosai yanda idan sultan ya ga result naki xai ji dad'i yayi farin ciki yace hidaya kinyi qoqari xo muyi wasa, muci abinci kuma muyi wanka tare, idan kuma kika qi karatu sultan ya ga result naki baxai ji dad'i ba fushi xai yi yaqi wasa dake qila ma yace kada a xo mashi dake.

Tace daddy shi kuma baffa sai yaushe xai dawo, shi meyasa baxaka kaini gurin sa ba shima.

Yace idan kin dage kinyi karatu shima da kaina xan kaiki gurin sa.

Sai tayi murmushi tana jinjina kanta.

Tun daga ranar da aka koma makaranta hidaya bata qara saka wasa a ranta ba, bata da wannan lokacin a yanxu, karatu take sosai akan abinda aka koyar dasu class idan sun dawo gida, wanda bata gane ba sai ta ajiye sai lesson teacher nasu yaxo ta nuna masa ya qara koya mata.

Sai ta xama wata irin yarinya da bata da lokacin kanta da komai sai nata da karatu, babu ruwan ta da kowa a gidan, idan kaji dariyar ta tabbas da yasmeen kawai.

Sakamakon jarabawa na fitowa sai gata da 3rd position yasmeen tayi na d'aya, mera ba qaramin farin ciki da hakan yayi ba, yayi masu kyauta babba irin wadda suke so.

Babu xancen sultan yanxu a xuciyar hidaya, tuni ta manta da shi da duk wani abu daya shafe shi, idan har ta tuna sa sai idan an d'auko xancen sa ko kuma ana waya dashi, duk yanda ya bugo waya ya gaisa da kowa baxata karba ba, juyin duniya Afiya xata yi amma taqi karba.

Hidaya mutum ce mai kafiya da riqo, duk yanda kaso tayi abu idan bata so ba baxata taba yin sa ba, ta wani bangaren tana da sanyi sosai da haquri dan bata da fad'a kamar yasmeen da kusan kullum sai tayi fad'a a class ko idan an tashi school, gata da wani irin qarfi dan tafi hidaya qarfi, da wuya kaga tayi fad'a an mata duka, duk xasu yi fad'a hidaya ce mai riqa mata kayanta kafin axo d'aukar su ake fad'an idan anxo d'aukar su washe gari tana shigowa xata tayar da fitinar baxata yarda ba sai anyi fad'an jiya, Allah ya shirya yasmeen cewar Afiya a ko yaushe idan hidaya taxo ta gayamata tayi fad'a a school.

Wasa wasa hidaya da fu'ad ba qaramin sabo suka yi ba, ko yaushe yaxo gidan suna tare, yana debe mata kewa sosai ita da yasmeen yana kulawa da ita, har tana ganin yafi sultan kirki nesa ba kusa ba, tana jin dad'in kasancewa dashi.

Mutum ne mai kyakkyawar xuciya da kirki na gasken gaske, tare da biyewa quruciyar ta batare da hantara ko tsangwama ba, duk abinda taxo dashi yakan duba mata idan tayi ba dai dai ya gyara mata.

*

A rayuwar sultan bai taba damuwa da wani abu , bayan iyayen sa, karatun sa da kuma wasan kwallon sa ba kamar yanda ya damu da hidaya a yanzu.

Ya kasa samun nutsuwar xuciyar sa a yanxu, bashi da aiki sai na tunanin ta, idan ya rumtse idanuwan sa ita yake hangowa, mafarkin sa duk akan suna wasa ko wanka tare, wannan halin ko in kula da take nuna wa a yanxu idan ya kira waya taki karba ya dame sa, yana son jin muryarta ko yaya ne, gashi mafarkin tauraruwar sa ya dawo masa a yanxu.

Ya rasa tunanin sa akan qanqanuwar yarinyar da bata fara sanin kanta ba, yarinyar da tasha fama dashi lokacin da yake cikin lalura, ta sadaukar da farin cikin ta domin ta bashi farin ciki a tasa rayuwar, ko meyasa ya damu da yarinyar a yanxu?

Bata da wani abu attractive da xai d'auki hankalin wani d'a namiji ta fannin sura yarinyace sharkaf, balle yace wani abu na jikinta ya jawo hankalinsa gare ta,

Ya lumshe idanun sa yana shafa sumar kansa a hankali, meyasa ya damu da hidaya fiye da kowa da komai a duniya?meyasa yake qalubantar xuciyarsa kullum akan ta?yana referring ko wanne motion na xuciyarsa? akan ta da soyayya, ya d'auki duk wani motsin da xuciyar sa da gangar jikin sa keyi akan ta da cewa yana sonta, he can feel the feelings a yanxu, tabbas yana SON HIDAYA.

*idan baka biya ba kada ka karanta, idan kana so kayi magana, 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=؞?

28

Hidaya meyasa kika xauna baki je airport mun raka yaya sultan ba, yasmeen ta fad'a tana kallon ta.

Hidaya ta dauke kanta gefe had'e da tunxuro baki, bana son ina ganin sa.

Yasmeen tace ai yanxu ma ya tafiyar shi shikenan munji dad'i mu riqa wasar mu.

Hidaya ta gyad'a kai tana murmushi.

*

Tun tafiyar sultan sai ta xama wata irin sukuku ba kuxari, ta saba da sultan, matuqar sabo kuwa.

Idan ta tuna yanda suke wasa, suke cin abinci tare, kwanciya tare, guje gujen da suke yi da kuma canxawar da yayi mata na lokaci d'aya wanda tana d'aukar hakan a matsayin fushi ne yake da ita mai tsanani tun lokacin da ta ture sa daga gado.

Ya shiga ranta fiye da tunanin mai karatu, yau sati d'aya da tafiyar sa amma har yau kewar shi ba ta sake ta ba, walwala ta ragu, farin cikinta ya taqaita.

Wannan hidaya ta yanxu ba waccan hidayar da kuka sani mai surutu bace, mai kaxar kaxar da son wasa, wadda da wuya kaga fushi akan fuskarta sabanin farin ciki, wannan hidayar ta xama ma'abociyar tunani da rashin walwala ko yaushe, yaushe baffan ta xai dawo ya d'auke ta daga gidan nan gabaki d'aya ta huta, yaushe baffa xai dawo ya xama abokin wasar ta na koda yaushe kamar daga farko babu kyama da hantara, babu fushi ko tsawa kome xata yi masa kuwa.

Ta goge wasu hawaye dake sintiri a kumatun ta, ta tuna wani lokaci sun fito xasu je School suna qoqarin shiga mota sai ga sultan shima yaxo shiga mota.

Amira tace yaya sultan ina xaka je School fa xamu je, yasmeen taje ta riqa hannunsa tana fad'in baxa muje da kai School ba kayi girma babu mai irin girman ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login